Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 21

Yadda Jehobah Yake Amsa Adduꞌoꞌinmu

Yadda Jehobah Yake Amsa Adduꞌoꞌinmu

“Kowane lokacin da muka roƙe shi wani abu, mun sani cewa za mu sami abin da muka roƙa.”​—1 YOH. 5:15.

WAƘA TA 41 Allah Ka Ji Roƙona

ABIN DA ZA A TATTAUNA a

1-2. Wace shakka ce za mu iya yi game da adduꞌoꞌinmu?

 KA TAƁA yin shakkar cewa Jehobah yana amsa adduꞌoꞌinka? Idan haka ne, ba kai kaɗai ka taɓa jin haka ba. ꞌYanꞌuwa maza da mata da yawa sun yi wannan shakkar musamman ma saꞌad da suke fama da matsaloli masu wuya. Idan mu ma muna fama da wata matsala, zai iya yi mana wuya mu yarda cewa Jehobah yana amsa adduꞌoꞌinmu.

2 Bari mu bincika abin da ya tabbatar mana cewa Jehobah yana amsa adduꞌoꞌin bayinsa. (1 Yoh. 5:15) Za mu kuma tattauna tambayoyin nan: Me ya sa a wasu lokuta mukan ga kamar Jehobah ba ya amsa adduꞌoꞌinmu? Ta waɗanne hanyoyi ne Jehobah yake amsa adduꞌoꞌinmu a yau?

JEHOBAH ZAI IYA AMSA ADDUꞌARMU YADDA BA MU ZATA BA

3. Me ya sa Jehobah yake so mu yi adduꞌa gare shi?

3 Littafi Mai Tsarki ya tabbatar mana cewa Jehobah yana ƙaunar mu sosai kuma yana ɗaukan mu da daraja. (Hag. 2:7; 1 Yoh. 4:10) Shi ya sa ya gaya mana mu yi adduꞌa gare shi don ya taimaka mana. (1 Bit. 5:​6, 7) Yana so ya taimaka mana mu ci gaba da zama aminansa kuma mu jimre matsalolin da muke fuskanta.

Jehobah ya amsa adduꞌoꞌin Dauda ta wajen ceton shi daga maƙiyansa (Ka duba sakin layi na 4)

4. Ta yaya muka san cewa Jehobah yana amsa adduꞌoꞌin bayinsa? (Ka kuma duba hoton.)

4 Mukan karanta a Littafi Mai Tsarki cewa Jehobah ya amsa adduꞌoꞌin bayinsa. Za ka iya tuna ɗaya daga cikin su? Akwai Sarki Dauda. A dukan rayuwarsa, ya fuskanci maƙiya masu haɗari kuma a kowane lokaci yakan nemi taimakon Jehobah. Akwai lokacin da ya roƙi Jehobah yana cewa: “Ji adduꞌata, ya Yahweh, cikin amincinka, kasa kunne ga kukana, cikin adalcinka, amsa mini!” (Zab. 143:1) Jehobah ya amsa adduꞌar Dauda kuma ya cece shi. (1 Sam. 19:​10, 18-20; 2 Sam. 5:​17-25) Hakan ya sa Dauda ya kasance da tabbaci kuma ya ce: “Yahweh yana kurkusa ga masu kira gare shi.” Mu ma za mu iya kasance da irin wannan tabbacin.​—Zab. 145:18.

