Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 17

Jehobah Zai Taimaka Maka Idan Ka Fuskanci Matsaloli Ba Zato

Jehobah Zai Taimaka Maka Idan Ka Fuskanci Matsaloli Ba Zato

“Mai adalci yakan sami wahaloli da yawa, amma Yahweh yakan kuɓutar da shi daga cikinsu duka.”​—ZAB. 34:19.

WAƘA TA 44 Addu’ar Wanda Ke Cikin Wahala

ABIN DA ZA A TATTAUNA a

1. Wane tabbaci ne muke da shi?

 A MATSAYINMU na bayin Jehobah, mun san cewa yana ƙaunar mu kuma yana so mu yi rayuwa mafi kyau. (Rom. 8:​35-39) Mun kuma tabbata cewa bin ƙaꞌidodin Littafi Mai Tsarki yana amfanar mu a kullum. (Isha. 48:​17, 18) Amma me ya kamata mu yi idan muka fuskanci matsalolin da ba mu yi zato ba?

2. Waɗanne matsaloli ne za mu iya fuskanta, kuma wane tunani ne za su iya sa mu yi?

2 Dukan bayin Jehobah suna fama da matsaloli. Alal misali, wani a iyalinmu zai iya yin abin da zai ɓata mana rai. Za mu iya kamuwa da muguwar cuta kuma ta hana mu bauta wa Jehobah yadda muke so. Za mu kuma iya fama da sakamakon wani balaꞌi da ya faru. Ko kuma za a iya tsananta mana saboda imaninmu. Idan mun fuskanci matsaloli kamar haka, za mu iya soma tunani cewa: ‘Me ya sa hakan yake faruwa da ni? Shin na yi wani laifi ne? Ko kuma hakan yana nufin cewa Jehobah ba ya yi min albarka ne?’ Idan ka taɓa jin hakan, kada ka yi sanyin gwiwa. Bayin Jehobah da yawa ma sun yi fama da irin wannan tunanin.​—Zab. 22:​1, 2; Hab. 1:​2, 3.

3. Me za mu iya koya daga Zabura 34:19?

3 Karanta Zabura 34:19. Ku yi laꞌakari da abubuwa guda biyu daga wannan nassin. (1) Masu adalci suna fuskantar matsaloli. (2) Jehobah yana kuɓutar da su daga matsalolin. Ta yaya Jehobah yake kuɓutar da mu? Hanya ɗaya da yake yin hakan ita ce ta wajen taimaka mana mu kasance da raꞌayin da ya dace game da rayuwa a wannan kwanakin ƙarshe. Ko da yake Jehobah ya yi mana alkawari cewa za mu yi farin ciki yayin da muke bauta masa, bai yi mana alkawari cewa za mu yi rayuwa ba tare da matsaloli ba. (Isha. 66:14) Yana dai so mu mai da hankali ga rayuwar da za mu more har abada a nan gaba. (2 Kor. 4:​16-18) Kafin lokacin, yana taimaka mana mu ci gaba da jimrewa a kullum.​—Mak. 3:​22-24.

4. Mene ne za mu tattauna a wannan talifin?

4 Bari mu tattauna darasin da za mu iya koya daga bayin Allah a zamanin dā da kuma a zamaninmu. Yayin da muke yin hakan, za mu ga cewa za mu iya fuskantar matsaloli ba zato. Amma idan muka dogara ga Jehobah, ba zai daina taimaka mana ba. (Zab. 55:22) Yayin da muke tattauna misalan, ka tambayi kanka: ‘Mene ne zan yi idan na shiga irin yanayin nan? Ta yaya misalan nan za su sa in ƙara dogara ga Jehobah? Waɗanne darussa ne na koya da zan so in bi a rayuwata?’

