Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 22

WAƘA TA 127 Irin Mutumin da Ya Kamata In Zama

Me Zai Taimaka wa Masu Neman Aure Su Yi Nasara?

Me Zai Taimaka wa Masu Neman Aure Su Yi Nasara?

“Ɓoyayyen mutum na zuciya . . . [yana] da tamani mai-girma.”1 BIT. 3:​4, Tsohuwar Hausa a Sauƙaƙe.

ABIN DA ZA MU KOYA

Za mu ga abin da zai taimaka ma ɗanꞌuwa da ꞌyarꞌuwa da suka soma neman aure su yi nasara, da yadda ꞌyanꞌuwa a ikilisiya za su taimaka musu.

1-2. Me wasu mutane suka ce game da lokacin da suke neman aure?

 IDAN namiji ya soma neman mace, hakan zai iya zama musu dalilin farin ciki sosai. Kuma in kun riga kun soma nema, za ku so kome ya tafi daidai. Akwai maꞌaurata da yawa da abubuwa suka tafi yadda suke so saꞌad da suke neman aure. Wata ꞌyarꞌuwa mai suna Tsion a daga ƙasar Itofiya ta ce: “Wani lokaci da na fi jin daɗin sa a rayuwata, shi ne lokacin da maigidana yake nema na. Mun tattauna batutuwa masu muhimmanci sosai, kuma mun yi hira da dariya. Na yi farin ciki da na ga cewa na samu wanda nake ƙauna kuma yana ƙaunata.”

2 Wani ɗanꞌuwa kuma mai suna Alessio daga Nezalan ya ce, “Da nake neman matata, na yi farin ciki kam, amma mun fuskanci wasu matsaloli.” A talifin nan, za mu tattauna wasu matsaloli da za su iya tasowa yayin da mutane biyu suke neman aure, da wasu ƙaꞌidodin Littafi Mai Tsarki da za su taimake su su yi nasara. Ƙari ga haka, za mu tattauna yadda ꞌyanꞌuwa a ikilisiya za su taimaka wa irin mutanen nan.

DALILIN NEMAN AURE TSAKANIN NAMIJI DA MACE

3. Wane dalili ne yake sa namiji ya nemi mace? (Karin Magana 20:25)

3 Idan namiji yana neman mace, hakan zai iya sa su biyun farin ciki, amma bai kamata su yi wasa da wannan lokacin ba domin neman zai iya kai su ga yin aure. A ranar aure, amarya da ango sukan yi alkawari a gaban Jehobah cewa za su ƙaunaci juna kuma su girmama juna muddin suna a raye. Kafin mu yi wani alkawari, yana da muhimmanci mu natsu kuma mu yi tunani da kyau a kan batun. (Karanta Karin Magana 20:25.) Abin da ya kamata mu yi ke nan kafin mu yi alkawarin aure. Idan ɗanꞌuwa yana neman ꞌyarꞌuwa, hakan zai ba su biyun damar sanin halin juna don su iya tsai da shawara mai kyau. Za su iya yanke shawarar yin aure, ko kuma su rabu. Idan suka rabu, hakan ba ya nufin cewa ba su yi nasara ba. A maimako, rabuwan nan da suka yi ya nuna cewa neman ya cim ma manufarsa, domin ya taimaka musu su ga cewa ba za su dace da juna ba.

4. Me ya sa ya kamata mu kasance da raꞌayi da ya dace game da neman aure?

4 Me ya sa yake da muhimmanci mu zama da raꞌayin da ya dace game da nema tsakanin namiji da ta mace? Idan wanda bai yi aure ba ya fahimci dalilin neman mace, ba zai soma neman wata ba tare da ya yi niyyar auranta ba. Dukanmu ne ya kamata mu kasance da raꞌayi da ya dace game da wannan batun, ba marasa aure kawai ba. Alal misali, wasu suna gani kamar da zarar nema ya shiga tsakanin wani da wata, dole ne su yi aure. Ta yaya hakan yake shafan marasa aure? Wata ꞌyarꞌuwa mai suna Melissa a Amurka, da ba ta yi aure ba ta ce: “Idan aka ga ɗanꞌuwa yana neman ꞌyarꞌuwa, akan matsa musu sosai. Don haka, wasu sukan ƙi rabuwa ko da sun ga cewa ba su dace da juna ba. Wasu ma sun gwammaci ƙin neman aure kwata-kwata. Irin matsin nan yana sa marasa aure cikin damuwa ba kaɗan ba.”

