TALIFIN NAZARI NA 13
Ku Koyar da Yaranku ta Wajen Halittu
“Wane ne ya halicci waɗannan abubuwa?”—ISHA. 40:26.
WAƘA TA 11 Halittun Allah Suna Yabon Sa
ABIN DA ZA A TATTAUNA a
1. Mene ne iyaye suke so su yi wa yaransu?
IYAYE, mun san cewa kuna so ku taimaka wa yaranku su san Jehobah kuma su ƙaunace shi. Amma ba a iya ganin Allah. Don haka, ta yaya za ku taimaka wa yaranku su san halayensa da kyau kuma su yi kusa da shi?—Yak. 4:8.
2. Ta yaya iyaye za su iya koya wa yaransu game da halayen Jehobah?
2 Wata hanya ta musamman da iyaye za su iya taimaka wa yaransu su yi kusa da Jehobah ita ce ta yin nazarin Littafi Mai Tsarki tare da su. (2 Tim. 3:14-17) Amma Littafi Mai Tsarki ya sake nuna wata hanya da yara za su iya koya game da Jehobah. A littafin Karin Magana, wani mahaifi ya gaya wa ɗansa kada ya manta da halayen Jehobah waɗanda zai iya gani ta halittunsa. (K. Mag. 3:19-21) Za mu tattauna wasu hanyoyin da iyaye za su iya amfani da halittu don su koya wa yaransu game da halayen Jehobah.
TA YAYA ZA KU KOYAR DA YARANKU TA WAJEN HALITTU?
3. Wane taimako ne ya kamata iyaye su yi wa yaransu?
3 Littafi Mai Tsarki ya ce “halin Allahntaka na Allah da kuma ikonsa na har abada ba abubuwan da aka iya gani da ido ba ne.” Amma ana “gane su bisa ga abubuwan da aka halitta.” (Rom. 1:20) Iyaye, babu shakka kuna jin daɗin zuwa shaƙatawa tare da yaranku. Ku yi amfani da waɗannan lokutan don ku taimaka wa yaranku su ga cewa akwai alaƙa tsakanin “abubuwan da aka halitta” da halayen Jehobah. Bari mu ga yadda Yesu ya kafa wa iyaye misali mai kyau a wannan batun.
4. Ta yaya Yesu ya yi amfani da halittu don ya koyar da almajiransa? (Luka 12:24, 27-30)
4 Ku lura da yadda Yesu ya yi amfani da halittu don ya yi koyarwa. Akwai lokacin da ya gaya wa mabiyansa su lura da tsuntsaye da kuma fulawoyi. (Karanta Luka 12:24, 27-30.) Yesu zai iya amfani da wata dabba ko shuka dabam. Amma ya zaɓi tsuntsu da kuma fulawa domin almajiransa sun san abubuwan nan sosai. Mai yiwuwa almajiransa sun sha ganin tsuntsayen nan suna firiya kuma sun sha ganin fulawoyin nan a gonaki. Ka yi tunanin yadda Yesu ya nuna abubuwan nan saꞌad da yake magana. Me ya yi bayan ya ambata su? Ya koya wa almajiransa darasi mai kyau game da yadda Ubansu na sama yake da karamci da kuma alheri. Wato Jehobah zai ciyar da su kuma ya tanada musu kayan sakawa kamar yadda yake yi wa tsuntsaye da fulawoyin da ke gonaki.
5. Waɗanne halittu ne iyaye za su iya amfani da su don su koya wa yaransu game da Jehobah?
5 Iyaye, ta yaya za ku yi koyi da yadda Yesu yake koyarwa? Za ku iya gaya wa yaranku game da wata dabba ko shukar da kuka fi so. Yayin da kuke hakan, ku gaya wa yaranku game da abin da dabbar ko kuma shukar ta koya muku game da Jehobah. Sai ku ce wa yaronku ya gaya muku dabba ko shukar da ya fi so. Mai yiwuwa zai saurare ku da kyau idan kuka yi amfani da halittar da ya fi so don ku koya masa game da Jehobah.
