Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 10

Me Ya Sa Ya Kamata Ka Yi Baftisma?

Me Ya Sa Ya Kamata Ka Yi Baftisma?

“A yi wa kowannenku baftisma.”​—A. M. 2:38.

WAƘA TA 34 Mu Zama Masu Aminci

ABIN DA ZA A TATTAUNA a

1-2. Mene ne yake faruwa saꞌad da mutane suke yin baftisma, kuma me ya kamata ka yi tunani a kai?

 KA TAƁA ganin waɗanda za su yi baftisma? Kafin su yi baftisma, ka ga yadda suka kasance da tabbaci kuma suka amsa tambayoyi guda biyu da babbar murya. Ka ga yadda iyalai da abokansu suke farin ciki sosai. Da waɗanda aka yi wa baftisma suka fito daga cikin ruwa, ka ji yadda mutane suka yi tafi kuma ka ga farin cikin da waɗannan ɗaliban suke yi. Kowane mako, aƙalla dubban mutane suna ɗaukan wannan matakin, wato suna alkawarin bauta wa Jehobah kuma su yi baftisma a matsayin Shaidun Jehobah.

2 Kai kuma fa? Idan kana tunanin yin baftisma, ka san cewa ka fita dabam daga waɗanda suke cikin muguwar duniyar nan domin kana “neman sanin Allah.” (Zab. 14:​1, 2) Ko da kai matashi ne ko ka tsufa, an shirya talifin nan ne musamman domin kai. Amma mu da muka riga muka yi baftisma ma, muna so mu ci gaba da bauta wa Jehobah har abada. Don haka, a cikin dalilai da yawa da suke sa mu bauta wa Jehobah, bari mu tattauna guda uku.

KANA ƘAUNAR GASKIYA DA ADALCI

Shaiɗan ya yi dubban shekaru yana ɓata sunan Jehobah kuma har yanzu yana yin hakan (Ka duba sakin layi na 3-4)

3. Me ya sa bayin Jehobah suke ƙaunar gaskiya da adalci? (Zabura 119:​128, 163)

3 Jehobah ya umurci bayinsa su “ƙaunaci gaskiya.” (Zak. 8:19) Yesu ya ƙarfafa mabiyansa su biɗi adalci. (Mat. 5:6) Hakan yana nufin cewa mutum yana bukatar ya so yin abin da yake da kyau kuma yake daidai a idon Allah. Shin kana son gaskiya da kuma adalci? Muna da tabbacin cewa kana ƙaunar gaskiya da adalci kuma ka tsani ƙarya da mugunta da dukan abubuwa marasa kyau. (Karanta Zabura 119:​128, 163.) Wanda yake ƙarya yana yin koyi da Shaiɗan ne, mai mulkin duniyar nan. (Yoh. 8:44; 12:31) Ɗaya daga cikin abubuwan da Shaiɗan yake so ya yi shi ne ya ɓata sunan Allah. Tun daga abin da ya faru a lambun Adnin, Shaiɗan ya yi ta yaɗa ƙararrayi game da Allahnmu. Yana ƙoƙari ya sa mutane su ga kamar Jehobah mai son kai ne kuma Shugaba ne marar gaskiya da ba ya son mutane su ji daɗin rayuwa. (Far. 3:​1, 4, 5) Ƙararrayin da Shaiɗan yake yaɗawa sun lalata raꞌayin mutane da zukatansu game da Jehobah. Idan mutane suka ƙi su “ƙaunaci gaskiya,” Shaiɗan zai iya sa su yi mugayen abubuwa.​—Rom. 1:​25-31.

