Amsoshin Tambayoyin Masu Karatu
Me ya sa mutumin da aka kira “Aboki” ya ce zai “ɓata” gādonsa idan ya auri Rut? (Rut 4:1, 6)
A zamanin dā, idan mutum ya mutu kuma ba shi da ꞌyaꞌya, ga wasu tambayoyin da sukan taso: Me zai faru da gonakinsa? Sunan iyalinsa zai ɓace har abada ke nan? Dokar Musa ta ba da amsar tambayoyin nan.
Mene ne zai faru da gonar mutumin da ya mutu ko ya talauce kuma ya sayar da gonarsa? Ɗanꞌuwansa ko danginsa na kusa zai iya fanshi gonar. Hakan zai sa gonar ta ci gaba da zama a iyalinsa.—L. Fir. 25:23-28; L. Ƙid. 27:8-11.
Ta yaya hakan zai sa ba za a manta da sunan mutumin da ya mutu ba? Matar mutumin da ya mutu takan auri ɗanꞌuwansa domin kada sunansa ya ɓace. Abin da ya faru da Rut ke nan. Mutumin zai auri matar ɗanꞌuwansa domin ta haifi yaro, amma yaron zai amsa sunan ɗanꞌuwansa da ya mutu ne kuma ya gāji gādonsa. Wannan shirin da aka yi ya taimaka wa gwauraye.—M. Sha. 25:5-7; Mat. 22:23-28.
Ka yi laꞌakari da misalin Naꞌomi. Ta auri wani mutum mai suna Elimelek. Da maigidanta da yaransu biyu suka mutu, ba namijin da zai kula da ita kuma. (Rut 1:1-5) Bayan da Naꞌomi ta koma Yahudiya tare da surkuwarta Rut, ta ce wa Rut ta gaya wa Boaz ya sayi gonarsu. Shi dangin Elimelek ne na kusa. (Rut 2:1, 19, 20; 3:1-4) Amma Boaz ya san cewa akwai wani a dangin da ya fi shi kusa da Elimelek da Littafi Mai Tsarki ya kira “Aboki.” Don haka, shi ne mutum na farko da zai iya fanshi gonar.—Rut 3:9, 12, 13.
Da farko, mutumin ya so ya taimaka. (Rut 4:1-4) Ko da yake hakan zai sa ya kashe kuɗi, mutumin ya san cewa Naꞌomi ba za ta iya haifi yaron da zai gāji gonar Elimelek ba. Don haka, gonar za ta zama gonarsa kuma hakan zai amfane shi.
Amma mutumin ya canja raꞌayinsa da ya gano cewa hakan zai sa ya auri Rut. Ya ce: “In haka ne ba zan iya fanshi gonar ba. Gama in na yi haka, zan ɓata gādon da zan ba ’ya’yana.” (Rut 4:5, 6) Me ya sa ya canja raꞌayinsa?
Idan mutumin ko wani mutum dabam ya auri Rut kuma ta haifi yaro, yaron zai gāji gonar Elimelek. Ta yaya hakan zai “ɓata gādon” mutumin? Littafi Mai Tsarki bai faɗa ba, amma ga wasu hanyoyi da hakan za iya faruwa.
Da farko, zai zama kamar ya kashe kuɗinsa a banza ne, da yake gonar ba za ta zama tasa ba. Yaron Rut ne zai gāji gonar.
Na biyu, zai zama hakkinsa ya kula da Rut da Naomi kuma ya ciyar da su.
Na uku, idan Rut ta sake haifa masa ꞌyaꞌya, yaran za su raba gādonsa da sauran yaransa.
Na huɗu, idan mutumin ba shi da yara, duk yaron da Rut za ta haifa zai gāji gonarsa da na Elimelek. Don haka, yaron da ke amsa sunan Elimelek ne zai gāji gonarsa. Mutumin bai so ya ɓata gādonsa don ya taimaka wa Naꞌomi ba. Ya yarda ya bar wa Boaz, wanda shi ne dangi na kusa bayan shi, ya ɗauki wannan hakkin. Boaz ya yarda yi hakan ne, domin “a iya haifi yaro wanda zai gāji abin da” Elimelek yake da shi.—Rut 4:10.
Mutumin ya fi damuwa da sunansa da gādonsa tsabar son kai. Ko da yake ya yi ƙoƙari ya kāre sunansa, abin da ya yi ya sa mutane ba su san sunansa ba har wa yau. Ƙari ga haka, ya rasa babban gatan da Boaz ya samu. Boaz ya zama ɗaya daga cikin kakannin Almasihu, wato Yesu Kristi. Hakan abin baƙin ciki ne ga wannan mutumin da ya ƙi ya taimaka ma wanda yake cikin bukata!—Mat. 1:5; Luk. 3:23, 32.