A ZAMANIN DĀ

Jehobah ya albarkaci Yakubu a lokacin da ya yi shekaru 20 yana aiki ma kawunsa Laban wanda ya yaudare shi (Ka duba sakin layi na 5)

5. Waɗanne matsaloli ne Yakubu ya fuskanta saboda Laban? (Ka duba hoton da ke shafin farko.)

5 Bayin Jehobah a zamanin dā sun fuskanci matsaloli da ba su yi tsammani ba. Ka yi laꞌakari da misalin Yakubu. An umurce shi ya auri ɗaya daga cikin yaran Laban, wato danginsa da suke bauta wa Jehobah, kuma an tabbatar masa cewa Jehobah zai yi masa albarka sosai. (Far. 28:​1-4) Don haka, Yakubu ya yi abin da ya dace. Ya bar ƙasar Kanꞌana kuma ya yi tafiya zuwa gidan Laban wanda yake da ꞌyan mata guda biyu, wato Laiꞌatu (Leya) da Rahila. Yakubu ya soma ƙaunar ƙaramar ꞌyar Laban, wato Rahila, kuma ya yarda ya yi wa babanta aiki na shekaru bakwai don ya samu ya aure ta. (Far. 29:18) Amma abubuwa ba su faru yadda Yakubu ya yi tsammani ba. Laban ya yaudare shi kuma ya sa shi ya auri babbar ꞌyarsa, wato Laiꞌatu. Laban ya yarda cewa bayan mako ɗaya zai ba wa Yakubu Rahila ya aura, amma sai ya ƙara yi masa aiki na shekaru bakwai. (Far. 29:​25-27) Laban ya kuma cuci Yakubu saꞌad da suke sanaꞌa tare. Duka-duka, Laban ya yi shekaru 20 yana cucin Yakubu!​—Far. 31:​41, 42.

6. Waɗanne ƙarin matsaloli ne Yakubu ya fuskanta?

6 Yakubu ya fuskanci wasu ƙarin matsaloli. Yana da babban iyali, amma akwai wasu lokuta da yaransa ba su zauna lafiya da juna ba. Har ma sun sayar da ɗanꞌuwansu Yusufu ya zama bawa. Biyu daga cikin yaransa, wato Simeon da Lawi sun yi abin da ya ɓata sunan iyalin da kuma sunan Jehobah. Ƙari ga haka, matar Yakubu da yake ƙauna, wato Rahila ta mutu saꞌad da take haifan ɗansu na biyu. Kuma a lokacin da Yakubu ya tsufa, tsananin yunwa da aka yi ya sa shi da iyalinsa sun ƙaura zuwa ƙasar Masar.​—Far. 34:30; 35:​16-19; 37:28; 45:​9-11, 28.

7. Ta yaya Jehobah ya nuna wa Yakubu cewa yana ƙaunar sa?

7 Duk da matsalolin da Yakubu ya fuskanta, ya ci gaba da gaskata da Jehobah da kuma alkawuran da Ya yi masa. Jehobah kuma ya nuna wa Yakubu cewa yana ƙaunar sa. Alal misali, duk da cewa Laban ya cuci Yakubu sosai, Jehobah ya ba wa Yakubu dukiya mai yawa. Kuma ka yi tunanin irin farin cikin da Yakubu ya yi saꞌad da ya sake haɗuwa da ɗansa wanda ya ɗauka cewa ya mutu da daɗewa. Dangantaka mai kyau da Yakubu yake da ita da Jehobah, ita ce ta taimaka masa ya jimre matsalolin nan. (Far. 30:43; 32:​9, 10; 46:​28-30) Mu ma idan muna da dangantaka mai kyau da Jehobah, za mu iya jimre matsaloli da za su iya abko mana ba zato.

8. Mene ne Sarki Dauda ya so ya yi?

8 Sarki Dauda bai iya yin dukan abubuwa da ya so ya yi a bautarsa ga Jehobah ba. Alal misali, Dauda ya so ya gina wa Allahnsa haikali. Ya gaya wa Nathan (Natan) haka, sai Nathan ya ce masa: “Ka yi duk abin da yake a zuciyarka, gama Allah yana tare da kai.” (1 Tar. 17:​1, 2) Ba shakka Dauda ya ji daɗi sosai da ya ji kalmomin nan. Wataƙila ma nan da nan ya soma shirin yadda zai yi wannan babban aikin.

