TALIFIN NAZARI NA 20
Yadda Za Mu Inganta Adduꞌoꞌinmu
“Ku faɗa masa dukan zuciyarku.”—ZAB. 62:8.
WAƘA TA 45 Abubuwan da Nake Tunani a Kai
ABIN DA ZA A TATTAUNA a
1. Mene ne Jehobah yake so bayinsa su riƙa yi? (Ka kuma duba hoton.)
IDAN muna bukatar ƙarfafa da kuma shawara, gun wa za mu je? Mun san amsar. Za mu iya zuwa gun Jehobah ta yin adduꞌa. Abin da Jehobah ya gaya mana mu yi ke nan. Yana so mu riƙa yin adduꞌa “babu fasawa.” (1 Tas. 5:17) Za mu iya yin adduꞌa ga Jehobah hankalinmu kwance, kuma mu nemi taimakonsa a dukan fannonin rayuwarmu. (K. Mag. 3:5, 6) Da yake Jehobah mai alheri ne sosai, ya ba mu dama mu yi adduꞌa gare shi ko da sau nawa ne a rana.
2. Me za mu tattauna a wannan talifin?
2 Muna godiya sosai don yadda Jehobah ya ba mu damar yin magana da shi. Amma da yake ayyuka suna mana yawa, zai iya mana wuya mu sami lokacin yin adduꞌa. Kuma wataƙila mu ga cewa ya kamata mu inganta adduꞌoꞌinmu. Abin farin cikin shi ne, za mu iya samun ƙarfafa da kuma shawarwari da za su taimaka mana a Littafi Mai Tsarki. A wannan talifin, za mu tattauna yadda za mu bi halin Yesu domin mu samu lokacin yin adduꞌa. Za mu kuma tattauna yadda za mu inganta adduꞌoꞌinmu ta wurin yin adduꞌa a kan abubuwa biyar masu muhimmanci.
YESU YA NEMI LOKACIN YIN ADDUꞌA
3. Mene ne Yesu ya sani game da adduꞌa?
3 Yesu ya san cewa Jehobah yana ɗaukan adduꞌoꞌinmu da muhimmanci. Tun kafin ya zo duniya, ya saba ganin Ubansa yana amsa adduꞌoꞌin bayinsa masu aminci. Alal misali, Yesu yana tare da Ubansa lokacin da ya amsa adduꞌar Hannatu, da Dauda, da Iliya da dai sauransu. (1 Sam. 1:10, 11, 20; 1 Sar. 19:4-6; Zab. 32:5) Shi ya sa Yesu ya ce wa mabiyansa su dinga yin adduꞌa da tabbacin cewa Allah zai ji su!—Mat. 7:7-11.
4. Wane darasi muka koya daga yadda Yesu ya yi adduꞌa?
4 Yesu ya kafa wa mabiyansa misali mai kyau ta yadda ya dinga yin adduꞌa ga Jehobah. Da yake hidimarsa, Yesu ya dinga yin adduꞌa. Shi mai ayyuka da yawa ne kuma a yawancin lokuta mutane suna tare da shi. Don haka, Yesu ya zaɓi lokacin da zai dinga yin adduꞌa. (Mar. 6:31, 45, 46) Akwai lokacin da ya tashi da sassafe don ya je inda babu kowa ya yi adduꞌa. (Mar. 1:35) Akwai kuma lokacin da ya kwana yana adduꞌa don ya iya tsai da wata shawara mai muhimmanci. (Luk. 6:12, 13) A daren da za a kama shi, Yesu ya yi ta yin adduꞌa domin ya san yana dab da fuskantar abu mafi wuya a hidimarsa a duniya.—Mat. 26:39, 42, 44.
5. Ta yaya za mu bi halin Yesu?
5 Misalin Yesu ya koya mana cewa komen yawan ayyukanmu, ya kamata mu keɓe lokaci musamman don yin adduꞌa. Za mu iya zaɓa mu dinga tashiwa da sassafe, ko kuma mu ce can da yamma ne za mu dinga yin adduꞌa. Hakan zai nuna wa Jehobah cewa muna godiya don wannan dama na musamman. Wata ꞌyarꞌuwa mai suna Lynne takan tuna yadda ta ji da ta gano cewa za ta iya yin adduꞌa ga Jehobah. Ta ce: “Da na gano cewa zan iya yin adduꞌa ga Jehobah a kowane lokaci, hakan ya sa na ji cewa Jehobah abokina ne na kurkusa, kuma ya kamata in kyautata adduꞌoꞌina.” Babu shakka, yawancinmu haka muke ji. Don haka, bari mu tattauna abubuwa masu muhimmanci guda biyar da za mu iya ambatawa a adduꞌarmu.
