TALIFIN NAZARI NA 48
Ka Zama Mai Hikima Idan Aka Jarraba Amincinka
“Ka zama mai hikima a cikin kowane yanayi.”—2 TIM. 4:5, New World Translation.
WAƘA TA 123 Mu Riƙa Bin Ja-gorancin Jehobah
ABIN DA ZA A TATTAUNA a
1. Mene ne zama mai hikima yake nufi? (2 Timoti 4:5, NWT)
IDAN wani abu ya faru da ba mu ji daɗinsa ba a cikin ikilisiya, hakan zai iya gwada amincinmu ga Jehobah da kuma ƙungiyarsa. Ta yaya za mu iya shawo kan irin ƙalubalen nan? Ya kamata mu zama masu hikima, mu zauna da shiri, mu tsaya sosai cikin bangaskiyarmu. (Karanta 2 Timoti 4:5. b) Za mu nuna cewa mu masu hikima idan muka natsu, muka yi tunani da kyau, kuma muka yi ƙoƙari mu kasance da raꞌayin Jehobah idan muna fuskantar ƙalubale. Idan muka yi hakan, yadda muke ji ba zai shafi tunaninmu ba.
2. Mene ne za mu tattauna a wannan talifin?
2 A talifin da ya gabata mun tattauna ƙalubale guda uku da za mu iya fuskanta da ba su fito daga ikilisiya ba. A wannan talifin, za mu tattauna ƙalubale guda uku daga cikin ikilisiya da za su iya gwada amincinmu ga Jehobah. Su ne (1) idan muna ganin cewa wani ɗanꞌuwa ko ꞌyarꞌuwa ta yi mana laifi, (2) idan aka yi mana horo, da kuma (3) idan yana yi mana wuya mu saba da canje-canje da ake yi a ƙungiyarmu. Ta yaya ne za mu zama masu hikima mu kuma kasance da aminci ga Jehobah da ƙungiyarsa idan muna fuskantar ƙalubalen nan?
IDAN MUNA GANIN WANI ƊANꞌUWA KO ꞌYARꞌUWA TA YI MANA LAIFI
3. Me za mu iya yi idan muna ganin kamar wani ɗanꞌuwa ko ꞌyarꞌuwa ta yi mana laifi?
3 Ka taɓa ji kamar wani ɗanꞌuwa ya yi maka laifi, wataƙila ɗanꞌuwan dattijo ne? Zai yiwu cewa ɗanꞌuwan bai yi niyya ya yi maka laifi ba. (Rom. 3:23; Yak. 3:2) Duk da haka abin da ya yi ya ɓata maka rai. Wataƙila ka ma daɗe kana tunani a kan batun. Mai yiwuwa ka tambayi kanka cewa, idan ɗanꞌuwa zai iya ya yi wannan abin, anya wannan ƙungiyar Jehobah ne kuwa? Yadda Shaiɗan yake son mu yi tunani ke nan. (2 Kor. 2:11) Idan muka yi irin wannan tunanin, hakan zai iya sa mu daina bauta ma Jehobah har ma mu bar ƙungiyarsa. Idan muna ganin kamar wani ɗanꞌuwa ko ꞌyarꞌuwa ta yi mana laifi, ta yaya ne za mu zama masu hikima kuma mu ƙi yin tunani yadda Shaiɗan yake so mu yi?
