Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 22

Shawarar da Za Ta Taimaka Mana a Kullum

Shawarar da Za Ta Taimaka Mana a Kullum

“Yahweh yana ba da hikima.”​—K. MAG. 2:6.

WAƘA TA 89 Mu Ji, Mu Yi Biyayya Don Mu Sami Albarka

ABIN DA ZA A TATTAUNA *

1. Me ya sa dukanmu muna bukatar hikima daga wurin Allah? (Karin Magana 4:7)

 IDAN ka taba yanke shawara mai muhimmanci, babu shakka ka roƙi Jehobah ya taimaka maka domin ka san kana bukatar hakan. (Yak. 1:5) Sarki Sulemanu ya rubuta cewa: “Muhimmin abu shi ne samun hikima.” (Karanta Karin Magana 4:7.) Hakika, ba kowace irin hikima ce Sulemanu yake magana a kai ba. Yana magana ne a kan hikimar da Allah yake bayarwa. (K. Mag. 2:6) Amma shin hikimar da Allah yake bayarwa za ta iya taimaka mana mu magance matsalolin da muke fama da su a yau? Ƙwarai kuwa. Za mu ga hakan a talifin nan.

2. Ta wace hanya ce za mu iya zama masu hikima?

2 Abin da zai taimaka mana mu sami ƙarin hikima shi ne yin nazari da kuma bin koyarwar mutane biyu da suka kasance da hikima sosai. Na farko, za mu tattauna misalin Sulemanu. Littafi Mai Tsarki ya ce “Allah ya ba Solomon [ko kuma Sulemanu] hikima da fahimtar da suka fi gaban misali.” (1 Sar. 4:29) Na biyu, za mu tattauna misalin Yesu wanda ya nuna hikima fiye da kowa. (Mat. 12:42) Littafi Mai Tsarki ya yi annabci game da Yesu cewa: “Ruhun Yahweh zai kasance tare da shi, ruhun hikima da na ganewa.”​—Isha. 11:2.

3. Mene ne za mu tattauna a wannan talifin?

3 Jehobah ya ba wa Sulemanu da kuma Yesu hikima sosai. Hakan ya sa sun ba da shawarwari masu kyau da za su amfani kowannenmu a yau. A wannan talifin, za mu tattauna uku daga cikin shawarwarin, wato yadda za mu kasance da ra’ayin da ya dace game da kuɗi da aikinmu da kuma kanmu.

RA’AYIN DA YA DACE GAME DA KUƊI

4. Ta yaya yanayin Sulemanu da Yesu suka bambanta?

4 Sulemanu ya yi arziki sosai kuma ya zauna a gida mai kyaun gaske. (1 Sar. 10:​7, 14, 15) Amma Yesu bai yi arziki ba kuma bai gina gida na kansa ba. (Mat. 8:20) Duk da haka, su biyun sun kasance da ra’ayin da ya dace game da abin duniya, domin daga wuri ɗaya suka sami hikimarsu, wato daga wurin Jehobah.

5. Yaya Sulemanu ya kasance da ra’ayin da ya dace game da kuɗi?

5 Sulemanu ya ce kuɗi yakan “tsare mutum.” (M. Wa. 7:12) Idan muna da kuɗi, za mu iya sayan abubuwan da muke bukata da waɗanda sha’awarsu kawai muke yi. Amma duk da cewa yana da arziki sosai, Sulemanu ya fahimci cewa akwai abin da ya fi kuɗi muhimmanci. Alal misali, ya ce: “Gwamma suna mai kyau da samun dukiya.” (K. Mag. 22:1) Sulemanu ya kuma lura cewa mutanen da suke son kuɗi ba sa gamsuwa da shi. (M. Wa. 5:​10, 12) Kuma ya gargaɗe mu cewa kada mu yi tunanin cewa kuɗi ne abu mafi muhimmanci domin za mu iya yin hasararsa farat ɗaya.​—K. Mag. 23:​4, 5.

