Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 23

Ku Sa “Harshen Wuta . . . na Ubangiji” Ya Ci Gaba da Ci

Ku Sa “Harshen Wuta . . . na Ubangiji” Ya Ci Gaba da Ci

“[Ƙauna] harshen wuta ne, harshen wuta mai-tsanani na Ubangiji.”​—W. WAƘ. 8:​6, Tsohuwar Hausa a Sauƙaƙe.

WAƘA TA 131 ‘Abin da Allah Ya Haɗa’

ABIN DA ZA A TATTAUNA a

1. Yaya Littafi Mai Tsarki ya kwatanta ƙauna ta gaskiya?

 ƘAUNA kamar harshen wuta take, harshen wuta mai tsanani na Ubangiji. “Ruwan ambaliya ba zai iya kashe wutar ƙauna ba. Koguna cike da ruwa ba za su iya share ƙauna ba.” b (W. Waƙ. 8:​6, 7) Yadda wannan nassin ya kwatanta ƙauna ta gaskiya yana da ban shaꞌawa, ko ba haka ba? Wannan abin ban ƙarfafa ne ga maꞌaurata. Ya nuna cewa za ku iya nuna wa juna ƙauna marar canjawa.

2. Mene ne dole mata da miji su yi idan ba sa son ƙaunarsu ta yi sanyi?

2 Idan maꞌaurata suna so su ƙaunaci juna muddin ransu, za su iya yin hakan, domin a hannunsu yake. Alal misali, idan aka hura wuta, wutar za ta ci gaba da ci muddin an ci gaba da ƙara mata itace. Amma idan ba a yi hakan ba, wutar za ta mutu. Haka ma, maꞌaurata za su iya ci gaba da ƙaunar juna muddin ransu idan suna ƙarfafa ƙaunar da ke tsakaninsu. Wani lokaci, maꞌaurata za su ga cewa ƙaunarsu tana yin sanyi, musamman idan suna fama da matsalar kuɗi, ko rashin lafiya, ko kuma renon yara. Don haka idan kuna da aure, me zai taimaka muku ku sa ‘harshen wuta na Ubangiji’ ya ci gaba da ci a iyalinku? A wannan talifin, za mu tattauna abubuwa uku da za su taimaka muku ku ci gaba da ƙaunar juna, kuma ku ji daɗin aurenku. c

KU CI GABA DA ƘARFAFA DANGANTAKARKU DA JEHOBAH

Kamar Yusufu da Maryamu, mata da miji suna bukatar su kasance da dangantaka mai kyau da Jehobah (Ka duba sakin layi na 3)

3. Idan mata da miji suna ƙaunar Jehobah sosai, ta yaya hakan zai taimaka musu su ci gaba da ƙaunar juna? (Mai-Wa’azi 4:12) (Ka kuma duba hoton.)

3 Idan namiji da mace suna so su sa ‘harshen wuta na Ubangiji’ ya ci gaba da ci a tsakaninsu, dole ne kowannensu ya sa ƙwazo don ya kusaci Jehobah sosai. Ta yaya kusantar Jehobah zai taimaka wa aurensu? Idan mata da miji suna ƙaunar Jehobah sosai, za su so bin shawararsa, kuma hakan zai taimaka musu su iya guje wa matsaloli da za su rage ƙaunar da ke tsakaninsu, ko kuma su magance matsalolin. (Karanta Mai-Wa’azi 4:12.) Waɗanda suke ƙaunar Jehobah sukan yi ƙoƙari su kasance da halaye irin na Jehobah, kamar yin alheri da haƙuri da kuma yafiya. (Afis. 4:32–5:1) Idan maꞌaurata suna nuna irin halayen nan, zai yi musu sauƙi su ci gaba da ƙaunar juna. Wata ꞌyarꞌuwa mai suna Lena, da ta fi shekaru 25 da aure ta ce: “Idan mutum yana ƙaunar Jehobah, ba zai yi maka wuya ka so shi kuma ka daraja shi ba.”

4. Me ya sa Jehobah ya zaɓi Yusufu da Maryamu su zama iyayen Almasihu?

4 Ga wani misali a Littafi Mai Tsarki. Akwai mutane da yawa da suka fito daga zuriyar Dauda, amma da Jehobah yake so ya zaɓi waɗanda za su haifi Almasihu, Yusufu da Maryamu ya zaɓa. Me ya sa? Domin su biyun suna da dangantaka mai kyau da Jehobah. Kuma Jehobah ya san cewa ba za su yi wasa da faranta masa rai a aurensu ba. Maꞌaurata, me za ku koya daga wurin Yusufu da Maryamu?

