Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 15

Mene ne Za Mu Iya Koya Daga Muꞌujizan Yesu?

Mene ne Za Mu Iya Koya Daga Muꞌujizan Yesu?

“Yesu ya bi dukan garuruwa da ƙauyuka, . . . yana kuma warkar da mutane daga kowane irin ciwo da rashin lafiya.”​—MAT. 9:35.

WAƘA TA 13 Mu Riƙa Bin Misalin Yesu

ABIN DA ZA A TATTAUNA a

1. Ka bayyana abin da ya faru saꞌad da Yesu ya yi muꞌujizarsa ta farko.

 KA ƊAUKA kana wajen saꞌad da Yesu ya soma hidimarsa a ƙarshen shekara ta 29. An gayyaci Yesu da mahaifiyarsa Maryamu da wasu mabiyansa zuwa ɗaurin aure a Kana, wani ƙauye da ke arewancin Nazarat inda Yesu ya yi girma. Maryamu abokiyar iyalin amarya da angon ne, kuma ba mamaki tana taimaka musu wajen kula da baƙi. Saꞌad da ake bikin auren, wata matsala ta taso da za ta iya kunyatar da iyalin da maꞌauratan, wato ruwan inabinsu ya ƙare. b Mai yiwuwa sun sami baƙi fiye da yadda suka yi tsammani. Nan da nan sai Maryamu ta je wurin ɗanta ta ce masa: “Ruwan inabinsu ya ƙāre.” (Yoh. 2:​1-3) Mene ne Yesu ya yi? Ya yi wani abin ban alꞌajibi, ya mai da ruwa ya zama “ruwan inabi.”​—Yoh. 2:​9, 10.

2-3. (a) Waɗanne irin muꞌujizai ne Yesu ya yi? (b) Ta yaya za mu amfana idan muka yi laꞌakari da muꞌujizan da Yesu ya yi?

2 Yesu ya yi muꞌujizai da yawa saꞌad da yake hidimarsa. c Ya yi amfani da ikonsa don ya taimaka wa dubban mutane. Alal misali, a wata muꞌujiza da ya yi, ya ciyar da maza 5,000, a wata kuma ya ciyar da maza 4,000. Idan aka haɗa da mata da yara, adadin zai fi 27,000. (Mat. 14:​15-21; 15:​32-38) A waɗannan lokutan ma, Yesu ya warkar da marasa lafiya da yawa. (Mat. 14:14; 15:​30, 31) Ku yi tunanin yadda mutanen suka yi mamaki saꞌad da Yesu ya warkar da su kuma ya ciyar da su!

3 Za mu iya koyan darussa da yawa daga muꞌujizai da Yesu ya yi. A talifin nan, za mu tattauna darussa masu ban ƙarfafa daga muꞌujizan nan. Bayan haka, za mu ga yadda za mu yi koyi da sauƙin kai da kuma tausayin da Yesu ya nuna saꞌad da yake yin muꞌujizan.

DARUSSA DA MUKA KOYA GAME DA JEHOBAH DA KUMA YESU

4. Muꞌujizan da Yesu ya yi suna koya mana darussa game da wa?

4 Muꞌujizan da Yesu ya yi suna koya mana darussa masu ban ƙarfafa game da shi da kuma Ubansa. Balle ma, Jehobah ne ya ba wa Yesu ikon yin waɗannan muꞌujizan. Ayyukan Manzanni 10:38 ta ce: “Allah ya shafe shi [Yesu] da Ruhu Mai Tsarki, da kuma iko. Domin Allah yana tare da shi, ya dinga zagayawa yana yin aikin alheri, yana warkar da waɗanda Shaiɗan ya matsa musu.” Ku tuna cewa Yesu ya yi koyi da halaye da tunanin Ubansa a cikin dukan abubuwan da ya yi da kuma abubuwan da ya ce, har ma a muꞌujizan da ya yi. (Yoh. 14:9) Ka ga wasu darussa guda uku da muka koya daga muꞌujizan da Yesu ya yi.