4. Ta yaya Jehobah ya nuna cewa shi “Allah na gaskiya” ne? (Ka kuma duba hoton.)

4 Jehobah “Allah na gaskiya” ne, kuma yana koya wa waɗanda suke ƙaunar sa wannan gaskiyar. (Zab. 31:​5, Tsohuwar Hausa a Sauƙaƙe) Ta haka, yana taimaka musu don kada Shaiɗan ya yi amfani da ƙararrayinsa ya yaudare su. Ƙari ga haka, Jehobah yana koya wa bayinsa su zama masu faɗin gaskiya da kuma adalci. Hakan yana kāre mutuncinsu kuma yana ba su kwanciyar hankali. (K. Mag. 13:​5, 6) Shin abin da ya faru da kai ke nan yayin da kake nazarin Littafi Mai Tsarki? Ka koyi cewa umurnan Jehobah don amfanin ka ne da kuma dukan ꞌyan Adam. (Zab. 77:13) Don haka, kana so ka yi abin da yake daidai a idon Allah. (Mat. 6:33) Kana so ka koya wa mutane gaskiya don su san cewa abubuwan da Shaiɗan yake faɗa game da Allahnmu Jehobah ba gaskiya ba ne. Ta yaya za ka iya yin hakan?

5. Ta yaya za ka goyi bayan gaskiya da kuma adalci?

5 Kai ma za ka iya zaɓa ka bauta wa Jehobah kuma ka ce: “Ba zan yarda da ƙararrayin Shaiɗan ba amma zan bi gaskiya. Jehobah ne nake so ya zama Allahna kuma ina so in yi abin da yake daidai a idonsa.” Ta yaya za ka yi hakan? Ka yi adduꞌa ga Jehobah kuma ka yi alkawarin bauta masa, sa’an nan ka yi baftisma don kowa ya san alkawarin da ka yi. Ƙaunar gaskiya da son yin abu mai kyau za su motsa ka ka yi baftisma.

KANA ƘAUNAR YESU KRISTI

6. Waɗanne dalilai ne Zabura 45:4 ta bayar da ya kamata su sa ka ƙaunaci Yesu Kristi?

6 Me ya sa kake ƙaunar Yesu Kristi? Ka ga wasu dalilai a cikin littafin Zabura 45:4. ‘(Karanta. b)’ Yesu yana ƙaunar gaskiya da adalci kuma shi mai tawaliꞌu ne. Idan har kana ƙaunar gaskiya da adalci, ba shakka kana ƙaunar Yesu Kristi ma. Ka yi tunanin yadda Yesu Kristi ya kasance da ƙarfin zuciya kuma ya kāre gaskiya da adalci. (Yoh. 18:37) Ta yaya Yesu ya koya mana halin tawaliꞌu?

7. Mene ne yake burge ka game da tawaliꞌun da Yesu yake da shi?

7 Yesu yana nuna cewa yana da tawaliꞌu ta ayyukansa. Alal misali, yana miƙa dukan yabo da ɗaukaka ga Ubansa ba ga kansa ba. (Mar. 10:​17, 18; Yoh. 5:19) Yaya kake ji game da tawaliꞌun da Yesu yake da shi? Shin hakan ba ya sa ka ƙaunaci Ɗan Allah kuma ka yi koyi da shi? Ƙwarai kuwa. Me ya sa Yesu yake da tawaliꞌu? Domin yana ƙaunar Ubansa, wanda shi ma mai tawaliꞌu ne kuma yana koyi da shi. (Zab. 18:​35, NWT; Ibran. 1:3) Babu shakka, za ka ƙaunaci Yesu wanda yake koyi da Ubansa.

8. Me ya sa muke ƙaunar Yesu a matsayin Sarkinmu?

8 Muna ƙaunar Yesu a matsayin Sarkinmu domin shi ne Sarkin da ya dace. Jehobah da kansa ne ya horar da Ɗansa kuma ya naɗa shi ya zama Sarki. (Isha. 50:​4, 5) Ka yi tunanin irin ƙaunar da Yesu ya nuna mana. (Yoh. 13:1) Da yake Yesu Kristi Sarkinka ne, ya kamata ka ƙaunace shi. Ya bayyana cewa waɗanda suke ƙaunar sa, wato waɗanda ya kira abokansa, suna nuna cewa suna ƙaunar sa ta wajen bin umurnansa. (Yoh. 14:15; 15:​14, 15) Zama abokin Ɗan Jehobah babban gata ne!

