TALIFIN NAZARI NA 12
WAƘA TA 77 Haske a Duniya Mai Duhu
Mu Kiyayi Duhu Kuma Mu Yi Zaman Mutanen Haske
“Dā kuna a duhu, amma a yanzu, kun sami haske.”—AFIS. 5:8.
ABIN DA ZA MU KOYA
Za mu koyi darussa daga abin da littafin Afisawa sura 5 ta ce game da haske da kuma duhu.
1-2. (a) A wane yanayi ne Bulus yake ciki lokacin da ya rubuta wasiƙarsa ga ꞌyanꞌuwan da ke Afisa, kuma me ya sa ya rubuta wasiƙar? (b) Waɗanne tambayoyi ne za mu nemi amsoshinsu?
A LOKACIN da aka kulle manzo Bulus a wani gida a Roma, ya so ya ƙarfafa ꞌyanꞌuwansa masu bi. Amma da yake ba zai iya zuwa ya gan su ba, sai ya tura musu wasiƙu. A wajen shekara ta 60 ko 61 bayan haihuwar Yesu ne ya rubuta ɗaya daga cikin wasiƙun nan zuwa ga ꞌyanꞌuwan da ke Afisa.—Afis. 1:1; 4:1.
2 Wajen shekaru goma kafin wannan lokacin, Bulus ya ɗauki lokaci sosai yana waꞌazi a Afisa. (A. M. 19:1, 8-10; 20:20, 21) Bulus yana ƙaunar ꞌyanꞌuwan da ke Afisa sosai, kuma yana so ya taimaka musu su riƙe amincinsu ga Jehobah. Amma, me ya sa ya yi ma waɗannan shafaffun Kiristoci zancen haske da kuma duhu? Kuma mene ne dukanmu za mu iya koya daga gargaɗin da ya ba su? Bari mu bincika amsoshin tambayoyin nan.
DAGA DUHU ZUWA HASKE
3. Wane kwatanci ne Bulus ya yi amfani da shi a wasiƙarsa ga Afisawan?
3 Bulus ya gaya wa Kiristocin da ke Afisa cewa: “Dā kuna a duhu, amma a yanzu, kun sami haske.” (Afis. 5:8) Bulus ya yi amfani da kwatancin haske da duhu ne don ya nuna abubuwa biyu da suka sha bamban. Bari mu ga abin da ya sa Bulus ya ce, a dā Afisawan ‘suna a duhu.’
4. Me ya sa za mu ce, a dā ꞌyanꞌuwan da ke Afisa suna cikin duhu?
4 Suna a duhu don suna bin addinin ƙarya. Kafin ꞌyanꞌuwan da ke Afisa su zama Kiristoci, sun gaskata da ayyukan sihiri kuma suna bin koyarwar addinin ƙarya. Ƙari ga haka, a birnin Afisa ne ake da babban haikalin alliyar nan mai suna Artemis, kuma mutane da yawa a lokacin suna ganin wannan ginin yana cikin manyan gine-ginen duniya da babu irinsu. Bautar gumaka ce zalla ake yi a haikalin. Akwai mutane da yawa da sanaꞌarsu ita ce ƙera siffofin alliyar nan Artemis suna sayarwa, kuma suna samun kuɗi sosai. (A. M. 19:23-27) Ban da haka ma, mutanen birnin suna tsafi ba kaɗan ba.—A. M. 19:19.
5. Mene ne kuma ya nuna cewa a dā Afisawan suna cikin duhu?
5 Suna a duhu don suna yin lalata. An san mutanen Afisa da yin lalata da kuma iskanci. Yawancin wasanni da bukukuwan addini da ake yi a manyan wuraren wasa da ke birnin, game da jimaꞌi ne. (Afis. 5:3) Yawancin mutanen garin, akwai su da “rashin kunya” wato, suna yin abubuwa marasa kyau kuma zuciyarsu ba ta damun su. (Afis. 4:17-19) Kafin ꞌyanꞌuwan nan da ke Afisa su koyi gaskiya kuma su san abin da ya dace da wanda bai dace ba, suna yin abubuwa marasa kyau kuma zuciyarsu ba ta damun su. Ƙari ga haka, ba sa tunanin cewa Allah zai shariꞌanta su. Shi ya sa manzo Bulus ya ce, “Zuciyarsu cike da duhu take. An raba su kuma da rai wanda Allah yake bayarwa.”