5. Me magidanta za su iya koya daga wurin Yusufu?

5 Yusufu ya dinga bin abin da Jehobah ya ce, kuma hakan ya sa ya ƙara zama mijin kirki. Aƙalla sau uku, ya samu umurni daga wurin Jehobah dangane da iyalinsa, kuma a dukan lokutan nan, bai ɓata lokaci wajen yin abin da Jehobah ya ce ba, komen wuyarsa. (Mat. 1:​20, 24; 2:​13-15, 19-21) Biyayya da Yusufu ya yi, ta sa ya kāre matarsa Maryamu kuma ya kula da ita. Ba kwa ganin abin da Yusufu ya yi ya sa Maryamu ta ƙara ƙaunarsa kuma ta daraja shi sosai? Mazaje, za ku iya bin misalin Yusufu ta wajen bin shawarwarin da ke Kalmar Allah a kan yadda za ku kula da iyalinku. d Idan kuna bin abin da Littafi Mai Tsarki ya ce ko da yin hakan yana da wuya, zai nuna cewa da gaske kuna ƙaunar matanku, kuma zai kyautata zamanku. Wata ꞌyarꞌuwa daga ƙasar da ake kira Vanuatu, ta fi shekaru 20 da aure. ꞌYarꞌuwar ta ce, “Idan na ga maigidana yana neman ja-gorancin Jehobah kuma yana bin ja-gorancin, abin yana sa in ƙara girmama shi. Yana ba ni kwanciyar hankali, kuma ba na shakkar shawarwarin da yake yankewa.”

6. Me mata za su iya koya daga wurin Maryamu?

6 Maryamu ita ma tana da dangantaka mai kyau da Jehobah. Ba ta dogara da mijinta kawai ba. Ta san nassosi sosai. e (Luk. 1:46) Ta kuma keɓe lokacin yin tunani a kan abin da take koya. (Luk. 2:​19, 51) Ba shakka, yadda maryamu take ƙaunar Jehobah ya sa ta ƙara zama macen kirki. A yau ma, akwai mata da suke iya ƙoƙarinsu su yi kamar Maryamu. Misali, wata ꞌyarꞌuwa mai suna Emiko ta ce: “Kafin in yi aure, ina da ayyukan ibada da nake yi a-kai-a-kai. Amma da na yi aure, maigidana ne yake mana adduꞌa, kuma shi yake mana ja-goranci a ibada ta iyali. Don haka, a-kwana-a-tashi, na soma dogara a kansa. Amma na gano cewa ni ne nake da hakkin kiyaye dangantakata da Jehobah. Don haka, yanzu na keɓe lokaci da zan dinga yin adduꞌa da kaina, ina karanta Littafi Mai Tsarki da kuma yin tunani a kai.” (Gal. 6:5) Mata, idan kuka ci gaba da ƙarfafa dangantakarku da Jehobah, hakan zai sa mazajenku su yabe ku, kuma su ƙara ƙaunarku.​—K. Mag. 31:30.

7. Me maꞌaurata za su iya koya daga wurin Yusufu da Maryamu game da bauta ma Jehobah tare?

7 Ƙari ga haka, Yusufu da Maryamu sun yi abubuwa da za su sa su daɗa kusantar Jehobah tare. Sun san muhimmancin bauta wa Jehobah tare a matsayin iyali. (Luk. 2:​22-24, 41; 4:16) Ba mamaki hakan bai yi musu sauƙi ba, musamman ma lokacin da suka samu ƙarin yara. Amma sun yi iya ƙoƙarinsu. Wannan misali ne mai kyau ga maꞌaurata a yau. Idan kuna da yara kamar Yusufu da Maryamu, wani lokaci ba zai yi muku sauƙi ku halarci taro ko ku yi ibada ta iyali ba. Zai ma iya yi muku wuya ku nemi lokacin da za ku dinga yin adduꞌa da yin nazari ku biyu. Amma ku tuna cewa, idan kuna bauta ma Jehobah tare, za ku ƙara kusantar Jehobah da kuma junanku. Don haka, kar ku yi wasa da ibadarku.