Jehobah ya amsa adduꞌoꞌin Bulus ta wajen ba shi ƙarfin jimre matsalar da yake fama da ita (Ka duba sakin layi na 5)

5. A kowane lokaci ne Jehobah yake amsa adduꞌoꞌin bayinsa yadda suka yi tsammani? Ka ba da misali. (Ka kuma duba hoton.)

5 Mai yiwuwa Jehobah ba zai amsa adduꞌoꞌinmu yadda muka yi tsammani ba. Abin da ya faru da manzo Bulus ke nan. Ya gaya wa Jehobah ya cire matsalar da ta zama masa “ƙaya a jiki.” Bulus ya yi adduꞌa game da wannan matsalar har sau uku. Shin Jehobah ya amsa adduꞌoꞌin nan? Ƙwarai kuwa, amma ba yadda Bulus ya yi tsammani ba. Maimakon Jehobah ya cire matsalar gabaki ɗaya, ya ba wa Bulus ƙarfin jimre matsalar don ya ci gaba da bauta masa da aminci.​—2 Kor. 12:​7-10.

6. Me ya sa wasu lokuta mukan ga kamar Jehobah ba ya amsa adduꞌoꞌinmu?

6 Mu ma Jehobah zai iya amsa adduꞌoꞌinmu yadda ba mu zata ba. Mu kasance da tabbaci cewa Jehobah ya san hanya mafi dacewa da zai taimaka mana. Zai ma iya yin “abubuwa fiye da dukan abin da za mu roƙa, ko abin da za mu yi tunaninsa.” (Afis. 3:20) Saboda haka, zai iya amsa adduꞌoꞌinmu a lokaci ko kuma hanyar da ba mu zata ba.

7. Me zai iya sa mu canja abin da muka roƙa? Ka ba da misali.

7 Idan muka fahimci nufin Jehobah da kyau, wataƙila hakan zai sa mu canja abin da muka roƙa. Ku yi laꞌakari da misalin Martin Poetzinger. Jim kaɗan bayan da Ɗanꞌuwa Poetzinger ya yi aure, an tsare shi a sansanin Nazi. Da farko, ya roƙi Jehobah ya fitar da shi daga wannan sansanin don ya kula da matarsa kuma ya soma yin waꞌazi. Amma bayan makonni biyu, ya ga cewa babu alamar za a sake shi. Sai ya yi adduꞌa ya ce: “Jehobah ka nuna mini abin da kake so in yi.” Bayan haka, ya soma tunani a kan abin da sauran ꞌyanꞌuwa a sansanin suke fama da shi. Da yawa daga cikinsu suna tunani game da matansu da yaransu. Sai Ɗanꞌuwa Poetzinger ya yi adduꞌa ya ce: “Jehobah na gode da wannan sabon aiki da ka ba ni. Ka taimaka mini don in iya ƙarfafa ꞌyanꞌuwana.” Ɗanꞌuwa Poetzinger ya yi shekaru tara a sansanin yana ƙarfafa ꞌyanꞌuwa.

8. Wane abu mai muhimmanci ne muke bukatar mu riƙa tunawa saꞌad da muke adduꞌa?

8 Ya kamata mu tuna cewa Jehobah yana da lokacin da ya adana da zai cika nufinsa. Ɗaya daga cikin nufin Jehobah shi ne ya cire dukan matsalolin da muke fuskanta a yau, kuma hakan ya ƙunshi balaꞌoꞌi, da cututtuka da kuma mutuwa. Jehobah zai yi amfani da Mulkinsa don ya cim ma hakan. (Dan. 2:44; R. Yar. 21:​3, 4) Amma kafin lokacin ya zo, Jehobah ya ƙyale Shaiɗan ya mulki duniyar nan. b (Yoh. 12:31; R. Yar. 12:9) Idan Jehobah yana magance matsalolin da ꞌyan Adam suke fuskanta a yau, abin zai yi kamar Shaiɗan ne yake nasara a mulkinsa. Ko da yake muna bukatar mu jira Jehobah ya cika wasu alkawuransa, Jehobah bai bar mu haka ba, yana taimaka mana ko a yanzu ma. Bari mu tattauna wasu hanyoyin da Jehobah yake taimaka mana.

