Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 19

Yadda Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna Ta Shafe Ka a Yau

Yadda Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna Ta Shafe Ka a Yau

“Mai albarka ne mutumin da yake karanta wannan kalmomin annabci.”​—R. YAR. 1:3.

WAƘA TA 15 Mu Yabi Ɗan Allah!

ABIN DA ZA A TATTAUNA *

1-2. Me ya sa ya kamata mu yi marmarin sanin abin da ke Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna?

 A CE wani da ka sani ya ba ka hotunansa ka kalla, kuma ba ka san yawancin mutanen da ke hotunan ba. Amma hoto ɗaya daga cikinsu ya ja hankalinka. Me ya sa? Domin kana cikin hoton. Yayin da kake kallon hoton, ka tuna lokaci da kuma wurin da kuka ɗauki hoton. Kuma ka yi ƙoƙari ka gane sauran mutanen da ke cikin hoton. Don haka, hoton ya kasance da muhimmanci sosai a gare ka.

2 Littafin Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna yana kama da wannan hoton. Me ya sa? Domin dalilai biyu. Na farko, an rubuta wannan littafin ne dominmu. Aya ta farko na littafin ta ce: ‘Ru’uyar Yesu Almasihu wanda Allah ya ba shi domin ya nuna wa bayinsa abin da zai faru ba da daɗewa ba.’ (R. Yar. 1:1) Don haka, abin da aka rubuta a littafin nan ba domin dukan mutane ba ne, amma domin mu bayin Allah ne. A matsayinmu na bayin Allah, ba abin mamaki ba ne cewa muna cika wasu annabce-annabcen da ke littafin nan. Don haka, a duk lokacin da muke karanta Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna muna karanta abubuwan da suka shafe mu ne.

3-4. Kamar yadda Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna ta nuna, yaushe ne annabce-annabcen nan za su cika, kuma me ya kamata su sa mu yi?

3 Dalili na biyu da ya kamata mu so sanin abin da ke littafin shi ne lokacin da annabce-annabcen za su cika. Manzo Yohanna ya faɗi lokacin da waɗannan annabce-annabcen za su cika, ya ce: ‘A ranar Ubangiji . . . Ruhu ya sauko a kaina.’ (R. Yar. 1:10) Yohanna ya rubuta kalmomin nan a wajen shekara ta 96 bayan haihuwar Yesu. Daga lokacin za a yi shekaru da yawa kafin “ranar Ubangiji” ta zo. (Mat. 25:​14, 19; Luk. 19:12) Annabcin Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa ranar nan ta soma ne a 1914 a lokacin da aka naɗa Yesu ya zama Sarki a sama. Daga wannan shekarar ne annabce-annabcen Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna da suka shafi mutanen Allah suka soma cika. Hakika, yanzu muna rayuwa a “ranar Ubangiji”!

4 Da yake muna rayuwa a kwanaki na ƙarshe, muna bukatar mu mai da hankali sosai ga gargaɗin da ke Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 1:​3, cewa: ‘Mai albarka ne mutumin da yake karanta wannan kalmomin annabci, da waɗanda suke jin wannan kalmomin annabci, suke kuma kiyaye abin da aka rubuta a cikin littafin, gama lokacin da waɗannan abubuwa za su faru ya yi kusa.’ Babu shakka, muna bukatar mu “karanta,” mu “ji wannan kalmomin annabci,” kuma mu “kiyaye” su. Waɗanne ne cikin kalmomin nan muke bukatar mu kiyaye?

KA TABBATA CEWA KANA BAUTA WA JEHOBAH YADDA YAKE SO

5. Ta yaya Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna ta nuna muhimmancin bauta wa Jehobah yadda yake so?

5 Tun daga sura ta farko na littafin, mun ga cewa Yesu ya san kome da ke faruwa a ikilisiyoyin mutanensa. (R. Yar. 1:​12-16, 20; 2:1) Mun ga tabbacin hakan a wasiƙu da Yesu ya tura wa ikilisiyoyi bakwai da ke Asiya Ƙarama. A wasiƙun, ya ba wa Kiristoci a ƙarni na farko takamammun umurnin da za su taimaka musu su bauta wa Jehobah yadda yake so. Kuma saƙonnin sun shafi dukan bayin Allah a yau. Darasin da muka koya daga hakan shi ne, shugabanmu Yesu Kristi ya san ko muna da dangantaka mai kyau da Jehobah. Yana yi mana ja-goranci, yana kāre mu kuma yana ganin kome da kome. Ya san abin da muke bukatar mu yi idan muna so Jehobah ya ci gaba da amincewa da mu. Wane umurni ne ya bayar a yau da muke bukatar mu bi?

6. (a) Bisa ga Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 2:​3, 4, wace matsala ce ikilisiyar Afisa take da shi? (b) Wane darasi ne za mu iya koya?