8. Idan akwai matsala tsakanin mata da miji, me zai taimaka musu su ji daɗin yin ibada ta iyali?

8 Idan akwai matsala a tsakaninku kuma fa? Wataƙila ba za ku so ku yi ibada ta iyali tare ba. In haka ne, ku soma da tattauna wani abin da ku biyun kuke so, wanda ba zai ci lokaci ba. Hakan zai taimaka muku ku ƙara kusantar juna, kuma ku soma yin abubuwan ibada tare.

KU DINGA KASANCEWA TARE DA JUNA

9. Me ya sa maꞌaurata suke bukatar kasancewa tare?

9 Maꞌaurata, wani abin da zai sa ku ƙara ƙaunar juna shi ne, idan kuna kasancewa tare. Hakan zai taimaka muku ku riƙa sanin abin da ke zuciyar junanku da kuma yadda kuke ji. (Far. 2:24) Abin da wata mai suna Lilia da maigidanta Ruslan suka gano ke nan bayan aurensu fiye da shekaru 15 da suka shige. Lilia ta ce: “Mun zata za mu dinga samun isasshen lokacin kasancewa tare, amma hakan bai faru ba. Ayyuka sun bi sun shawo kanmu. Ga na gida, ga na wurin aiki, sai ga kuma renon yara. Da haka muka gano cewa idan ba mu nemi lokacin kasancewa tare ba fa, ƙaunarmu za ta yi sanyi.”

10. Ta yaya maꞌaurata za su bi shawarar da ke Afisawa 5:​15, 16?

10 Me zai taimaka wa maꞌaurata su dinga samun lokacin kasancewa tare? Kuna bukatar ku zaɓi lokacin da za ku dinga kasancewa tare. (Karanta Afisawa 5:​15, 16.) Wani ɗanꞌuwa mai suna Uzondu daga Najeriya ya ce: “Idan ina shirya abubuwa da zan yi, nakan shirya har da lokacin da zan kasance da matata, kuma ba na wasa da wannan lokacin.” (Filib. 1:10) Wata ꞌyarꞌuwa mai suna Anastasia wadda mijinta mai kula da daꞌira ne a Moldova, ta faɗi yadda take amfani da lokacinta da kyau. Ta ce: “Idan maigidana yana yin aikinsa, ni ma nakan yi amfani da lokacin in yi nawa ayyukan da ya kamata in yi. Hakan yana ba mu damar kasancewa tare in ya gama.” Amma idan samun lokacin kasancewa tare yana yi muku wuya don yanayin aikinku kuma fa?

Me da me za ku iya yi tare? (Ka duba sakin layi na 11-12)

11. Waɗanne ayyuka ne Biriska da Akila suka riƙa yi tare?

11 Maꞌaurata za su iya bin halin Biriska da Akila waɗanda maꞌaurata ne da Kiristoci a ƙarni na farko suke ƙaunarsu sosai. (Rom. 16:​3, 4) Littafi Mai Tsarki bai faɗi abubuwa da yawa game da aurensu ba. Amma ya nuna cewa suna aiki da waꞌazi da kuma taimaka wa mutane tare. (A. M. 18:​2, 3, 24-26) A Littafi Mai Tsarki, idan aka ambaci sunan Biriska, za ka ji an ambaci Akila.

12. Mene ne mata da miji za su iya yi don su ƙara samun lokacin kasancewa tare? (Ka kuma duba hoton.)

12 Ta yaya maꞌaurata za su bi halin Biriska da Akila a yau? Ku yi tunanin ayyuka da yawa da kuke bukatar yi. Za ku iya yin wasu daga cikin ayyukan nan tare? Alal misali, Biriska da Akila sun dinga yin waꞌazi tare. Ku ma kuna shirya yadda za ku riƙa yin waꞌazi tare? Biriska da Akila sun kuma yi aiki tare. Ko da ba kwa aiki iri ɗaya, za ku iya yin ayyukan gida tare. (M. Wa. 4:9) Idan kuka yi wani aiki tare, hakan zai haɗa kanku, kuma zai ba ku zarafin tattaunawa. Robert da Linda sun fi shekaru 50 da aure. Robert ya ce: “A gaskiya ba ma yawan samun lokacin yin nishaɗi tare. Amma idan ni da matata muka wanke kwanuka tare, ko na fita ina cire ciyawa kuma ta zo tana taya ni, nakan yi farin ciki sosai. Yin abubuwa tare yana ƙara danƙon zumuncinmu, kuma ƙaunarmu sai ƙaruwa take yi.”

