Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 11

Yadda Za Ka Shirya Kanka don Yin Baftisma

Yadda Za Ka Shirya Kanka don Yin Baftisma

“Mene ne zai hana a yi mini baftisma?”​—A. M. 8:36.

WAƘA TA 50 Alkawarin Bauta wa Jehobah

ABIN DA ZA A TATTAUNA a

A duk faɗin duniya, yara da manya suna yin baftisma (Ka duba sakin layi na 1-2)

1-2. Idan ba ka cancanci yin baftisma ba, me ya sa bai kamata ka yi sanyin gwiwa ba? (Ka duba hoton da ke shafin farko.)

 IDAN kana so ka yi baftisma, maƙasudi mai kyau ne ka kafa wa kanka. Kana a shirye ka yi baftisma yanzu? Idan ka tabbata cewa kana a shirye kuma dattawa sun yarda da hakan, kada ka ɓata lokacin yin baftisma. Idan ka yi baftisma, za ka ji daɗin hidimarka ga Jehobah.

2 Amma wani ya taɓa gaya maka cewa akwai gyaran da ya kamata ka yi kafin ka cancanci yin baftisma? Ko dai ka gano hakan ne da kanka? Idan haka ne, kada ka yi sanyin gwiwa. Za ka iya samun ci gaba har ka yi baftisma ko da kai matashi ne ko ka tsufa.

“MENE NE ZAI HANA A YI MINI BAFTISMA?”

3. Mene ne wani mutumin Itiyofiya ya tambayi Filibus, kuma wace tambaya ce ta taso? (Ayyukan Manzanni 8:​36, 38)

3 Karanta Ayyukan Manzanni 8:​36, 38. Wani mutumin Itiyofiya ya tambayi Filibus cewa: “Mene ne zai hana a yi mini baftisma?” Mutumin Itiyofiyan yana so ya yi baftisma, amma yana a shirye don ya yi baftisma kuwa?

Mutumin Itiyofiya ya so ya ci gaba da koya game da Jehobah (Ka duba sakin layi na 4)

4. Ta yaya mutumin Itiyofiya ya nuna cewa yana so ya ci gaba da koya daga Littafi Mai Tsarki?

4 Mutumin Itiyofiyan ya je “Urushalima ne domin ya yi sujada.” (A. M. 8:27) Da alama, mutumin ya riga ya karɓi addinin Yahudawa. Babu shakka, ya koyi game da Jehobah daga Nassosin Ibrananci. Duk da haka, ya so ya ƙara koya game da Jehobah. Shi ya sa da Filibus ya haɗu da mutumin a kan hanya, ya gan shi yana karanta littafin annabi Ishaya. (A. M. 8:28) Abubuwan da yake karantawa batutuwa masu zurfi ne daga Littafi Mai Tsarki. Mutumin bai so ya koyi abubuwa masu sauƙi kawai ba, amma ya so ya ci gaba da koya daga Littafi Mai Tsarki.

5. Mene ne mutumin Itiyofiyan ya yi don abin da ya koya?

5 Mutumin mai babban matsayi ne a mulkin Sarauniya Kandis na Itiyofiya. “Shi ne kuma ma’ajin sarauniyar.” (A. M. 8:27) Babu shakka, shi mutum ne mai ayyuka da yawa. Duk da haka, ya nemi lokaci don ya yi wa Jehobah sujada. Bai gamsu da koya game da Jehobah kawai ba, amma ya aikata abin da ya koya. Don haka, ya yi tafiya mai nisa daga Itiyofiya don ya yi wa Jehobah sujada a haikalin da ke Urushalima. Tafiyar ta ɗauki lokaci kuma ta ci masa kuɗi sosai. Amma mutumin yana so ya bauta wa Jehobah ko da hakan zai yi wuya sosai.

6-7. Ta yaya mutumin Itiyofiyan ya ci gaba da ƙaunar Jehobah?