6. Me ya sa Manzo Bulus ya ce ꞌyanꞌuwan da ke Afisa sun “sami haske”?
6 Amma, wasu mutanen Afisa ba su ci-gaba da kasancewa cikin duhu ba. Manzo Bulus ya ce, sun “sami haske ta wurin Ubangiji.” (Afis. 5:8) Yanzu sun koyi gaskiyar da ke Kalmar Allah kuma suna bin ta, ta zama musu haske. (Zab. 119:105) ꞌYanꞌuwan nan da ke Afisa sun daina bin koyarwar addinin ƙarya da yin lalata. Yanzu sun zama masu yin koyi da Allah kuma suna iya ƙoƙarinsu su bauta masa kuma su faranta masa rai.—Afis. 5:1.
7. Ta yaya muka yi kama da Kiristocin da ke Afisa?
7 Kafin mu san gaskiya, mu ma a cikin duhu muke a batun addini da kuma lalata. Wasunmu mun yi bukukuwan addinan ƙarya da kuma lalata. Amma, da muka fahimci ƙaꞌidodin Jehobah, sai muka canja rayuwarmu kuma muka soma yin rayuwa yadda za ta gamshe shi. Matakin nan da muka ɗauka ya amfane mu sosai. (Isha. 48:17) Amma da sauran aiki. Muna bukatar mu ci-gaba da kiyaye kanmu daga wannan duhun da muka bari kuma mu yi “zaman mutanen haske.” Ta yaya za mu yi hakan?
KA KIYAYI DUHU
8. Bisa ga Afisawa 5:3-5, mene ne Kiristocin da ke Afisa suke bukatar su kiyaye?
8 Karanta Afisawa 5:3-5. Idan Kiristocin nan da ke Afisa suna so su kiyayi duhu gabaki ɗaya, suna bukatar su ci-gaba da ƙin abubuwan da Jehobah ba ya so. Wato, su guji ayyukan lalata da kuma maganganun batsa. Manzo Bulus ya tuna ma Afisawan cewa dole ne su kiyayi irin abubuwan nan idan suna so su samu “rabon gādo a mulkin Almasihu da Allah.”
9. Me ya sa muke bukatar mu kiyayi abubuwan da za su iya kai mu ga yin lalata?
9 Mu ma dole mu ci-gaba da yin hattara don kada mu shiga yin “ayyukan duhu marasa amfani.” (Afis. 5:11) Abin da ya faru da mutane da yawa ya nuna cewa da gaske, idan mutum yana kallo ko yana sauraron abubuwan lalata, ko yana yin maganganun batsa, ba zai yi wa mutumin wuya ya shiga yin abubuwan da ba su dace ba. (Far. 3:6; Yak. 1:14, 15) Abin da ya faru ke nan a wata ƙasa. Wasu ꞌyanꞌuwa da yawa sun soma yin hira da juna a dandalin sada zumunta. Da suka fara wannan tarayyar abubuwan ibada ne suke magana a kai. Amma a-kwana-a-tashi, sai suka soma yin zancen abubuwa marasa kyau har sun shiga yin zancen jimaꞌi. Ƙarshenta, da yawa daga cikin ꞌyanꞌuwan nan sun ce maganganun iskanci da suka yi sun kai su ga yin lalata.
10. Ta yaya Shaiɗan yake ƙoƙari ya ruɗe mu? (Afisawa 5:6)
10 Mutanen duniyar nan da ke hannun Shaiɗan, suna ƙoƙari su ruɗar da mu don mu ga kamar abubuwan da Jehobah ya ce ba su da kyau ba laifi ba ne. (2 Bit. 2:19) Wannan ba abin mamaki ba ne domin Shaiɗan ya daɗe yana rikitar da mutane don kar su iya gane bambancin da ke tsakanin abu mai kyau da marar kyau. (Isha. 5:20; 2 Kor. 4:4) Shi ya sa da yawa daga cikin fina-finai, da shirye-shiryen talabijin, da kuma dandalin intane da ake da su a yau, suna ɗaukaka abubuwan da Jehobah ya ce ba su da kyau. Ƙoƙarin Shaiɗan shi ne ya ruɗe mu mu ga kamar yin abubuwa marasa kyau da yin rayuwar lalata bai da wani illa, cewa abu ne ma mai kyau kuma jin daɗi ne.—Karanta Afisawa 5:6.