Shin yadda muke ɗaukan abubuwan duniya yana hana mu saka Mulkin Allah farko a rayuwarmu? (Ka duba sakin layi na 6-7) *

6. Ta yaya Yesu ya kasance da ra’ayi mai kyau game da abin duniya? (Matiyu 6:​31-33)

6 Yesu ya kasance da ra’ayin da ya dace game da abin duniya. Ya ji daɗin abinci da kuma abin sha. (Luk. 19:​2, 6, 7) Alal misali a mu’ujizarsa ta farko, ya yi ruwan inabi mai kyau sosai. (Yoh. 2:​10, 11) Kuma a ranar da ya mutu, yana sanye da kaya mai sada. (Yoh. 19:​23, 24) Amma Yesu bai ɗauki abin duniya da muhimmanci fiye da kome a rayuwarsa ba. Ya gaya wa almajiransa cewa: “Ba wanda zai iya bauta wa shugabanni biyu . . . Ba dama ku sa ranku ga bin Allah ku kuma sa ga bin kuɗi duk gaba ɗaya.” (Mat. 6:24) Yesu ya koyar da cewa idan muka sa Mulkin Allah farko a rayuwarmu, Jehobah zai tanada mana abubuwan da muke bukata.​—Karanta Matiyu 6:​31-33.

7. Ta yaya wani ɗan’uwa ya amfana domin ya kasance da ra’ayin da ya dace game da kuɗi?

7 ’Yan’uwanmu da yawa sun amfana domin sun bi shawarar da Littafi Mai Tsarki ya bayar game da kuɗi. Ka yi la’akari da misalin wani ɗan’uwa mai suna Daniel. Ya ce: “Sa’ad da nake matashi, na yanke shawara cewa zan sa ayyukan ibada farko a rayuwata.” Da yake Daniel ya sauƙaƙa rayuwarsa, hakan ya sa ya iya yin abubuwa da yawa a bautarsa ga Jehobah, kamar ayyukan ba da agaji da kuma yin hidima a Bethel. Ya ƙara da cewa: “A gaskiya, ban yi nadamar matakin da na ɗauka ba ko kaɗan. Da na sa neman kuɗi ne farko a rayuwata, da mai yiwuwa na yi kuɗi sosai. Amma kuɗi bai kai abokan kirki da na samu a yanzu ba. Bai ma kai farin cikin da nake yi a yanzu domin na sa Mulkin Allah farko a rayuwata ba. Babu yawan kuɗi da zai kai albarku da Jehobah ya yi mini a yanzu.” Babu shakka, muna amfana a duk lokacin da muka mai da hankali ga ayyukan ibada maimakon neman kuɗi.

RA’AYIN DA YA DACE GAME DA AIKINMU

8. Ta yaya muka san cewa Sulemanu ya kasance da ra’ayin da ya dace game da aiki? (Mai-Wa’azi 5:​18, 19)

8 Sulemanu ya ce yin aiki zai sa mutum farin ciki sosai, kuma ya ce hakan “kyauta ce daga Allah.” (Karanta Mai-Wa’azi 5:​18, 19.) Ya rubuta cewa: “A cikin dukan aiki akwai lada.” (K. Mag. 14:23) Sulemanu ya tabbatar da abin da ya faɗa domin shi ma’aikaci mai ƙwazo ne! Ya gina gidaje da gonakin inabi, da lambuna da kuma tafkuna. Ya kuma gina birane. (1 Sar. 9:19; M. Wa. 2:​4-6) Ya yi aiki da ƙwazo kuma babu shakka ya gamsu da hakan. Amma Sulemanu ya san cewa ba abubuwan nan ne kaɗai za su sa shi farin ciki na ƙwarai ba. Ya kuma yi ayyukan ibada da dama. Alal misali, ya ja-goranci gina haikali mai kyaun gaske da za a riƙa bauta ma Jehobah a ciki. Aikin ya ɗauke shi shekaru bakwai! (1 Sar. 6:38; 9:1) Bayan Sulemanu ya yi ayyuka dabam-dabam, ya gano cewa aiki mafi muhimmanci da mutum zai iya yi shi ne aikin ibada. Ya rubuta cewa: “Bayan wannan duka, ga ƙarshen zancen, ka ji tsoron Allah, ka kiyaye umarnansa.”​—M. Wa. 12:13.

