Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 24

Za Ka Iya Cim ma Makasudan da Ka Kafa a Bautarka ga Jehobah

Za Ka Iya Cim ma Makasudan da Ka Kafa a Bautarka ga Jehobah

“Kada mu gaji da yin abin da yake da kyau. Gama idan ba mu gaji muka bar ƙoƙari ba, lokaci zai zo da za mu yi girbi mai albarka.”​—GAL. 6:9.

WAƘA TA 84 Yin Hidima a Inda Akwai Bukata

ABIN DA ZA A TATTAUNA a

1. Wane abu ne yawancinmu muke fama da shi?

 SHIN ka taɓa kafa maƙasudi a hidimarka ga Jehobah kuma ka kasa cikawa? b Idan haka ne, ka san cewa ba kai kaɗai ba ne, ya taɓa faruwa da wasu ma. Alal misali, Ɗanꞌuwa Philip yana so ya riƙa yin adduꞌa a-kai-a-kai kuma ya inganta yadda yake yin adduꞌa, amma ya gagara samun lokacin yin hakan. ꞌYarꞌuwa Erika tana so ta riƙa zuwa taron fita waꞌazi a kan lokaci amma ta ci gaba da zuwa latti kusan kowane lokaci. Ɗanꞌuwa Tomáš ma ya sha yin iya ƙoƙarinsa don ya karanta Littafi Mai Tsarki gabaki ɗaya. Ya ce: “Ba na jin daɗin karanta Littafi Mai Tsarki. Na yi ƙoƙarin yin hakan sau uku amma in na fara, sai in tsaya a Littafin Firistoci.”

2. Me ya sa bai kamata mu yi sanyin gwiwa ba idan mun gagara cim ma maƙasudinmu?

2 Idan ka riga ka kafa maƙasudi kuma ka kasa cikawa, kada ka yi sanyin gwiwa. Komen ƙanƙancin maƙasudin da muka kafa, muna bukatar lokaci da kuma ƙoƙari don mu iya cim ma shi. Da yake kana so ka cim ma maƙasudinka, hakan ya nuna cewa kana ɗaukan dangantakarka da Jehobah da daraja sosai kuma kana so ka bauta masa iya gwargwadonka. Jehobah yana farin ciki don ƙoƙarin da kake yi. Ba ya bukatar ka yi abin da ya fi ƙarfinka. (Zab. 103:14; Mik. 6:8) Don haka, ya kamata ka kafa maƙasudi daidai ƙarfinka. Bayan ka yi hakan, me za ka yi don ka iya cim ma shi? Bari mu ga wasu shawarwari.

KA KASANCE DA NIYYAR CIKA MAƘASUDINKA

Ka roƙi Allah ya ƙara maka niyya (Ka duba sakin layi na 3-4)

3. Me ya sa niyya take da muhimmanci?

3 Yana da muhimmanci sosai ka kasance da niyyar cika maƙasudinka. Idan kana da niyya, za ka yi iya ƙoƙarinka don ka cika maƙasudin. Niyyar da muke da ita tana kama da iska da ke taimaka wa jirgin ruwa ya isa inda za shi. Idan iskar ta ci gaba da busawa, za ta taimaka wa matuƙin jirgin ya isa inda za shi. Kuma idan iskar tana da ƙarfi, hakan zai sa ya isa a kan lokaci. Haka ma, idan muna da niyya sosai, zai taimaka mana mu iya cim ma maƙasudinmu. Wani ɗanꞌuwa mai suna David a ƙasar El Salvador ya ce: “Idan kana da niyya, zai taimaka maka ka ƙara yin ƙoƙari. Ba za ka bar wani abu ya hana ka cim ma maƙasudinka ba.” To, mene ne za ka iya yi don ka daɗa kasancewa da niyya?

4. Wane abu ne za mu iya yin adduꞌa a kai? (Filibiyawa 2:13) (Ka kuma duba hoton.)

4 Ka roƙi Allah ya ƙara maka niyya. Jehobah zai ba ka ruhunsa mai tsarki don ya taimaka maka ka iya cim ma maƙasudinka. (Karanta Filibiyawa 2:13.) A wasu lokuta, mukan kafa maƙasudi domin mun san cewa abu ne da ya kamata mu yi kuma ya dace. Amma mai yiwuwa ba mu da niyyar cika maƙasudin. Abin da ya faru ke nan da wata ꞌyarꞌuwa mai suna Norina a Uganda. Ta kafa maƙasudin soma nazari da mutane, amma ba ta da niyya sosai na cim ma shi domin tana ganin ita ba ƙwararriyar malama ba ce. Me ya taimaka mata? Ta ce: “Na soma yin adduꞌa a kullum ina roƙan Jehobah ya ƙara min niyyar gudanar da nazarin Littafi Mai Tsarki. Yayin da nake roƙan sa ya taimaka min, na soma koyan yadda zan gudanar da nazarin Littafi Mai Tsarki da kyau. Bayan ꞌyan watanni, sai na ga cewa ina da niyya fiye da dā. Kuma a shekarar, na soma nazarin Littafi Mai Tsarki da ɗalibai guda biyu.”