HANYOYIN DA JEHOBAH YAKE AMSA ADDUꞌOꞌINMU A YAU

9. Ta yaya Jehobah yake taimaka mana mu yanke shawarwari? Ka ba da misali.

9 Yana ba mu hikima. Jehobah ya yi alkawari zai ba mu hikima da za ta taimaka mana mu yanke shawarwari masu kyau. Muna bukatar hikimar Allah musamman ma saꞌad da za mu yanke shawarwarin da za su shafi rayuwarmu, kamar ko za mu yi aure ko ba za mu yi ba. (Yak. 1:5) Ku yi laꞌakari da wata ꞌyarꞌuwa marar aure mai suna Maria. c Tana jin daɗin yin hidimar majagaba, sai ta haɗu da wani ɗanꞌuwa. Ta ce: “Yayin da muke daɗa sanin juna, ƙaunarmu ta ƙara yin zurfi. Na san cewa ina bukatar in tsai da shawara. Na yi adduꞌa sosai game da batun. Ina bukatar taimakon Jehobah amma na san cewa ba shi ne zai tsai da min shawarar ba.” Ta ce Jehobah ya amsa adduꞌar da ta yi cewa ya ba ta hikima. Ta yaya? Ta bincika littattafanmu kuma ta samo talifofin da suka amsa tambayoyin da take da su. Ƙari ga haka, ta bi shawarar da mahaifiyarta wadda take bauta wa Jehobah da aminci ta ba ta. Shawarar da ta ba ta, ta taimaka wa Maria ta san abin da take so. A ƙarshe dai, Maria ta yanke shawarar da ta dace.

Ta yaya Jehobah yake ba mu ƙarfin jimrewa? (Ka duba sakin layi na 10)

10. Bisa ga abin da ke 2 Korintiyawa 4:​7, mene ne Jehobah zai yi don ya taimaka wa bayinsa? Ka ba da misali. (Ka kuma duba hoton.)

10 Yana ba mu ƙarfin jimrewa. Kamar yadda Jehobah ya yi wa manzo Bulus, haka ma zai iya ba mu ƙarfin jimre matsalolin da muke fuskanta. (Karanta 2 Korintiyawa 4:7.) Ku yi laꞌakari da yadda Jehobah ya taimaka wa ɗanꞌuwa Benjamin ya jimre wani yanayi mai wuya. Benjamin ya yi yawancin rayuwarsa a matsayin matashi a sansanin ꞌyan gudun hijira tare da iyayensa da ꞌyanꞌuwansa a Afirka. Benjamin ya ce: “Na yi adduꞌa sosai ga Jehobah, ina roƙon sa ya taimaka mini in yi abin da zai faranta masa rai. Jehobah ya amsa adduꞌoꞌina ta wajen ba ni kwanciyar hankali da ƙarfin zuciyar yin waꞌazi. Ya kuma ba ni littattafan da za su taimaka mini in ci gaba da bauta masa.” Ya ci gaba da cewa: “Karanta yadda Jehobah ya taimaka wa ꞌyanꞌuwa maza da mata su jimre, ya taimaka mini in riƙe amincina.”

Shin Jehobah ya taɓa taimaka maka ta wajen ꞌyanꞌuwa maza da mata? (Ka duba sakin layi na 11-12) d

11-12. Ta yaya Jehobah yake amfani da ꞌyanꞌuwanmu don ya amsa adduꞌoꞌinmu? (Ka kuma duba hoton.)

11 Yana amfani da ꞌyanꞌuwanmu Kiristoci. A dare na ƙarshe kafin Yesu ya mutu, ya yi adduꞌa sosai. Ya roƙi Jehobah kada ya bar mutane su ɗauke shi a matsayin mai saɓo kuma su hukunta shi saboda hakan. Maimakon Jehobah ya yi hakan, ya aika wani malaꞌika wurin Yesu don ya ƙarfafa shi. (Luk. 22:​42, 43) Mu ma Jehobah zai iya sa ꞌyanꞌuwanmu su kira mu ko su ziyarce mu don su ƙarfafa mu. Dukanmu za mu iya neman zarafin gaya wa ꞌyanꞌuwanmu “kalmar ƙarfafawa.”​—K. Mag. 12:25.