6 Mutumin Itiyofiyan ya koyi sabbin abubuwa masu muhimmanci daga Littafi Mai Tsarki, kuma ɗaya daga cikinsu shi ne cewa Yesu ne Almasihu. (A. M. 8:​34, 35) Mutumin ya yi farin ciki da ya san abin da Yesu ya yi masa. Mene ne ya yi bayan da ya koya abubuwan nan? Da ya so, da ya ci gaba da bin addinin Yahudawa kawai. A maimakon haka, yadda yake ƙaunar Jehobah da kuma Yesu ya daɗa ƙaruwa. Hakan ya sa ya yanke shawara mai muhimmanci na yin baftisma a matsayin mabiyin Yesu Kristi. Da Filibus ya ga cewa mutumin na nan a shirye, sai ya yi masa baftisma.

7 Idan ka bi misalin da mutumin Itiyofiyan ya kafa, kai ma za ka cancanci yin baftisma. Za ka iya faɗa da tabbaci cewa, “Mene ne zai hana a yi mini baftisma?” Bari mu bincika yadda za ka iya yin abubuwan da mutumin Itiyofiyan ya yi, wato ya ci gaba da koyo, ya aikata abin da ya koya kuma ya ci gaba da ƙaunar Allah.

KA CI GABA DA KOYO

8. Mene ne Yohanna 17:3 ta ce da ya zama wajibi ne mu yi?

8 Karanta Yohanna 17:3. Shin abin da Yesu ya faɗa ne ya taimaka maka ka soma yin nazarin Littafi Mai Tsarki? Abin da ya faru da yawancin mu ke nan. Amma kalamansa suna nufin mu ci gaba da koyo ne? Ƙwarai kuwa. Ba za mu daina ci gaba da sanin “Allah makaɗaici na gaskiya” ba. (M. Wa. 3:11) Har abada za mu ci gaba da koya game da Jehobah. Yayin da muke ci gaba da koya game da Jehobah, hakan zai sa mu kusace shi sosai.​—Zab. 73:28.

9. Mene ne ya kamata mu yi bayan mun koyi batutuwa masu sauƙi daga Littafi Mai Tsarki?

9 Saꞌad da muka fara koya game da Jehobah, mun soma ne da batutuwa masu sauƙin fahimta. A wasiƙar da manzo Bulus ya rubuta wa Ibraniyawa, ya kira batutuwan nan “koyarwa mai sauƙi ta kalmar Allah.” Ba wai ya rena “koyarwar nan ta farko” ba ne, amma ya kwatanta ta ne da madarar da ake ba wa jariri. (Ibran. 5:12; 6:1) Ƙari ga haka, ya ƙarfafa dukan Kiristoci su ci gaba da koyan batutuwa masu zurfi daga Kalmar Allah ba masu sauƙi kawai ba. Shin kana marmarin koyan batutuwa masu zurfi daga Kalmar Allah? Kana so ka ci gaba da koya game da Jehobah da kuma nufinsa?

10. Me ya sa yana yi ma wasu wuya su yi nazari?

10 Amma yakan yi wa da yawa daga cikinmu wuya mu yi nazari. Kai kuma fa? A makaranta, ka koyi yadda za ka yi karatu da nazari da kyau? Shin ka ji daɗin yin nazarin kuma kana ganin ka amfana daga hakan? Ko dai kana tsammani cewa ba za ka taɓa iya koyan abubuwa ta yin karatu ba? Mutane da yawa sukan ji hakan, amma Jehobah zai iya taimaka maka. Shi kamiltacce ne kuma babu Malami kamar sa.

11. Ta yaya Jehobah ya nuna cewa shi ne Babban Malaminmu?

11 Jehobah ya kira kansa “[Babban, NWT] Malaminku.” (Isha. 30:​20, 21) Shi Malami ne mai haƙuri, mai alheri kuma ya fahimci yanayinmu. Yana mai da hankali ga halaye masu kyau na ɗalibansa. (Zab. 130:3) Kuma ba ya sa mu yi abin da ya fi ƙarfin mu. Ka tuna cewa shi ne ya yi ƙwaƙwalwarmu, wadda babbar kyauta ce a gare mu. (Zab. 139:14) Ya halicce mu da marmarin koyan abubuwa. Mahaliccinmu yana so mu ci gaba da koyan abubuwa har abada kuma mu ji daɗin yin hakan. Don haka, yana da kyau ka yi “marmarin” Kalmar Allah yanzu. (1 Bit. 2:2) Ka kafa maƙasudan da za ka iya cim ma wa, kuma ka riƙa karanta da yin nazarin Littafi Mai Tsarki a-kai-a-kai. (Yosh. 1:8) Da taimakon Jehobah, za ka koyi yadda za ka ji daɗin karanta da kuma koya game da shi.