5. Wane abu ne za mu iya yin tunani a kai da zai sa mu ƙara kasancewa da niyya?

5 Ka yi tunani a kan abubuwan da Jehobah ya yi maka. (Zab. 143:5) Manzo Bulus ya yi tunani a kan alherin da Jehobah ya yi masa kuma hakan ya ƙarfafa shi ya daɗa yin iya ƙoƙarinsa a hidimarsa ga Jehobah. (1 Kor. 15:​9, 10; 1 Tim. 1:​12-14) Haka ma, idan ka ci gaba da yin tunani a kan abubuwan da Jehobah ya yi maka, za ka kasance da niyya. (Zab. 116:12) Ka yi laꞌakari da abin da ya taimaka wa wata ꞌyarꞌuwa a ƙasar Honduras ta iya cim ma maƙasudinta na zama majagaba na kullum. Ta ce: “Na yi tunani a kan yadda Jehobah ya nuna min ƙauna. Ya jawo ni cikin ƙungiyarsa, ya kula da ni kuma ya kāre ni. Tunanin nan ya sa na daɗa ƙaunar Jehobah kuma na daɗa kasancewa da niyyar cim ma maƙasudina.”

6. Wane abu ne kuma zai iya ƙara mana niyya?

6 Ka mai da hankali ga amfanin da za ka samu. ꞌYarꞌuwa Erika da muka ambata ɗazu ta faɗi abin da ya taimaka mata ta iya cim ma maƙasudinta na zuwa taron fita waꞌazi a kan lokaci. Ta ce: “Na gano cewa rashin zuwa na a kan lokaci ya sa ba na amfana daga taron. Amma idan na je taron da wuri, zan iya gai da ꞌyanꞌuwa kuma in ɗan kasance tare da su. Ƙari ga haka, zan iya sauraran shawarwari masu kyau da akan bayar da za su taimaka mini in ji daɗin yin waꞌazi.” Erika ta mai da hankali ga yadda za ta amfana idan ta je a kan lokaci, kuma hakan ya taimaka mata ta cim ma maƙasudinta. Wane amfani ne za ka iya mai da hankali a kai? Idan burinka shi ne ka kyautata yadda kake yin adduꞌa ko karanta Littafi Mai Tsarki, ka yi tunanin yadda hakan zai ƙarfafa dangantakarka da Jehobah. (Zab. 145:​18, 19) Idan kana so ka kasance da halaye masu kyau na Kirista, ka mai da hankali ga yadda hakan zai kyautata dangantakarka da mutane. (Kol. 3:14) Kana iya rubuta duka dalilan da suka sa kake so ka cim ma maƙasudinka. Kuma ka riƙa duba dalilan a kullum. Tomáš da aka ambata ɗazu ya ce: “Yayin da nake ƙara ganin dalilan da suka sa ya kamata in cim ma maƙasudina, hakan yana taimaka min kada in karaya.”

7. Mene ne ya taimaka wa Julio da matarsa su cim ma maƙasudinsu?

7 Ka yi abokantaka da waɗanda za su ƙarfafa ka ka cim ma maƙasudinka. (K. Mag. 13:20) Ka yi laꞌakari da abin da ya taimaka wa Julio da matarsa su iya cim ma maƙasudinsu na daɗa yin ƙwazo a hidimarsu. Ya ce: “Mun yi abokantaka da waɗanda suke ƙarfafa mu mu cim ma maƙasudinmu, kuma mukan tattauna maƙasudin da su. Yawancinsu sun riga sun cim ma nasu maƙasudin, don haka suna iya ba mu shawarwarin da za su taimaka mana. Abokanmu sukan tambaye mu yaya abubuwa suke tafiya, kuma su ƙarfafa mu a lokacin da muke bukatar hakan.”

