Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 23

Iyaye, Ku Koya wa Yaranku Su Ƙaunaci Jehobah

Iyaye, Ku Koya wa Yaranku Su Ƙaunaci Jehobah

“Ka ƙaunaci Ubangiji Allahnka da dukan zuciyarka, da dukan ranka, da dukan hankalinka.”​—MAT. 22:37

WAƘA TA 134 Yara Amana Ne Daga Allah

ABIN DA ZA A TATTAUNA *

1-2. Me ya sa wasu nassosi za su iya daɗa kasancewa da muhimmanci a gare mu sa’ad da yanayinmu ya canja?

 A RANAR aure, ango da kyakkyawar amaryarsa suna saurarar jawabin da ake bayarwa daga Littafi Mai Tsarki a kan batun aure. Ba karo na farko ke nan da suke jin jawabi kamar haka ba. Amma tun daga ranar auren, nassosin za su daɗa kasancewa musu da muhimmanci. Me ya sa? Domin ƙa’idodin da za su bi ke nan a matsayin ma’aurata.

2 Abin da yake faruwa ke nan sa’ad da ma’aurata Kiristoci suka haifi yara. Sun yi shekaru suna jin jawabai a kan renon yara. Amma bayan sun haifi yara, ƙa’idodin za su daɗa kasancewa da muhimmanci a gare su don za su yi renon yaransu. Hakan babban gata ne! Sa’ad da yanayinmu ya canja, wasu nassosi za su daɗa kasancewa da muhimmanci a gare mu. Wani dalilin da yake sa bayin Jehobah karanta Littafi Mai Tsarki ke nan. Kuma kamar yadda aka gaya wa sarakuna a Isra’ila ta dā su yi, ya kamata iyaye ma su yi bimbini a kan abubuwa da suka karanta ‘dukan kwanakin ransu.’​—M. Sha. 17:19.

3. Me za mu tattauna a wannan talifin?

3 Iyaye, Jehobah ya ba ku ɗaya daga cikin gata mafi muhimmanci da Kiristoci suke da shi, wato gatan koya wa yaranku game da Jehobah. Amma ba koya musu game da Jehobah ne kaɗai kuke bukatar ku yi ba. Ya kamata ku taimaki yaranku su ƙaunaci Jehobah da dukan ransu. Me za ku iya yi don ku taimaki yaranku su ƙaunaci Jehobah? A wannan talifin, za mu tattauna ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki guda huɗu da za su taimake ku ku yi renon yaranku. (2 Tim. 3:16) Za mu kuma ga yadda wasu iyaye Kiristoci suka amfana daga bin ƙa’idodin.

ƘA’IDODI HUƊU DA ZA SU TAIMAKA MA IYAYE

Ta yaya yaranku za su amfana idan kuna neman ja-gorancin Jehobah a kowane lokaci kuma kuna kafa musu misali mai kyau? (Ka duba sakin layi na 4, 8)

4. Wace ƙa’ida ce za ta iya taimakon iyaye su koya wa yaransu su ƙaunaci Jehobah? (Yakub 1:5)

4 Ƙa’ida ta 1: Ka nemi taimakon Jehobah. Ka roƙi Jehobah ya ba ka hikimar da kake bukata don ka koya wa yaranka su ƙaunace shi. (Karanta Yakub 1:5.) Shi ne ya fi dacewa ya ba ka shawara. Akwai dalilai da dama da suka sa muka faɗi hakan. Ka yi la’akari da guda biyu daga cikinsu. Na farko, Jehobah ne ya fi ƙwarewa a matsayin Uba. (Zab. 36:9) Na biyu, shawarwari da yake bayarwa suna amfanar mu a koyaushe.​—Isha. 48:17.

5. (a) Mene ne ƙungiyar Jehobah take tanadarwa don ta taimaka wa iyaye? (b) Kamar yadda aka nuna a cikin bidiyon, me ka koya daga yadda Ɗan’uwa da ’Yar’uwa Amorim suka yi renon yaransu?

5 Jehobah ya tanadar wa iyaye abubuwa da yawa daga Littafi Mai Tsarki da za su taimake su su koya wa yaransu su ƙaunace shi. (Mat. 24:45) Alal misali, za ka iya samun shawarwari daga jerin talifofin nan “Taimako don Iyali,” wanda a dā ake wallafawa a mujallar Awake! amma a yanzu ana wallafa shi a dandalin jw.org. Ƙari ga haka, bidiyoyi da yawa da ke jw.org za su iya taimaka wa iyaye su bi shawarwarin Jehobah yayin da suke renon yaransu. *​—K. Mag. 2:​4-6.