5. Mene ne ya motsa Yesu ya yi muꞌujizai? (Matiyu 20:​30-34)

5 Na farko, Yesu da Ubansa suna ƙaunar mu sosai. Saꞌad da Yesu yake duniya, ya nuna cewa yana ƙaunar mutane ta wajen yin amfani da ikonsa na yin muꞌujiza don ya taimaka wa waɗanda suke shan wahala. Akwai wani lokacin da wasu makafi guda biyu suka roƙi Yesu ya taimaka musu. (Karanta Matiyu 20:​30-34.) Ku lura cewa “saboda tausayi,” Yesu ya je ya warkar da su. Irin wannan tausayin ne ya motsa shi ya ciyar da mayunwata, kuma ya warkar da wani kuturu. (Mat. 15:32; Mar. 1:41) Muna da tabbacin cewa Jehobah Allahnmu mai “yawan jinƙai” da kuma Ɗansa suna ƙaunar mu sosai kuma suna baƙin ciki saboda wahalar da muke sha. (Luk. 1:78; 1 Bit. 5:7) Hakika, suna marmarin su cire matsalolin da ꞌyan Adam suke fuskanta.

6. Wane irin iko ne Allah ya ba wa Yesu?

6 Na biyu, Allah ya ba wa Yesu ikon magance matsalolin ꞌyan Adam. Yesu ya yi amfani da muꞌujizan da ya yi don ya nuna cewa zai iya magance dukan matsalolin da mu ba za mu iya magancewa ba. Alal misali, yana da ikon ꞌyantar da mu daga zunubi, wanda shi ne sanadiyyar matsalolin da ꞌyan Adam suke fuskanta, wato cututtuka da kuma mutuwa. (Mat. 9:​1-6; Rom. 5:​12, 18, 19) Muꞌujizan da ya yi sun nuna cewa zai iya warkar da kowane irin ciwo. Waɗanda suka mutu ma zai iya ta da su. (Mat. 4:23; Yoh. 11:​43, 44) Ƙari ga haka, yana da ikon kawar da guguwar iska mai ƙarfi da kuma fitar da mugayen ruhohi. (Mar. 4:​37-39; Luk. 8:2) Abin ban ƙarfafa ne sanin cewa Jehobah ya ba wa Ɗansa irin wannan ikon!

7-8. (a) Wane tabbaci ne muꞌujizan Yesu suke ba mu? (b) Wace muꞌujiza ce kake marmarin gani a sabuwar duniya?

7 Na uku, sun ba mu tabbaci cewa dukan alkawuran da Allah ya yi game da Mulkinsa za su faru da gaske. Muꞌujizai da Yesu ya yi saꞌad da yake duniya sun koya mana abubuwan ban alꞌajibi da zai yi saꞌad da ya soma sarauta. Ka ga abubuwan da za mu more a lokacin sarautar Yesu. Za mu kasance da ƙoshin lafiya domin zai cire dukan cututtuka da kuma naƙasar da mutane suke fama da su. (Isha. 33:24; 35:​5, 6; R. Yar. 21:​3, 4) Ba za mu taɓa rasa abincin da za mu ci ba ko mu yi fama da matsalolin da balaꞌoꞌi ke jawowa. (Isha. 25:6; Mar. 4:41) Za mu yi farin cikin marabtar ꞌyanꞌuwanmu da abokan kirki da za a tayar daga “kaburbura.” (Yoh. 5:​28, 29) Wace muꞌujiza ce kake marmarin gani a sabuwar duniya?

8 Saꞌad da Yesu yake yin muꞌujizai, ya nuna sauƙin kai da tausayi kuma waɗannan halaye ne da ya kamata mu yi koyi da su. Bari mu yi laꞌakari da misalai guda biyu. Za mu soma da abin da ya faru a ɗaurin auren da aka yi a Kana.