11. Ta yaya labarin Angela ya nuna cewa bin shawarar da ke Afisawa 5:7 yana da amfani sosai? (Ka kuma duba hoton.)
11 Shaiɗan yana so mu yi abokantaka da mutanen da za su sa ya yi mana wuya mu bi ƙaꞌidodin Jehobah. Shi ya sa manzo Bulus ya gargaɗi Afisawan cewa: “Kada ku haɗa kai da su,” wato waɗanda suke yin abubuwan da Allah ya haramta. (Afis. 5:7) Ya kamata mu fi ꞌyanꞌuwan nan da suke Afisa yin hattara, domin a yau za mu iya yin abokantaka da mutane ta dandalin sada zumunta ba sai muna tare da su a zahiri ba. Wata ꞌyarꞌuwa mai suna Angela a da take zama a Asiya, ta ga irin haɗari da ke tattare da dandalin sada zumunta. Ta ce: “Da sannu-sannu dandalin sada zumunta zai iya canja tunaninka. Na soma gani kamar yin abokantaka da waɗanda ba su damu da ƙaꞌidodin Jehobah ba, ba wani abu ba ne. Ƙarshenta, na soma ɗauka cewa yin abubuwan da Jehobah ba ya so ba laifi ba ne.” Godiya ga Allah, wasu dattawa sun taimaka wa Angela don suna ƙaunar ta. Angela ta ce: “Yanzu, maimakon in duƙufa amfani da dandalin sada zumunta, ayyukan ibada ne nake cika zuciyata da su.”
12. Me zai taimaka mana mu ci-gaba da bin ƙaꞌidodin Jehobah?
12 Ya kamata mu yi hattara don kar mu yi irin tunanin mutanen duniyar nan, cewa yin lalata ba laifi ba ne. Don mun san cewa zunubi ne babba. (Afis. 4:19, 20) Zai dace kowannenmu ya tambayi kansa cewa: ‘Ina guje wa yin abokantaka da waɗanda muke aiki tare, ko ꞌyan ajinmu, ko duk wani mutum da ba ya bin ƙaꞌidodin Jehobah? Nakan tsaya kafa biyu kuma in yi abin da Jehobah yake so ko da mutane za su ce na cika nacewa a kan abin da ba kome ba ne?’ Kuma kamar yadda 2 Timoti 2:20-22 sun ce, muna bukatar mu yi hankali saꞌad da muke zaɓan waɗanda za mu yi abokantaka da su ko a cikin Ikilisiya. Mu tuna cewa akwai wasu a ikilisiya da ba za su taimaka mana mu riƙe amincinmu ba.
MU “YI ZAMAN MUTANEN HASKE”
13. Idan aka ce mu “yi zaman mutanen haske,” me ake nufi? (Afisawa 5:7-9)
13 Bayan da manzo Bulus ya gargaɗi Kiristocin da suke Afisa cewa su kiyayi ayyukan duhu, ya kuma ce musu su “yi zaman mutanen haske.” (Karanta Afisawa 5:7-9.) Me hakan yake nufi? Yana nufin cewa a koyaushe, halinmu ya nuna cewa mu Kiristoci na gaskiya ne. Wani abin da zai taimaka mana mu yi hakan shi ne, mu sa ƙwazo wajen karanta Littafi Mai Tsarki da littattafanmu da yin nazarin su. Kuma yayin da muke yin hakan, zai dace mu mai da hankali sosai ga misalin Yesu da kuma koyarwarsa, domin shi ne “hasken duniya.”—Yoh. 8:12; K. Mag. 6:23.
14. Wane taimako ne ruhu mai tsarki zai iya yi mana?
14 Wani abin da muke bukata kuma don mu ci-gaba da yin “zaman mutanen haske,” shi ne ruhu mai tsarki. Me ya sa? Domin yin rayuwa mai tsarki a wannan duniyar da ke cike da halin lalata, bai da sauƙi ko kaɗan. (1 Tas. 4:3-5, 7, 8) Ruhu mai tsarki zai iya taimaka mana mu kauce ma irin tunanin mutanen da ke duniyar nan, waɗanda raꞌayinsu dabam yake da na Allah. Ruhu mai tsarki zai kuma taimaka mana mu dinga yin “ayyuka masu kyau, da zaman adalci.”—Afis. 5:9.
15. Ta yaya za mu samu ruhu mai tsarki? (Afisawa 5:19, 20)
15 Wani abin da za mu iya yi don mu sami ruhu mai tsarki shi ne, mu roƙi Allah cewa ya ba mu ruhunsa. Yesu ya ce Jehobah ‘zai ba da ruhu mai tsarki ga masu roƙonsa.’ (Luk. 11:13) Ƙari ga haka, idan muna yabon Jehobah tare da ꞌyanꞌuwanmu a taro, Jehobah zai ba mu ruhunsa. (Karanta Afisawa 5:19, 20.) Idan muna da ruhu mai tsarki, zai taimaka mana mu riƙa yin abin da Allah yake so.
