TALIFIN NAZARI NA 14
“Ta Haka Kowa Zai Sani Ku Almajiraina Ne”
“Ta haka kowa zai sani ku almajiraina ne, in dai kuna ƙaunar juna.”—YOH. 13:35.
WAƘA TA 106 Mu Riƙa Nuna Ƙauna
ABIN DA ZA A TATTAUNA a
1. Mene ne yake burge mutane da yawa idan suka halarci taronmu? (Ka kuma duba hoton.)
A CE wasu maꞌaurata sun halarci taro a karo na farko a Majamiꞌar Mulki. Yadda ꞌyanꞌuwa suka marabce su kuma suka nuna musu ƙauna ya burge su sosai. Da suke komawa gida bayan taron, matar ta gaya wa maigidanta cewa, ‘Mutanen nan sun fita dabam da sauran mutanen da na haɗu da su kuma na ji daɗin kasancewa tare da su.’
2. Me ya sa wasu suka daina bauta wa Jehobah?
2 Hakika, ƙaunar da ꞌyanꞌuwa suke nunawa a cikin ikilisiya tana da ban shaꞌawa sosai. Amma Shaidun Jehobah ba kamiltattu ba ne. (1 Yoh. 1:8) Yayin da muke daɗa sanin ꞌyanꞌuwa a cikin ikilisiya, hakan zai sa mu soma ganin kasawarsu. (Rom. 3:23) Abin baƙin ciki shi ne, wasu sun bar waɗannan kasawar su sa su daina bauta wa Jehobah.
3. Ta yaya mutane za su gane mabiyan Yesu na gaske? (Yohanna 13:34, 35)
3 Ka sake duba Nassin da aka ɗauko jigon talifin nan. (Karanta Yohanna 13:34, 35.) Ta yaya mutane za su san mabiyan Kristi na gaskiya? Ƙauna ce, ba wai za su zama kamiltattu ba. Ka lura cewa Yesu bai ce: ‘Ta haka za ku san cewa ku almajiraina ne’ ba. Amma ya ce: ‘Ta haka kowa zai sani ku almajiraina ne.’ Wato har waɗanda ba Kiristoci ba ma za su gane mabiyansa na gaske ta ƙaunar da suke nuna wa junansu.
4. Mene ne wasu za su so su sani game da Kiristoci na gaske?
4 Wasu da ba Shaidun Jehobah ba suna iya cewa: ‘Ta yaya ƙauna take taimaka mana mu san mabiyan Yesu na gaske? Ta yaya Yesu ya nuna wa manzanninsa ƙauna? Ta yaya za mu iya yin koyi da irin wannan ƙaunar a yau?’ Shaidun Jehobah ma suna bukatar su yi tunani game da amsoshin waɗannan tambayoyin. Yin hakan zai iya taimaka mana mu nuna wa juna ƙauna musamman saꞌad da ꞌyanꞌuwa suka yi kuskure.—Afis. 5:2.
WACE IRIN ƘAUNA CE TAKE SA A GANE MABIYAN YESU NA GASKE?
5. Ka bayyana abin da Yesu yake nufi a Yohanna 15:12, 13.
5 Yesu ya bayyana cewa mabiyansa za su nuna wa juna ƙauna a hanya ta musamman. (Karanta Yohanna 15:12, 13.) Ku ga abin da Yesu ya umurci mabiyansa su yi, ya ce: ‘Ku ƙaunaci juna kamar yadda na ƙaunace ku.’ Me hakan yake nufi? Yesu ya bayyana abin da hakan yake nufi. Wannan ƙaunar tana motsa mutum ya ƙaunaci mutane fiye da kansa. Ƙari ga haka, tana iya sa Kirista ya sadaukar da ransa a madadin ꞌyanꞌuwansa idan da bukata. b
6. Ta yaya Kalmar Allah ta nanata muhimmancin ƙauna?
6 Littafi Mai Tsarki ya nanata muhimmancin ƙauna. Wasu daga cikin Nassosin da mutane suka fi so su ne waɗanda suka ce: “Allah ƙauna ne.” (1 Yoh. 4:8) “Ka ƙaunaci maƙwabcinka kamar yadda kake ƙaunar kanka.” (Mat. 22:39) “Ƙauna . . . takan yafe laifofi masu ɗumbun yawa.” (1 Bit. 4:8) “Ƙauna ba ta ƙārewa har abada.” (1 Kor. 13:8) Ya kamata waɗannan ayoyin da wasu ma su nuna wa dukanmu cewa yana da muhimmanci mu kasance da wannan halin.