DARASI GAME DA SAUƘIN KAI

9. Me ya sa Yesu ya yi muꞌujizar da ya yi a wurin bikin ɗaurin aure? (Yohanna 2:​6-10)

9 Karanta Yohanna 2:​6-10. Da ruwan inabin ya kare a bikin ɗaurin auren, shin hakkin Yesu ne ya yi wani abu? Aꞌa. Babu inda aka yi annabci cewa Almasihu zai mai da ruwa ya zama ruwan inabi. Amma ka yi tunanin yadda za ka ji idan ruwan inabi ya kare a bikin ɗaurin aurenka. Ba shakka Yesu ya ji tausayin iyalin musamman ma amarya da angon kuma bai so wani abu ya faru da zai kunyatar da su ba. Don haka, ya yi muꞌujiza kamar yadda aka ambata a baya. Ya mai da ruwa da ya kai wajen lita 390 zuwa ruwan inabi mai kyau sosai. Wataƙila dalilin da ya sa ya tanada ruwan inabi da yawa shi ne, don a iya amfani da wanda ya rage a nan gaba, ko kuma a sayar da shi don maꞌauratan su yi amfani da kuɗin su biya bukatunsu. Hakika, waɗannan sabbin maꞌauratan sun yi farin ciki sosai!

Ku yi koyi da Yesu ta wajen ƙin yin takama da abubuwan da kuka cim ma a rayuwa (Ka duba sakin layi na 10-11) e

10. Waɗanne ƙarin bayani ne aka yi a littafin Yohanna sura 2? (Ka kuma duba hoton.)

10 Ku ga wasu ƙarin bayani masu muhimmanci da aka yi a littafin Yohanna sura 2. Kun lura cewa ba Yesu ne ya cika randunan da ruwa ba? Maimakon ya jawo hankalin mutane gare shi, ya gaya wa masu hidima su cika randunan da ruwa. (Aya 6, 7) Kuma bayan da ya mai da ruwan zuwa ruwan inabi, Yesu bai ɗibi ruwan inabin kuma ya je ya ba wa uban bikin da kansa ba. A maimakon haka, ya gaya wa masu hidimar su yi hakan. (Aya 8) Ƙari ga haka, Yesu bai zuba ruwan inabin a cikin kofi kuma ya ɗaga kofin a gaban baƙi ba yana cewa, ‘Ku ɗanɗana ruwan inabin da na yi yanzu!’

11. Mene ne za mu iya koya daga muꞌujizar da Yesu ya yi?

11 Mene ne za mu iya koya daga yadda Yesu ya mai da ruwa ya zama ruwan inabi? Ya koya mana darasi game da sauƙin kai. Yesu bai yi takama game da wannan muꞌujizar ba. Ban da haka ma, bai taɓa yin takama game da abubuwan da ya cim ma ba. A maimakon haka, ya kasance da sauƙin kai kuma ya miƙa yabo da ɗaukaka ga Ubansa a kowane lokaci. (Yoh. 5:​19, 30; 8:28) Idan muka yi koyi da Yesu kuma muka kasance da sauƙin kai, ba za mu riƙa yin takama game da abubuwan da muka cim ma ba. Ko da mene ne muka cim ma a hidimarmu ga Jehobah, kada mu yi takama da kanmu. Amma mu yi takama da Allahnmu mai alheri, wanda muke bauta wa. (Irm. 9:​23, 24) Mu miƙa masa dukan yabo da ɗaukaka. Balle ma, babu wani abu mai kyau da za mu iya yi in ba da taimakonsa ba.​—1 Kor. 1:​26-31.

12. A wace hanya ce kuma za mu iya yin koyi da sauƙin kan Yesu? Ka bayyana.

12 Bari mu yi laꞌakari da wata hanya da za mu iya yin koyi da sauƙin kan Yesu. A ce wani dattijo ya taimaka wa bawa mai hidima ya shirya jawabinsa na farko. Hakan ya sa ɗanꞌuwan nan da matashi ne ya ba da jawabi mai ban ƙarfafa kuma ꞌyanꞌuwa a ikilisiya sun ji daɗinsa sosai. Bayan taron, sai wani ya je ya sami dattijon ya ce masa, ‘Wani ya ba da jawabi mai daɗi sosai, ko ba haka ba?’ Shin dattijon zai ce: ‘Haka ne, amma na ɗauki lokaci sosai don in taimaka masa’? Ko dai zai kasance da sauƙin kai kuma ya ce: ‘Ƙwarai kuwa, jawabin ya yi daɗi. Ina alfahari da shi sosai’? Idan muna da sauƙin kai, ba za mu riƙa son karɓan yabo don abubuwa masu kyau da muka yi wa mutane ba. Za mu gamsu da sanin cewa Jehobah yana gani kuma yana daraja abubuwan da muke yi. (Ka kuma duba Matiyu 6:​2-4; Ibran. 13:16) Hakika, za mu faranta wa Jehobah rai idan muka yi koyi da sauƙin kan da Yesu yake da shi.​—1 Bit. 5:6.