9. Mene ne Dauda ya yi saꞌad da ya ji saƙo marar daɗi?

9 Jim kaɗan, sai annabin Jehobah ya sake zuwa wurin Dauda da saƙo marar daɗi. “A daren,” Jehobah ya gaya wa Natan cewa ba Dauda ba ne zai gina masa haikali, amma ɗaya daga cikin yaransa ne zai yi hakan. (1 Tar. 17:​3, 4, 11, 12) Me Dauda ya yi da ya ji hakan? Ya canja abin da yake so ya yi wa Jehobah. Ya mai da hankali wajen tattara kuɗi da kuma kayan ginin da ɗansa Sulemanu zai yi amfani da su wajen gina haikalin.​—1 Tar. 29:​1-5.

10. Ta yaya Jehobah ya albarkaci Dauda?

10 Bayan Jehobah ya gaya wa Dauda cewa ba shi ne zai gina masa haikali ba, nan da nan sai ya yi yarjejeniya da Dauda. Jehobah ya yi wa Dauda alkawari cewa wani daga zuriyarsa zai yi sarauta har abada. (2 Sam. 7:16) Wannan alkawarin zai cika a sabuwar duniya a lokacin da Yesu zai yi Sarauta na Shekara Dubu. Babu shakka, Dauda zai yi farin ciki sosai idan ya ji cewa wannan Sarkin wato Yesu Kristi, daga zuriyarsa ya fito! Wannan labarin ya nuna mana cewa ko da ba mu iya yin dukan abubuwan da muke so mu yi wa Jehobah ba, Allahnmu zai ba mu albarku da ba mu taɓa yin tsammanin su ba.

11. Wace albarka ce Jehobah ya yi wa Kiristocin ƙarni na farko duk da cewa Mulkin Allah bai zo a lokacin da suke tsammani ba? (Ayyukan Manzanni 6:7)

11 Kiristocin ƙarni na farko ma sun fuskanci matsalolin da ba su yi tsammanin su ba. Alal misali, sun yi marmarin zuwan Mulkin Allah, amma ba su san yaushe hakan zai faru ba. (A. M. 1:​6, 7) To me suka yi? Sun ci gaba da yin waꞌazi da ƙwazo. Da waꞌazin Mulkin ya yi ta yaɗuwa, sun ga tabbacin cewa Jehobah yana yi musu albarka.​—Karanta Ayyukan Manzanni 6:7.

12. Mene ne Kiristocin ƙarni na farko suka yi saꞌad da ake yunwa?

12 Akwai lokacin da aka yi yunwa sosai “a duniya duka.” (A. M. 11:28) Yunwar ta shafi Kiristocin ƙarni na farko ma. Ka yi tunanin yadda suka sha wahala saboda yunwar. Babu shakka, iyaye daga cikinsu sun yi ta tunani a kan yadda za su tanada wa iyalinsu. Wataƙila hakan ya shafi matasa da suke so su daɗa ƙwazo a waꞌazi. Shin sun yi tunanin jira har sai yunwar ta ƙare kafin su yi hakan? Mai yiwuwa. Duk da matsaloli da Kiristocin nan suke fuskanta, hakan bai hana su yin waꞌazi ba. Sun ci gaba da yin iya ƙoƙarinsu a waꞌazi kuma sun ba ꞌyanꞌuwansu da ke Yahudiya abubuwan da suke da shi da zuciya ɗaya.​—A. M. 11:​29, 30.