6. Yaya wani mahaifi yake ji game da shawarwari da shi da matarsa suke samuwa daga ƙungiyar Jehobah?

6 Iyaye da yawa sun nuna godiyarsu don abubuwa da ƙungiyar Jehobah take tanadarwa don ta taimake su. Wani mahaifi mai suna Joe ya ce: “Yin renon yaranmu uku don su ƙaunace Jehobah ba ƙaramin aiki ba ne. Ni da matata mukan roƙi Jehobah a kowane lokaci don ya taimaka mana. Kuma a yawancin lokuta mukan ga cewa wani talifi ko bidiyo ya fito a daidai lokacin da muke bukatar mu taimaka wa yaranmu. A kullum, muna bin shawarwari da Jehobah yake bayarwa.” Joe da matarsa sun gano cewa waɗannan abubuwan ne suke taimaka wa yaransu su ƙaunace Jehobah.

7. Me ya sa yake da muhimmanci iyaye su yi iya ƙoƙarinsu don su kafa wa yaransu misali mai kyau? (Romawa 2:21)

7 Ƙa’ida ta 2: Ku kafa wa yaranku misali mai kyau. Yara suna lura da iyayensu sosai kuma sukan bi misalinsu. Hakika iyaye ajizai ne. (Rom. 3:23) Duk da haka, ya kamata iyaye su yi iya ƙoƙarinsu don su kafa wa yaransu misali mai kyau. (Karanta Romawa 2:21.) Ga abin da wani mahaifi ya faɗa game da yara. Ya ce: “Kamar yadda burodi yake shanye ruwa da aka saka shi a ciki, haka ma yara suna koyan abubuwa da suka gani.” Ya ƙara da cewa: “Za su gaya mana idan ba ma bin abin da muke koya musu.” Saboda haka, idan muna so yaranmu su ƙaunace Jehobah, mu ma muna bukatar mu nuna musu cewa muna ƙaunar Jehobah da dukan zuciyarmu.

8-9. Me ka koya daga abin da Andrew da kuma Emma suka faɗa?

8 Akwai hanyoyi da yawa da iyaye za su iya koya wa yaransu su ƙaunaci Jehobah. Ga abin da wani ɗan’uwa mai suna Andrew ɗan shekara 17 ya faɗa. Ya ce: “A kowane lokaci, iyayena suna tuna min yadda yin addu’a yake da muhimmanci sosai. Kowane dare, babana yakan yi addu’a tare da ni ko da na riga na yi addu’a da kaina. Iyayenmu sukan gaya wa ni da ƙanwata cewa: ‘Za ku iya yin addu’a ga Jehobah a duk lokacin da kuke so.’ Abin da suke gaya mana ya sa addu’a ta kasance da muhimmanci sosai a rayuwata. Yanzu yana min sauƙi in yi addu’a kuma in ɗauke Jehobah a matsayin Uba da yake ƙaunata.” Iyaye, a kowane lokaci ku tuna cewa yadda kuke ƙaunar Jehobah zai iya taimaka wa yaranku su ma su ƙaunace shi.

9 Ku yi la’akari da misalin Emma. Babansu ya ci bashi sosai kafin ya rabu da iyalinsu kuma mamarsu ce ta biya bashin. Emma ta ce: “Akwai lokuta da yawa da mamata ta rasa kuɗi. Amma a kullum takan yi magana game da yadda Jehobah yake kula da kuma tanada wa bayinsa. Yadda mamarmu take yin abubuwa ya nuna min cewa tana bin abin da take gaya mana.” Wane darasi ne za mu iya koya? Iyaye za su iya koya wa yaransu misali mai kyau ko da suna cikin mawuyacin yanayi.

10. Wace dama ce iyaye Isra’ilawa da yawa suka samu na tattaunawa da yaransu game da Jehobah? (Maimaitawar Shari’a 6:​6, 7)

10 Ƙa’ida ta 3: Ku riƙa tattaunawa da yaranku. Jehobah ya umurci Isra’ilawa a zamanin dā cewa su riƙa koya wa yaransu game da shi a kullum. (Karanta Maimaitawar Shari’a 6:​6, 7.) Daga safe har dare, iyaye a lokacin suna da damar koya wa yaransu yadda za su ƙaunaci Jehobah. Alal misali, yaro Ba’isra’ile zai iya kasancewa tare da babansa na tsawon lokaci suna shuki ko girbi. ’Yar’uwarsa kuma za ta iya kasancewa da mamarta daga safe har dare tana taimaka wa mamar da ɗinki da saƙa da kuma wasu ayyukan gida. Yayin da yara da iyaye suke aiki tare, sukan sami damar tattaunawa game da batutuwa masu muhimmanci sosai. Alal misali, za su iya tattaunawa da yaransu game da yadda Jehobah yake da alheri kuma yake taimaka wa iyalinsu.