4. Mene ne Yusufu ya yi da ya nuna cewa shi mai hikima ne a lokacin da aka yi masa rashin adalci, kuma waɗanne darussa ne za mu iya koya daga misalinsa? (Farawa 50:19-21)
4 Kada ka riƙe ꞌyanꞌuwa a cikin zuciya. A lokacin da Yusufu yake matashi, yayunsa sun yi masa rashin adalci. Sun tsane shi kuma wasunsu sun so su kashe shi. (Far. 37:4, 18-22) Daga baya sun sayar da shi ya zama bawa a ƙasar Masar. A sakamakon haka, Yusufu ya sha wahala sosai na tsawon shekaru 13. Hakan zai iya sa Yusufu ya yi tunani cewa Jehobah ba ya ƙaunarsa, kuma ya yashe shi a lokacin da yake bukatar taimako. Amma Yusufu bai riƙe batun a zuciya ba. A maimakon haka ya zama mai hikima ta wurin kwantar da hankalinsa. A lokacin da ya sami dama ya rama muguntar da ꞌyanꞌuwansa sun yi masa, bai yi hakan ba. A maimakon haka, ya nuna musu ƙauna kuma ya gafarta musu. (Far. 45:4, 5) Yusufu ya yi hakan ne domin ya yi tunani da kyau. Bai yi tunani a kan damuwoyinsa ba amma ya yi ta tunani a kan abin da Jehobah yake so. (Karanta Farawa 50:19-21.) Wane darasi ne muka koya daga hakan? Idan an yi maka rashin adalci, kada ka yi fushi da Jehobah ko kuma ka yi tunani cewa Jehobah ya yashe ka. A maimakon haka, ka mai da hankali a kan yadda yake taimaka maka ka jimre matsalar. Ƙari ga haka, idan wasu sun yi maka rashin adalci, za ka iya nuna musu ƙauna ta wurin gafarta musu.—1 Bit. 4:8.
5. Ta yaya ne Miqueas ya kasance mai hikima a lokacin da yake ganin cewa an yi masa rashin adalci?
5 Ka yi laꞌakari da misalin wani dattijo a zamaninmu daga Amirka ta Kudu mai suna Miqueas. c Ya tuna lokacin da yake ganin cewa wasu dattawa sun yi masa rashin adalci. Ya ce: “Abu bai taɓa damu na haka ba. Abin ya ɗaga min hankali sosai. Na kasa barci da dare kuma na yi ta kuka domin na ji kamar babu abin da zan iya yi a kan batun.” Duk da haka, Miqueas ya kasance mai hikima, kuma ya yi ƙoƙari don kada ya bar yadda yake ji ya shawo kansa. Ya yi ta adduꞌa a kai a kai yana roƙon Jehobah ya ba shi ruhu mai tsarki da ƙarfin jimrewa. Kuma ya karanta talifofi a cikin littattafanmu da za su iya taimaka masa. Wane darasi ne muka koya daga hakan? Idan kana ganin kamar wani ɗanꞌuwa ko ꞌyarꞌuwa ta yi maka rashin adalci, ka kwantar da hankalinka kuma ka yi ƙoƙari don kada ka yi tunani marar kyau. Wataƙila ba ka san dalilin da ya sa mutumin ya yi magana ko ya yi abin da ya ɓata maka rai ba. Don haka, ka yi adduꞌa ga Jehobah kuma ka roƙe shi ya taimaka maka ka fahimci dalilin da ya sa mutumin ya yi abin da ya ɓata maka rai. Hakan zai taimaka maka ka yi tunani cewa ɗanꞌuwa ko ꞌyarꞌuwar ba ta so ta yi abin da zai ɓata maka rai da gangan ba, kuma zai sa ka gafarta musu. (K. Mag. 19:11) Ka tuna cewa Jehobah ya san yanayinka, kuma zai ba ka ƙarfin da kake bukata don ka jimre.—2 Tar. 16:9; M. Wa. 5:8.
IDAN JEHOBAH YA YI MANA HORO
6. Me ya sa yake da muhimmanci mu ɗauki horon da Jehobah yake yi mana a matsayin ƙaunarsa a gare mu? (Ibraniyawa 12:5, 6, 11)
6 Idan Jehobah ya yi mana horo, hakan na iya sa mu baƙin ciki. Amma idan muna yawan tunani a kan yadda muke ji, za mu iya ɗauka cewa horon bai dace da mu ba ko kuma an yi mana rashin adalci ne. Hakan zai iya hana mu fahimtar abin da ya fi muhimmanci, wato sanin cewa Jehobah yana ƙaunar mu ne shi ya sa yake yi mana horo. (Karanta Ibraniyawa 12:5, 6, 11.) Kuma idan mun ci gaba da yin tunani a kan yadda muke ji game da horon, za mu ba Shaiɗan dama ya sa mu yi zunubi. Shaiɗan yana so mu ƙi karɓan horon, kuma a hankali mu daina bauta wa Jehobah. Idan an yi maka horo, ta yaya ne za ka kasance mai hikima?
7. (a) Kamar yadda aka nuna a hoton, a waɗanne hanyoyi ne Jehobah ya yi amfani da Bitrus domin ya karɓi horo? (b) Mene ne ka koya daga misalin Bitrus?
