Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 21

Abin da Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna Ya Ce Zai Faru da Kai a Nan Gaba

Abin da Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna Ya Ce Zai Faru da Kai a Nan Gaba

“Amin. Zo, Ubangiji Yesu!”​—R. YAR. 22:20.

WAƘA TA 142 Mu Jimre, Aljanna Ta Kusa

ABIN DA ZA A TATTAUNA *

1. Wane zaɓi mai muhimmanci ne dukan ’yan Adam suke bukata su yi?

 A YAU, mutane suna da zaɓi mai muhimmanci da suke bukatar su yi. Za su goyi bayan Jehobah wanda shi ne yake da ikon yin sarauta a sama da ƙasa, ko kuma za su goyi bayan babban maƙiyinsa Shaiɗan Iblis? Dole ne kowa ya yi zaɓi kuma zaɓin zai shafi rayuwarsa har abada. (Mat. 25:​31-33, 46) A lokacin ‘azaba mai zafi’ ko kuma ƙunci mai girma, za a saka musu lambar shaida a matsayin waɗanda za a hallaka ko kuma za su tsira.​—R. Yar. 7:14; 14:​9-11; Ezek. 9:​4, 6.

2. (a) Mene ne Ibraniyawa 10:​35-39 suka ƙarfafa mu mu yi? (b) Ta yaya Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna za ta iya taimaka mana?

2 Karanta Ibraniyawa 10:​35-39. Idan ka riga ka zaɓi ka goyi bayan Mulkin Jehobah, ka yanke shawarar da ta dace. Yanzu kana a shirye ka taimaka ma wasu ma su yi zaɓi mai kyau. Don haka, za ka iya yin amfani da abin da ke Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna ka taimaka musu. Littafin ya bayyana abin da zai faru da waɗanda suka ƙi goyon bayan Mulkin Jehobah, kuma ya bayyana yadda Jehobah zai yi ma waɗanda suka goyi bayan Mulkinsa albarka. Yana da kyau mu yi nazarin waɗannan abubuwan. Yin hakan zai ƙarfafa mu mu ci gaba da bauta wa Jehobah. Ƙari ga haka, za mu iya yin amfani da abubuwan da muka koya don mu taimaka wa mutane su yi zaɓin da ya dace kuma su tsaya a kan shi.

3. Mene ne za mu tattauna a wannan talifin?

3 A wannan talifin, za mu tattauna tambayoyin nan: Wace albarka ce waɗanda suka goyi bayan Mulkin Allah za su samu? Amma mene ne zai faru da waɗanda suke goyon bayan jar dabbar nan da aka ambata a littafin Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna?

MENE NE ZAI FARU DA MASU AMINCI?

4. Wane rukuni ne manzo Yohanna ya gani tare da Yesu a sama?

4 A wahayi, Yohanna ya ga rukunoni biyu da suke goyon bayan Mulkin Jehobah, kuma suka sami rai na har abada. A rukuni na farko akwai mutane 144,000. (R. Yar. 7:4) An ɗauke su daga duniya kuma aka kai su sama don su yi sarauta tare da Yesu bisa duniya. (R. Yar. 5:​9, 10; 14:​3, 4) A wahayin, Yohanna ya gan su suna tsaye tare da Yesu a kan Tudun Sihiyona da ke sama.​—R. Yar. 14:1.

5. Mene ne zai faru da shafaffu da suka rage a duniya nan ba da daɗewa ba?

5 Daga zamanin manzanni har zuwa zamaninmu, an zaɓi dubban mutane su kasance cikin mutane 144,000 ɗin. (Luk. 12:32; Rom. 8:17) Amma an gaya wa Yohanna cewa kaɗan daga cikinsu ne za su kasance a raye a kwanaki na ƙarshe. Kuma za a saka musu “hatimi” a goshinsu kafin ƙunci mai girma ya soma don a nuna cewa Jehobah ya amince da su. (R. Yar. 7:​2, 3; 12:17) Jim kaɗan bayan an soma ƙunci mai girma, za a ɗauke shafaffu da suka rage zuwa sama don su kasance tare da sauran shafaffu 144,000 da suka riga suka mutu da aminci. Za su yi sarauta tare da Yesu a Mulkin Allah.​—Mat. 24:31; R. Yar. 5:​9, 10.