12. Me ya sa yake da muhimmanci mu yi nazari a kan rayuwar Yesu da hidimarsa?

12 Ka riƙa ɗaukan lokaci a-kai-a-kai don ka yi tunani a kan rayuwar Yesu da hidimarsa. Yana da muhimmanci mu bi misalin Yesu idan muna so mu bauta wa Jehobah a wannan mawuyacin lokaci. (1 Bit. 2:21) Yesu ya gaya wa mabiyansa cewa za su fuskanci matsaloli. (Luk. 14:​27, 28) Amma ya kasance da tabbaci cewa mabiyansa za su yi nasara kamar yadda ya yi. (Yoh. 16:33) Ka yi nazari a kan rayuwar Yesu, kuma ka kafa maƙasudin bin misalinsa a rayuwarka.

13. Mene ne ya kamata ka ci gaba da roƙon Jehobah a kai kuma me ya sa?

13 Ba ilimi ne kawai muke bukata ba. Dalilin da ya sa muke bukatar ilimi shi ne don mu ci gaba da koya game da Jehobah, mu ƙaunace shi kuma mu ba da gaskiya gare shi. (1 Kor. 8:​1-3) Yayin da kake koya game da Jehobah, ka ci gaba da roƙon sa ya taimaka maka ka kasance da bangaskiya. (Luk. 17:5) Yakan amsa irin adduꞌoꞌin nan. Ilimin nan zai sa ka ƙara kasancewa da bangaskiya kuma zai taimaka maka ka ɗauki wasu matakai.​—Yak. 2:26.

KA CI GABA DA AIKATA ABIN DA KA KOYA

Kafin Ambaliyar, Nuhu da iyalinsa sun yi abin da suka ji (Ka duba sakin layi na 14)

14. Ta yaya manzo Bitrus ya nanata muhimmancin aikata abin da muka koya? (Ka kuma duba hoton.)

14 Manzo Bitrus ya nanata dalilin da ya sa yake da muhimmanci mabiyan Kristi su ci gaba da aikata abin da suka koya. Ya yi amfani da misalin Nuhu daga Littafi Mai Tsarki. Jehobah ya gaya wa Nuhu cewa zai halaka mugayen mutane a zamaninsa da ambaliyar ruwa. Sanin cewa ambaliyar na zuwa kawai bai isa ya ceci Nuhu da iyalinsa ba. Ka lura cewa Bitrus yana magana ne a kan lokacin da ba a yi Ambaliyar ba, da kuma ‘lokacin da Nuhu yake sassaƙa jirgin.’ (1 Bit. 3:20) Nuhu da iyalinsa sun yi abin da suka ji daga wurin Allah ta wajen gina wani babban jirgi. (Ibran. 11:7) Sai Bitrus ya kwatanta abin da Nuhu ya yi da yin baftisma kuma ya rubuta cewa: “Ruwan kuwa kwatanci ne na wankan baftismar da ta cece ku a yanzu.” (1 Bit. 3:21) Kamar yadda Nuhu da iyalinsa sun yi aiki tuƙuru na tsawon shekaru don su gina jirgin, haka ma kana bukatar ka yi ƙoƙari sosai kafin ka cancanci yin baftisma. Mene ne ya kamata ka yi don ka shirya kanka don yin baftisma?

15. Ta yaya za mu nuna cewa mun tuba da gaske?

15 Ɗaya daga cikin abubuwa na farko da ya zama wajibi ne mu yi shi ne, mu tuba daga zunubanmu. (A. M. 2:​37, 38) Idan muka tuba da gaske, hakan zai sa mu canja halayenmu. Shin ka riga ka daina yin abubuwan da suke ɓata wa Jehobah rai, kamar halin lalata da shan taba da kuma zage-zage ko yin maganganun banza? (1 Kor. 6:​9, 10; 2 Kor. 7:1; Afis. 4:29) Idan ba ka riga ka yi hakan ba, ka ci gaba da yin iya ƙoƙarinka don ka yi canji. Ka nemi taimako daga wurin wanda yake nazari da kai ko kuma dattawa. Idan kai matashi ne kuma kana zama da iyayenka, ka riƙa gaya musu su taimaka maka don ka daina halaye marasa kyau da za su iya hana ka yin baftisma.