ABUBUWA BIYAR MASU MUHIMMANCI DA ZA MU IYA AMBATAWA
6. Kamar yadda Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 4:10, 11 suka ce, mene ne Jehobah ya cancanta?
6 Mu yabi Jehobah. Jehobah ya nuna wa manzo Yohanna wani wahayi mai ban mamaki. A wahayin, Yohanna ya ga dattawa 24 a sama suna masa sujada. Sun yabi Allah suna cewa ya cancanci ya karɓi “ɗaukaka, da girma, da iko.” (Karanta Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 4:10, 11.) Malaꞌiku masu aminci su ma suna da dalilai da dama na yabon Jehobah da kuma ɗaukaka shi. Don suna tare da shi a sama kuma sun san shi sosai. Suna ganin halayensa ta abubuwa da yake yi, kuma hakan yana motsa su su yabe shi.—Ayu. 38:4-7.
7. Me da me za mu iya yabon Jehobah a kai?
7 Mu ma zai dace mu dinga yabon Jehobah idan muna yin adduꞌa, ta wajen faɗin abubuwa da suka sa muke ƙaunarsa kuma muke girmama shi. Yayin da kake karanta Littafi Mai Tsarki kuma kake nazarin sa, ka yi ƙoƙari ka gano halayen Jehobah da suke burge ka. (Ayu. 37:23; Rom. 11:33) Saꞌan nan a cikin adduꞌarka, ka gaya masa yadda kake ji game da halayen. Za mu kuma iya yabon Jehobah don yadda yake taimaka mana da ꞌyanꞌuwanmu Kiristoci. Domin a koyaushe, Jehobah yana kula da mu kuma yana kāre mu.—1 Sam. 1:27; 2:1, 2.
8. Waɗanne dalilai ne muke da su na yin godiya ga Jehobah? (1 Tasalonikawa 5:18)
8 Mu gode wa Jehobah. Muna da dalilai da yawa na yin godiya ga Jehobah. (Karanta 1 Tasalonikawa 5:18.) Zai dace mu gode masa don duk wani abu mai kyau da muke da shi, domin kowace kyakkyawar kyauta daga wurinsa take. (Yak. 1:17) Misali, za mu iya gode wa Jehobah don yadda duniya take da kyau, da halittunsa masu ban mamaki. Za mu kuma iya yi masa godiya don ranmu, da iyalanmu, da abokanmu, da kuma bege da ya ba mu. Mu kuma gode masa don yadda ya ba mu dama mu zama abokansa.
9. Me ya sa muke bukatar yin ƙoƙari sosai don mu zama masu yin godiya ga Jehobah?
9 Muna bukatar mu natsu, mu yi tunani kafin mu ga dalilan da suka sa ya kamata mu gode wa Jehobah. Yawancin mutane a yau marasa godiya ne. Yawancin lokaci, abin da mutane suke so ne suke sa a gaba, maimakon su yi godiya don abin da suke da shi. Idan mu ma muka soma bin halinsu, roƙe-roƙe kawai za mu riƙa yi a adduꞌarmu. Don kar mu faɗa a wannan tarkon, dole mu ci gaba da lura da abubuwan da Jehobah yake mana kuma mu dinga gode masa.—Luk. 6:45.
10. Ta yaya halin godiya ya taimaka ma wata ꞌyarꞌuwa ta jimre? (Ka kuma duba hoton.)
10 Kasancewa da halin godiya zai iya taimaka mana mu jimre matsaloli. Wata ꞌyarꞌuwa mai suna Kyung-sook, da aka ba da labarinta a Hasumiyar Tsaro ta 15 ga Janairu, 2015, ta shaida hakan. Ta kamu da cutar kansa a huhunta. Ta ce: “Wannan cutar ta girgiza ni sosai. Na ji kamar na yi hasarar kome kuma hakan ya sa na tsorata ba kaɗan ba.” Me ya taimake ta ta iya jimrewa? Ta ce kowane dare kafin ta yi barci, takan hau saman gidansu kuma ta yi adduꞌa da babbar murya game da abubuwa guda biyar da Jehobah ya yi mata a ranar. Hakan yana sa ta wartsake kuma yana motsa ta ta nuna yadda take ƙaunar Jehobah. Ta fahimci cewa Jehobah yana taimaka mana a lokacin wahala kuma albarkun da muke samu sun fi matsalolin da muke fuskanta. Kamar ꞌyarꞌuwa Kyung-sook, mu ma muna da dalilai da yawa na yin godiya ga Jehobah ko da muna cikin matsala. Idan muna gode wa Jehobah saꞌad da muke adduꞌa, hakan zai taimaka mana mu jimre matsalolinmu kuma mu samu kwanciyar hankali.