13. Idan maꞌaurata suna so su ci gaba da kusantar juna, me zai taimaka musu?

13 Amma fa ku tuna cewa kasancewa tare, ba shi ne kawai zai sa ku kusaci juna ba. Wata mata a ƙasar Brazil ta ce: “A yau, akwai abubuwa da yawa da sukan ɗauke hankalin mutum. Don haka, za mu iya yin tsammanin cewa muna tare don muna zama a gida ɗaya, amma ba haka ba ne. Na gano cewa ba kawai kasancewa tare muke bukatar mu yi ba. Idan muna a tare ɗin ma, ya kamata in ba wa maigidana hankalina.” Ku ga abin da wani mai suna Bruno da matarsa Tays suka yi don su tabbata cewa suna ba wa juna hankalinsu. Bruno ya ce: “Idan muna tare, mukan ajiye wayoyinmu a gefe don mu ji daɗin kasancewa tare.”

14. Idan maꞌaurata ba sa jin daɗin kasancewa tare, me zai taimaka musu?

14 Amma idan ba kwa jin daɗin kasancewa tare kuma fa? Ƙila don abubuwan da kuke son yi ba iri ɗaya ba ne ko akwai wani abu game da matarka ko mijinki da ba ki so, me za ku yi? Ku tuna da wutar da muka ambata dazu. Ba nan take ne wutar take fara ci sosai ba. Akan soma ne da ƙananan itace. A hankali sai a dinga ƙara manyan itace har wutar ta fara ci sosai. Haka ma, zai fi alheri idan kuka soma da yin abubuwa tare na ɗan ƙanƙanin lokaci kowace rana. Ku dai tabbata cewa abu ne da ku biyun kuke son yi, ba abin da zai jawo rikici ba. (Yak. 3:18) Idan kuka soma da-kaɗan-da-kaɗan, ƙila ku ga ƙaunar da kuke yi wa juna ta ƙaru.

KU DINGA GIRMAMA JUNA

15. Me ya sa maꞌaurata suke bukatar su riƙa girmama juna?

15 Bangirma yana da muhimmanci a zaman aure. Kamar iska yake. Idan babu iska, wuta za ta mutu. Haka ma, idan maꞌaurata ba sa girmama juna, ƙaunar da take tsakaninsu za ta yi saurin yin sanyi. Amma idan maꞌaurata suna ƙoƙari su girmama juna, hakan zai taimaka musu su ci gaba da ƙaunar juna. Amma fa, ba kai ne za ka ce kana girmama matarka ba, ko ki ce kina girmama mijinki ba. Abin shi ne, matarka ko mijinki yana ji cewa kina girmama shi kuwa? Penny da Aret, sun fi shekara 25 da aure. Penny ta ce: “Yadda muke girmama juna ya sa muna ƙaunar juna a iyalinmu. Mukan gaya wa juna yadda muke ji a sake, don mun san cewa muna daraja raꞌayin juna.” To me za ka yi don ka sa matarka, ko ki sa maigidanki ya ji cewa kina daraja shi? Bari mu tattauna misalin Ibrahim da Saratu.

Maigida da yake ƙaunar Jehobah zai nuna cewa yana daraja matarsa ta wajen sauraronta da kyau (Ka duba sakin layi na 16)