KU SAN JUNA SOSAI

5-6. Me ya kamata ɗanꞌuwa da ꞌyarꞌuwa da suke neman aure su yi ƙoƙari su sani game da juna? (1 Bitrus 3:4)

5 Idan kana neman wata ko wani yana neman ki, me zai taimaka muku ku zaɓa ko za ku yi aure ko ba za ku yi ba? Ku san juna sosai. Ba shakka kun san wasu abubuwa game da juna tun kafin ka soma nemanta. Amma yanzu ne za ku iya sanin “ɓoyayyen mutum na zuciya.” (Karanta 1 Bitrus 3:4. b) Hakan yana nufin ka san ko tana ƙaunar Jehobah da gaske, yaya halinta yake, kuma yaya take tunani. Macen ma ta yi hakan. Da shigewar lokaci, ya kamata a ce kun samu amsoshin tambayoyin nan: ‘Shin idan muka yi aure, za mu dace kuwa?’ (K. Mag. 31:​26, 27, 30; Afis. 5:33; 1 Tim. 5:8) ‘Za mu iya ba wa juna ƙauna da kulawa da kowannenmu yake bukata? Za mu iya ci-gaba da yin haƙuri da juna?’ c (Rom. 3:23) Yayin da kuke ƙara sanin juna, ku tuna cewa ba in kuna da hali iri ɗaya ne za ku dace da juna ba. Dacewa yana nufi ku iya yin haƙuri da juna, kuma ku iya yin wasu canje-canje don ku zauna tare.

6 Mene ne kuma ya kamata ku yi ƙoƙari ku sani game da juna a wannan lokacin? Tun kafin soyayyar ta yi nesa a zukatanku, zai yi kyau ku tattauna wasu batutuwa masu muhimmanci kamar abin da mutumin yake da burin yi nan gaba a rayuwarsa. Amma zancen abubuwa kamar lafiyar mutum, da matsalolin kuɗi, ko kuma abubuwa da suka taɓa faruwa da shi da suka shafi tunaninsa, da yadda yake ji a ransa, ko halinsa fa? Ba kome ne kuke bukatar ku tattauna a lokacin da kuka fara neman aure ba. (Ka ga misali da ke Yohanna 16:12.) Don haka, idan kana ganin lokacin da za ka gaya wa mutum wasu abubuwa bai yi ba tukuna, ka sanar da shi. Amma a-kwana-a-tashi, wadda kake nema, ko wanda yake neman ki, zai bukaci ya san waɗannan bayanan don ya iya tsai da shawara mai kyau. Saboda haka, idan lokaci ya yi, dole ku gaya wa juna gaskiya game da abubuwan nan.

7. Ta yaya waɗanda suke neman aure za su san juna sosai? (Ka kuma duba akwatin nan, “ Neman Aure Tsakanin Waɗanda Suke da Nesa da Juna.”) (Ka kuma duba hotunan.)

7 Ta yaya za ka san ainihin halin mutum? Za ka iya yin haka ta wurin yi masa tambayoyi, da kuma sauraronsa da kyau. (K. Mag. 20:5; Yak. 1:19) Shi ya sa zai yi kyau ku dinga yin abubuwa da za su ba ku damar yin hira sosai, kamar cin abinci, da zuwa zagaya a inda akwai mutane, da yin waꞌazi tare. Za ku kuma iya ƙara sanin juna idan kuka ziyarci abokanku da ꞌyan iyalinku. Ƙari ga haka, zai dace ku shirya yin abubuwa da mutane dabam-dabam kuma a yanayoyi dabam-dabam, hakan zai taimaka muku ku ga halin da kowannenku yake nunawa a yanayoyi dabam-dabam. Ka lura da abin da Ɗanꞌuwa Aschwin daga ƙasar Nezalan ya yi lokacin da yake neman matarsa mai suna Alicia, ya ce: “Mun yi ta yin ayyuka da suka taimaka mana mu ƙara sanin juna, kuma a yawancin lokuta ba wani abin a-zo-a-gani muke yi ba. Alal misali, mukan yi dafuwa tare ko mu yi ayyukan gida tare. Yin abubuwan nan ya sa mun ga inda kowannenmu yake ƙoƙari da kuma inda yake da kasawa.”