6-7. (a) Wane rukuni ne kuma Yohanna ya gani, kuma me aka gaya mana game da su? (b) Me ya sa abin da ke Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna sura 7 yake da muhimmanci ga shafaffu da kuma “babban taro”?

6 Bayan Yohanna ya ga shafaffu a sama, sai ya ga “wani babban taro,” amma Littafi Mai Tsarki bai ba da adadin mutanen da suke wannan rukunin ba. (R. Yar. 7:​9, 10) Mene ne aka gaya mana game da su? An gaya wa Yohanna cewa: “Su ne waɗanda suka fito daga azabar nan mai zafi. Sun wanke rigunansu da jinin Ɗan Ragon, suka zama farare.” (R. Yar. 7:14) Bayan sun tsira daga ƙunci mai girma, wannan “babban taro” za su yi rayuwa a duniya kuma za su mori albarku sosai.​—Zab. 37:​9-11, 27-29; K. Mag. 2:​21, 22; R. Yar. 7:​16, 17.

7 Ko da muna cikin waɗanda za su je sama ko kuma su yi rayuwa a duniya, shin mun gaskata cewa za mu ga cikar annabce-annabcen da ke Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna sura 7? Ya kamata mu gaskata hakan. Waɗanda za su je sama da waɗanda za su yi rayuwa a duniya za su yi farin cikin ganin cikar annabce-annabcen nan! Za mu yi murna sosai cewa mun zaɓi mu goyi bayan Mulkin Jehobah. Mene ne kuma Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna ta gaya mana game da ƙunci mai girma?​—Mat. 24:21.

MENE NE ZAI FARU DA MAƘIYAN ALLAH

8. Ta yaya ƙunci mai girma zai soma, kuma mene ne yawancin mutane za su yi?

8 Kamar yadda aka nuna a talifin baya, nan ba da daɗewa ba, gwamnatocin duniya za su hallaka Babila Babba wato daular addinin ƙarya. (R. Yar. 17:​16, 17) Wannan matakin da za su ɗauka ne zai zama somawar ƙunci mai girma. Shin hakan zai sa mutane da yawa su soma bauta wa Jehobah ne? A’a. A maimakon haka, Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna sura 6 ta nuna cewa a wannan lokacin, mutanen da ba sa bauta wa Jehobah za su nemi kāriya daga gwamnatocin duniya, da kuma ’yan kasuwan duniya waɗanda aka kwatanta su da manyan tuddai. Da yake sun ƙi goyan bayan Mulkin Allah, Jehobah zai ɗauke su a matsayin maƙiyansa.​—Luk. 11:23; R. Yar. 6:​15-17.

9. Ta yaya bayin Jehobah za su fita dabam a lokacin ƙunci mai girma, kuma wane sakamako ne hakan zai jawo?

9 A lokacin ƙunci mai girman, bayin Jehobah za su fita dabam. Su ne kaɗai rukunin da za su ci gaba da bauta wa Jehobah kuma su ƙi goyon bayan “dabbar.” (R. Yar. 13:​14-17) Don haka, maƙiyan Jehobah za su yi fushi sosai. A sakamakon haka, rundunar haɗin gwiwa na ƙasashe za su kai hari wa bayin Allah a dukan duniya. Littafi Mai Tsarki ya kira wannan harin, harin Gog na Magog.​—Ezek. 38:​14-16.

10. Kamar yadda Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 19:​19-21 suka nuna, mene ne Jehobah zai yi sa’ad da aka kai wa mutanensa hari?

10 Mene ne Jehobah zai yi idan suka kai wa mutanensa hari? Ya gaya mana cewa: “Fushina mai zafi zai tashi.” (Ezek. 38:​18, 21-23) Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna sura 19 ta bayyana abin da zai faru bayan hakan. Jehobah zai aiki Ɗansa ya kāre mutanensa kuma ya hallaka maƙiyansu. “Rundunar yaƙi na sama” wanda ya ƙunshi mala’iku, da shafaffu 144,000 tare da Yesu za su yaƙi Gog na Magog. (R. Yar. 17:14; 19:​11-15) Me zai zama sakamakon wannan yaƙin? Za a hallaka dukan ’yan Adam da kuma ƙungiyoyi da suka ƙi goyon bayan Mulkin Jehobah!​—Karanta Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 19:​19-21.