7 Ka karɓi horo kuma ka yi gyarar da ya kamata. Yesu ya yi wa Bitrus gyara sau da yawa a gaban sauran manzannin. (Mar. 8:33; Luk. 22:31-34) Wataƙila hakan ya sa Bitrus ya ji kunya sosai. Duk da haka, ya ci gaba da bin Yesu! Ya karɓi horon kuma ya koyi darasi daga hakan. Hakan ya sa Jehobah ya albarkaci Bitrus domin amincinsa kuma ya ba shi ayyuka masu muhimmanci a cikin ikilisiya. (Yoh. 21:15-17; A. M. 10:24-33; 1 Bit. 1:1) Wane darasi ne za mu iya koya daga misalin Bitrus? Idan ba mu mai da hankali ga yadda horon ya sa mun ji kunya ba amma mun karɓi horon kuma mun yi gyarar da ya kamata, za mu amfani kanmu da ma wasu. Ƙari ga hakan, za mu daɗa zama da amfani ga Jehobah da kuma ꞌyanꞌuwanmu.
8-9. Yaya Bernardo ya ji da farko da aka yi masa horo, amma mene ne ya taimaka masa ya gyara tunaninsa?
8 Ka yi la’akari da abin da ya faru da wani ɗan’uwa a Mozambik mai suna Bernardo. An saukar da shi daga zama dattijo. Yaya ne Bernardo ya ji da farko? Ya ce: “Na yi fushi sosai don ban so horon da aka yi min ba.” Ya damu a kan yadda ’yan’uwa a ikilisiya za su ɗauke shi. Ya ce: “Ya ɗauke ni ’yan watanni kafin in karɓi horon hannu bibbiyu kuma in sake yarda da Jehobah da kuma ƙungiyarsa.” Mene ne ya taimaka wa Bernardo ya gyara ra’ayinsa?
9 Bernardo ya canja tunaninsa. Ya bayyana cewa: “A lokacin da ni dattijo ne, nakan yi amfani da Ibraniyawa 12:7 wajen taimaka ma wasu su kasance da ra’ayi mai kyau game da horon da Jehobah yake yi musu. Sai na tambayi kaina, ‘Wane ne ya kamata ya bi umurnin da ke nassin nan?’ Dukan bayin Jehobah ne har da ni.” Sai Bernardo ya sake yin wasu canje-canje don ya sake yarda da Jehobah da kuma ƙungiyarsa. Ya ƙara tsawon lokacin da yake karanta Littafi Mai Tsarki da kuma yin bimbini a kansa. Ko da yake ya damu a kan yadda ’yan’uwa suke ganin sa, ya ci gaba da yin wa’azi tare da su da kuma yin kalamai a duk lokacin da ya halarci taro. A kwana a tashi, an sake naɗa Bernardo ya zama dattijo. Kamar Bernardo, idan aka yi maka horo, ka yi ƙoƙari kada ka yi tunani a kan kunyar da hakan ya sa ka ji amma ka karɓi gyarar kuma ka yi canje-canje da suka dace. d (K. Mag. 8:33; 22:4) Idan ka yi hakan, za ka iya kasancewa da tabbaci cewa Jehobah zai albarkaci amincinka gare shi da kuma ƙungiyarsa.
