Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 21

WAƘA TA 107 Mu Yi Koyi da Allah a Nuna Ƙauna

Ya Za Ka Sami Macen Kirki?

Ya Za Ka Sami Macen Kirki?

“Wane ne zai iya samun mace mai kirki? Darajarta ta fi ta dutse mafi daraja.”—K. MAG. 31:10.

ABIN DA ZA MU KOYA

Za mu ga ƙaꞌidodin Littafi Mai Tsarki da za su taimaka wa mutum ya samu macen kirki, da kuma yadda ꞌyanꞌuwa a ikilisiya za su iya taimaka ma waɗanda ba su yi aure ba amma suna shaꞌawar yin hakan.

1-2. (a) Waɗanne abubuwa ne ya kamata Kirista ya yi laꞌakari da su kafin ya fara neman wadda zai aura? (b) Idan aka ce mutum yana neman mace me ake nufi? (Ka duba “Maꞌanar wasu kalmomi.”)

 ZA KA so ka yi aure? Ko da yake ba sai mutum ya yi aure ne zai yi farin ciki ba, matasa da waɗanda suka manyanta da yawa suna marmarin yin aure. Hakika, kafin mutum ya fara neman wadda zai aura, zai dace ya kasance da dangantaka mai kyau da Jehobah, ya manyanta kuma ya tabbata cewa zai iya biyan bukatunsa da na iyalinsa. a (1 Kor. 7:36) Yin hakan zai taimaka wa mutum ya ji daɗin aurensa.

2 Amma samun macen kirki bai da sauƙi. (K. Mag. 31:10) Kuma ko da ka samu ꞌyarꞌuwa da kake so, zai iya yi maka wuya ka soma neman ta. b A talifin nan, za mu tattauna abin da zai taimaka wa mutum ya sami macen da yake so kuma ya soma nemanta. Za mu kuma koyi yadda ꞌyanꞌuwa a ikilisiya za su iya taimaka ma waɗanda suke so su yi aure.

YADDA ZA KA SAMO MACEN DA TA DACE

3. Waɗanne abubuwa ne ya kamata Kirista ya sani idan yana neman wadda zai aura?

3 Idan kana so ka yi aure, zai dace ka san irin halaye da kake so matarka ta kasance da su kafin ka soma nema. c In ba haka ba, za ka iya kin neman ꞌyarꞌuwar da ta dace da kai ko ka soma neman ꞌyarꞌuwar da ba ta dace da kai ba. Duk wadda za ka nema dai, ya kamata ta zama wadda ta yi baftisma. (1 Kor. 7:39) Amma fa, ba kowace ꞌyarꞌuwa da ta yi baftisma ce za ta dace da kai ba. Don haka, zai dace ka yi wa kanka wannan tambayar: ‘Mene ne burina a rayuwa? Waɗanne halaye ne nake so matata ta kasance da su? Abubuwa da nake bukata daga wadda nake so in aura masu yiwuwa ne?’

4. Waɗanne abubuwa ne wasu ꞌyanꞌuwa suke yin adduꞌa a kai?

4 Idan kana so ka yi aure, ba shakka ka riga ka yi adduꞌa game da batun. (Filib. 4:6) Gaskiyar ita ce, Jehobah bai yi wa kowa alkawari cewa zai sami matar aure ba. Amma ya damu da kai da kuma yadda kake ji, kuma zai taimaka maka ka iya samun macen da ta dace da kai. Don haka, ka ci-gaba da gaya masa yadda kake ji da kuma burinka. (Zab. 62:8) Ka roƙe shi ya ba ka hikima kuma ya taimaka maka ka zama mai haƙuri. (Yak. 1:5) Wani ɗanꞌuwa mai suna John, d daga Amurka, ya bayana wasu abubuwa da yake ambatawa a adduꞌarsa. Ya ce: “Nakan gaya wa Jehobah irin halaye da nake so matata ta kasance da su. Ina roƙon sa ya taimaka min in haɗu da wadda ta dace. Ina kuma roƙan Jehobah ya taimaka mini in koyi halaye da za su sa in zama mijin kirki. Wata ꞌyarꞌuwa mai suna Tanya daga ƙasar Sri Lanka ta ce: “Yayin da nake neman aure, ina roƙan Jehobah ya taimaka min in ci-gaba da bauta masa da aminci kuma in ci-gaba da yin farin ciki.” Ko da ba ka samu a yanzu ba, Jehobah ya yi alkawari cewa zai ci-gaba da ƙaunar ka kuma zai ba ka kulawar da kake bukata.—Zab. 55:22.