16. Me zai taimaka mana mu dinga tsai da shawara mai kyau? (Afisawa 5:10, 17)
16 Idan muna so mu tsai da shawara mai muhimmanci, muna bukatar mu fahimci mene ne “nufin Ubangiji,” kuma mu bi shi. (Karanta Afisawa 5:10, 17.) Idan muna neman ƙaꞌidodin Littafi Mai Tsarki da suka dace da yanayin da muke ciki, muna neman sanin raꞌayin Jehobah game da batun ke nan. Kuma idan muka gano ƙaꞌidodin Jehobah kuma muka bi su, za mu iya yin zaɓi mai kyau.
17. Ta yaya za mu nuna cewa muna amfani da lokacinmu da kyau? (Afisawa 5:15, 16) (Ka kuma duba hoton.)
17 Bulus ya kuma gargaɗi Afisawan cewa su yi amfani da lokacinsu da kyau. (Karanta Afisawa 5:15, 16. b) “Mugun nan,” wato maƙiyinmu Shaiɗan, zai so ya cika mu da ayyuka da yawa har ma mu rasa lokacin bauta ma Jehobah. (1 Yoh. 5:19) Kirista zai iya sa neman abin duniya, ko makaranta, ko kuma aikin da yake yi, ya zama farko a rayuwarsa, maimakon ya nemi hanyoyin da zai bauta ma Jehobah. Idan ya yi hakan, ya nuna cewa ya soma bin tunanin mutanen duniyar nan ke nan. Hakika, biɗan abubuwan nan ba laifi ba ne. Amma bai kamata a ce su ne muka sa a kan-gaba ba. Idan muna so mu “yi zaman mutanen haske,” muna bukatar mu ‘yi amfani da lokacinmu da kyau,’ wato mu mai da hankali ga abin da ya fi muhimmanci.
18. Waɗanne matakai ne Donald ya ɗauka don ya yi amfani da lokacinsa da kyau?
18 Ka riƙa neman hanyoyi da za ka ƙara ƙwazo a hidimarka ga Jehobah. Abin da wani ɗanꞌuwa mai suna Donald da ke ƙasar Afrika ta Kudu ya yi ke nan. Ɗanꞌuwan ya ce: “Da na dubi rayuwata, sai na roƙi Jehobah ya taimaka min in inganta yadda nake waꞌazi. Na roƙe shi ya taimake ni in samu aikin da zai ba ni lokacin yin waꞌazi. Kuma da taimakon Jehobah na samu irin aikin da nake so. Sai ni da matata muka soma yin hidima ta cikakken lokaci.”
19. Me zai taimaka mana mu ci-gaba da yin “zaman mutanen haske”?
19 Babu shakka wasiƙar da Bulus ya rubuta wa Afisawan ta taimaka musu su ci-gaba da bauta wa Jehobah da aminci. Kuma wannan gargaɗi da Jehobah ya sa Bulus ya rubuta, za ta amfane mu a yau. Kamar yadda muka gani, zai taimaka mana mu iya zaɓan irin nishaɗin da za mu yi da irin abota da za mu ƙulla. Zai kuma taimaka mana mu ci-gaba da yin nazarin Littafi Mai Tsarki a-kai-a-kai domin hasken da ke Kalmar Allah ta ja-goranci rayuwarmu. Ya kuma nuna cewa muna bukatar ruhu mai tsarki sosai don ya taimaka mana mu zama masu halin kirki. Idan muna bin gargaɗin nan da Bulus ya rubuta, hakan zai sa mu iya tsai da shawarwari masu kyau, wato waɗanda suka jitu da raꞌayin Jehobah. Ta hakan, za mu kiyayi duhun da ke duniyar nan kuma mu ci-gaba da yin zaman mutanen haske.
MECE CE AMSARKA?
-
Wane irin “duhu” da kuma “haske” ne aka yi maganarsu a littafin Afisawa 5:8?
-
Ta yaya za mu kiyayi “duhu”?
-
Ta yaya za mu ci-gaba da yin “zaman mutanen haske”?
WAƘA TA 95 Muna Samun Ƙarin Haske
a An canja sunayen.
b Afisawa 5:15, 16 (NWT): “Saboda haka sai ku mai da hankali ƙwarai ga zamanku. Kada ku zama kamar wawaye, amma ku zama masu hikima. 16 Ku yi amfani da lokacinku da kyau, domin muna a miyagun kwanaki.”
c BAYANI A KAN HOTO: Hoton ya nuna wasiƙar da manzo Bulus ya rubuta wa ꞌyanꞌuwa da suke Afisa.