IDAN MUN KASA KASANCEWA DA NIYYA

Ka yi abubuwan da za su taimaka maka ka cim ma maƙasudinka (Ka duba sakin layi na 8

8. Me zai faru idan sai a lokacin da muke da niyya ne muke ƙoƙarin cim ma burinmu? (Ka kuma duba hoton.)

8 Gaskiyar ita ce, a wasu lokuta yakan yi wa dukanmu wuya mu kasance da niyya. Amma hakan yana nufin cewa ba za mu iya yin ƙoƙari mu cim ma maƙasudinmu ba? Aꞌa. Alal misali, iska tana taimaka ma jirgin ruwa sosai ya iya isa inda za shi. Amma ba a koyaushe ne iskar take kasancewa da ƙarfi ba. A wasu lokuta, babu ma iskar gabaki ɗaya. Shin hakan na nufin cewa matuƙin jirgin zai daina tafiya ne? Ba lallai ba. Wasu jiragen ruwa suna da inji, wasu kuma da hannu ake tuƙa su. Matuƙin jirgin zai ci gaba da yin amfani da hanyoyin nan har sai ya isa inda za shi. Niyya kamar iska take. A wasu lokuta za ta iya kasancewa da ƙarfi, a wasu lokuta kuma aꞌa. Ƙari ga haka, wasu lokuta za mu ji ba mu da niyyar cika burinmu. Amma idan muka ce za mu jira sai muna da niyya kafin mu cika burinmu, ba za mu iya cika shi ba. Kamar yadda matuƙin jirgin ruwa yake neman wasu hanyoyin da za su sa ya isa inda za shi, mu ma za mu iya yin ƙoƙarin cim ma burinmu ko da ba mu da niyya. Ko da yake yin hakan bai da sauƙi, amma za mu yi farin ciki idan muka iya cim ma su. Kafin mu tattauna abin da za mu iya yi, bari mu tattauna wata tambaya da za ta iya tasowa.

9. Laifi ne mu ci gaba da yin ƙoƙarin cika maƙasudinmu ko da ba mu da niyya? Ka yi bayani.

9 Jehobah yana so mu bauta masa da farin ciki da kuma yardar rai. (Zab. 100:2; 2 Kor. 9:7) Amma zai dace mu ci gaba da yin ƙoƙarin cika maƙasudinmu ko da ba mu da niyya? Ka yi laꞌakari da misalin manzo Bulus. Ya ce: “Ina horon jikina, na mai da shi bawana.” (1 Kor. 9:​25-27) Ko a lokacin da manzo Bulus bai da niyyar yin abin da Jehobah yake so ya yi, ya tilasta wa kansa ya yi hakan. Jehobah ya amince da hidimar Bulus? Ƙwarai kuwa! Kuma Jehobah ya yi masa albarka domin ƙoƙarinsa.​—2 Tim. 4:​7, 8.

10. Waɗanne albarku ne za mu samu idan mun yi iya ƙoƙarinmu don mu cim ma maƙasudinmu ko da ba mu da niyya?

10 Jehobah yana farin cikin ganin ƙoƙarin da muke yi don mu cim ma maƙasudinmu ko da ba mu da niyyar yin hakan. Yana farin ciki domin ya san cewa muna ƙoƙari ne don muna ƙaunarsa ba don muna jin daɗin yin abin a koyaushe ba. Kamar yadda Jehobah ya albarkaci Bulus, Zai albarkace mu don ƙoƙarin da muke yi. (Zab. 126:5) Kuma idan muna ganin yadda yake mana albarka, hakan zai sa mu soma kasancewa da niyya. Wata ꞌyarꞌuwa mai suna Lucyna daga Poland ta ce: “A wasu lokuta, ba na marmarin zuwa waꞌazi musamman ma idan na gaji. Duk da haka, ina farin ciki sosai idan na fita waꞌazi.” Bari mu ga abin da za mu iya yi idan muna ganin kamar ba mu da niyya.

11. Ta yaya Jehobah zai taimaka mana mu ƙara kasancewa da kamun kai?

11 Ka roƙi Allah ya ba ka kamun kai. A yawancin lokuta, kamun kai yana nufin hana kanmu yin abin da bai dace ba. Amma muna bukatar kamun kai don mu iya yin aikin da yake da wuya ko kuma idan ba ma marmarin yin sa. Ka tuna cewa kamun kai yana ɗaya daga cikin halayen da ruhu mai tsarki yake taimaka mana mu kasance da su. Don haka, ka roƙi Jehobah ya taimaka maka da ruhunsa mai tsarki don ka iya ƙara kasancewa da wannan halin. (Luk. 11:13; Gal. 5:​22, 23) Ɗanꞌuwa David da muka ambata ɗazu ya ambata yadda adduꞌa ta taimaka masa. Yana so ya riƙa yin nazarin Littafi Mai Tsarki a-kai-a-kai. Ya ce: “Nakan roƙi Jehobah ya taimaka min in kasance da kamun kai. Da taimakonsa, na soma nazarin Littafi Mai Tsarki da kyau kuma na ci gaba da yin hakan.”