6 Karanta Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 2:​3, 4Kada mu bar ƙaunarmu ta farko. Wasiƙar da Yesu ya tura wa ikilisiyar Afisa ta nuna cewa Afisawan sun jimre kuma sun bauta wa Jehobah duk da matsaloli. Duk da haka, sun bar ƙaunarsu ta farko. Idan ba su sake kasancewa da ƙaunar ba, Allah ba zai amince da ibadarsu ba. Haka ma a yau, ba jimrewa ne kawai ya kamata mu yi ba. Ya kamata mu jimre da manufa mai kyau. Ba abin da muke yi ne kawai yake da muhimmanci ga Allahnmu ba. Amma dalilin da ya sa muke yin sa ma yana da muhimmanci a gare shi, domin yana so mu bauta masa saboda ƙauna da kuma godiya don abubuwan da ya yi mana.​—K. Mag. 16:2; Mar. 12:​29, 30.

7. (a) Bisa ga Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 3:​1-3, wace matsala ce Yesu ya lura da ita a ikilisiyar Sardis? (b) Mene ne muke bukatar mu yi?

7 Karanta Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 3:​1-3. Dole ne mu ci gaba da kasancewa a faɗake. Ikilisiyar Sardis ta fuskanci wata matsala dabam. Ko da yake sun bauta wa Jehobah a dā, sun daina yin hakan. Saboda haka, Yesu ya ce musu su “farka daga barci.” Wane darasi ne muka koya? Hakika, Jehobah ba zai manta da ayyukanmu ba. (Ibran. 6:10) Amma kada mu ɗauka cewa domin mun yi wa Jehobah hidima da ƙwazo a dā ba ma bukatar mu yi hakan a yanzu. Ko da yake ba za mu iya yin ayyukan da muke yi a dā ba, muna bukatar mu ci gaba da yin “aikin Ubangiji” iya ƙarfinmu kuma mu kasance a faɗake har zuwa ƙarshe.​—1 Kor. 15:58; Mat. 24:13; Mar. 13:33.

8. Wane darasi ne muka koya daga abin da Yesu ya gaya wa ikilisiyar Lawudikiya a Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 3:​15-17?

8 Karanta Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 3:​15-17. Muna bukatar mu bauta wa Jehobah da dukan zuciyarmu. Saƙon Yesu ga ikilisiyar Lawudikiya ta nuna wata matsala dabam. Suna “tsaka-tsaka” a ibadarsu, wato ba su daina bauta wa Jehobah ba amma ba sa ƙwazo a hidimarsu. Saboda haka, Yesu ya gaya musu cewa su ‘marasa kome ne, abin tausayi.’ Suna bukatar su saka ƙwazo sosai a hidimarsu ga Jehobah. (R. Yar. 3:19) Wane darasi ne muka koya? Idan ba ma ƙwazo a hidimarmu, zai dace mu yi tunani a kan abubuwa masu kyau da Jehobah da ƙungiyarsa suka yi mana. (R. Yar. 3:18) Bai kamata mu biɗi abin duniya har mu mance da hidimarmu ga Jehobah ba.

9. Kamar yadda saƙon Yesu zuwa ga ikilisiya Birgamum da Tiyatira ya nuna, wace matsala ce muke bukatar mu guje wa?

9 Muna bukatar mu guji koyarwar ’yan ridda. Yesu ya yi wa ’yan’uwan da ke Birgamum gargaɗi domin suna yaɗa koyarwar ƙarya kuma suna raba kan ikilisiya. (R. Yar. 2:​14-16) Ya yaba ma waɗanda suke Tiyatira domin suna ƙoƙari su guje wa “asiran Shaiɗan masu zurfi,” kuma ya ƙarfafa su su riƙe bangaskiyarsu da ƙarfi. (R. Yar. 2:​24-26) An bukaci Kiristoci da suka soma bin koyarwar Shaiɗan su komo ga Jehobah. Mu kuma a yau fa? Muna bukatar mu guje wa duk wata koyarwar da ta saɓa wa Littafi Mai Tsarki. Da farko, ’yan ridda suna iya nuna kamar sun damu da abin da ke Littafi Mai Tsarki, amma ayyukansu ba sa nuna hakan. (2 Tim. 3:5) Idan muna yin nazarin Littafi Mai Tsarki da kyau, zai yi mana sauƙi mu san koyarwar ’yan ridda kuma mu guje musu.​—2 Tim. 3:​14-17; Yahu. 3, 4.