5. Mene ne zai ba wa Kiristoci marasa aure zarafin haɗuwa da wanda ko wadda take ƙaunar Jehobah? (1 Korintiyawa 15:58) (Ka kuma duba hoton.)

5 Littafi Mai Tsarki ya ce a kullum mu “yalwata cikin aikin Ubangiji.” (Karanta 1 Korintiyawa 15:58.) Idan kana yin aikin Ubangiji a kullum kuma kana kasancewa da ꞌyanꞌuwa maza da mata, za su ƙarfafa ka kuma za ka haɗu da ꞌyanꞌuwa marasa aure da suka sa bautar Jehobah farko a rayuwarsu. Kuma yayin da kake yin iya ƙoƙarinka don ka faranta wa Jehobah rai, za ka yi farin ciki.

Idan ka ci-gaba da sa ƙwazo a yin ayyukan ibada kuma kana cuɗanya da ꞌyanꞌuwa maza da mata dabam-dabam, mai yiwuwa ka haɗu da wasu da suke son yin aure (Ka duba sakin layi na 5)


6. Mene ne ya kamata Kirista ya tuna yayin da yake neman wadda zai aura?

6 Amma zai dace ka yi hankali don kada neman wadda za ka aura ya zama abu mafi muhimmanci a rayuwarka. (Filib. 1:10) Ba sai mutum ya yi aure ne zai yi farin ciki na gaske ba. Dangantakarsa da Jehobah ce za ta sa ya yi hakan. (Mat. 5:3) Yanzu da ba ka yi aure ba, kana da zarafin yin abubuwa da dama a ƙungiyar Jehobah. (1 Kor. 7:​32, 33) Ka yi amfani da wannan zarafi da kake da shi da kyau. Wata ꞌyarꞌuwa mai suna Jessica a ƙasar Amurka da ta yi aure saꞌad da ta kusan shekara 40, ta ce: “Kafin in yi aure, na yi ta yin waꞌazi da ƙwazo duk da cewa ina shaꞌawar yin aure a lokacin.”

KA ƊAU LOKACI KA LURA DA HALAYEN ꞌYARꞌUWAR

7. Me ya sa zai dace ka ɗau lokaci kana lura da ꞌyarꞌuwa kafin ka gaya mata cewa kana son ta? (Karin Magana 13:16)

7 Me za ka yi idan ka sami wata da kake gani za ta iya dace da kai? Zai dace ka gaya mata cewa kana son to nan-da-nan ne? Littafi Mai Tsarki ya ce mutum mai hikima yakan yi tunani kafin ya ɗau mataki. (Karanta Karin Magana 19:2.) Don haka, zai dace ka ɗan ɗau lokaci kana lura da halayen ꞌyarꞌuwar ba tare da sanin ta ba kafin daga baya ka gaya mata cewa kana son ta. Wani ɗanꞌuwa mai suna Aschwin daga ƙasar Nezalan ya ce: “Za ka iya son wata farat ɗaya kuma jim kaɗan ka daina son ta. Don haka, idan ka ɗan ɗau lokaci ka lura da halinta, ba za ka soma soyayyar da za ta mutu jim kaɗan ba.” Ƙari ga haka, yayin da kake lura da halayenta, mai yiwuwa ka ga cewa ba ta dace da kai ba.