9. Mene ne alaƙar da ke tsakanin baftismar Yesu da na mabiyansa?

9 Ɗaya daga cikin umurnan da Yesu ya ba wa mabiyansa shi ne su yi baftisma. (Mat. 28:​19, 20) Yesu ya kafa mana misali game da hakan. Amma baftismar Yesu ta bambanta da baftismar da mabiyansa suka yi a wasu hanyoyi. (Ka duba akwatin nan “ Bambancin da Ke Tsakanin Baftismar da Yesu Ya Yi da Na Mabiyansa.”) A wani fanni kuma, baftismar Yesu da na mabiyansa iri ɗaya ne. Ta yaya? Da Yesu ya yi baftisma, ya nuna cewa yana a shirye ya yi nufin Ubansa. (Ibran. 10:7) Hakazalika, mabiyan Yesu suna yin baftisma don su nuna cewa sun yi alkawarin bauta wa Jehobah. Wato abin da ya fi muhimmanci a rayuwarsu yanzu shi ne yin nufin Jehobah ba na kansu ba. Don haka, suna yin koyi da Ubangijinsu.

 

10. Me ya sa yadda kake ƙaunar Yesu ya kamata ya motsa ka ka yi baftisma?

10 Ka gaskata cewa Yesu shi ne Ɗan Allah makaɗaici kuma kana farin ciki cewa shi ne wanda Allah ya naɗa ya zama Sarkinmu. Ka ga cewa Yesu yana da tawaliꞌu kuma yana nuna halaye irin na Ubansa. Ka koyi cewa ya ciyar da mayunwata, ya ƙarfafa masu baƙin ciki, har ma ya warkar da cututtuka. (Mat. 14:​14-21) Ka ga yadda yake yi wa mutanensa ja-goranci a yau. (Mat. 23:10) Kuma ka san cewa zai yi abubuwan ban alꞌajabi a nan gaba saꞌad da yake sarauta a Mulkin Allah. Ta yaya za ka nuna cewa kana ƙaunar sa? Ta wajen bin misalinsa. (Yoh. 14:21) Za ka iya soma yin hakan ta wajen yin alkawarin bauta wa Jehobah kuma ka yi baftisma.

KANA ƘAUNAR JEHOBAH

11. Wane dalili mafi muhimmanci ne kake ganin ya kamata ya sa mutum ya yi baftisma?

11 Wane dalili mafi muhimmanci ne ya kamata ya sa ka yi baftisma? Yesu ya ambata dokar Allah mafi girma ta cewa: “Ka ƙaunaci Ubangiji Allahnka da dukan zuciyarka, da dukan ranka, da dukan hankalinka, da kuma dukan ƙarfinka.” (Mar. 12:30) Shin kalaman nan sun bayyana irin ƙaunar da kake yi wa Allah?

Jehobah ne Wanda yake ba ka dukan abubuwan da kake morewa da kuma waɗanda za ka more a nan gaba (Ka duba sakin layi na 12-13)

12. Me ya sa kake ƙaunar Jehobah? (Ka kuma duba hoton.)

12 Akwai dalilai da yawa da za su sa mu ƙaunaci Jehobah. Alal misali, ka koyi cewa shi ne “mai ba da ruwan rai,” da mai ba da “kowace baiwa mai kyau, da kowace cikakkiyar kyauta.” (Zab. 36:9; Yak. 1:17) Duk wani abin da kake jin daɗin sa ya fito ne daga wurin Allahnmu mai alheri.