9. Ta yaya Yesu ya tabbata cewa aikinsa bai zama abu na farko a rayuwarsa ba?

9 Yesu ma mutum ne da ya yi aiki da ƙwazo. Sa’ad da yake matashi, ya yi aikin kafinta. (Mar. 6:3) Babu shakka iyayensa sun yi farin ciki sosai domin aikin da ya yi don ya tanada ma iyalinsu da ke da girma. Da yake Yesu kamili ne, ya iya aikin kafinta da kyau. Kuma babu shakka mutane da yawa za su so ya yi musu aiki. Hakika, Yesu ya ji daɗin yin aikinsa. Ko da yake Yesu ya yi aiki da ƙwazo, yakan keɓe lokaci don ya yi ayyukan ibada. (Yoh. 7:15) Daga baya, sa’ad da ya soma yin wa’azi da dukan lokacinsa, ya ba wa masu sauraronsa shawara cewa: “Kada ku yi wahalar aiki a kan neman abinci mai lalacewa, amma ku yi aiki a kan abincin da zai dawwama zuwa ga rai na har abada.” (Yoh. 6:27) A Huɗubarsa a kan Dutse kuma, Yesu ya ce: “Ku tara wa kanku dukiya a sama.”​—Mat. 6:20.

Ta yaya za mu tabbata cewa aikinmu ba ya hana mu yin ayyukan ibada? (Ka duba sakin layi na 10-11) *

10. Wace matsala ce za mu iya fuskanta idan muna aiki da ƙwazo?

10 Hikimar da Allah yake ba mu tana taimaka mana mu kasance da ra’ayin da ya dace game da aikinmu. Littafi Mai Tsarki ya gaya ma kowane Kirista cewa “ya yi aiki, da hannuwansa yana aika abin da yake da kyau.” (Afis. 4:28) Oganmu a wurin aiki za iya lura da yadda muke aiki da ƙwazo da kuma gaskiya. Kuma zai iya gaya mana cewa yana jin daɗin yadda muke aiki. Hakan zai iya sa mu ƙara yawan lokaci da muke yi a wurin aiki domin muna so ya kasance da ra’ayin da ya dace game da Shaidun Jehobah. Amma idan muka soma yin haka, ba za mu sami isasshen lokacin da za mu kasance da iyalinmu ko kuma mu yi ayyukan ibada ba. Shi ya sa muke bukatar mu yi gyara domin mu sami isasshen lokacin yin abubuwa da suka fi muhimmanci.

11. Mene ne wani ɗan’uwa ya koya a kan yadda za mu kasance da ra’ayin da ya dace game da aikinmu?

11 Wani ɗan’uwa matashi mai suna William ya ga amfanin kasancewa da ra’ayin da ya dace game da aiki. Wani dattijo ya taɓa ɗaukan sa aiki kuma ga abin da William ya faɗa game da dattijon, ya ce: “[Ɗan’uwan] ya nuna yadda za a kasance da ra’ayin da ya dace game da aiki. Yana aiki da ƙwazo, kuma yana da dangantaka mai kyau da waɗanda yake yi musu aiki domin yana yin aikinsa da kyau. Amma bayan ya tashi aiki, sai ya mai da hankali ga iyalinsa da kuma ayyukan ibada. Yana ɗaya daga cikin mutanen da suka fi farin ciki da na sani!” *