16. Mene ne ya zama dole mu yi idan muna so mu bauta wa Jehobah a koyaushe?

16 Yana da muhimmanci mu riƙa yin ayyukan ibada a-kai-a-kai. Hakan ya ƙunshi halartar taro da yin kalamai a taro. (Ibran. 10:​24, 25) Kuma idan ka cancanci ka yi waꞌazi, ka riƙa yin hakan a-kai-a-kai. Yayin da kake daɗa yin waꞌazi, za ka daɗa jin daɗin sa. (2 Tim. 4:5) Idan kai matashi ne kuma kana zama da iyayenka, ka tambayi kanka cewa, ‘Sai iyayena sun tuna min ne nake zuwa taro ko waꞌazi? Ko kuma ina yin hakan da kaina?’ In kana yin waɗannan abubuwan da kanka, za ka nuna cewa kana da bangaskiya, kana ƙaunar Jehobah kuma kana gode masa don abubuwan da yake ba ka. Hakan kyauta ne da kake ba wa Jehobah, wato yin “rayuwa mai tsarki.” (2 Bit. 3:11; Ibran. 13:15) Dukan abubuwan da muke yi wa Jehobah da yardar rai suna faranta masa rai. (Ka kuma duba 2 Korintiyawa 9:7.) Muna yin hakan ne domin yana sa mu farin ciki a duk lokacin da muka yi wa Jehobah hidima da dukan zuciyarmu.

KA CI GABA DA ƘAUNAR JEHOBAH

17-18. Wane hali mai muhimmanci ne zai taimaka maka ka cancanci yin baftisma, kuma me ya sa? (Karin Magana 3:​3-6)

17 Yayin da kake ci gaba da yin abubuwan da za su sa ka cancanci yin baftisma, za ka fuskanci matsaloli. Wasu mutane za su yi maka baꞌa don imaninka ko kuma su tsananta maka. (2 Tim. 3:12) Yayin da kake iya ƙoƙarinka don ka daina wani hali marar kyau, a wasu lokuta kana iya komawa gidan jiya. Ko ka ƙasa yin haƙuri da kanka, ko kuma ka yi fushi don kana ganin ba za ka iya cim ma maƙasudinka ba. Mene ne zai taimaka maka ka jimre? Ƙaunarka ga Jehobah ce abu mai muhimmanci da zai taimaka maka.

18 Ƙaunarka ga Jehobah ce hali mafi kyau da kake da shi. (Karanta Karin Magana 3:​3-6.) Idan kana ƙaunar Allah sosai, za ka ci gaba da bauta masa ko da kana fuskantar matsaloli. Littafi Mai Tsarki yana yawan ambata ƙaunar Jehobah marar canjawa ga bayinsa. Ƙauna marar canjawa tana nufin Jehobah ba zai taɓa barin bayinsa ko ya daina ƙaunar su ba. (Zab. 100:5) Allah ya halicce ka a kamaninsa. (Far. 1:26) Ta yaya za ka iya nuna irin wannan ƙaunar?

Ka yi adduꞌa a koyaushe ga Jehobah don ka nuna godiyarka (Ka duba sakin layi na 19) c

