Shawara A Kan Yin Nazari
Kana amfana daga bayanan da aka yi a kan Nassosi da ke Littafin Bincike Don Shaidun Jehobah?
Bayanan nan za su taimaka maka ka daɗa fahimtar Kalmar Allah. Suna nuna yadda abubuwa suke saꞌad da labarin da aka rubuta a Littafi Mai Tsarki yake faruwa, da dalilin da ya sa aka rubuta labarin, da kuma wanda labarin ya shafa. Ƙari ga haka, suna iya nuna maꞌanar kalmomi.
Idan kana karanta Littafi Mai Tsarki daga Watchtower LABURARE NA INTANE da manhajar JW Library, za ka iya ganin bayanan da ke Littafin Bincike Don Shaidun Jehobah kai tsaye. Za ka iya ganin bayanan idan ka danna alamar nazari da ke cikin kowane juyin Littafi Mai Tsarki da ke wurin.
Idan kana karanta bayanan, ka mai da hankali ga shekarar da aka wallafa su. Littattafai na kwana-kwanan nan sukan kasance a sama. Littattafan da ke ƙasa kuma tsofaffin littattafai ne da mai yiwuwa suna ɗauke da bayanan da an riga an yi musu gyarar fuska.
Ba ka bukatar ka sauƙar da Littafin Bincike Don Shaidun Jehobah a Watchtower LABURARE NA INTANE.
Don ka ga bayanan a manhajar JW Library, ka sauƙar da Littafin Bincike Don Shaidun Jehobah kuma idan an sake ƙara bayanai a littafin, ka sake sauƙar da shi. Za ka iya yin hakan idan ka danna alamar nazari da ke kowanne surar Littafi Mai Tsarki.