12. Ta yaya ƙaꞌidar da ke littafin Mai-Wa’azi 11:4 ta shafi maƙasudan da muke kafawa a hidimarmu ga Jehobah?

12 Kada ka jira sai kome ya yi sumul. A wannan duniyar, ba za mu iya samun lokacin da babu abin da zai iya hana mu cim ma maƙasudinmu ba. Idan mun jira lokacin, ba za mu taɓa iya cim ma maƙasudinmu ba. (Karanta Mai-Wa’azi 11:4.) Wani ɗanꞌuwa mai suna Dayniel ya ce: “Ba za mu taɓa samun lokacin da babu wani abin da zai hana mu cim ma maƙasudinmu ba. Don haka, maimakon mu jira, zai dace mu soma yin hakan.” Wani ɗanꞌuwa mai suna Paul daga ƙasar Uganda ya bayyana wani dalili kuma da ya sa bai dace mu yi jinkiri ba. Ya ce: “Idan mun soma duk da matsalolin da muke fuskanta, Jehobah zai yi mana albarka.”​—Mal. 3:10.

13. Me ya sa zai dace mu soma da ƙananan maƙasudai?

13 Ka soma da ƙananan maƙasudai. Idan maƙasudinmu yana da wuyar cim mawa, ba za mu kasance da niyyar cika shi ba. Idan haka yanayinka yake, za ka iya somawa da ƙananan maƙasudai. Idan kana so ka kasance da wani hali, za ka iya soma nuna halin kaɗan da kaɗan. Idan kana so ka karanta Littafi Mai Tsarki gabaki ɗaya, za ka iya somawa da karanta shi kaɗan da kaɗan. Ɗanꞌuwa Tomáš da aka ambata a gabatarwar wannan talifin ya kasa cim ma maƙasudinsa na karanta Littafi Mai Tsarki gabaki ɗaya cikin shekara ɗaya. Ya ce: “Na gano cewa na tsara karatun da yawa a kowace rana. Sai na sake soma karatun kuma, amma na yanke shawarar karanta ayoyi kaɗan a kowace rana da yin bimbini a kansu. Hakan ya sa na soma jin daɗin karatun.” Yayin da Tomáš yake daɗa jin daɗin karatun, sai ya ƙara yawan ayoyin da yake karantawa. A ƙarshe, ya karanta Littafi Mai Tsarki gabaki ɗaya. c

KADA KA YI SANYIN GWIWA IDAN KANA SAMUN KOMA BAYA

14. Me zai iya faruwa da zai sa mu samu koma baya?

14 Gaskiyar ita ce, ko da muna da niyya da kuma kamun kai, zai iya yi mana wuya mu cim ma burinmu. Alal misali, wani abu zai iya faruwa ba tsammani kuma zai ɗauke lokacin da ya kamata mu yi amfani da shi mu cim ma burinmu. (M. Wa. 9:11) Za mu iya shiga yanayi mai wuya da zai iya sa mu sanyin gwiwa. (K. Mag. 24:10) Da yake mu ajizai ne, za mu iya yin kuskure kuma hakan zai iya sa mu samu koma baya. (Rom. 7:23) Ko kuma mu ji mun gaji. (Mat. 26:43) Me zai iya taimaka mana idan mun samu koma baya?

15. Me ya sa bai kamata ka yi sanyin gwiwa ba idan matsaloli sun hana ka cim ma maƙasudinka? Ka yi bayani. (Zabura 37:​23, 24)

15 Ka tuna cewa idan ka samu koma baya, hakan ba ya nufin cewa ba za ka iya ba. Littafi Mai Tsarki ya ce za mu iya fuskantar matsaloli a-kai-a-kai. Amma ya kuma nuna cewa Jehobah zai iya taimaka mana mu sake yin ƙoƙari kuma mu cim ma maƙasudinmu. (Karanta Zabura 37:​23, 24.) Ɗanꞌuwa Philip da muka ambata a baya ya ce: “Ba na mai da hankali a kan lokutan da na kasa cim ma maƙasudina. A maimakon haka, nakan mai da hankali a kan lokutan da na sake yin ƙoƙari don in iya cim ma maƙasudin.” David da muka ambata a baya ya ce: “Idan matsaloli sun hana ni cim ma maƙasudina, ina amfani da zarafin in nuna wa Jehobah cewa ina ƙaunar sa.” Idan ka ci gaba da yin ƙoƙari don ka cim ma maƙasudinka duk da matsalolin da kake fuskanta, za ka nuna wa Jehobah cewa kana so ka faranta masa rai. Jehobah zai yi farin ciki sosai idan ya ga yadda kake ƙoƙarin cim ma maƙasudinka.