11. Wace dama ce iyaye suke da ita na tattaunawa da yaransu?

11 Amma a yanzu, abubuwa sun canja. A ƙasashe da yawa, iyaye da yaransu ba sa iya zama tare daga safe har dare. Iyaye za su bukaci su je aiki, yara kuma su je makaranta. Saboda haka, ya zama dole iyaye su nemi damar tattaunawa da yaransu. (Afis. 5:​15, 16; Filib. 1:10) Yin ibada ta iyali zai iya ba su dama su yi hakan. Wani ɗan’uwa matashi mai suna Alexander ya ce: “A kowane lokaci, babana yakan shirya yadda za mu yi ibada ta iyali kuma ba ya barin kome ya hana mu yin hakan. Bayan mun gama ibada ta iyali, sai mu zauna muna taɗi kawai.”

12. Mene ne magidanci yake bukatar ya tuna yayin da suke ibada ta iyali?

12 Idan kai magidanci ne, me za ka iya yi don yaranka su ji daɗin ibada ta iyali? Tare da matarka, za ku iya yin nazari da yaranku ta wajen amfani da littafin nan Ka Ji Daɗin Rayuwa Har Abada! Littafin zai iya sa ya kasance muku da sauƙi ku tattauna da juna. Kuna so yaranku su gaya muku abin da ke zuciyarsu, saboda haka, kada ku yi amfani da lokacin ibada ta iyali ku yi ta gaya musu abin da suke yi da ba daidai ba. Kuma kada ku yi fushi idan yaranku sun gaya muku abin da bai jitu da ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki ba. A maimakon haka, ku gode musu cewa sun gaya muku abin da ke zuciyarsu kuma ku sa ya yi musu sauƙi su ci gaba da yin hakan. Sai kun san abin da ke zuciyar yaranku ne za ku iya taimaka musu.

Ta yaya iyaye za su iya amfani da halittun Jehobah don su koya ma yaransu game da halayensa? (Ka duba sakin layi na 13)

13. A waɗanne lokuta ne iyaye za su iya taimaka wa yaransu su kusace Jehobah?

13 Iyaye, a kowace rana ku nemi damar taimaka wa yaranku su kusaci Jehobah. Ba sai kun jira lokacin da kuke nazari da su kafin ku koya musu game da Jehobah Allahnmu mai ƙauna ba. Wata mahaifiya mai suna Lisa ta ce: “Mukan yi amfani da duk abin da muka gani don mu taimaka wa yaranmu su koya game da Jehobah. Alal misali, idan karenmu ya yi wani abu da ya sa yaran dariya, sai mu ce musu hakan ya nuna cewa Jehobah Allah ne mai farin ciki kuma shi ne ya yi mu a hanyar da za mu yi farin ciki kuma mu ji daɗin abubuwa masu ban dariya.”

Iyaye, kun san abokan yaranku? (Ka duba sakin layi na 14) *

14. Me ya sa yake da muhimmanci iyaye su taimaka wa yaransu su zaɓi abokan kirki? (Karin Magana 13:20)

14 Ƙa’ida ta 4: Ku taimaka wa yaranku su zaɓi abokan kirki. Kalmar Allah ta nuna cewa abokanmu za su iya taimaka mana mu kasance da halaye masu kyau ko kuma munanan halaye. (Karanta Karin Magana 13:20.) Iyaye, kun san abokan yaranku? Kun taɓa haɗuwa da su kuma kun tattauna da su? Me za ku iya yi don ku taimaka wa yaranku su yi abokantaka da waɗanda suke ƙaunar Jehobah? (1 Kor. 15:33) Za ku iya taimaka wa yaranku su yi abokan kirki ta wajen gayyatar ’yan’uwan da suke ƙaunar Jehobah su zo gidanku yayin da kuke ayyukan iyali.​—Zab. 119:63.

15. Mene ne iyaye za su iya yi don su taimaka wa yaransu su sami abokan kirki?

15 Ka yi la’akari da misalin wani mahaifi mai suna Tony. Ya bayyana abin da shi da matarsa suka yi don su taimaka wa yaransu su sami abokan kirki. Ya ce: “Ni da matata mun yi shekaru da yawa muna gayyatar ’yan’uwa manya da ƙanana zuwa gidanmu. Sukan ci abinci tare da mu kuma su yi ibada ta iyali tare da mu. Wannan kyakkyawar hanya ce ta sanin waɗanda suke ƙaunar Jehobah kuma suna bauta masa da farin ciki. Mun gayyaci masu kula da da’ira, da masu wa’azi a ƙasashen waje da dai wasu ’yan’uwa gidanmu. Yaranmu sun koyi abubuwa da yawa daga labaransu, daga yadda suke nuna ƙwazo da kuma abubuwa da suke yi a hidimarsu ga Jehobah kuma hakan ya taimaki yaranmu su ma su ƙaunace Jehobah.” Iyaye, ku yi iya ƙoƙarinku ku taimaka wa yaranku su nemi abokan kirki.