8. Ta yaya Kirista marar aure zai iya lura da halin wadda yake so? (Ka kuma duba hoton.)

8 Ta yaya za ka lura da halin ꞌyarꞌuwar ba tare da saninta ba? A tarukan ikilisiya da kuma saꞌad da kuke yin nishaɗi, za ka iya lura da halinta, da yadda take ƙaunar Jehobah. Su wane ne abokanta, kuma me take yawan magana a kai? (Luk. 6:45) Abubuwan da take burin yi a ƙungiyar Jehobah sun yi daidai da naka? Za ka iya yin magana da dattawan ikilisiyarsu ko kuma wani Kirista da ya manyanta game da ita. (K. Mag. 20:18) Za ka iya tambayarsu game da halinta da kuma yadda mutane suke ganin ta. (Rut 2:11) Yayin da kake lura da ꞌyarꞌuwar, kada ka yi abin da zai sa ta ji wani iri, wato kada ka matsa mata lamba kuma kada ka yi ƙoƙarin sanin kome-da-kome game da ita.

Kafin ka gaya ma wata ꞌyarꞌuwa cewa kana son ta, ka ɗan ɗau lokaci ka lura da halinta (Ka duba sakin layi na 7-8)


9. Kafin ka gaya ma wata ꞌyarꞌuwa cewa kana son ta, me ya kamata ka tabbatar da shi?

9 Yaya tsawon lokaci da ya kamata ka ɗauka kana lura da halinta? Idan ka yi saurin gaya ma wata cewa kana son ta, za ta iya ɗauka cewa kai mai yin abu cikin garaje ne. (K. Mag. 29:20) Amma kuma idan ka daɗe kana lura da halinta, za ta iya ɗauka cewa ba ka san abin da kake so ba musamman idan ta riga ta ɗago cewa kana son ta. (M. Wa. 11:4) Ka tuna cewa ba sai ka tabbatar wa kanka cewa za ka aure ta ne za ka gaya mata yadda kake ji ba. Amma ka tabbata cewa ka yi shirin yin aure kuma cewa za ku iya dacewa da juna.

10. Me ya kamata ka yi idan ka lura cewa wata tana son ka amma ba ka da niyyar yin soyayya da ita?

10 Me za ka yi idan ka lura cewa wata tana ƙaunar ka? Idan ba ka da niyyar neman ta, ka yi abubuwa da za su sa ta gane hakan. Ba zai dace ka yi kamar kana so ku yi soyayya da ita, alhali kuma ba niyyarka ke nan ba.—1 Kor. 10:24; Afis. 4:25.

11. Idan a ƙasarmu wasu ne suke zaɓa wa mutum wadda zai aura, ko su nemo masa wadda zai duba ya ga ko ta dace da shi, me ya kamata mu tuna?

11 A wasu ƙasashe, iyayen mutum ko kuma danginsa da suka manyanta ne suke zaɓa masa wadda zai aura. A wasu ƙasashen kuma, dangin mutum ko kuma abokansa ne za su nemo masa wata, saꞌan nan su shirya yadda shi da ita za su haɗu don su tattauna kuma su ga ko sun dace da juna. Idan wani ya ce maka ka nema masa wadda zai aura, ka yi laꞌakari da abin da shi da kuma ꞌyarꞌuwar da ka samo suke so da kuma bukatunsu. Idan ka samo wata da kake ganin za ta dace da mutumin, ka yi ƙoƙari ka san halinta, mafi muhimmanci ma ka san ko tana ƙaunar Jehobah. Wanda yake ƙaunar Jehobah ya fi mai kuɗi, ko mai ilimi ko mai babban matsayi, ko da daga wane iyali ya fito. Amma ka tuna cewa ɗanꞌuwan da kuma ꞌyarꞌuwar su ne za su yanke shawarar ko sun dace da juna.—Gal. 6:5.