Idan kuna yin abubuwa da za su ba ku damar yin hira, hakan zai taimaka muku ku ƙara sanin juna (Ka duba sakin layi na 7-8)


 

8. Wane amfani ne waɗanda suke neman aure za su iya samuwa idan suna nazari tare?

8 Za ku kuma san juna sosai idan kuna nazarin Littafi Mai Tsarki tare. Idan kuka yi aure dole ku nemi lokacin yin ibada ta iyali don Allah ya kasance tare da ku a aurenku. (M. Wa. 4:12) Shi ya sa zai dace ku shirya lokacin da za ku riƙa nazari tare yanzu da kuke neman aure? Waɗanda suke neman aure ba su zama iyali ba tukun, kuma namijin bai riga ya zama kan macen ba. Amma idan kuna nazari tare a-kai-a-kai, zai taimaka muku ku san ko kowannenku na ƙaunar Jehobah. Yin hakan ya amfani Ɗanꞌuwa Max da Laysa a wata hanya dabam, su daga ƙasar Amurka ne. Max ya ce: “Da na soma neman matata, ba da daɗewa ba sai muka soma nazarin littattafai da suka yi magana game da neman aure, da yin aure, da kuma zaman aure. Hakan ya buɗe mana hanyar tattauna wasu batutuwa masu muhimmanci da ba don littattafan nan ba, zai yi mana wuya mu tattauna su.”

ƘARIN ABUBUWA DA YA KAMATA KU YI LAꞌAKARI DA SU

9. Me zai taimaka wa masu neman aure su san wa za su gaya ma cewa suna hakan?

9 Wa ya kamata ku gaya wa cewa kuna neman aure? Kai da wadda kake nema ne za ku tsai da wannan shawara. Lokacin da kuka soma neman, za ku iya tsai da shawara cewa mutane ƙalila ne kawai za ku gaya wa. (K. Mag. 17:27) Idan kuka yi hakan, wataƙila ba za a matsa muku ko a yi muku tambayoyi da yawa ba. Amma fa, idan kuma ba ku gaya ma kowa ba, hakan zai sa ku riƙa yin abubuwa a ɓoye. Kuma kasancewa tare ku kaɗai yana da haɗari sosai. Don haka zai dace ku gaya ma wasu. Aƙalla dai, ku gaya ma waɗanda za su iya ba ku shawara mai kyau kuma su taimaka muku. (K. Mag. 15:22) Alal misali, za ku iya gaya ma wasu ꞌyan iyalinku, da abokanku da suka manyanta, ko dattawa a ikilisiya.

10. Mene ne masu neman aure za su iya yi don kar su yi abin da zai ɓata ma Jehobah rai? (Karin Magana 22:3)

10 Me zai taimake ku ku guji yin abin da zai ɓata ma Jehobah rai? Da shigewar lokaci, za ku ƙara son juna kuma za ku ƙara yin kusa da juna. Me zai taimaka muku kar ku yi abin da zai ɓata ma Jehobah rai? (1 Kor. 6:18) Ku guji yin maganganun batsa, da kasancewa tare ku kaɗai, da kuma shan giya da yawa. (Afis. 5:3) Don abubuwan nan za su iya tayar muku da shaꞌawa, kuma su sa ya yi muku wuya ku guji yin zunubi. Zai dace ku keɓe lokaci don ku riƙa tattauna matakai da za ku ɗauka don ku guji yin abin da zai ɓata ma Jehobah rai. (Karanta Karin Magana 22:3.) Ga abin da ya taimaka ma wani mai suna Dawit da matarsa Almaz. Su daga ƙasar Itofiya ne. Dawit ya ce: “A lokacin, mukan yi hirarmu a inda akwai mutane da yawa, ko kuma tare da abokanmu. Ba mu taɓa kasancewa mu kaɗai a gida ko a cikin mota ba. Hakan ya taimaka mana mu guji yanayi da zai sa mu cikin jarraba.”