12 Ku yi laꞌakari da misalin wata ꞌyarꞌuwa mai suna Miriam. Bayan mijinta ya yi wasu makonni da mutuwa, Miriam ta ci gaba da baƙin ciki kuma ita kaɗai ce a gida. Ta yi ta kuka sosai kuma tana bukatar wanda za ta yi magana da shi. Ta ce: “Ba ni da ƙarfin da zan iya kiran wani, don haka na yi adduꞌa ga Jehobah. Yayin da nake kan kuka da adduꞌa, sai wayata ta soma kara. Wani dattijo ne ya kira ni, kuma shi amininmu ne.” Dattijon da matarsa sun ƙarfafa Miriam. Tana da tabbacin cewa Jehobah ne ya sa ɗanꞌuwan nan ya kira ta.

Ta yaya Jehobah zai iya sa wasu su taimaka mana? (Ka duba sakin layi na 13-14)

13. Ka ba da misalin yadda Jehobah yake amsa adduꞌoꞌinmu ta wajen mutanen da ba sa bauta masa.

13 Yana iya yin amfani da mutanen da ba sa bauta masa. (K. Mag. 21:1) A wasu lokuta, Jehobah yana amsa adduꞌoꞌin mutanensa ta wajen sa mutanen da ba sa bauta masa su taimake su. Alal misali, saꞌad da Nehemiya ya roƙi Sarki Artazekzes ya bar shi ya je Urushalima don ya taimaka wa Yahudawa su sake gina birnin, Jehobah ya sa sarkin ya amince da hakan. (Neh. 2:​3-6) A yau ma, Jehobah zai iya amfani da waɗanda ba sa bauta masa don su taimaka mana saꞌad da muke cikin matsala.

14. Mene ne ya ƙarfafa ka game da labarin Soo Hing? (Ka kuma duba hoton.)

14 Wata ꞌyarꞌuwa mai suna Soo Hing ta ce Jehobah ya taimaka mata ta wajen likitanta. Ɗanta ya yi fama da cututtukan ƙwaƙwalwa da yawa. Ƙari ga haka, saꞌad da ya yi mugun hatsari, ita da maigidanta sun bar aikinsu don su iya kula da shi. Hakan ya sa sun shiga rashin kuɗi. ꞌYarꞌuwa Soo Hing ta ce ta ji kamar ba za ta iya jimre matsalolin ba. Sai ta yi adduꞌa ga Jehobah tana neman taimakonsa. Likitan da yake kula da su ya soma neman hanyar da zai taimaka mata da iyalinta. Hakan ya sa gwamnati ta taimaka musu kuma sun samu gida mai sauƙin kuɗi. Daga baya Soo Hing ta ce: “Mun ga yadda Jehobah ya taimaka mana a yanayin nan. Da gaske shi ‘mai jin adduꞌoꞌi’ ne.”​—Zab. 65:2.

SAI DA BANGASKIYA ZA MU IYA GANIN YADDA JEHOBAH YAKE AMSA ADDUꞌOꞌINMU

15. Mene ne ya taimaka ma wata ꞌyarꞌuwa ta gano cewa Jehobah yana amsa adduꞌoꞌinta?

15 Ba a kowane lokaci ne Jehobah yake amsa adduꞌoꞌinmu a hanyoyi masu ban alꞌajibi ba. Amma yana amsawa ta wajen tanada mana abubuwan da muke bukata don mu ci gaba da bauta masa. Don haka, ku riƙa lura da yadda Jehobah yake amsa adduꞌoꞌinku. Wata ꞌyarꞌuwa mai suna Yoko ta ji kamar Jehobah ba ya amsa adduꞌoꞌinta. Sai ta soma lissafta abubuwan da ta roƙe shi. Bayan wasu lokuta, sai ta duba takardar da ta rubuta roƙe-roƙenta, kuma ta gano cewa Jehobah ya amsa yawancinsu har ma da waɗanda ta manta da su. Zai dace a wasu lokuta mu dakata kuma mu yi tunani a kan yadda Jehobah yake amsa adduꞌoꞌinmu.​—Zab. 66:​19, 20.