7. Me ya sa Shaiɗan ba zai taɓa iya sa mutane a faɗin duniya su ƙaunaci juna ba?
7 Mutane da yawa sukan ce: ‘Ta yaya za mu iya sanin addini na gaske? Dukan addinai suna daꞌawa cewa suna koyar da gaskiya, amma kowannensu yana koyar da abubuwa dabam-dabam game da Allah.’ Shaiɗan ya sa an samu addinan ƙarya da yawa, kuma hakan ya sa yana yi wa mutane wuya su gane addini na gaske. Amma ba zai iya sa mutanen da suka fito daga wurare dabam-dabam a faɗin duniya su ƙaunaci juna ba. Jehobah ne kaɗai zai iya yin hakan. Mun san da hakan domin Jehobah ne tushen ƙauna ta gaskiya. Waɗanda suke da ruhunsa da kuma taimakonsa ne kawai za su iya nuna wa juna ƙauna ta gaskiya. (1 Yoh. 4:7) Shi ya sa Yesu ya ce mabiyansa na gaske ne kaɗai za su nuna ƙauna ta gaskiya.
8-9. Ta yaya ƙaunar da Shaidun Jehobah suke nuna wa junansu ta shafi mutane da yawa?
8 Kamar yadda Yesu ya annabta, mutane da yawa sun gano mabiyan Yesu na gaske ta ƙaunar da suke nuna wa junansu. Alal misali, wani ɗanꞌuwa mai suna Ian ya tuna taron yanki na farko da ya halarta, wanda aka yi a babban filin wasa da ke kusa da gidansa. ꞌYan makonni kafin taron, Ian ya je kallon wasa a filin. Ya ce: “Halayen Shaidun Jehobah a taron sun yi dabam da halayen waɗanda suka zo kallon wasan. Suna da kirki kuma sun saka tufafi masu kyau, yaransu ma suna da tarbiyya mai kyau.” Ya ƙara da cewa: “Abin da ya fi muhimmanci shi ne, mutanen nan suna da kwanciyar hankali da kuma gamsuwa kuma abin da nake so a rayuwata ke nan. Ba zan iya tuna jawaban da aka bayar a ranar ba amma ina tunawa da halaye masu kyau da Shaidun suka nuna.” c Ƙauna ta gaskiya da muke nuna wa juna ce take sa mu kasance da halayen nan. Da yake muna ƙaunar ꞌyanꞌuwanmu maza da mata, muna daraja su kuma muna yi musu alheri.
9 Wani ɗanꞌuwa mai suna John ya ji kamar haka saꞌad da ya soma halartar taro da Shaidun Jehobah. Ya ce: “ꞌYanꞌuwa sun yi mini alheri sosai . . . har na ɗauka cewa su kamiltattu ne. Ƙaunar da suke nuna wa junansu ce ta tabbatar min da cewa na samo addini na gaske.” d Labarai da yawa kamar haka suna tabbatar da cewa mutanen Jehobah su ne Kiristoci na gaske.
10. A wane lokaci ne muke da damar nuna ƙauna ta Kirista? (Ka kuma duba ƙarin bayani.)
10 Kamar yadda muka ambata da farko, ꞌyanꞌuwanmu ajizai ne. A wasu lokuta, suna iya faɗa ko su yi wani abin da zai ɓata mana rai. e (Yak. 3:2) Idan hakan ya faru, mu yi amfani da wannan damar don mu nuna wa ꞌyanꞌuwanmu ƙauna ta yadda za mu bi da yanayin. Mene ne za mu iya koya daga misalin da Yesu ya kafa mana a wannan batun?—Yoh. 13:15.
TA YAYA YESU YA NUNU WA MANZANNINSA ƘAUNA?
11. Waɗanne halaye marasa kyau ne Yaƙub da Yohanna suka nuna? (Ka kuma duba hoton.)
11 Yesu bai bukaci mabiyansa su yi kome daidai kamar kamilai ba. A maimakon haka, cikin ƙauna, Yesu ya taimaka musu su gyara halaye marasa kyau da suke da su don su sami amincewar Jehobah. Alal misali, akwai lokacin da biyu daga cikin su, wato Yaƙub da Yohanna suka gaya wa mahaifiyarsu ta roƙi Yesu ya ba su matsayi mai muhimmanci a Mulkin Allah. (Mat. 20:20, 21) Ta haka, Yaƙub da Yohanna sun nuna cewa suna da girman kai kuma suna so su fi sauran muhimmanci.—K. Mag. 16:18.