YADDA ZA KA SOMA NEMAN WADDA KAKE SO

12. Idan kana so ka soma neman wata ꞌyarꞌuwa, ta yaya za ka gaya mata hakan?

12 Idan kana so ka soma neman wata ꞌyarꞌuwa, ta yaya za ka gaya mata? e Za ka iya yin shiri don ku tattauna da juna a wani wuri da akwai mutane ko kuma ku tattauna ta waya. Ka bayyana mata dalla-dalla cewa kana son ta, kuma za ka so ku ƙara sanin juna. (1 Kor. 14:9) Ka ba ta lokaci ta yi tunani idan da bukata. (K. Mag. 15:28) Idan kuma ba ta amince ku yi soyayya ba, ka amince da amsar da ta ba ka kuma ka daraja ta.

13. Me za ka yi idan wata ta ce tana son ka? (Kolosiyawa 4:6)

13 Amma me za ka yi idan wata ta ce tana son ka? Ka san cewa bai yi mata sauƙi ta gaya maka hakan ba. Don haka, ka daraja ta kuma ka amsa mata da alheri. (Karanta Kolosiyawa 4:6.) Idan za ka bukaci lokaci kafin ka ba ta amsa, ka gaya mata. Amma zai dace ka ba ta amsa ba tare da ɓata lokaci ba. (K. Mag. 13:12) Idan ba za ka so ku yi soyayya ba, ka gaya mata hakan dalla-dalla kuma ka yi hakan cikin daraja. Abin da wani ɗanꞌuwa mai suna Hans da ke Ostriya ya yi ke nan saꞌad da wata ꞌyarꞌuwa ta ce tana son shi. Ya ce: “Na gaya mata shawarar da na yanke dalla-dalla kuma na yi hakan cikin daraja. Na ba ta amsa nan take don ba na so ta sa rai cewa za mu yi soyayya. Kuma bayan haka, na yi hankali da abubuwan da nake gaya mata da kuma abubuwan da nake yi don kar ta ɗauka cewa na soma son ta.” Amma idan ka yarda ku yi soyayya, zai dace ka gaya mata hakan, kuma ku tattauna yadda kuke so soyayyar ta kasance, da abubuwan da za ku riƙa yi. Mai yiwuwa yadda kake so abubuwa su kasance zai yi dabam da yadda take so, saboda bambancin alꞌada da dai sauransu.

TA YAYA ꞌYANꞌUWA ZA SU TAIMAKA WA MARASA AURE?

14. Ta yaya za mu taimaka wa Kiristoci marasa aure da furucinmu?

14 Ta yaya dukanmu za mu taimaka wa ꞌyanꞌuwa da suke so su yi aure? Wani abin da za mu yi shi ne mu yi hankali da abubuwan da muke faɗa. (Afis. 4:29) Za mu iya tambayar kanmu: ‘Shin ina zolayar waɗanda suke so su yi aure? Idan na ga ɗanꞌuwa da ꞌyarꞌuwa suna magana da juna, nakan yi zaton cewa suna soyayya ne?’ (1 Tim. 5:13) Ƙari ga haka, kada mu sa ꞌyanꞌuwa da ba su yi aure ba su ji kamar suna rashin wani abu mai muhimmanci. Ɗanꞌuwa Hans da muka ambata ɗazu ya ce: “Wasu ꞌyanꞌuwa sukan ce, ‘Ka yi aure mana. Yanzu fa kai ba yaro ba ne.’ Irin maganganun nan sukan sa ꞌyanꞌuwa marasa aure su ji kamar su ba wani abu ba ne, kuma yana ƙara matsa musu su yi aure.” Hakika zai fi dacewa mu nemi hanyoyi don mu yaba ma ꞌyanꞌuwa marasa aure.—1 Tas. 5:11.

15. (a) Bisa ga ƙaꞌidar da ke Romawa 15:​2, mene ne ya kamata mu yi laꞌakari da shi kafin mu soma nema ma wani wadda zai aura? (Ka kuma duba hoton.) (b) Wane darasi mai muhimmanci ne ka koya daga bidiyon? (Ka duba ƙarin bayanin.)