13. Waɗanne albarku ne Kiristocin suka samu a lokacin yunwar?

13 Waɗanne albarku ne Kiristocin ƙarni na farko suka samu a lokacin da ake yunwar? Waɗanda suka sami kayan agaji sun shaida yadda Jehobah ya taimaka musu. (Mat. 6:​31-33) Ba mamaki sun ƙara ƙaunar ꞌyanꞌuwan nan da suka taimaka musu. Waɗanda suka ba da gudummawar da waɗanda suka yi aikin agajin, sun shaida farin cikin da ake samu daga bayarwa. (A. M. 20:35) Da suka ci gaba da bauta ma Jehobah duk da matsalolin da suka fuskanta, Jehobah ya yi wa dukansu albarka.

14. Mene ne ya faru da Bulus da Barnaba, kuma wane sakamako ne hakan ya kawo? (Ayyukan Manzanni 14:​21, 22)

14 An tsananta wa Kiristocin ƙarni na farko sosai, a wasu lokuta ma hakan ya faru a lokacin da ba su yi tsammani ba. Ka yi laꞌakari da abin da ya faru da manzo Bulus da kuma Barnaba saꞌad da suke waꞌazi a Listira. Da farko, mutanen sun marabce su kuma sun saurare su. Amma jim kaɗan, wasu maƙiya sun “rinjayi taron,” kuma hakan ya sa wasu daga cikin mutanen da suka marabci Bulus da Barnaba, sun jejjefi Bulus da duwatsu da niyyar kashe shi. (A. M. 14:19) Duk da haka, Bulus da Barnaba sun ci gaba da yin waꞌazi a wani wuri dabam. A sakamakon haka, sun “sami almajirai da yawa,” kuma maganarsu da abin da suka yi sun ƙarfafa ꞌyanꞌuwansu Kiristoci. (Karanta Ayyukan Manzanni 14:​21, 22.) Da yake Bulus da Barnaba ba su daina yin waꞌazi ba duk da tsanantawa da aka yi musu, mutane da yawa sun amfana. Mu ma idan ba mu daina yin aikin da Jehobah ya ba mu ba, zai yi mana albarka.

A ZAMANINMU

15. Wane darasi ne muka koya daga misalin Ɗanꞌuwa A. H. Macmillan?

15 A ꞌyan shekaru kafin 1914, mutanen Jehobah sun sa rai cewa wani abu zai faru. Ka yi laꞌakari da misalin Ɗanꞌuwa A. H. Macmillan. Ɗanꞌuwa Macmillan ya yi tsammanin cewa zai tafi sama nan ba da jimawa ba, kuma abin da ke zuciyar mutane da yawa a lokacin ke nan. A jawabin da ya bayar a watan Satumba, 1914, ya ce: “Wataƙila wannan shi ne jawabi na ƙarshe da zan bayar.” Amma ba haka abin ya kasance ba. Daga baya, Ɗanꞌuwa Macmillan ya rubuta cewa: “Kamar dai wasunmu mun yi hanzari a tunanin da muka yi cewa mun kusa mu tafi sama.” Ya ƙara da cewa: “Abin da ya dace mu yi shi ne mu ci gaba da yin aikin da Ubangiji ya ba mu da ƙwazo.” Kuma Ɗanꞌuwa Macmillan ya yi hakan. Ya ci gaba da yin waꞌazi da ƙwazo. Ya kuma sami zarafin ƙarfafa ꞌyanꞌuwa da yawa da aka saka a kurkuku domin sun ƙi shiga aikin soja. Kuma ya ci gaba da halartan taron ikilisiya babu fashi har a lokacin da ya tsufa. Ta yaya Ɗanꞌuwa Macmillan ya amfana da ya ci gaba da yin ƙwazo a hidimarsa yayin da yake jiran lokacin da Jehobah zai ba sa ladansa? Da ya yi kusan mutuwa a 1966, ya rubuta cewa: “Bangaskiyata ba ta taɓa yin sanyi ba.” Ya kamata dukanmu mu bi halin Ɗanꞌuwa Macmillan, musamman ma idan muna fuskantar matsaloli kuma muna ganin ya kamata a ce aljanna ta riga ta zo!​—Ibran. 13:7.