RA’AYIN DA YA DACE GAME DA KANMU

12. Ta yaya Sulemanu ya nuna cewa yana da ra’ayin da ya dace game da kansa, amma ta yaya ya canja daga baya?

12 Sa’ad da Sulemanu yake bauta ma Jehobah da aminci, ya kasance da ra’ayin da ya dace game da kansa. A lokacin da yake matashi, ya san cewa yana da kasawa, kuma ya roƙe Jehobah ya taimaka masa. (1 Sar. 3:​7-9) Kuma a lokacin da Sulemanu ya soma sarauta, ya gano cewa girman kai yana da haɗari sosai. Ya rubuta cewa: “Girman kai yakan kai ga halaka, ɗaga kai kuma yakan kai ga fāɗuwa.” (K. Mag. 16:18) Amma abin baƙin ciki, daga baya Sulemanu bai bi shawarar da ya bayar ba. Sa’ad da ya ci gaba da sarauta, sai ya soma girman kai, kuma hakan ya sa ya yi banza da umurnan Jehobah. Alal misali, ɗaya daga cikin dokokin Jehobah ya ce kada sarkin Isra’ila ya “tara wa kansa mata . . . domin kada su juya zuciyarsa daga Yahweh.” (M. Sha. 17:17) Sulemanu ya yi banza da wannan dokar, kuma ya auri mata 700 sa’an nan ya ajiye wasu mata 300. Da yawa daga cikinsu ba su bauta ma Jehobah ba! (1 Sar. 11:​1-3) Mai yiwuwa Sulemanu ya ɗauka cewa abin da ya yi ba zai zama masa da damuwa ba. Amma daga baya, rashin biyayyar Sulemanu ya jawo masa mummunar sakamako.​—1 Sar. 11:​9-13.

13. Mene ne za mu iya koya daga yin bimbini a kan yadda Yesu ya nuna sauƙin kai?

13 Yesu ya kasance da ra’ayin da ya dace game da kansa duk rayuwarsa. Kafin Yesu ya zo duniya, ya yi abubuwa masu ban mamaki a hidimarsa ga Jehobah. Ta wurin Yesu ne “aka yi kome da kome, abubuwan da suke a sammai da kuma a nan duniya.” (Kol. 1:16) A lokacin da ake yi masa baftisma, da alama Yesu ya tuna da abubuwan da ya yi sa’ad da yake tare da Ubansa a sama. (Mat. 3:16; Yoh. 17:5) Amma duk da haka, Yesu bai nuna girman kai ba, kuma bai taɓa nuna cewa ya fi wasu muhimmanci ba. Ya gaya ma almajiransa cewa, bai zo “domin a bauta masa ba, sai dai domin ya yi bauta, ya kuma ba da ransa domin ceton mutane da yawa.” (Mat. 20:28) Ya kuma faɗi cewa ba ya yin abin da ya ga dama. (Yoh. 5:19) Hakika, Yesu ya nuna sauƙin kai sosai! Ya kafa wa dukanmu misali mai kyau.

14. Mene ne Yesu ya koya mana a kan yadda za mu kasance da ra’ayin da ya dace game da kanmu?

14 Yesu ya koya wa almajiransa cewa su kasance da ra’ayin da ya dace game da kansu. Akwai lokacin da Yesu ya tabbatar musu cewa: “Ko gashin kanku ma an ƙirga su.” (Mat. 10:30) Abin da Yesu ya faɗa yana da ban ƙarfafa, musamman ma idan muna ganin kamar ba mu da daraja. Abin da ya faɗa ya nuna mana cewa Ubanmu na sama yana ƙaunar mu sosai, kuma muna da daraja a idanunsa. Tun da Jehobah ya yarda mu bauta masa kuma a ganinsa mun cancanci mu yi rayuwa har abada a duniya, ba zai dace mu ɗauka cewa ya yi kuskure ba.

Mene ne zai iya faruwa idan ba mu da ra’ayin da ya dace game da kanmu? (Ka duba sakin layi na 15) *

15. (a) Yaya Hasumiyar Tsaro ta ce ya kamata mu ɗauki kanmu? (b) Kamar yadda hotunan da ke shafi na 24 suka nuna, idan muna yawan mai da hankali ga kanmu, waɗanne albarku ne za mu iya rasawa?