16. Mene ne magidanta za su iya koya daga wurin Ibrahim? (1 Bitrus 3:7) (Ka kuma duba hoton.)

16 Ibrahim ya girmama Saratu. Ya saurare ta kuma ya yi laꞌakari da yadda za ta ji. Akwai lokacin da ran Saratu ya ɓace kuma ta gaya wa maigidanta yadda take ji, har ma ta ce laifinsa ne. Ibrahim ya amsa da faɗa ne? Aꞌa. Don ya san cewa Saratu tana masa ladabi kuma ta saba tallafa masa. Ibrahim ya saurare ta kuma ya yi ƙoƙarin magance matsalar. (Far. 16:​5, 6) Me wannan ya koya mana? Magidanta, kuna da ikon tsai da shawarwari a madadin iyalinku. (1 Kor. 11:3) Amma fa, zai fi dacewa ka tattauna da matarka kafin ka yanke shawara. Musamman ma idan abin zai shafe ta. (1 Kor. 13:​4, 5) Wani lokaci, wani abu yana iya damun matarka kuma mai yiwuwa za ta so ta bayyana yadda take ji. Idan ka saurare ta da kyau, hakan zai nuna cewa kana girmama ta. (Karanta 1 Bitrus 3:7.) Wani ɗanꞌuwa mai suna Dmitry da matarsa Angela sun kusan shekaru 30 da aure. Angela ta bayyana abin da ya sa take ji cewa maigidanta yana girmama ta. Ta ce: “Idan raina ya ɓace, ko ina dai so in gaya wa maigidana wani abu, yakan kasa kunne ya saurare ni. Ko da yaya na yi maganar, yakan saurare ni da haƙuri.”

17. Mene ne mata za su iya koya daga wurin Saratu? (1 Bitrus 3:​5, 6)

17 Saratu ta girmama maigidanta ta wajen bin umurninsa. (Far. 12:5) Akwai lokacin da Ibrahim ya samu baƙi babu zato, kuma ya so ya yi musu karamci. Sai ya ce wa Saratu ta bar abin da take yi kuma ta je ta yi musu abin da za su ci. (Far. 18:6) Nan da nan Saratu ta yi abin da Ibrahim ya ce. Mata, za ku iya yin koyi da Saratu ta wajen bin umurnin mazajenku. Idan kuna hakan, za ku kyautata zamanku. (Karanta 1 Bitrus 3:​5, 6.) Ɗanꞌuwa Dmitry da muka ambata a sakin layin da ya gabata, ya bayyana abin da ya sa yake ji cewa matarsa tana girmama shi. Ya ce: “Nakan ji daɗi idan na ga matata tana ƙoƙari ta bi abin da na ce, ko da ba ta so hakan ba. Idan ma abin bai gama lafiya ba, ba ta sūka na.” Hakika, idan mutum yana daraja ka, za ka so shi!

18. Ta yaya maꞌaurata za su amfana idan suka yi iya ƙoƙarinsu don su ci gaba da ƙaunar juna?

18 A yau, burin Shaiɗan shi ne ya ga ya sa maꞌaurata Kiristoci su daina ƙaunar juna. Ya san cewa idan mata da miji suka daina ƙaunar juna, hakan zai iya sa su daina ƙaunar Jehobah. Amma idan har ƙauna ta gaskiya ce, Shaiɗan ba zai yi nasara ba. Don haka, bari ƙauna da ke tsakaninku ta zama kamar wadda aka kwatanta a littafin Waƙar Waƙoƙi. Ku ƙudura cewa za ku sa Jehobah farko a aurenku. Ku nemi lokacin kasancewa tare, kuma ku dinga girmama juna. Idan kuka yi hakan, aurenku zai faranta ma Jehobah rai, wanda shi ne tushen ƙauna ta gaskiya. Kuma kamar wuta da ake kula da ita sosai, ƙaunarku za ta ci gaba da ci muddin kuna raye.

WAƘA TA 132 Yanzu Mun Zama Ɗaya

a Aure kyauta ne da Jehobah ya ba wa ꞌyan Adam. Idan namiji da tamace suka yi aure, za su iya nuna wa juna ƙauna a hanya ta musamman. Amma wani lokaci, wannan ƙaunar takan yi sanyi. Idan kuna da aure, wannan talifin zai taimaka muku ku san yadda za ku ci gaba da ƙaunar juna, kuma ku ji daɗin aurenku.

b Littafi Mai Tsarki ya ce ƙauna ‘harshen wuta na Ubangiji’ ne, domin Jehobah shi ne tushen irin wannan ƙaunar. Wannan ƙaunar ba ta canjawa kuma ba ta ƙarewa.

c Ko da mijinki ko matarka ba ta bauta ma Jehobah, shawarwarin da za a bayar a wannan talifin, za su iya taimaka maka sosai.​—1 Kor. 7:​12-14; 1 Bit. 3:​1, 2.

d Alal misali, ka duba shawarwari masu kyau da suke jerin talifofin nan, “Taimako Don Iyali.” Za ka iya samunsa a jw.org/ha da kuma JW Library®.