BAYAN YAƘIN, ZA A ƊAURA AURE

11. Wane abu mafi muhimmanci ne zai faru da aka ambata a Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna?

11 Ka yi tunanin yadda masu aminci a duniya za su ji bayan an hallaka maƙiyan Allah! Kowa a duniya zai yi farin ciki sosai! Ko da yake za a yi farin ciki sosai a sama bayan an hallaka Babila Babba, akwai wani abu dabam kuma da zai sa a yi murna sosai. (R. Yar. 19:​1-3) Abin yana da muhimmanci sosai kuma shi ne “bikin auren Ɗan Ragon” da aka ambata a littafin Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna.​—R. Yar. 19:​6-9.

12. Kamar yadda Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 21:​1, 2 suka nuna, yaushe ne za a yi auren Ɗan Ragon?

12 Yaushe ne za a yi bikin auren? Dukan shafaffu 144,000 za su kasance a sama kafin yaƙin Armageddon ya soma. Amma ba a lokacin ne za a yi auren Ɗan Ragon ba. (Karanta Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 21:​1, 2.) Za a yi auren Ɗan Ragon bayan an yi yaƙin Armageddon kuma an hallaka dukan maƙiyan Allah.​—Zab. 45:​3, 4, 13-17.

13. Mene ne zai faru a bikin auren Ɗan Ragon?

13 Mene ne zai faru a bikin auren Ɗan Ragon? Kamar yadda aure yake haɗa mata da miji, haka ma wannan auren a alamance zai haɗa Sarki Yesu Kristi da ‘amaryarsa,’ wato shafaffu 144,000. Wannan auren ne zai kafa sabon gwamnati da zai yi iko bisa duniya har na tsawon shekara 1,000.​—R. Yar. 20:6.

YADDA ZA KA AMFANA DAGA WANI BIRNI MAI ƊAUKAKA

Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna sura 21 ta nuna cewa Sabuwar Urushalima a alamance “tana saukowa daga sama daga wurin Allah.” A lokacin Sarautar Kristi na Shekara Dubu Ɗaya, zai kawo wa biliyoyin ’yan Adam albarka (Ka duba sakin layi na 4-16)

14-15. Da me Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna sura 21 ya kwatanta shafaffu 144,000? (Ka duba hoton da ke shafin farko.)

14 Bayan haka, Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna sura 21 ta kwatanta shafaffu 144,000 da wani birni mai kyaun gaske da aka kira “Sabuwar Urushalima.” (R. Yar. 21:​2, 9) An gina tushen wannan birnin a kan duwatsu goma sha biyu, kuma a kai an “rubuta sunayen almajirai goma sha biyu na Ɗan Ragon.” Me ya sa wannan wahayin ya ja hankalin Yohanna? Domin ya ga sunansa a jikin ɗaya daga cikin waɗannan duwatsun. Hakika wannan gata ce babba!​—R. Yar. 21:​10-14; Afis. 2:20.

15 Wannan birnin babu kamar shi. Yana da babban titi da aka yi da zallar zinariya, da ƙofofin lu’u’lu’ai goma sha biyu. Katangar birnin da kuma tushensa an yi su ne da duwatsu masu daraja kuma kowane gefensa daidai ne da sauran. (R. Yar. 21:​15-21) Amma Yohanna ya lura da wani abin da babu a birnin! Ga abin da Yohanna ya ce: “Ban ga haikali a birnin nan ba, gama Ubangiji Allah Mai Iko Duka da Ɗan Ragon su ne haikalin birnin. Birnin kuwa ba ya bukatar rana ko wata su haskaka shi, gama ɗaukakar Allah ita ce take haskaka shi, Ɗan Ragon kuma shi ne fitilar birnin.” (R. Yar. 21:​22, 23) Waɗanda aka yi Sabuwar Urushalima da su za su kasance tare da Jehobah. (Ibran. 7:27; R. Yar. 22:​3, 4) Saboda haka, Jehobah da Yesu su ne haikalin birnin.