12. Shin Yaƙub da Yohanna ne kaɗai suka nuna halaye marasa kyau? Ka bayyana.
12 Amma ba Yaƙub da Yohanna ne kaɗai suka nuna halaye marasa kyau a wannan lokacin ba. Ku ga abin da sauran manzannin suka yi: “Da sauran almajiran goma suka ji haka, sai suka ji haushin ꞌyanꞌuwan nan guda biyu.” (Mat. 20:24) Ba mamaki, sauran manzannin sun yi rigima da Yaƙub da Yohanna. Mai yiwuwa sun ce: ‘Kuna ganin kun fi mu daraja ne da har za ku ce a ba ku babban matsayi a Mulkin Allah? Ba ku kaɗai ba ne kuka yi aiki sosai tare da Yesu ba. Mu ma mun cancanci a ba mu babban matsayi.’ Ko da ya suka yi, a wannan lokacin dai, sun manta su nuna wa juna ƙauna kuma su yi wa juna alheri.
13. Mene ne Yesu ya yi saꞌad da manzanninsa suka yi kuskure? (Matiyu 20:25-28)
13 Yaya Yesu ya bi da wannan yanayin? Yesu bai yi fushi da su ba. Bai ce zai je ya nemi manzanni da suke da halaye masu kyau, masu sauƙin kai da ƙaunar juna ba. A maimakon haka, Yesu ya yi haƙuri da su kuma ya daidaita tunaninsu domin ya san cewa suna so su yi abin da ya dace. (Karanta Matiyu 20:25-28.) Ya ci gaba da nuna musu ƙauna duk da cewa ba wannan ba ne ƙaro na farko ko na ƙarshe da manzannin suka yi gardama a kan wanda ya fi muhimmanci a cikinsu ba.—Mar. 9:34; Luk. 22:24.
14. Wane irin hali ne mutane suke da shi a inda manzannin Yesu suka taso?
14 Babu shakka, Yesu ya tuna cewa inda manzanninsa suka taso ya shafi tunaninsu. (Yoh. 2:24, 25) Sun taso ne a inda malaman addinai suka koya wa mutane cewa wanda yake da babban matsayi ne kawai yake da muhimmanci. (Mat. 23:6; ka kuma duba talifin nan, “Majami’a—Wurin da Yesu da Almajiransa Suka Yi Wa’azi” da ke Hasumiyar Tsaro ta 1 ga Afrilu 2010, shafi na 16-18.) Ƙari ga haka, malaman nan suna ganin cewa sun fi wasu. f (Luk. 18:9-12) Yesu ya san cewa irin wannan yanayin zai shafi yadda manzannin suke ɗaukan kansu da kuma sauran mutane. (K. Mag. 19:11) Bai yi zaton cewa mabiyansa ba za su taɓa yin kuskure ba, kuma ya yi haƙuri da su saꞌad da suka yi hakan. Ya san cewa suna da zuciyar kirki. Don haka, ya taimaka musu su kasance da sauƙin kai kuma su nuna wa mutane ƙauna, maimakon su riƙa yin ƙoƙarin zama waɗanda suka fi muhimmanci.
TA YAYA ZA MU YI KOYI DA YESU?
15. Wane darasi ne muka koya daga abin da ya faru da Yaƙub da Yohanna?
15 Za mu iya koyan darasi daga abin da ya faru da Yaƙub da Yohanna. Bai kamata su ce a ba su babban matsayi a Mulkin Allah ba. Sauran manzannin ma sun yi laifi. Bai kamata su bar hakan ya lalata haɗin kan da suke da shi ba. Amma Yesu ya yi wa dukan manzanninsa alheri kuma ya nuna musu ƙauna. Mene ne darasin da muka koya? Ba abin da mutane suka yi mana ne kawai yake da muhimmanci ba, amma yadda muka bi da kurakurensu ma yana da muhimmanci. Mene ne zai taimaka mana? Idan wani ɗanꞌuwa ya ɓata mana rai, mu tambayi kanmu cewa: ‘Me ya sa abin da ya yi ya ɓata min rai sosai? Shin hakan ya nuna wani hali marar kyau da nake bukatar in kawar? Shin wanda ya ɓata min rai, yana fama da wasu matsaloli ne? Ko da ina ganin cewa fushin da na yi ba laifi ba ne, zan iya nuna ƙauna ta wajen yafe wa mutumin?’ Idan muka ci gaba da nuna wa mutane ƙauna, hakan zai nuna cewa mu mabiyan Yesu ne na gaske.
16. Wane darasi ne muka koya daga wurin Yesu?
16 Yadda Yesu ya bi da yanayin ma ya koya mana cewa mu riƙa kasance da raꞌayin da ya dace game da ꞌyanꞌuwanmu. (K. Mag. 20:5) Hakika, Yesu zai iya ganin zuciya, mu kuma ba za mu iya ba. Amma za mu iya haƙuri da ꞌyanꞌuwanmu idan suka yi mana laifi. (Afis. 4:1, 2; 1 Bit. 3:8) Yin hakan zai fi mana sauƙi idan muka san game da alꞌadun ꞌyanꞌuwanmu da inda suka taso. Ku yi laꞌakari da misalin nan.