11. Bayan da Yesu ya koma sama, me ya sa mabiyansa suka bukaci yin ƙarfin zuciya?
11 Mu roƙi Jehobah ya ba mu ƙarfin zuciyar yin waꞌazi. Da ya kusan komawa sama, Yesu ya tuna wa mabiyansa aikin da ya ba su na yin waꞌazi “a Urushalima, da cikin dukan yankin Yahudiya, da Samariya, har zuwa iyakar duniya.” (A. M. 1:8; Luk. 24:46-48) Jim kaɗan bayan hakan, sai shugabannin Yahudawa suka kama manzo Bitrus da Yohanna suka kai su gaban majalisa kuma suka ce musu su daina yin waꞌazi, har da yi musu barazana. (A. M. 4:18, 21) Me Bitrus da Yohanna suka yi?
12. Bisa ga Ayyukan Manzanni 4:29, 31, mene ne almajiran Yesu suka yi?
12 Bayan da shugabannin Yahudawa suka yi wa Bitrus da Yohanna barazana, sai Bitrus da Yohanna suka ce: “To, ko daidai ne a wurin Allah mu fi jin maganarku fiye da maganar Allah? Sai ku duba ku gani. Don mu kam, ba za mu iya yin shiru a kan abin da muka ji, muka kuma gani ba.” (A. M. 4:19, 20) Da aka saki Bitrus da Yohanna, sai almajiran gabaki ɗaya suka haɗa muryoyinsu suna roƙon Jehobah ya sa nufinsa ya tabbata. Sun ce: “Ka ba bayinka ƙarfin halin faɗin kalmarka babu tsoro.” Jehobah ya amsa wannan adduꞌar da suka yi da dukan zuciyarsu.—Karanta Ayyukan Manzanni 4:29, 31.
13. Me muka koya daga labarin Jin-hyuk?
13 Za mu iya yin koyi da almajiran Yesu ta wajen ci gaba da yin waꞌazi ko da hukuma ta ce mu daina yin hakan. Ka yi laꞌakari da labarin wani ɗanꞌuwa mai suna Jin-hyuk wanda aka tsare a kurkuku don ya ƙi yin aikin soja. A kurkukun, an sa shi ya riƙa kai ma wasu fursunoni abinci da wasu abubuwa da suke bukata, amma an dokace shi cewa kar ya yi zancen kome da su, har da na Littafi Mai Tsarki, ban da aikin da aka sa shi. Sai ya yi adduꞌa ya roƙi Jehobah ya ba shi ƙarfin zuciya da kuma hikima, don ya iya yin waꞌazi duk saꞌad da ya samu dama. (A. M. 5:29) Ya ce: “Jehobah ya amsa adduꞌata. Ya ba ni ƙarfin zuciya da basira har na iya soma nazari na minti biyar da ꞌyan kurkukun. Da dare kuma, nakan rubuta wasiƙun da zan ba su washe gari.” Mu ma za mu iya bin halin Jin-hyuk. Mu roƙi Jehobah ya ba mu ƙarfin zuciya da hikima. Ba shakka, Jehobah zai taimaka mana mu yi nasara a hidimarmu.
14. Me zai iya taimaka mana saꞌad da muke cikin matsala? (Zabura 37:3, 5)
14 Mu roƙi Jehobah ya taimake mu mu iya jimre matsalolinmu. Yawancinmu muna fama da matsaloli dabam-dabam. Ko rashin lafiya, ko rasuwar wani da muke ƙauna, ko wata matsala a iyalinmu, ko tsanantawa da dai sauransu. Annoba da tashe-tashen hankula sun sa jimre wa matsalolin nan ya ƙara yin wuya. Idan kana cikin matsala, ka faɗa wa Jehobah duk abin da ke zuciyarka. Ka bayyana masa abin da ke faruwa da kai kamar yadda za ka gaya wa amininka. Tabbas, Jehobah zai taimake ka, “zai lura da kai.”—Karanta Zabura 37:3, 5.