Su waye ne za su amfana daga albarkun da aka yi amfani da “kogi” da kuma “itatuwa” don a kwatanta su? (Ka duba sakin layi na 16-17)

16. Mene ne zai faru da ’yan Adam a lokacin Sarautar Yesu na Shekara Dubu?

16 Yin tunanin wannan birnin yana sa shafaffu farin ciki. Ya kamata waɗanda suke da begen yin rayuwa a duniya su ma su yi farin cikin yin hakan. A lokacin Sarautar Yesu na Shekara Dubu, Sabuwar Urushalima za ta kawo albarku masu yawa a duniya. Yohanna ya ga waɗannan albarkun suna fitowa daga kursiyi kamar “kogin ruwa mai ba da rai.” Kuma a kowane gefen kogin “akwai Itace Mai Ba Da Rai” da yake fitar da ganyaye domin “warkar da dukan al’ummai.” (R. Yar. 22:​1, 2) Dukan ’yan Adam da suke rayuwa a lokacin za su amfana daga waɗannan albarkun. A sannu a hankali, dukan ’yan Adam masu biyayya za su zama kamilai. Ba za a sake yin rashin lafiya, ko baƙin ciki ko kuka ko azaba ba.​—R. Yar. 21:​3-5.

17. Kamar yadda Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 20:​11-13 suka nuna, su waye ne za su amfana daga Sarautar Yesu na Shekara Dubu?

17 Su waye ne za su amfana daga waɗannan albarkun? Da farko, waɗanda suka tsira daga yaƙin Armageddon za su amfana, ƙila tare da yaran da za a haifa a sabuwar duniya. Amma Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna sura 20 ta ce waɗanda suka mutu za su tashi. (Karanta Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 20:​11-13.) Za a tā da “masu adalci” da suka mutu, da kuma “marasa adalci” da ba su sami damar koya game da Jehobah kafin su mutu ba don su yi rayuwa a nan duniya. (A. M. 24:15; Yoh. 5:​28, 29) Shin hakan yana nufin za a tā da kowa da kowa su yi rayuwa a duniya a lokacin Sarautar Yesu na Shekara Dubu? A’a. Ba za a tā da masu mugunta da suka ƙi bauta wa Jehobah kafin su mutu ba. An ba su dama amma sun nuna cewa ba su cancanci yin rayuwa a sabuwar duniya ba.​—Mat. 25:46; 2 Tas. 1:9; R. Yar. 17:8; 20:15.

GWAJI NA ƘARSHE

18. Yaya yanayin ’yan Adam zai kasance a ƙarshen shekaru dubun?

18 A ƙarshen Sarautar Yesu na Shekara Dubu, dukan mutanen da ke rayuwa a duniya za su zama kamilai. Babu wanda zunubin Adamu zai shafa kuma. (Rom. 5:12) Za a cire zunubin da muka gāda daga Adamu gabaki ɗaya. Ta haka, mutane za su sake rayuwa a matsayin kamiltattu a ƙarshen shekaru dubun.​—R. Yar. 20:5.

19. Me ya sa ake bukatar gwaji na ƙarshe?

19 Yesu ya riƙe amincinsa sa’ad da Shaiɗan ya jarraba shi. Shin ’yan Adam kamilai za su riƙe amincinsu sa’ad da aka ba Shaiɗan damar jarraba su? Kowa ne zai ba da amsar wannan tambayar da kansa a lokacin da za a saki Shaiɗan daga rami a ƙarshen shekaru dubun. (R. Yar. 20:7) Waɗanda suka riƙe amincinsu a wannan gwaji na ƙarshe, za su sami rai na har abada da kuma ’yanci na ƙwarai. (Rom. 8:21) Za a hallaka waɗanda suka yi tawaye tare da Iblis da aljanunsa har abada.​—R. Yar. 20:​8-10.

20. Yaya annabce-annabcen da ke littafin Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna yake sa ka ji?

20 Ya ka ga wannan gajeriyar bitar littafin Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna? Hakika yin tunanin yadda za ka ga cikar annabce-annabcen nan yana sa ka farin ciki, kuma yana sa ka yin iya ƙoƙarinka don ka yi wa mutane wa’azi domin su zo su bauta wa Jehobah. (R. Yar. 22:17) Yanzu da mun tattauna abubuwan da za su faru a nan gaba, muna farin ciki sosai, kuma kamar manzo Yohanna, mu ma muna cewa: “Amin. Zo, Ubangiji Yesu!”​—R. Yar. 22:20.

WAƘA TA 27 Allah Zai Bayyana ’Ya’yansa

^ Wannan ne talifi na ƙarshe a jerin talifofi game da Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna. Kamar yadda za mu tattauna a wannan talifin, waɗanda suka riƙe aminci ga Jehobah za su more rayuwa a nan gaba. Amma waɗanda suka ƙi goyon bayan mulkinsa za su sha kunya kuma su hallaka.