16. Ta yaya za mu nuna bangaskiya a batun adduꞌa? (Ibraniyawa 11:6)

16 Yin adduꞌa hanya ce da muke nuna bangaskiya. Amma za mu kuma nuna bangaskiya idan muna amincewa da yadda Jehobah yake amsa adduꞌoꞌinmu. (Karanta Ibraniyawa 11:6.) Ku yi laꞌakari da misalin ɗanꞌuwa Mike da matarsa Chrissy. Suna so su yi hidima a Bethel. Mike ya ce: “Mun yi shekaru da yawa muna cika fom ɗin yin hidima a Bethel kuma mun yi adduꞌa game da hakan sau da yawa. Amma ba a gayyace mu ba.” Mike da Chrissy sun ci gaba da kasance da tabbacin cewa Jehobah ya san hanyar da ta fi dacewa ya yi amfani da su. Sun ci gaba da yin iya ƙoƙarinsu yayin da suke yin hidima a inda akwai bukata da yin gine-gine. Yanzu sun zama masu kula da daꞌira. Mike ya ce: “Ba a kowane lokaci ne Jehobah ya amsa adduꞌoꞌinmu yadda muka yi tsammani ba, amma ya amsa su a hanyoyi da suka fi yadda muka yi tsammani.”

17-18. Bisa ga abin da ke Zabura 86:​6, 7, wane tabbaci ne za mu iya kasancewa da shi?

17 Karanta Zabura 86:​6, 7. Dauda yana da tabbacin cewa Jehobah ya ji adduꞌarsa kuma ya amsa. Kai ma za ka iya kasancewa da wannan tabbacin. Labaran da muka tattauna a wannan talifin sun tabbatar mana cewa Jehobah zai iya ba mu hikima da kuma ƙarfin jimre matsaloli. Zai iya yin amfani da ꞌyanꞌuwanmu maza da mata ko waɗanda ba sa bauta masa yanzu ya taimaka mana a wasu hanyoyi.

18 Ko da yake ba a kowane lokaci ne Jehobah zai amsa adduꞌoꞌinmu yadda muka yi tsammani ba, muna da tabbacin cewa zai amsa su. Zai ba mu ainihin abin da muke bukata a lokacin da ya dace. Don haka, ka ci gaba da yin adduꞌa, ka gaskata cewa zai amsa adduꞌoꞌinka, zai kula da kai yanzu kuma zai “ƙosar da kowane mai rai bisa ga bukatarsa” a sabuwar duniya.​—Zab. 145:16.

WAƘA TA 46 Muna Godiya, Ya Jehobah

a Jehobah ya ba mu tabbacin cewa zai amsa adduꞌoꞌinmu idan har sun jitu da nufinsa. Idan muna fuskantar matsaloli, za mu iya kasance da tabbacin cewa zai taimaka mana in mun ci gaba da bauta masa da aminci. Bari mu tattauna yadda Jehobah yake amsa adduꞌoꞌinmu.

b Don ka ga dalilin da ya sa Jehobah ya ƙyale Shaiɗan ya yi sarauta a duniya, ka duba talifin nan “Ka Mai da Hankali ga Batun da Ya Fi Muhimmanci,” da ke Hasumiyar Tsaro ta Yuni 2017.

c An canja sunayen.

d BAYANI A KAN HOTO: Wata mahaifiya da ꞌyarta sun je wata ƙasa a matsayin ꞌyan gudun hijira. ꞌYanꞌuwa Kiristoci sun marabce su da kyau kuma sun taimaka musu.