17. Ta yaya wani mai kula da daꞌira ya amfana saꞌad da ya yi ƙoƙari don ya san wani ɗanꞌuwa da kyau?
17 Wani mai kula da daꞌira da ya yi hidima a Gabashin Afirka ya tuna wani ɗanꞌuwa da yake wata ikilisiya da ya ziyarta. Da farko mai kula da daꞌirar yana ganin cewa ɗanꞌuwan nan ba shi da kirki. Mene ne mai kula da daꞌirar ya yi? Ya ce: “Maimakon in guji ɗanꞌuwan, na yanke shawarar cewa zan yi ƙoƙari in san abubuwa game da shi.” Ta haka, mai kula da daꞌirar ya gano cewa inda ɗanꞌuwan ya taso ya shafi halayensa. Mai kula da daꞌirar ya ci gaba da cewa: “Da na gano yadda ɗanꞌuwan yake iya ƙoƙarinsa ya zauna lafiya da mutane, da wasu halayensa da ya riga ya canja, hakan ya sa na ƙaunace shi sosai kuma mun zama abokai.” Hakika, idan muka yi ƙoƙari don mu san ꞌyanꞌuwanmu da kyau, hakan zai sa ya yi mana sauƙi mu nuna musu ƙauna.
18. Idan wani ɗanꞌuwa ya yi mana laifi, waɗanne tambayoyi ne za mu iya yi wa kanmu? (Karin Magana 26:20)
18 A wasu lokuta, za mu ji kamar muna bukatar mu je mu sami wani ɗanꞌuwa da ya ɓata mana rai. Amma kafin mu yi hakan, zai dace mu yi wa kanmu tambayoyin nan: ‘Ina da cikakken bayani game da abin da ya faru?’ (K. Mag. 18:13) ‘Shin ɗanꞌuwan ya ɓata min rai da gangan ne?’ (M. Wa. 7:20) ‘Shin ni ma na taɓa yin irin wannan kuskuren?’ (M. Wa. 7:21, 22) ‘Idan na je na sami mutumin, hakan ba zai sa yanayin ya daɗa muni ba?’ (Karanta Karin Magana 26:20.) Idan muka ɗauki lokaci don mu yi laꞌakari da tambayoyin nan, za mu ga cewa ƙauna za ta sa mu mance da abin da ya faru.
19. Mene ne ka ƙuduri niyyar yi?
19 Shaidun Jehobah suna nuna cewa su mabiyan Kristi ne na gaske ta wajen nuna wa juna ƙauna. Kowannenmu zai nuna cewa shi mabiyin Yesu Kristi ne na gaske ta wajen nuna wa ꞌyanꞌuwa maza da mata ƙauna duk da ajizancinsu. Idan muna yin hakan, za mu taimaka ma wasu su san addini na gaske kuma su bauta wa Jehobah Allah mai ƙauna tare da mu. Bari mu ci gaba da nuna wannan ƙaunar da ke sa a san mabiyan Kristi na gaske.
WAƘA TA 17 “Na Yarda”
a Mutane da yawa suna so su koya game da Jehobah da kuma Kalmarsa saboda ƙauna ta gaskiya da suke gani muke nuna wa juna. Amma mu ajizai ne. Don haka a wasu lokuta, yakan yi mana wuya mu nuna wa juna ƙauna. Bari mu tattauna dalilin da ya sa ƙauna take da muhimmanci sosai da kuma yadda za mu yi koyi da misalin Yesu saꞌad da ꞌyanꞌuwanmu suka yi mana kuskure.
b Ka duba littafin nan “Come Be My Follower,” babi na 17, sakin layi na 10-11.
c Ka duba talifin nan “At Last, My Life Has a Purpose,” a Hasumiyar Tsaro ta 1 ga Nuwamba, 2012, shafuffuka na 13-14 a Turanci.
d Ka shiga jw.org/ha kuma ka rubuta “Ba abin da na rasa,” a inda aka ce “bincika”, sai ka bincika don ka karanta talifin. Yana cikin jerin talifofin nan, “Littafi Mai Tsarki Yana Gyara Rayuwar Mutane.”
e Wannan talifin ba ya magana ne game da zunubai masu tsanani waɗanda ya kamata a gaya wa dattawa, kamar zunuban da aka ambata a 1 Korintiyawa 6:9, 10.
f An sami rahoto cewa daga baya wani malami ya ce: “Aƙalla akwai mutane talatin masu adalci kamar Ibrahim a duniya. Idan su talatin ne, to ni da ɗana muna cikinsu; idan goma ne, ni da ɗana muna cikinsu; idan biyar ne, ni da ɗana muna cikinsu; idan biyu ne, ni da ɗana ke nan; amma idan ɗaya ne, to ni ne.”