13. Me ya sa fansa kyauta ce mai ban shaꞌawa?

13 Fansa wata kyauta ce mai ban shaꞌawa da Jehobah ya ba mu. Me ya sa muka ce hakan? Ka yi lakaꞌari da irin dangantaka ta kud da kud da ke tsakanin Jehobah da Ɗansa. Yesu ya ce: “Uba yana ƙaunata” kuma “ina ƙaunar Uban.” (Yoh. 10:17; 14:31) Dangantakarsu ta daɗa yin ƙarfi yayin da suka yi biliyoyin shekaru suna aiki tare. (K. Mag. 8:​22, 23, 30) Ka yi tunanin irin baƙin cikin da Allah ya yi saꞌad da ya bar Ɗansa ya sha wahala kuma ya mutu. Jehobah yana ƙaunar mutane sosai har da kai ma, kuma hakan ya sa ya yarda ya ba da Ɗansa wanda yake ƙauna a matsayin hadaya don mu iya yin rayuwa har abada. (Yoh. 3:16; Gal. 2:20) Wannan shi ne dalili mafi girma da ya kamata ya sa mu ƙaunaci Allah.

14. Wane abu mafi kyau ne za ka iya yi da rayuwarka?

14 Ƙaunarka ga Jehobah za ta daɗa ƙaruwa yayin da kake koyan abubuwa game da shi. Hakika, za ka so ka ƙara kusantar sa yanzu da har abada. Kuma za ka iya yin hakan. Yana ƙarfafa ka ka faranta masa rai. (K. Mag. 23:​15, 16) Za ka iya yin hakan a ayyukanka ba a kalamanka kawai ba. Yadda kake yin rayuwarka zai nuna ko kana ƙaunar Jehobah da gaske. (1 Yoh. 5:3) Babu wani abu mafi kyau da za ka yi da rayuwarka kamar yin nufin Jehobah.

15. Ta yaya za ka nuna cewa kana ƙaunar Jehobah?

15 Ta yaya za ka nuna cewa kana ƙaunar Jehobah? Da farko, ka yi adduꞌa ga Jehobah don ka yi alkawarin bauta masa. (Zab. 40:8) Sai ka nuna wa mutane cewa ka yi alkawarin nan ta wajen yin baftisma. Kamar yadda muka tattauna a talifin nan, baftisma abu mai muhimmanci ne a rayuwarka kuma zai sa ka farin ciki. Za ka soma yin rayuwa ba don kanka ba amma don Jehobah. (Rom. 14:8; 1 Bit. 4:​1, 2) Kana iya ganin cewa wannan babban mataki ne kake so ka ɗauka, kuma hakan gaskiya ne. Amma zai sa ka ji daɗin rayuwa. Ta yaya?

16. Kamar yadda Zabura 41:12 ta nuna, ta yaya Jehobah zai saka ma waɗanda suka yi amfani da rayuwarsu don su bauta masa?

16 Babu wanda yake bayarwa kamar Jehobah. Ko da mene ne ka ba shi, zai ba ka wanda ya fi hakan. (Mar. 10:​29, 30) Idan ka ba shi rayuwarka, zai sa ka ji daɗin rayuwa, zai yi maka albarka sosai, kuma zai biya bukatunka ko a yanzu a cikin muguwar duniyar nan. Kuma wannan soma taɓi ne. Ka ci gaba da kasance da dangantaka mai kyau da Jehobah bayan baftisma. Za ka iya ci gaba da bauta wa Ubanka na sama har abada. Ƙaunar da ke tsakanin ka da Ubanka za ta ci gaba da girma kuma za ka yi rayuwa har abada kamar sa.​—Karanta Zabura 41:12.

17. Mene ne za ka iya ba wa Jehobah da bai da shi?

17 Idan ka yi alkawarin bauta wa Jehobah kuma ka yi baftisma, hakan zai ba ka damar ba wa Ubanka wani abu mai daraja sosai. Ya ba ka dukan abubuwa masu kyau da dukan abubuwan more rayuwa. Don ka nuna godiyarka, kana iya bauta masa da son ranka da kuma dukan zuciyarka, wannan shi ne abin da Mai sama da ƙasa bai da shi da za ka iya ba shi. (Ayu. 1:8; 41:11; K. Mag. 27:11) Babu abin da za ka yi da rayuwarka da zai fi hakan. Hakika, ƙaunarka ga Jehobah ce dalili mafi muhimmanci da ya kamata ya sa ka yi baftisma.