10. Wane darasi ne kuma za mu iya koya daga abin da Yesu ya gaya wa ikilisiyar Birgamum da Tiyatira?

10 Muna bukatar mu guje wa kowace irin lalata. Akwai wata matsala kuma da ikilisiyar Birgamum da Tiyatira suke da ita. Yesu ya yi Allah wadai da wasu a ikilisiyoyin domin sun soma lalata. (R. Yar. 2:​14, 20) Wane darasi ne za mu iya koya? Ko da mun yi shekaru da yawa muna bauta wa Jehobah, kuma muna yin ayyuka da yawa a ƙungiyarsa, Jehobah ba zai amince da ibadarmu ba idan muna yin abin da ba ya so kamar yin lalata da dai sauransu. (1 Sam. 15:22; 1 Bit. 2:16) Yana so mu ci gaba da bin ƙa’idodinsa duk da cewa ɗabi’un mutane na daɗa lalacewa.​—Afis. 6:​11-13.

11. Mene ne muka koya? (Ka duba akwatin nan “ Darussan da Za Mu Iya Koya a Yau.”)

11 Ta yaya za mu iya taƙaita abin da muka koya? Mun ga cewa muna bukatar mu bauta wa Jehobah yadda yake so. Idan muna yin abin da zai sa Jehobah ya ƙi amincewa da ibadarmu muna bukatar mu yi gyara ba tare da ɓata lokaci ba. (R. Yar. 2:​5, 16; 3:​3, 16) Yesu ya sake faɗan wani abu a saƙonsa ga ikilisiyoyin. Me ke nan?

MU SHIRYA DON TSANANTAWA DA ZA MU FUSKANTA

Bayan an kori Shaiɗan daga sama, ta yaya yake kai wa bayin Allah hari? (Ka duba sakin layi na 12-16)

12. Wane darasi ne za mu iya koya daga abin da Yesu ya gaya ’yan’uwa a Simirna da kuma Filadelfiya? (Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 2:10)

12 Bari mu tattauna wasiƙar da Yesu ya tura wa ikilisiyar Simirna da Filadelfiya. Ya gaya wa Kiristoci a ikilisiyoyin kada su ji tsoron tsanantawa domin Allah zai yi musu albarka don bangaskiyarsu. (Karanta Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 2:10; 3:10) Wane darasi ne za mu iya koya a yau? Ya kamata mu san cewa za a tsananta mana amma muna bukatar mu jimre. (Mat. 24:​9, 13; 2 Kor. 12:10) Me ya sa wannan tunasarwar take da muhimmanci?

13-14. Ta yaya abin da aka bayyana a Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna sura 12 ya shafi bayin Allah?

13 Littafin Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna ya bayyana mana cewa za a tsananta wa mutanen Allah a “ranar Ubangiji,” wato a zamaninmu. Sura 12 ta bayyana cewa an soma yaƙi a sama nan da nan bayan an naɗa Yesu ya zama sarki. Mika’ilu wanda shi ne Yesu tare da mala’iku sun yaƙi Shaiɗan da aljanunsa. (R. Yar. 12:​7, 8) A sakamakon haka, sun yi nasara a kan maƙiyan Allah kuma suka jefo su duniya. Yanzu Shaiɗan da aljanunsa suna jawo wa mutane matsaloli sosai. (R. Yar. 12:​9, 12) Ta yaya hakan yake shafan mutanen Allah?

14 Littafin ya sake bayyana mana abin da Shaiɗan ya yi. Ba zai iya zuwa sama ba, don haka, yana kai wa shafaffun bayin Allah hari, wato waɗanda suke wakiltar Mulkin Allah, “suna kuma riƙe da shaidar Yesu.” (R. Yar. 12:17; 2 Kor. 5:20; Afis. 6:​19, 20) Ta yaya wannan annabcin ya cika?

15. Su waye ne suke wakiltar “shaidun nan biyu” da aka ambata a Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna sura 11, kuma me ya faru da su?

15 Shaiɗan ya sa maƙiya su kai wa shafaffu da ke ja-goranci a ƙungiyar Jehobah hari. ’Yan’uwan suna wakiltar “shaidun nan biyu” da aka ce an kashe. * (R. Yar. 11:​3, 7-11) A shekara ta 1918, an tuhumi ’yan’uwa guda takwas da ke yin ja-goranci a ƙungiyar Jehobah da laifin da ba su yi ba, kuma aka yanke musu hukuncin yin shekaru da yawa a kurkuku. Mutane da yawa sun ɗauka cewa an dakatar da aikinsu ke nan.

16. Wane abin mamaki ne ya faru a 1919, amma mene ne Shaiɗan ya ci gaba da yi tun daga lokacin?

16 Sura ta 11 ta sake annabta cewa “shaidun nan biyu” za su sake tashi bayan ɗan lokaci. Wannan annabcin ya cika a hanya mai ban mamaki. Ta yaya? An saki ’yan’uwan bayan sun yi ƙasa da shekara ɗaya a kurkuku. A watan Maris na 1919 ne aka saki waɗannan ’yan’uwan kuma aka wanke su daga zargi. Nan da nan suka ci gaba da yin aiki. Amma hakan bai sa Shaiɗan ya daina kai wa mutanen Allah hari ba. Tun daga lokacin, ya sa an daɗa tsananta wa mutanen Allah. (R. Yar. 12:15) Hakika dukanmu muna “bukatar jimrewa da bangaskiya.”​—R. Yar. 13:10.