15 Wajen shekaru 15 da suka shige, an rubuto a Hasumiyar Tsaro cewa ya kamata mu kasance da ra’ayin da ya dace game da kanmu. An ce: “A gaskiya, ba zai dace mu soma mai da hankali ga kanmu sosai har mu soma girman kai ba, kuma ba zai dace mu ƙasƙantar da kanmu har mu soma baƙin ciki ba. Maimakon haka, zai dace mu san cewa muna da iyawa da kuma kasawa. Ga yadda wata ’yar’uwa ta bayyana wannan batun, ta ce: ‘Ni ba shaiɗaniya ba ce, amma kuma ni ba mala’ika ba ce. Kamar kowa da kowa, ni ma ina da iyawata da kuma kasawata.’ ” * Hakika, mun ga cewa yana da muhimmanci mu kasance da ra’ayin da ya dace game da kanmu.

16. Me ya sa Jehobah yake ba mu shawarwari masu kyau?

16 Jehobah yana ba mu shawarwari masu kyau ta wajen Kalmarsa Littafi Mai Tsarki. Yana ƙaunar mu kuma yana so mu yi farin ciki. (Isha. 48:​17, 18) Abu mafi muhimmanci da za mu iya yi da zai sa mu farin ciki a rayuwa, shi ne mu ci gaba da yin abubuwan da Jehobah yake so. Idan mun yi hakan, ba za mu shiga matsaloli da masu mai da hankali sosai ga kuɗi ko aikinsu ko kuma kansu suke shiga ba. Bari dukanmu mu yi iya ƙoƙarinmu mu riƙa nuna hikima domin mu sa Jehobah farin ciki!​—K. Mag. 23:15.

WAƘA TA 94 Muna Godiya Jehobah Don Kalmarka

^ Sulemanu da Yesu sun kasance da hikima sosai. Allahnmu Jehobah ne ya ba su hikimar. A wannan talifin, za mu tattauna darussan da za mu iya koya daga shawarwari da Sulemanu da Yesu suka bayar a kan yadda za mu kasance da ra’ayin da ya dace game da kuɗi da aikinmu da kuma kanmu. Za mu kuma ga yadda ’yan’uwanmu suka amfana domin sun bi shawarar Littafi Mai Tsarki a fannonin nan.

^ Ka duba talifin nan “How to Enjoy Hard Work” a Hasumiyar Tsaro ta 1 ga Fabrairu, 2015, a Turanci.

^ Ka duba talifin nan “Littafi Mai Tsarki Zai Sa Ka Sami Farin Ciki” a Hasumiyar Tsaro ta 1 ga Agusta, 2005.

^ BAYANI A KAN HOTO: John da Tom matasa ne da suke ikilisiya ɗaya. John yana yawan amfani da lokacinsa ya kula da motarsa. Tom yana amfani da motarsa ya kai ’yan’uwa wa’azi da kuma taro.

^ BAYANI A KAN HOTO: John yana zarce lokaci a wurin aiki. Yana so ya burge ogansa a wurin aiki. Don haka, a duk lokacin da ogansa ya ce masa ya yi aiki har dare, yakan yarda da hakan. A yammar, Tom wanda bawa mai hidima ne, ya ziyarci wata ’yar’uwa tare da wani dattijo don su ƙarfafa ta. Tun dā ma, Tom ya gaya wa ogansa a wurin aiki cewa ba zai riƙa yin aiki da yamma a wasu ranaku ba domin yana amfani da lokacin ya yi ayyukan ibada.

^ BAYANI A KAN HOTO: John ya mai da hankali ga kansa. Tom ya sa ayyukan ibada farko a rayuwarsa, kuma hakan ya sa ya sami abokai da yawa sa’ad da yake taimaka wajen gyara wata Majami’ar Babban Taro.