16. Mene ne za mu iya koya daga abubuwan da suka hana mu cim ma maƙasudanmu?

16 Ka koyi darasi daga abubuwan da suka sa ka samu koma baya. Ka yi tunanin abin da ya faru kuma ka tambayi kanka cewa: ‘Shin akwai abin da nake bukatar na canja don kada hakan ya sake faruwa?’ (K. Mag. 27:12) A wasu lokuta, idan yana mana wuya mu cim ma maƙasudinmu, hakan zai iya nuna mana cewa mun kafa maƙasudin da ya fi ƙarfinmu. Idan haka yanayinka yake, zai dace ka sake yin tunani game da maƙasudinka don ka san ko za ka iya cika shi. d Jehobah ba zai yi baƙin ciki domin ka kasa cim ma maƙasudin da ya fi ƙarfinka ba.​—2 Kor. 8:12.

17. Me ya sa ya dace mu tuna da abubuwan da mun riga mun cim ma?

17 Ka riƙa tunanin abubuwan da ka cim ma. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Allah ba marar adalci ba ne. Ba zai ƙyale ayyukanku da kuka yi ba.” (Ibran. 6:10) Don haka, bai kamata kai ma ka manta ba. Ka yi tunani a kan abubuwan da ka riga ka cim ma kamar ƙarfafa dangantakarka da Jehobah, da yin waꞌazi da kuma yin baftisma. Kamar yadda ka cim ma maƙasudanka a dā, haka ma za ka iya ci gaba da yin ƙoƙari har sai ka cim ma waɗanda kake da su a yanzu.​—Filib. 3:16.

Ka yi farin ciki yayin da kake ƙoƙarin cim ma maƙasudinka (Ka duba sakin layi na 18)

18. Me ya kamata mu yi yayin da muke ƙoƙarin cim ma maƙasudinmu? (Ka kuma duba hoton.)

18 Kamar yadda matuƙin jirgin ruwa yake farin ciki saꞌad da ya isa inda za shi, kai ma za ka iya cim ma maƙasudinka da taimakon Jehobah. Amma ka tuna cewa matuƙan jirgin ruwa da yawa suna jin daɗin tafiyar. Haka ma, yayin da kake ƙoƙari don ka cim ma maƙasudinka, ka riƙa tuna da yadda Jehobah yake taimaka maka da kuma albarka da yake maka, domin yin hakan zai sa ka farin ciki. (2 Kor. 4:7) Idan ba ka gaji ba, za ka samu ƙarin albarka.​—Gal. 6:9.

WAƘA TA 126 Mu Yi Tsaro, Mu Riƙe Aminci, Mu Yi Ƙarfi

a Akan ƙarfafa mu mu kafa maƙasudai a hidimarmu ga Jehobah. Amma idan mun riga mun kafa maƙasudai kuma mun kasa cika su fa? Wannan talifin zai ba mu shawarwari dabam-dabam a kan yadda za mu iya cim ma maƙasudanmu.

b MAꞌANAR WASU KALMOMI: Maƙasudin da muka kafa a hidimarmu ga Jehobah zai iya ƙunshi duk wani abin da muke so mu yi, ko muke bukatar mu inganta yadda muke yin sa, don mu iya bauta wa Jehobah da ƙwazo kuma mu sa shi farin ciki. Alal misali, za ka iya kafa maƙasudin kasancewa da wani hali da Kirista ya kamata ya kasance da shi. Ko ka so ka kyautata yadda kake yin wasu ayyukan ibada, kamar karanta Littafi Mai Tsarki, da yin nazari da kuma zuwa waꞌazi.

d Don ƙarin bayani, ka duba talifin nan “Ka Kafa Maƙasudai da Za Su Yiwu Kuma Ka Yi Farin Ciki” da ke Hasumiyar Tsaro ta 15 ga Yuli 2008.