16. Wane yanayi ne Ɗanꞌuwa Jennings da matarsa suka fuskanta? (Yakub 4:14)

16 Bayin Jehobah da yawa suna fama da rashin lafiya da ba su yi zato ba. Abin da ya faru da Ɗanꞌuwa Herbert Jennings ke nan. b A labarinsa, ya bayyana yadda shi da matarsa suka ji daɗin yin hidima a ƙasar Ghana. Da shigewar lokaci, ɗanꞌuwan ya kamu da rashin lafiyar da ke shafan tunaninsa. Wani lokaci sai ya ji baƙin ciki sosai, a wani lokaci kuma sai ya ji wani irin farin ciki. Ɗanꞌuwa Jennings ya yi ƙaulin Yakub 4:​14, kuma ya ce kafin ya kamu da cutar, “bai san haka ‘gobe’ zai zama ba.” (Karanta.) Ya rubuta cewa: “Da muka ga yadda yanayin yake, mun yanke shawarar barin Ghana da abokai da yawa da muke da su, kuma mun koma ƙasar Kanada [don mu yi jinya].” Jehobah ya taimaka ma Ɗanꞌuwa Jennings da matarsa su ci gaba da bauta masa babu fasawa duk da matsaloli da suke fuskanta.

17. Ta yaya misalin Ɗanꞌuwa Jennings ya ƙarfafa wasu Kiristoci?

17 Yadda Ɗanꞌuwa Jennings ya bayyana yanayinsa dalla-dalla ba tare da ɓoye-ɓoye ba, ya taimaka ma wasu ꞌyanꞌuwa. Wata ꞌyarꞌuwa ta rubuta cewa: “Ban taɓa karanta labarin da ya tsotsa zuciyata kamar wannan ba. . . . Da na karanta yadda Ɗanꞌuwa Jennings ya bar hidimar da yake yi don ya kula da lafiyarsa, hakan ya taimaka min in kasance da raꞌayin da ya dace game da nawa yanayin.” Wani ɗanꞌuwa ma ya ce: “Bayan na yi shekaru goma ina hidima a matsayin dattijo, sai na daina hidimar don na kamu da rashin lafiya da ta shafi ƙwaƙwalwata. Ban so in daina hidimar ba kuma na ji kamar laifina ne. Hakan ya dame ni sosai har ya yi min wuya in karanta labaran ꞌyanꞌuwa. . . . Amma yadda Ɗanꞌuwa Jennings ya ci gaba da bauta ma Jehobah duk da yanayinsa, ya ƙarfafa ni.” Hakan ya tuna mana cewa idan muka shiga wani yanayi ba zato kuma muka jimre, halinmu zai ƙarfafa wasu. Ko da wasu abubuwa sun faru a rayuwarmu da ba mu yi zato ba, za mu iya kafa misali mai kyau ta wajen jimrewa da kuma kasancewa da bege.​—1 Bit. 5:9.

Idan muka dogara ga Jehobah, ko da mun fuskanci matsaloli ba zato, hakan zai sa mu daɗa yin kusa da shi (Ka duba sakin layi na 18)

18. Mene ne ka koya daga labarin gwauruwar nan daga Najeriya da aka kwatanta a hoton?

18 Balaꞌoꞌi kamar annobar korona sun shafi bayin Jehobah da yawa. Alal misali, wata gwauruwa a Najeriya ta yi ƙarancin kuɗi da abinci sosai. Wata rana da safe, ꞌyarta ta tambaye ta me za su ci bayan sun gama cin abincinsu na ƙarshe. ꞌYarꞌuwar ta gaya wa ꞌyarta cewa ba su da abinci ko kuɗi, amma su yi koyi da gwauruwar Zarefat, wato su dafa abinci na ƙarshe da suke da shi su ci, saꞌan nan su dogara ga Jehobah. (1 Sar. 17:​8-16) Kafin ma su soma tunanin abin da za su ci da rana, ꞌyanꞌuwa da ke raba kayan agaji sun kawo musu abinci. Kuma abincin da aka ba su zai ishe su ci fiye da mako biyu. ꞌYarꞌuwar ta ce ba ta san cewa Jehobah yana sauraran abin da take gaya wa ꞌyarta ba. Hakika, idan muka dogara ga Jehobah, yanayoyi da ba mu yi zaton su ba za su iya sa mu yi kusa da Jehobah.​—1 Bit. 5:​6, 7.