11. Me ya kamata masu neman aure su duba don su san ko za su iya yin abubuwan soyayya da juna?

11 Zai dace ku yi abubuwan soyayya? Yayin da kuke ƙara kusantar juna, ba laifi ba ne ku yi wasu abubuwa don ku nuna wa juna so. (W. Waƙ. 1:2; 2:6) Amma fa, idan kuka tayar ma juna shaꞌawa, zai yi muku wuya ku guji yin abin da bai dace ba. Yin abubuwan soyayya zai iya sa ku kasa kame kanku kuma ku yi zunubi. (K. Mag. 6:27) Don haka tun ba ka daɗe kana nemanta ba, ku tattauna abubuwan soyayya da za ku yi da waɗanda ba za ku yi ba bisa ga kaꞌidodin Littafi Mai Tsarki. d (1 Tas. 4:​3-7) Ku tambayi kanku: ‘Mene ne mutanen yankinmu za su ce idan suka gan mu muna yin abubuwan soyayya? Yin abubuwan nan zai tayar mana da shaꞌawa?’

12. Me ya kamata waɗanda suke neman aure su sani game da matsaloli da kuma samun saɓani?

12 Ta yaya za ku magance matsaloli? Idan kuna samun saɓani a wasu lokuta, hakan yana nufin cewa ba ku dace da juna ba ne? Ba lallai ba, don duka masu neman aure da maꞌaurata sukan sami saɓani. Abin da yake sa aure ya jimre shi ne idan mutane biyun suna girmama juna, kuma suna yarda su yi wasu canje-canje don su gamshi juna. Saboda haka, yadda kuke ƙoƙarin magance matsalolinku yanzu zai nuna ko aurenku zai jimre. Ku tambayi kanku: ‘Muna iya tattauna batutuwa cikin natsuwa da bangirma? Muna saurin amincewa da kuskurenmu kuma mu yi ƙoƙarin yin gyara? Muna saurin yarda da shawarar juna, da ba wa juna haƙuri, da yafe wa juna?’ (Afis. 4:​31, 32) Amma fa, idan kun cika samun saɓani, ko kuna yawan gardama a yanzu, da wuya ku daina idan kuka yi aure. Don haka idan ka ga cewa ba ta dace da kai ba, ko kin ga cewa bai dace da ke ba, rabuwa zai fi muku alheri. e

13. Me zai taimaka ma waɗanda suke neman aure su san tsawon lokacin da ya kamata su yi suna hakan?

13 Yaya tsawon lokaci da ya kamata ku yi kana nemanta? Yanke shawara da garaje yakan kawo sakamako marar kyau. (K. Mag. 21:5) Saboda haka, zai dace ku ɗau lokacin da zai ishe ku ku iya sanin halayen juna da kyau. Amma kada ka ci-gaba da nemanta na dogon lokaci haka kawai. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Sa rai wanda ba ta biya bukata ba, takan sa zuciya ta ɓace.” (K. Mag. 13:12) Ƙari ga haka, idan kuka ci-gaba da kasancewa tare, zai ƙara yi muku wuya ku shawo kan shaꞌawar yin jimaꞌi. (1 Kor. 7:9) Maimakon ku yi ta tunani a kan tsawon lokaci da kuka yi kuna wannan neman auren, kowa ya tambayi kansa, ‘Shin akwai wani abu kuma da nake bukata in sani game da ita ko game da shi, kafin in yanke shawara?’

TA YAYA ꞌYANꞌUWA ZA SU TAIMAKA WA MASU NEMAN AURE?

14. Waɗanne abubuwa ne za mu iya yi don mu taimaka wa masu neman aure? (Ka kuma duba hoton.)

14 Idan mun san wasu da suke neman aure, ta yaya za mu taimaka musu? Za mu iya gayyatar su su zo mu ci abinci tare, ko mu yi ibada ta iyali, ko mu shaƙata. (Rom. 12:13) Hakan zai ba su damar ƙara sanin juna. Idan kuma mun ga cewa suna bukatar wani ya kasance da su, ko ya bi su su je wani wuri, ko suna bukatar inda za su zauna su yi magana, zai yi kyau mu taimaka musu. (Gal. 6:10) ꞌYarꞌuwa Alicia da muka ambata a baya, ta tuna yadda aka taimaka mata da maigidanta Aschwin. Ta ce: “Mun ji daɗi sosai da wasu ꞌyanꞌuwa suka ce mana za mu iya zuwa gidansu idan muna neman inda za mu yi hira tare da wani a kusa.” Idan wasu sun ce ka riƙa kasancewa tare da su a wasu lokuta, ka ɗauki hakan a matsayin dama mai kyau na taimaka musu. Kuma in kana hakan, kada ka bar su su kaɗai, amma in ka lura cewa suna bukatar su yi magana su biyu kawai, ka ba su rata, yayin da kake lura da su.—Filib. 2:4.