DARASI GAME DA TAUSAYI

13. Me Yesu ya gani saꞌad da yake kusa da garin Nayin kuma me ya yi game da hakan? (Luka 7:​11-15)

13 Karanta Luka 7:​11-15. Ka lura da abin da ya faru saꞌad da Yesu ya yi kusan shekaru biyu yana hidima. Ya yi tafiya zuwa Nayin wanda bai da nisa daga Shunem. Kuma a wurin ne annabi Elisha ya tayar da ɗan wata mata shekaru 900 kafin lokacin. (2 Sar. 4:​32-37) Da ya kusan shiga ƙofar garin, sai ya ga wasu mutane suna fitar da gawa. Yanayin na da ban tausayi, domin wata gwauruwa ce ta rasa ɗanta guda ɗaya da take da shi. Amma ba matar ce kaɗai a wurin ba. Akwai taron jamaꞌa tare da ita. Yesu ya dakatar da mutanen kuma ya yi ma wannan matar wani abin ban alꞌajibi. Ya ta da ɗanta da ya mutu. Wannan ɗaya ne daga cikin mutane uku da Yesu ya ta da wanda aka ambata a cikin littafin Linjila.

Ku yi koyi da Yesu ta wajen tausaya ma waɗanda wani nasu ya rasu (Ka duba sakin layi na 14-16)

14. Waɗanne bayanai masu muhimmanci ne aka rubuta a Luka sura 7? (Ka kuma duba hoton.)

14 Ku ga wasu bayanai masu muhimmanci da aka rubuta a littafin Luka sura 7. Kun lura cewa Yesu ya “ga” mahaifiyar da ke baƙin ciki, saꞌan nan ya “ji tausayinta”? (Aya 13) Mai yiwuwa Yesu ya gan ta tana kuka yayin da take tafiya kusa da gawar ɗanta, kuma hakan ya sa ya tausaya mata sosai. Yesu bai ji tausayin wannan matar kawai ba, amma ya nuna yadda ya tausaya mata. Ya yi mata magana a hanya mai ban ƙarfafa kuma ya ce: “Kada ki yi kuka!” Sai ya yi wani abu don ya taimaka mata. Ya ta da ɗanta daga mutuwa kuma “ya miƙa shi ga mamarsa.”​—Aya 14, 15.

15. Mene ne za mu iya koya daga muꞌujizar Yesu?

15 Me za mu iya koya daga yadda Yesu ya yi muꞌujiza kuma ya ta da ɗan wannan gwauruwar? Hakika ba za mu iya ta da matattu kamar yadda Yesu ya yi ba. Amma kamar Yesu, idan muna lura da waɗanda wani nasu ya rasu, za mu iya tausaya musu. Za mu iya nuna cewa muna tausaya musu ta furucinmu, da yin abubuwan da za su taimaka da taꞌazantar da su. d (K. Mag. 17:17; 2 Kor. 1:​3, 4; 1 Bit. 3:8) Ko da abin da za mu yi ƙarami ne, zai iya ƙarfafa su kuma ya taꞌazantar da su sosai.