19. Ta yaya za ka daɗa nuna godiya don dukan abubuwan da Jehobah ya yi maka? (Galatiyawa 2:20)

19 Ka fara da gode wa Jehobah. (1 Tas. 5:18) A koyaushe, ka tambayi kanka cewa, ‘Ta yaya Jehobah ya nuna min ƙauna?’ Saꞌan nan ka tabbatar cewa ka yi wa Jehobah godiya a adduꞌarka kuma ka ambata abubuwan da ya yi maka. Ka san cewa Jehobah yana yi maka alheri domin yana ƙaunar ka ne, kamar yadda manzo Bulus ya gano hakan game da Jehobah. ‘(Karanta Galatiyawa 2:20. b)’ Ka tambayi kanka cewa, ‘Ina so in nuna masa ƙauna kamar yadda yake nuna min?’ Idan kana ƙaunar Jehobah, hakan zai taimaka maka ka ƙi faɗa wa jarabobi kuma ka iya jimre matsaloli. Zai taimaka maka ka riƙa yin ayyukan ibada a-kai-a-kai kuma ka riƙa nuna wa Ubanka cewa kana ƙaunar sa a koyaushe.

20. Mene ne ya zama wajibi ka yi kafin ka yi alkawarin bauta wa Jehobah, kuma me ya sa hakan yake da muhimmanci?

20 Da shigewar lokaci, yadda kake ƙaunar Jehobah zai taimaka maka ka yi adduꞌa don ka yi alkawarin bauta masa da dukan ranka. Ka tuna cewa da zarar ka yi alkawarin bauta wa Jehobah, za ka zama nasa har abada kuma wannan bege ne mai ban shaꞌawa. Idan ka yi alkawarin bauta wa Jehobah da dukan ranka, ka yi alkawarin bauta masa ne ko da wane irin yanayi ne ka sami kanka a ciki. Ba ka bukatar ka riƙa yin alkawarin a-kai-a-kai. A gaskiya, yin alkawarin bauta wa Jehobah ba abin wasa ba ne. Ka yi tunani a kan wannan, za ka yanke shawarwari a rayuwarka kuma wasunsu masu kyau ne, amma ba za ka taɓa yanke shawarar da ta fi yin alkawarin bauta wa Jehobah kyau ba. (Zab. 50:14) Shaiɗan zai yi ƙoƙari ya sa ka daina ƙaunar Ubanka don ka daina bauta masa. Kada ka bar Shaiɗan ya yi nasara! (Ayu. 27:5) Ƙaunar da kake yi wa Jehobah za ta taimaka maka ka cika alkawarin da ka yi na bauta masa har abada kuma za ta sa ka daɗa kusantar Ubanka na sama.

21. Me ya sa za mu iya ce ba baftisma ne ƙarshen abin da ya kamata mu yi ba, amma somawa ne kawai?

21 Bayan ka yi alkawarin bauta wa Jehobah, ka yi magana da dattawan da ke ikilisiyarku don ku shirya yadda za ka yi baftisma. Amma ka riƙa tuna cewa ba baftisma ne ƙarshen ibadarka ba, shi ne farkon abin da ya kamata ka yi. Wato rayuwar bauta wa Jehobah har abada. Don haka, ka daɗa ƙaunar Ubanka yanzu. Ka kafa maƙasudai da za su taimaka maka ka daɗa ƙaunar Jehobah a koyaushe. Yin hakan zai kai ka ga yin baftisma. Ba ƙaramin farin ciki ne za ka yi a ranar ba. Amma hakan somawa ne kawai. Muna fatan za ka ci gaba da ƙaunar Jehobah da kuma Ɗansa har abada!

WAƘA TA 135 Jehobah Ya Ce: “Ɗana Ka Yi Hikima”

a Ya kamata mu kasance da raꞌayin da ya dace kafin mu yi baftisma kuma ya kamata mu yi abin da ya dace. A wannan talifin, za mu yi amfani da misalin mutumin Itiyofiya don mu nuna abubuwan da ɗalibin Littafi Mai Tsarki ya kamata ya yi kafin ya cancanci yin baftisma.

b Galatiyawa 2:20 (NWT): “An rataye ni a kan gungume tare da Kristi. Yanzu ba ni ne nake rayuwa ba, amma Kristi ne yake rayuwa a zuciyata. Wannan rayuwa ta jiki da nake yi, rayuwa ce ta wurin bangaskiya ga Ɗan Allah, wanda ya ƙaunace ni har ya ba da ransa domina.”

c BAYANI A KAN HOTUNA: Wata ꞌyarꞌuwa tana adduꞌa ga Jehobah kuma tana gaya masa yadda take godiya don abubuwan da ya yi mata.