Idan mun san cewa wani ɗanꞌuwa yana neman wata ꞌyarꞌuwa, zai yi kyau mu nemi hanyoyi da za mu taimaka musu (Ka duba sakin layi na 14-15)


15. Wane abu ne kuma abokai za su iya yi don su taimaka wa masu neman aure? (Karin Magana 12:18)

15 Wata hanya kuma da za mu taimaka ma waɗanda suke neman aure, ita ce ta wurin lura da furucinmu. Wani lokaci muna bukatar kamun kai. (Karanta Karin Magana 12:18.) Alal misali, wani lokaci za mu ji kamar mu gaya wa mutane cewa wani yana neman wata. Amma wataƙila za su fi so su gaya wa mutane da kansu. Kar mu yi gulman waɗanda suke neman aure, ko mu riƙa sukan su a kan abin da bai shafe mu ba. (K. Mag. 20:19; Rom. 14:10; 1 Tas. 4:11) Ƙari ga haka, wataƙila ba za su so mu yi maganganu da za su nuna cewa za su yi aure, ko ya kamata su yi aure ba. Wata ꞌyarꞌuwa mai suna Elise da maigidanta sun ce, “Mun ji kunya da wasu suka yi mana tambaya game da yadda muke shirin bikin aurenmu, domin a lokacin ba mu riga mun tattauna wannan batu ba.”

16. Me ya kamata mu yi idan mun ga cewa wasu da suke neman aure sun rabu?

16 Idan waɗanda suke neman aure sun tsai da shawara cewa za su rabu fa? Mu guji yi musu tambayoyi, kuma kada mu goyi bayan waninsu. (1 Bit. 4:15) Wata ꞌyarꞌuwa mai suna Lea ta ce: “Na ji cewa wasu suna faɗan wasu abubuwa, cewa wataƙila abin da ya sa muka rabu da wani ɗanꞌuwa da ya neme ni ke nan. Abin ya dame ni ba kaɗan ba.” Kamar yadda muka tattauna dazu, idan wani yana neman wata kuma sun rabu, hakan ba ya nufin cewa ba su yi nasara ba. A maimako, hakan ya nuna cewa nema da suka yi ya cim-ma manufarsa, don ya sa sun iya tsai da shawarar da ta dace. Amma rabuwa za ta iya sa su yi baƙin ciki kuma su yi fama da kaɗaici. Don haka, zai yi kyau mu nemi yadda za mu ƙarfafa su.—K. Mag. 17:17.

17. Me ya kamata waɗanda suke neman aure su ci-gaba da yi?

17 Kamar yadda muka gani, idan ɗanꞌuwa yana neman ꞌyarꞌuwa, za su fuskanci wasu matsaloli, amma za su iya jin daɗin wannan lokacin. Wata mai suna Jessica ta ce: “A gaskiya, wannan lokacin bai yi mini sauƙi ba. Amma na ji daɗin duk ƙoƙari da muka yi da yadda muka iya sanin halin juna sosai.” Idan kuna neman aure, ku ci-gaba da yin ƙoƙari don ku san halin juna da kyau. Hakan zai sa ku yi nasara, don zai taimake ku ku tsai da shawara da ta dace.

WAƘA TA 49 Mu Riƙa Faranta Ran Jehobah

a An canja wasu sunayen.

b 1 Bitrus 3:4 (Tsohuwar Hausa a Sauƙaƙe): “Amma ya zama ɓoyayyen mutum na zuciya, cikin tufafi waɗanda ba su lalacewa, na ruhu mai-ladabi mai-lafiya, abin da ke da tamani mai-girma a gaban Allah.”

c Don ka ga wasu tambayoyi kuma da za ka iya neman amsoshinsu, ka duba littafin nan, Questions Young People Ask—Answers That Work, Littafi na 2, shafuffuka na 39-40.

d Tattaɓa alꞌaurar wani ko wata, hanyar yin lalata ne kuma hakan zai bukaci dattawa su kafa wa mutum kwamitin shariꞌa. Tattaɓa nonuwa kuma, ko yin maganganu ko aika ma juna saƙonnin batsa ta waya, za su iya sa a kafa wa mutum kwamitin shariꞌa.

e Don ƙarin bayani, ka duba talifin nan “Tambayoyi Daga Masu Karatu” da ke Hasumiyar Tsaro ta 1 ga Maris, 2000.