6. Me za mu iya koya daga mahaifiyar Christopher?
6 Shin iyaye suna bukatar su ɗauki lokaci da yawa don su yi bincike game da abin da wata dabba ko shuka take koya mana game da Jehobah? Ba lalle ba. Yesu bai yi dogon bayani game da yadda tsuntsaye suke cin abinci da kuma yadda fulawoyin suke girma ba. Gaskiya ne cewa yaronka zai ji daɗi idan ka yi masa bayani mai zurfi game da halittun Jehobah. Amma a wasu lokuta, bayani mai sauƙi ko tambaya za su iya taimaka ma yaronka ya fahimci darasin. Ka yi laꞌakari da abin da wani ɗanꞌuwa mai suna Christopher ya faɗa game da abubuwan da ya koya saꞌad da yake ƙarami, ya ce: “Mamata takan yi gajeren bayani don ta taimaka mana mu daraja halittun da muke gani. Alal misali, idan muna kusa da tuddai, za ta iya cewa: ‘Ku ga yadda tuddan nan suke da girma da kuma kyau! Jehobah Allah ne mai ban alꞌajabi, ko ba haka ba?’ Ko kuma idan muna kusa da teku, za ta iya cewa: ‘Ku ga yadda rakuman ruwan suke da ƙarfi! Allah yana da iko sosai, ko ba haka ba?’ ” Christopher ya ce: “Waɗannan gajerun bayanan sun taimaka mana mu yi tunani sosai.”
7. Ta yaya za ku taimaka wa yaranku su yi tunani game da halittu?
7 Yayin da yaranku suke girma, za ku iya taimaka musu su soma tunani game da halittu kuma su koya game da Jehobah. Za ku iya magana game da ɗaya daga cikin abubuwan da Jehobah ya halitta, sai ku tambayi yaranku cewa, “Mene ne hakan ya koya muku game da Jehobah?” Za ku yi mamakin jin abin da yaranku za su faɗa game da halittun.—Mat. 21:16.
A WANE LOKACI NE ZA KU IYA AMFANI DA HALITTU KU KOYAR DA YARANKU?
8. Wane zarafi ne iyaye Israꞌilawa suke da shi saꞌad da suke “tafiya”?
8 An gaya wa iyaye Israꞌilawa su koyar da yaransu game da dokokin Allah saꞌad da suke “tafiya.” (M. Sha. 11:19) Akwai hanyoyi a dukan faɗin ƙasar Israꞌila. Mutane suna iya ganin dabbobi dabam-dabam da tsuntsaye da kuma fulawoyi. Saꞌad da iyalan Israꞌilawa suke tafiya a kan hanya, iyaye a cikinsu suna iya tattaunawa da yaransu game da abubuwan da Jehobah ya halitta. Iyaye, ba mamaki ku ma kuna da zarafin da za ku iya amfani da halittu ku koya wa yaranku game da Jehobah. Ku yi laꞌakari da yadda wasu iyaye suka yi hakan.
9. Mene ne za ka iya koya daga Punitha da Katya?
9 Wata mahaifiya mai suna Punitha da take zama a wani dabban birni da ke ƙasar Indiya ta ce: “Saꞌad da muke ziyarar iyalinmu, muna amfani da zarafin don mu taimaka ma yaranmu su ga yadda halittun Jehobah suke da ban alꞌajabi. Ina ganin yarana sun fi koya game da halittu a duk lokacin da suka bar babban birnin da muke zama.” Iyaye, yaranku ba za su manta da lokacin da kuka je wurin shaƙatawa tare ba. Wata ꞌyarꞌuwa mai suna Katya da ke zama a Moldova ta ce: “Abin da na fi tunawa game da yarantakata shi ne lokacin da ni da iyayena muka je ƙauye. Ina gode musu domin tun ina ƙarama, sun koya min yadda zan lura da halittun Jehobah kuma in koyi halayensa daga hakan.”
10. Mene ne iyaye za su yi idan yana musu wuya su je ƙauye? (Ka duba akwatin nan “ Abin da Zai Taimaka wa Iyaye.”)
10 Idan ba za ku iya zuwa ƙauye kuma ba fa? Wani ɗanꞌuwa mai suna Amol da shi ma yake zama a Indiya ya ce: “A inda muke, iyaye suna aiki na dogon lokaci kuma tafiya zuwa ƙauye yana da tsada sosai. Amma za ku iya lura da abubuwan da Jehobah ya halitta kuma ku tattauna a kai a wurin shaƙatawa ko a saman gidanku.” Idan kun lura da kyau, za ku ga halittun Jehobah da ke kusa da ku da za ku iya nuna wa yaranku. (Zab. 104:24) Za ku iya ganin tsuntsaye, ƙwari, shuke-shuke da dai sauransu. Wata ꞌyarꞌuwa mai suna Karina daga Jamus ta ce: “Mahaifiyata tana son fulawoyi. Don haka, da nake ƙarama, takan nuna min fulawoyi saꞌad da muke tafiya.” Iyaye, za ku iya amfani da bidiyoyi da yawa da littattafan da ƙungiyarmu ta wallafa game da halittu don ku koyar da yaranku. Ko da a ina ne kuke zama, za ku iya taimaka wa yaranku su lura da abubuwan da Jehobah ya halitta. A yanzu, bari mu yi laꞌakari da wasu halayen Jehobah da za ku iya taimaka wa yaranku su mai da hankali a kai.