A SHIRYE KAKE KA YI BAFTISMA?

18. Waɗanne tambayoyi ne za ka iya yi wa kanka?

18 Mene ne za ka ce idan aka tambaye ka, ‘Za ka yi baftisma?’ Kai da kanka ne za ka iya ba da amsar. Amma za ka amfana idan ka tambayi kanka cewa, ‘Me nake jira da ban yi baftisma ba har yanzu?’ (A. M. 8:36) Ka tuna da dalilai guda uku da muka tattauna. Kana ƙoƙari sosai a wannan fannin. Na farko, kana ƙaunar gaskiya da adalci. Na biyu, kana ƙaunar Yesu Kristi. Na uku kuma mafi muhimmanci shi ne, kana ƙaunar Jehobah. Don haka, ka tambayi kanka cewa, ‘Ina marmarin ganin lokacin da kowa zai riƙa faɗin gaskiya kuma ya yi abu mai kyau?’ ‘Ina son Ɗan Allah ya zama Sarkina, kuma ina son in yi koyi da shi?’ ‘Shin ina so in faranta ran Jehobah ta wajen bauta masa?’ Idan amsoshinka ga tambayoyin nan e ne, to me ya sa ba za ka yi baftisma ba? Mene ne kake jira?​—A. M. 16:33.

19. Me ya sa bai kamata ka yi jinkirin yin baftisma ba? Ka ba da kwatanci. (Yohanna 4:34)

19 Idan kana jinkirin yin baftisma, ka yi laꞌakari da kwatancin da Yesu ya yi. (Karanta Yohanna 4:34.) Ka lura cewa Yesu ya kwatanta yin nufin Ubansa da abinci. Me ya sa? Abinci yana da amfani a gare mu. Yesu ya san cewa dukan abin da Jehobah ya ce mana mu yi don amfanin kanmu ne. Jehobah ba ya so mu yi abin da zai iya jawo mana lahani. Shin kana ganin Jehobah yana so ka yi baftisma? Ƙwarai kuwa. (A. M. 2:38) Saboda haka, ka kasance da tabbacin cewa idan ka yi biyayya ga wannan umurnin, za ka amfana. Idan ba za ka yi jinkirin cin abinci mai daɗi ba, me ya sa za ka yi jinkirin yin baftisma?

20. Mene ne za mu tattauna a talifi na gaba?

20 Me ya sa wasu suke jinkirin yin baftisma? Da yawa daga cikinsu sukan ce, “Ban shirya ba tukuna.” Amma gaskiyar ita ce, shawarar da ka yanke na yin alkawarin bauta wa Jehobah da kuma baftisma ita ce shawara mafi muhimmanci da za ka yi a rayuwarka. Don haka, kana bukatar ka ɗauki lokaci don ka yi tunani sosai game da shawarar nan da kuma abin da zai sa ka cancanci yin baftisma. Amma idan kana so ka yi baftisma, wane shiri ne za ka iya yi yanzu don ka yi hakan? Za mu tattauna amsar tambayar nan a talifi na gaba.

WAƘA TA 28 Yadda Za Mu Zama Abokan Jehobah

a Baftisma abu mai muhimmanci ne da kowane ɗalibin Littafi Mai Tsarki ya kamata ya yi. Mene ne zai motsa ɗalibi ya ɗauki wannan matakin? Ƙauna ce. Amma ƙaunar me ke nan, kuma ga wa? A wannan talifin, za mu ga amsoshin tambayoyin nan kuma za mu tattauna yadda rayuwarmu za ta kasance bayan mun yi baftisma.

b Zabura 45:4 (NWT): “Ka yi tafiya cikin darajarka, har sai ka yi nasara; Hau ka yi tafiya domin ka tsare gaskiya da tawali’u da adalci, Hannun damanka zai aikata ayyukan ban mamaki!”