15 Idan kuma muna gani kamar wani ɗanꞌuwa zai dace da wata ꞌyarꞌuwa fa? Littafi Mai Tsarki ya gargaɗe mu cewa mu lura da yadda mutane suke ji. (Karanta Romawa 15:2.) ꞌYanꞌuwa da yawa ba sa so wani ya yi ƙoƙarin haɗa su da wata. Don haka mu daraja su kuma kada mu yi hakan. (2 Tas. 3:11) Wasu kuma za su bukaci mu taimaka musu, amma zai dace mu jira sai sun ce mu yi hakan. f (K. Mag. 3:27) Wasu marasa aure kuma ba sa so a haɗa su da wani ɗanꞌuwa ko ꞌyarꞌuwa kai tsaye. Wata ꞌyarꞌuwa mai suna Lydia a ƙasar Jamus da ita ma ba ta yi aure ba ta ce: “Za ka iya gayyatar wasu ꞌyanꞌuwa tare da ɗanꞌuwan da ꞌyarꞌuwar. Hakan zai ba wa ɗanꞌuwan da ꞌyarꞌuwar damar haɗuwa da juna. Sai ka bar su su ci-gaba daga nan idan suna so.”

Idan ꞌyanꞌuwa da yawa suna cuɗanya tare, hakan zai ba marasa aure damar haɗuwa da juna (Ka duba sakin layi na 15)


16. Me ya kamata Kiristoci marasa aure su tuna?

16 Dukanmu za mu iya yin rayuwa mai gamsarwa kuma mu yi farin ciki ko mun yi aure ko ba mu yi ba! (Zab. 128:1) Don haka, idan kana so ka yi aure amma ba ka samu wadda kake so ba tukuna, ka ci-gaba da mai da hankali ga ibadarka. Wata ꞌyarꞌuwa mai suna Sin Yi daga birnin Macao ta ce: “Ko da a yanzu ba mu yi aure ba, tsawon lokaci da za mu ɗauka muna rayuwa a matsayin marasa aure, ba kome ba ne idan aka kwatanta shi da ɗimbin lokaci da za mu yi muna rayuwa da matarmu ko mijinmu a Aljanna. Don haka, mu ji daɗin wannan lokaci da ba mu yi aure ba, kuma mu yi amfani da shi da kyau.” Amma idan ka riga ka samu wadda kake so kuma ka riga ka fara neman ta fa? A talifi na gaba, za mu tattauna abin da za ka iya yi a wannan lokacin don ka iya yanke shawarar da ta dace.

WAƘA TA 137 Mata Masu Aminci

a Don ka san ko ka yi shirin yin aure, ka bincika talifin nan, Dating—Part 1: Am I Ready to Date? a dandalin jw.org.

b MAꞌANAR WASU KALMOMI: A wannan talifin da kuma na gaba, furucin nan “nema” yana nufin lokacin da namiji da tamace suke yin kusa da juna don su ƙara sanin juna, kuma su san ko za su dace a matsayin mata da miji. A wasu wurare, akan ce suna fita zance ko kuma soyayya. Hakan yana somawa ne saꞌad da namiji da tamace suka gaya wa juna cewa suna son juna, kuma zai ci-gaba har lokacin da suka yi aure ko suka daina neman.

c Don bayanin ya zo da sauƙi, a talifin nan, za mu yi magana game da ꞌyanꞌuwa maza, amma shawarwarin da za a bayar don maza da mata ne.

d An canja wasu sunayen.

e A alꞌadar wasu, namiji ne yake zuwa wurin mace ya gaya mata cewa yana son ta. Amma ba laifi ba ne idan ꞌyarꞌuwa ce ta gaya wa ɗanꞌuwa cewa tana son shi. (Rut 3:​1-13) Don ƙarin bayani, ka duba talifin nan Young People Ask . . . How Can I Tell Him How I Feel? a Awake! na 22 ga Oktoba, 2004.