ANA IYA GANE HALAYEN ALLAH DAGA ABUBUWAN DA YA HALITTA
11. Ta yaya iyaye za su taimaka wa yaransu su fahimci yadda Jehobah yake ƙaunar mu?
11 Don ku taimaka wa yaranku su fahimci yadda Jehobah yake da ƙauna, ku nuna musu yadda wasu dabbobi suke kula da yaransu. (Mat. 23:37) Za ku kuma iya bayyana abubuwa dabam-dabam da Allah ya halitta da muke jin daɗinsu. ꞌYarꞌuwa Karina da aka ambata a baya ta ce: “A duk lokacin da ni da mahaifiyata muka fita waje, mahaifiyata takan gaya mini in lura da yadda kowane fulawa ya fita dabam da kuma yadda kyaunsa ya nuna ƙaunar Allah. Shekaru bayan haka, ina kan lura da yadda kowane fulawa ya yi dabam, da yadda aka tsara shi, da kuma kalarsa. Har yanzu suna nuna mini yadda Allah yake ƙaunar mu.”
12. Ta yaya iyaye za su iya taimaka wa yaransu su fahimci hikimar Allah? (Zabura 139:14) (Ka kuma duba hoton.)
12 Ku taimaka wa yaranku su fahimci hikimar Allah. Jehobah yana da hikima sosai fiye da mu. (Rom. 11:33) Alal misali, za ku iya gaya wa yaranku yadda ruwa yake tashi sama kuma ya zama hadari, da kuma yadda hadarin yake kai ruwan wurare dabam-dabam cikin sauƙi. (Ayu. 38:36, 37) Za ku kuma iya bayyana hanya mai ban alꞌajabi da Allah ya tsara jikin ꞌyan Adam. (Karanta Zabura 139:14.) Ku yi laꞌakari da yadda wani mahaifi mai suna Vladimir ya yi hakan. Ya ce: “Wata rana ɗanmu ya faɗi daga kekensa kuma ya ji ciwo. Bayan kwanaki kaɗan, sai ciwon ya warke. Ni da matata mun bayyana masa cewa Jehobah ya halicci jikinmu yadda zai iya warkewa da kansa. Mun gaya masa cewa ba haka abubuwan da ꞌyan Adam suka ƙera suke ba. Alal misali, mota ba ta iya gyara kanta bayan ta yi hatsari. Abin da ya faru ya taimaka wa ɗanmu ya fahimci hikimar Allah.”
13. Ta yaya iyaye za su iya taimaka wa yaransu su fahimci ikon Allah? (Ishaya 40:26)
13 Jehobah ya gaya mana mu ta da idanunmu sama kuma mu yi tunanin yadda ikon da yake da shi ya sa taurari suka kasance yadda suke. (Karanta Ishaya 40:26.) Za ku iya gaya wa ꞌyaꞌyanku su dubi sama kuma su yi tunani a kan abin da suka gani. Ku lura da abin da wata ꞌyarꞌuwa mai suna Tingting ta tuna game da lokacin da take ƙarama. Ta ce: “Akwai lokacin da ni da mamata muka fita shaƙatawa kuma muka ɗaga ido muka ga taurari da yawa domin ba a birni muke ba, inda akwai hasken lantarki a koꞌina. A lokacin, ina ganin ba zan riƙe amincina ga Jehobah ba domin ꞌyan ajinmu sun yi ƙoƙari su hana ni yin biyayya ga Allah. Mahaifiyata ta ƙarfafa ni in yi tunani a kan ikon da Jehobah ya yi amfani da shi ya halicci dukan taurarin kuma in tuna cewa zai iya amfani da ikon nan ya taimaka min in jimre duk wata jarabawar da zan fuskanta. Lura da halittun Jehobah da muka yi a ranar ya sa na daɗa koya game da Jehobah kuma na ƙudiri niyyar ci gaba da bauta masa.”