15. Ta yaya yin adduꞌa zai taimaka mana mu jimre azaba? Ka ba da misali.
15 Idan muka nace da yin adduꞌa, zai taimaka mana mu “yi haƙuri a cikin azaba.” (Rom. 12:12) Jehobah ya san matsalolin da bayinsa suke fuskanta. “Yakan kuma ji kukansu ya cece su.” (Zab. 145:18, 19) Wata majagaba mai suna Kristie ta ga tabbacin wannan. Shekarunta 29. Ana nan kawai sai ta soma ciwo iri-iri, kuma hakan ya sa ta shiga cikin damuwa sosai. Daga baya kuma ta samu labari cewa mahaifiyarta ta kamu da wata cuta mai kisa, kuma bai da magani. Kristie ta ce: “Na yi ta roƙon Jehobah ya ba ni ƙarfi in iya jimre matsalolina na kowace rana. Na ƙoƙarta in ci gaba da yin ayyukan ibadata, ina zuwa taro kuma ina yin nazari.” Ta ƙara da cewa: “Adduꞌa ce ta taimaka mini in jimre wannan yanayi mai muni. A kullum na san Jehobah yana nan, kuma wannan tunanin ya ƙarfafa ni ba kaɗan ba. Ko da yake matsalar ba ta tafi ba, Jehobah ya amsa adduꞌata. Ya ba ni salama da kwanciyar hankali.” A ko da yaushe, mu tuna cewa Jehobah “yana iya ceton masu halinsa daga cikin gwaje-gwajensu.”—2 Bit. 2:9.
16. Me ya sa muke bukatar taimakon Jehobah don kar mu faɗa wa jarabobi?
16 Mu roƙi Jehobah ya taimake mu kar mu faɗa wa jaraba. Da shike mu ajizai ne, kullum yana mana wuya mu yi abin da ya dace. Shaiɗan yana iya ƙoƙarinsa ya sa yin hakan ya ƙara yi mana wuya. Yakan yi amfani da abubuwan nishaɗi marasa kyau don ya ɓata tunaninmu. Irin nishaɗin nan zai iya sa mu yi tunanin abubuwa da ba su dace ba, da za su ƙazantar da mu kuma su sa mu yi zunubi.—Mar. 7:21-23; Yak. 1:14, 15.
17. Bayan mun roƙi Jehobah ya taimaka mana, me muke bukatar mu yi don kar mu faɗa cikin jaraba? (Ka kuma duba hoton.)
17 Sai da taimakon Jehobah za mu iya yin tsayayya da jaraba. A adduꞌar da Yesu ya koya wa mabiyansa, ya ce: “Kada ka kai mu cikin jarraba, amma ka tsare mu daga Mugun nan.” (Mat. 6:13) Jehobah yana so ya taimaka mana, amma muna bukatar mu roƙe shi ya yi hakan. Bayan mun roƙa, dole mu yi iya ƙoƙarinmu mu guji abin da zai sa mu yi zunubi. Za mu iya ɗaukan matakan da za su taimaka mana mu guji kallo, ko kuma karanta abubuwa marasa kyau da suke a koꞌina a yau. (Zab. 97:10) Karanta Littafi Mai Tsarki da kuma nazarin sa zai sa mu cika zuciyarmu da abubuwa masu kyau. Wani abin da zai kāre zuciyarmu kuma shi ne zuwa taro da kuma yin waꞌazi. Idan muna hakan, Jehobah ya ce ba zai bari a gwada mu fiye da ƙarfinmu ba.—1 Kor. 10:12, 13.
18. A batun yin adduꞌa, mene ne ya kamata kowannenmu ya yi?
18 Kowannenmu yana bukatar yin adduꞌa ga Jehobah sosai fiye da dā, don ya iya riƙe aminci ga Jehobah a wannan kwanaki na ƙarshe. Ka keɓe lokacin yin adduꞌa ga Jehobah kowace rana. Jehobah yana so mu ‘faɗa masa dukan zuciyarmu.’ (Zab. 62:8) Ka dinga yabon Jehobah kana gode masa don abubuwan da yake yi. Ka roƙe shi ya ba ka ƙarfin zuciya don ka iya yin waꞌazi. Ka roƙe shi ya taimake ka ka iya jimre matsalolin da kake fuskanta kuma ka ƙi faɗa wa jarabobi. Kada ka bar kome ya hana ka yin adduꞌa ga Jehobah a-kai-a-kai. Amma ta yaya Jehobah yake amsa adduꞌoꞌinmu? Abin da za mu tattauna a talifi na gaba ke nan.
WAƘA TA 42 Adduꞌar Bawan Allah
a Muna son adduꞌoꞌinmu su zama kamar wasiƙu da muka rubuta wa amininmu. Amma samun lokacin yin adduꞌa bai da sauƙi. Kuma zai iya yi mana wuya mu san abin da za mu yi adduꞌa a kai. Abubuwan da za mu tattauna a wannan talifin ke nan.