16. Kamar yadda aka kwatanta a hoton, mene ne ka koya daga abin da ya faru da wata mahaifiya da ta rasa ꞌyarta?

16 Ka lura da wannan labarin. A ꞌyan shekarun da suka shige, wata ꞌyarꞌuwa ta lura cewa wata mahaifiya a Majamiꞌar Mulki tana kuka yayin da ake rera waƙa a taro. Waƙar tana magana ne game da tashin matattu kuma bai jima ba da mahaifiyar ta rasa ꞌyarta. Da yake ꞌyarꞌuwar ta san da haka, nan da nan ta je wajen mahaifiyar, ta rungume ta kuma suka rera waƙar tare. Daga baya mahaifiyar ta ce: ‘Na ga yadda ꞌyanꞌuwa maza da mata suka nuna mini ƙauna sosai.’ Ta yi farin ciki cewa ta je taro. Mahaifiyar ta ce: ‘A Majamiꞌar Mulki ne muke samun taimako.’ Za mu iya kasance da tabbaci cewa Jehobah yana ganin abubuwan da muke yi don mu tausaya ma waɗanda suka “fid da zuciya” sanadiyyar rasuwar da aka musu, kuma yana daraja hakan komin ƙanƙantar su.​—Zab. 34:18.

NAZARI MAI BAN ƘARFAFA DA ZA KA IYA YI

17. Me muꞌujizan Yesu suka koya mana?

17 Idan muka yi nazari game da muꞌujizai da Yesu ya yi, za mu samu ƙarfafa sosai. Labaran suna koya mana cewa Jehobah da Yesu suna ƙaunar mu sosai kuma Yesu yana da ikon warware dukan matsalolin ꞌyan Adam. Ƙari ga haka, suna koya mana cewa za mu iya gaskata alkawuran da za su cika nan ba da daɗewa ba saꞌad da Mulkin Allah ya soma sarauta a duniya. Yayin da muke bincika waɗannan labaran, za mu iya yin bimbini a kan yadda za mu yi koyi da halayen Yesu. Kana iya yin bincike game da wasu muꞌujizan Yesu saꞌad da kake nazari ko kuma a ibadarku ta iyali. Ka nemi darussan da za ka iya koya kuma ka gaya wa wasu game da abubuwan da ka koya. Ba shakka, za ka ji daɗin tattaunawar da za ku yi.​—Rom. 1:​11, 12.

18. Me za mu tattauna a talifi na gaba?

18 Da Yesu ya kusan kammala hidimarsa a duniya, ya tayar da wani daga mutuwa kuma mutumin ne na ƙarshe da ya tayar. Abokinsa ne ya ta da kuma ya yi hakan a yanayin da ya yi dabam da na sauran. Waɗanne darussa ne za mu iya koya daga wannan muꞌujizar? Ta yaya za mu ƙarfafa begenmu game da tashin matattu? Talifi na gaba zai amsa waɗannan tambayoyin.

WAƘA TA 20 Ka Ba da Ɗanka Mai Daraja

a Muna jin daɗin karanta game da muꞌujizan da Yesu ya yi. Alal misali, ya dakatar da guguwa mai ƙarfi, ya warkar da marasa lafiya, har ya ta da matattu. An rubuta waɗannan labaran a Littafi Mai Tsarki ba don su nishaɗantar da mu ba amma don su koya mana darussa. Yayin da muke bincika su, za mu koyi darussa masu ban ƙarfafa game da Jehobah da Yesu da kuma halaye masu kyau da ya kamata mu kasance da su.

b Wani masanin Littafi Mai Tsarki ya ce: “A zamanin dā, mutane ba sa wasa da nuna karamci kuma mutum yana bukatar ya tanada wa baƙinsa fiye da abin da suke bukata, musamman ma a bikin ɗaurin aure.”

c Littafin Linjila yana ɗauke da muꞌujizai fiye da 30 da Yesu ya yi. Yesu ya yi ƙarin wasu muꞌujizai da yawa, amma Littafi Mai Tsarki ya ambace su tare maimakon ɗaya bayan ɗaya. Akwai wani lokacin da “dukan mutanen garin” suka zo wurin sa kuma “ya warkar da marasa lafiya da yawa.”​—Mar. 1:​32-34.

d Ka ga wasu shawarwari game da abin da za ka iya cewa ko abin da za ka iya yi don ka ƙarfafa waɗanda wani nasu ya rasu a talifin nan, “Yadda Za a Ta’azantar da Masu Makoki,” da ke Hasumiyar Tsaro ta 3, 2016.

e BAYANI A KAN HOTUNA: Yesu yana tsaye a baya, amarya da angon da baƙinsu kuma suna jin daɗin ruwan inabin da ya tanadar.