19. Wane tsanantawa ne Ɗanꞌuwa Aleksey Yershov ya fuskanta?

19 A shekarun baya-bayan nan, ꞌyanꞌuwanmu sun fuskanci tsanantawa ba zato. Abin da ya sami Ɗanꞌuwa Aleksey Yershov da ke zama a ƙasar Rasha ke nan. A lokacin da Ɗanꞌuwa Yershov ya yi baftisma a 1994, Shaidun Jehobah suna da ꞌyanci a ƙasar Rasha. Amma bayan wasu shekaru, abubuwa sun canja a ƙasar Rasha. A 2020, hukumomi sun bincika gidan Ɗanꞌuwa Yershov, kuma sun kwace abubuwan da ya mallaka da yawa. Bayan wasu watanni, sun kai ƙararsa a kotu cewa ya yi laifi. Ashe wani mutum ne ya ɗauki bidiyon ɗanꞌuwan. Mutumin ya ce a yi nazari da shi, kuma sun yi fiye da shekara ɗaya suna nazari da ɗanꞌuwan. Bidiyon ne hukumomi suka yi amfani da shi wajen kai ƙarar ɗanꞌuwan kotu. Abin baƙin ciki. Wannan ba ƙaramin cin amana ba ne!

20. Me Ɗanꞌuwa Yershov ya yi don ya ƙarfafa dangantakarsa da Jehobah?

20 Shin tsanantawa da aka yi wa Ɗanꞌuwa Yershov ya kawo sakamako mai kyau? E. Dangantakarsa da Jehobah ta daɗa yin ƙarfi. Ya ce: “Yanzu ni da matata muna adduꞌa sosai fiye dā. Na gano cewa ba zan iya jimre yanayin da kaina ba, sai da taimakon Jehobah.” Ya ƙara da cewa: “Yin nazarin Littafi Mai Tsarki ya taimaka min in iya shawo kan sanyin gwiwa. Nakan yi tunani a kan misalan bayin Jehobah masu aminci a zamanin dā. Akwai labarai da yawa da aka rubuta a cikin Littafi Mai Tsarki da suka nuna muhimmancin kwantar da hankalinmu da kuma dogara ga Jehobah.”

21. Me muka koya a wannan talifin?

21 Mene ne muka koya a wannan talifin? A wasu lokuta, za mu iya fuskantar matsaloli ba zato. Duk da haka, a kullum Jehobah yana taimaka wa bayinsa idan suka dogara gare shi. Kamar yadda nassin da aka ɗauko jigon wannan talifin ya faɗa, “mai adalci yakan sami wahaloli da yawa, amma Yahweh yakan kuɓutar da shi daga cikinsu duka.” (Zab. 34:19) Don haka, maimakon mu mai da hankali ga matsalolin da muke fuskanta, bari mu mai da hankali ga yadda Jehobah yake taimaka wa bayinsa. Idan muka yi hakan, mu ma za mu zama da raꞌayin manzo Bulus wanda ya ce: “Zan iya yin kome ta wurin Almasihu wanda yake ƙarfafa ni.”​—Filib. 4:13.

WAƘA TA 38 Zai Ƙarfafa Ka

a Muna da tabbaci cewa Jehobah zai taimaki bayinsa idan sun fuskanci matsaloli ba zato. Ta yaya Jehobah ya taimaka wa bayinsa a zamanin dā? Ta yaya yake taimaka mana a yau? Tattauna misalan bayin Allah na zamanin dā, da na zamaninmu zai taimaka mana mu kasance da tabbaci cewa idan mun dogara ga Jehobah, mu ma zai taimaka mana.