KADA KU FID DA RAI

16. Me iyaye za su yi idan yaro ya ce ba ya so ya bauta wa Jehobah?

16 Amma idan duk da ƙoƙarin da kuka yi, ɗaya daga cikin yaranku ya ce ba ya so ya bauta wa Jehobah fa? Kada ku ce kun kasa a matsayin iyaye. Jehobah ya ba kowannenmu, har da yaranku, ’yancin zaɓa ko za mu bauta masa ko ba za mu bauta masa ba. Idan ɗanku ya yanke shawara cewa ba ya so ya bauta wa Jehobah, kar ku fid da rai. Zai iya dawowa wata rana. Ku tuna da kwatancin ɗa mubazzari. (Luk. 15:​11-19, 22-24) Matashin ya bar gida kuma ya yi abubuwa marasa kyau da yawa amma a ƙarshe ya koma gida. Wasu za su iya cewa, “Ai wannan labarin tatsuniya ce kawai. Ba zai iya faruwa da gaske ba.” Amma hakan zai iya faruwa da gaske. Abin da ya faru da wani matashi mai suna Elie ke nan.

17. A wace hanya ce labarin Elie ya ƙarfafa ka?

17 Ga abin da Elie ya faɗa game da iyayensa. Ya ce: “Sun yi iya ƙoƙarinsu su koya min in ƙaunace Jehobah da kuma Kalmarsa. Amma sa’ad da na kai wajen shekara 15, sai na soma rashin ji.” Elie ya soma yin abubuwa marasa kyau a ɓoye. Iyayensa sun yi ƙoƙari su taimaka masa ya kyautata dangantakarsa da Jehobah amma ya ƙi jin su. A kwana a tashi, ya bar gida kuma ya soma munanan abubuwa sosai. Duk da haka, a wasu lokuta, yakan nuna wa abokinsa wasu abubuwa daga Littafi Mai Tsarki. Elie ya ce: “Yayin da nake daɗa tattaunawa da shi game da Jehobah, na gano cewa ni ma ina daɗa tunani game da Jehobah. Da sannu a hankali, ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki da iyayena sun koya mini kuma sun yi ƙoƙari su taimaka min in bi, sun soma tasiri a zuciyata.” Da shigewar lokaci, Elie ya komo ga Jehobah. * Ku yi tunanin irin farin ciki da iyayensa suka yi cewa sun yi iya ƙoƙarinsu su koya masa game da Jehobah tun yana yaro.​—2 Tim. 3:​14, 15.

18. Yaya kuke ji game da iyayen da suke iya ƙoƙarinsu su koya wa yaransu game da Jehobah?

18 Iyaye, Jehobah ya ba ku babban gata na taimaka wa yaranku su bauta masa sa’ad da suka yi girma. (Zab. 78:​4-6) Wannan ba ƙaramin aiki ba ne kuma muna yaba muku don kuna yin iya ƙoƙarinku ku taimaka wa yaranku! Idan kuka ci gaba da yin iya ƙoƙarinku ku taimaka wa yaranku su ƙaunaci Jehobah kuma su yi masa biyayya, za ku iya kasancewa da tabbaci cewa Jehobah, Ubanmu na sama mai ƙauna, zai yi farin ciki.​—Afis. 6:4.

WAƘA TA 135 Jehobah Ya Ce: “Ɗana Ka Yi Hikima”

^ Iyaye Kiristoci suna ƙaunar yaransu sosai. Suna iya ƙoƙarinsu su tanadar wa yaransu abubuwan da suke bukata kuma su sa su farin ciki. Amma abu mafi muhimmanci da suke yi shi ne taimaka wa yaransu su ƙaunaci Jehobah da dukan ransu. Wannan talifin zai tattauna ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki guda huɗu da za su taimaki iyaye su cim ma hakan..

^ Ka duba talifin nan “Littafi Mai Tsarki Yana Gyara Rayuwar Mutane” a Hasumiyar Tsaro ta 1 ga Afrilu, 2012.

^ BAYANI A KAN HOTO: Wani mahaifi yana buga wasan ƙwallon kwando da ɗansa da kuma abokin ɗansa don yana so ya san halin abokin.