KA YI IYA ƘOƘARINKA A AIKIN DA JEHOBAH YA BA MU

17. Wane taimako ne mutanen Allah suka samu da ba su yi tsammani ba duk da cewa Shaiɗan yana kai musu hari?

17 Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna sura 12 ta bayyana cewa mutanen Allah za su sami taimako daga wurin da ba su yi tsammani ba. Littafin ya bayyana cewa ‘ƙasa ta buɗe bakinta ta shanye ruwan kogin’ da ke wakiltar tsanantawa. (R. Yar. 12:16) Abin da ya faru ke nan. A wasu lokuta, mukan sami taimako daga wani sashe na duniyar Shaiɗan, wato wasu sassan shari’a. Sau da yawa, bayin Jehobah sun yi nasara a kotu, kuma sun sami ’yancin ci gaba da yin aikinsu. Ta yaya suka yi amfani da ’yancin da suka samu? Sun yi amfani da wannan ’yancin yadda ya kamata don yin aikin da Jehobah ya ba su. (1 Kor. 16:9) Mene ne wannan aikin ya ƙunsa?

Waɗanne saƙonni biyu ne bayin Allah suke shelar su? (Ka duba sakin layi na 18-19)

18. Wane aiki ne musamman muke yi a wannan kwanaki na ƙarshe?

18 Yesu ya annabta cewa bayin Allah za su yi wa’azin “labari mai daɗi na mulkin [Allah]” a dukan duniya kafin ƙarshe ya zo. (Mat. 24:14) A duk lokacin da suke yin wa’azi, suna samun taimako daga mala’iku ko kuma mala’ikan da Littafi Mai Tsarki ya ce yana “riƙe da madawwamin saƙo na labari mai daɗi domin ya sanar wa mazaunan duniya, wato ga kowace al’umma, da zuriya, da yare, da kabila.”​—R. Yar. 14:6.

19. Wane saƙo ne waɗanda suke ƙaunar Jehobah za su yi wa’azinsa?

19 Ban da shelar labari mai daɗi game da Mulkin Allah, mutanen Allah suna bukatar su goyi bayan aikin da mala’ikun da aka ambata a Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna sura 8 zuwa 10 suke yi. Mala’ikun sun annabta annobar da za su auko wa waɗanda suka ƙi Mulkin Allah. Don haka, Shaidun Jehobah suna yin shelar saƙon da Littafi Mai Tsarki ya kwatanta da “ƙanƙara da wuta,” wato saƙon hukunci na ƙarshe da Allah zai yi wa sashe dabam-dabam na duniyar Shaiɗan. (R. Yar. 8:​7, 13) Mutane suna bukatar su san cewa ƙarshe ya kusa, kuma suna bukatar su yi canje-canje a rayuwarsu don su tsira. (Zaf. 2:​2, 3) Amma wannan saƙo ne da mutane ba sa so su ji. Muna bukatar ƙarfin zuciya don mu yi shelar wannan saƙon. A lokacin ƙunci mai girma, saƙon hukuncin zai daɗa ɓata wa mutane rai sosai.​—R. Yar. 16:21.

KA KIYAYE KALMOMIN ANNABCIN NAN

20. Mene ne za mu tattauna a talifofi na gaba?

20 Muna bukatar mu kiyaye ‘kalmomin annabcin’ nan domin abubuwan da muka karanta a littafin Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna sun shafe mu. (R. Yar. 1:3) Amma ta yaya za mu ci gaba da kasancewa da bangaskiya da kuma jimre tsanantawa yayin da muke shelar wannan saƙon da ƙarfin zuciya? Ga abubuwa biyu da za su iya ƙarfafa mu: Na farko, abin da littafin Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna ya bayyana game da maƙiyan Allah, na biyu, albarkun da za mu samu idan muka kasance da aminci. Za mu tattauna batutuwan nan a talifofi biyu na gaba.

WAƘA TA 32 Mu Kasance da Aminci ga Jehobah!

^ Muna rayuwa ne a kwanakin ƙarshe! Annabce-annabcen da ke littafin Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna suna cika a yau. Ta yaya annabce-annabcen suka shafe mu a yau? A wannan talifin da kuma talifofi biyu na gaba, za mu tattauna wasu batutuwa daga littafin. Za mu ga cewa idan muka bi abin da ke littafin, za mu bauta wa Jehobah a hanyar da yake so.

^ Ka duba “Tambayoyin Masu Karatu” a Hasumiyar Tsaro ta 15 ga Nuwamba, 2014, shafi na 30.