14. Ta yaya iyaye za su iya amfani da halittu don su taimaka wa yaransu su san cewa Jehobah Allah ne mai farin ciki?
14 Halittun Jehobah suna nuna mana cewa shi Allah ne mai farin ciki kuma yana so mu ma mu yi farin ciki. ꞌYan kimiyya sun gano cewa dabbobi da yawa suna wasa har ma da tsuntsaye da kuma kifaye. (Ayu. 40:20) Shin yaranku sun taɓa yin dariya da suka ga yadda dabbobi suke wasa? Mai yiwuwa sun taɓa ganin yaran ƙarnuka suna kokawa da juna. Idan kuka ga yaranku sun yi dariya domin sun ga yadda dabbobi suke wasa, ku tuna musu cewa muna bauta wa Allah mai farin ciki.—1 Tim. 1:11.
KU JI DAƊIN HALITTUN JEHOBAH A MATSAYIN IYALI
15. Mene ne zai taimaka wa iyaye su iya sanin abin da ke damun yaransu? (Karin Magana 20:5) (Ka kuma duba hoton.)
15 A wasu lokuta, zai iya yi wa iyaye wuya su sa yaransu su gaya musu matsalolin da suke fuskanta. Idan yanayin da kuke fuskanta ke nan, kuna bukatar ku yi amfani da hikima don ku san matsalolin da suke fuskanta. (Karanta Karin Magana 20:5.) Yana yi ma wasu iyaye sauƙi su yi hakan yayin da suke lura da halittun Jehobah tare da yaransu. Me ya sa? Dalili ɗaya shi ne, babu abubuwan da za su iya raba hankalinsu da yawa. Wani mahaifi mai suna Masahiko daga ƙasar Taiwan ya faɗi wani dalilin. Ya ce: “A duk lokacin da muka je shaƙatawa da yaranmu kamar hawan dutse ko kuma zagayawa kusa da teku, sukan saki jiki sosai. Hakan yana sa ya yi mana sauƙi mu san abin da yake zuciyarsu.” Katya da muka ambata ɗazu ta ce: “Mahaifiyata takan kai ni wurin shaƙatawa bayan na tashi daga makaranta. A wurin, nakan saki jiki kuma in gaya mata abin da ya faru da ni a makaranta da abubuwan da suke damu na.”
16. Ta yaya iyalai za su shaƙata kuma su ji daɗi saꞌad da suke lura da abubuwan da Jehobah ya halitta?
16 Yayin da iyalai suke lura da halittun Jehobah, za su iya saki jiki da juna kuma su shaƙata. Hakan zai iya taimaka musu su daɗa ƙaunar juna. Littafi Mai Tsarki ya ce akwai “lokacin dariya” da “lokacin farin ciki” ko lokacin wasa. (M. Wa. 3:1, 4) Jehobah ya halicci wurare masu kyau a duniya inda za mu riƙa shaƙatawa. Iyalai da yawa suna jin daɗin zuwa wurin shaƙatawa ko hawan dutse ko kuma zuwa baƙin teku tare. Wasu yara suna jin daɗin yin guje-guje a wurin shaƙatawa ko kallon dabbobi ko kuma yin iyo a kogi. Muna da zarafi da yawa na jin daɗin abubuwan da Jehobah ya halitta.
17. Me ya sa ya dace iyaye su taimaka wa yaransu su so halittun Jehobah?
17 A sabuwar duniya, iyaye da yaransu za su iya jin daɗin halittun Jehobah fiye da yadda suke yi a yanzu. A lokacin, ba za mu ji tsoron dabbobi ba kuma su ma ba za su ji tsoron mu kamar yadda suke ji a yanzu ba. (Isha. 11:6-9) Za mu ci gaba da jin daɗin abubuwan da Jehobah ya halitta har abada. (Zab. 22:26) Amma iyaye, kada ku jira sai sabuwar duniya ta zo kafin ku taimaka wa yaranku su ji daɗin abubuwan da Jehobah ya halitta. Yayin da kuke yin amfani da halittu don ku koya wa yaranku game da Jehobah, yaranku za su yarda da abin da Sarki Dauda ya faɗa, wato: “Ya Ubangiji, . . . babu wani aikin da za a gwada da naka.”—Zab. 86:8.
WAƘA TA 134 Yara Amana Ne Daga Allah
a ꞌYanꞌuwa da yawa suna yawan tuna lokacin da suka ji daɗin kallon halittu tare da iyayensu. Ba su manta da yadda iyayensu suka yi amfani da halittun nan don su koya musu game da halayen Jehobah ba. Ta yaya za ka yi amfani da halittu don ka koya wa yaranka game da halayen Jehobah? Wannan talifin zai amsa tambayar nan.