IDAN YANA MANA WUYA MU SABA DA WANI CANJIN DA ƘUNGIYARMU TA YI
10. Wane canji ne aka yi a zamanin Isra’ilawa da wataƙila ya gwada amincin wasunsu?
10 Canje-canje da ƙungiyarmu take yi za su iya gwada amincinmu. Idan ba mu yi hankali ba, za mu iya barin canje-canjen su raba mu da Jehobah. Alal misali, ka yi tunanin yadda abubuwa sun canja wa Isra’ilawa a dā. Kafin Jehobah ya ba su doka ta hannun Musa, iyaye maza ne suke yin abubuwan da firistoci suke yi. Sukan gina bagade kuma su yi hadayu a kai a madadin iyalansu. (Far. 8:20, 21; 12:7; 26:25; 35:1, 6, 7; Ayu. 1:5) Amma bayan an ba da dokar, ba a yarda wa iyaye maza su sake yin hadayun ba. Jehobah ya naɗa firistoci daga iyalin Haruna kuma ya ba su hakkin yin hadayu. Tun daga lokacin, idan wani da ba ya cikin zuriyar Haruna ya soma yin ayyukan firist, za a iya kashe shi. e (L. Fir. 17:3-6, 8, 9) Shin, wannan canjin yana ɗaya daga cikin dalilai da suka sa Kora da Dathan da Abiram da wasu shugabannin jama’a 250 suka yi wa Musa da Haruna tawaye? (L. Ƙid. 16:1-3) Ba mu sani ba. Amma ko da mene ne dalilin, Kora da abokansa sun ƙi su kasance da aminci ga Jehobah. Idan canje-canje da ake yi a ƙungiyarmu sun gwada amincinka, mene ne za ka iya yi?
11. Mene ne muka koya daga misalin wasu ’yan zuriyar Kohath daga cikin Lawiyawa?
11 Ka ba da haɗin kai idan ƙungiyarmu ta yi canje-canje. A lokacin da Isra’ilawa suke tafiya a daji, ’yan zuriyar Kohath sun yi wani aiki mai muhimmanci. A duk lokacin da Isra’ilawa suke canja sansani, wasu daga cikin ’ya’yan Kohath ne suke ɗaukan Akwatin Yarjejeniya kafin sauran al’ummar su bi su. (L. Ƙid. 3:29, 31; 10:33; Yosh. 3:2-4) Wannan babban gata ne! Amma abubuwa sun canja a lokacin da Isra’ilawa suka isa Ƙasar Alkawari. Ba a bukaci a sake yawo da Akwatin Yarjejeniyar kuma ba. Shi ya sa a lokacin da Sulemanu yake mulki, ya zaɓi wasu daga cikin iyalin Kohath su zama mawaƙa, da masu kula da ƙofofi da kuma ɗakunan ajiyar abinci. (1 Tar. 6:31-33; 26:1, 24) Babu abin da ya nuna cewa zuriyar Kohath sun yi gunaguni ko kuma sun nemi ayyukan da za su sa mutane su san da su domin ayyuka masu muhimmanci da suka yi a dā. Wane darasi ne muka koya daga hakan? Ka goyi bayan canje-canje da ƙungiyar Jehobah take yi da dukan zuciyarka ko da canjin ya shafe aikin da kake yi. Ka ji daɗin duk wani aikin da aka ba ka ka yi. Ka tuna cewa ba aikinka ne zai sa ka kasance da daraja a gaban Jehobah ba. Jehobah ya fi daraja biyayyar da kake yi fiye da duk wani aiki da kake yi.—1 Sam. 15:22.
12. Yaya Zaina ta ji da aka ce ta daina hidima a Bethel?
12 Ka yi la’akari da misalin wata ’yar’uwa mai suna Zaina a Gabas ta Tsakiya, da aka canja mata hidima kuma hakan ya sa ta rasa aikin da take yi a ƙungiyarmu. Bayan da ta yi shekara 23 tana hidima a Bethel, an mai da ita majagaba ta musamman. Ta ce: “Da aka canja hidimar da nake yi, hakan ya ba ni mamaki sosai. Na ji kamar ba ni da wani amfani kuma na yi ta tambayar kaina, ‘Wane laifi ne na yi?’ ” Abin takaici, wasu ’yan’uwa a ikilisiya sun daɗa sa ta baƙin ciki, suna ce mata: “Da a ce kina aikinki da kyau a Bethel, da hakan bai faru ba.” Zaina ta daɗe tana baƙin ciki kuma ta yi ta kuka kowane dare. Amma ta ce: “Ban yi shakka cewa Jehobah da ƙungiyarsa suna ƙaunata ba.” Me ya taimaka wa Zaina ta nuna cewa ita mai hikima ce?
13. Me ya taimaki Zaina ta daina baƙin ciki da kuma ji kamar ba ta da amfani?
13 Zaina ta yi ƙoƙari don ta daina tunani marar kyau. Ta yaya ta yi hakan? Ta karanta talifofi a littattafanmu da suka tattauna irin yanayin da take ciki kuma sun taimaka mata ta iya jimrewa. Alal misali, ta karanta wani talifi da ya bayyana yadda wani marubucin Littafi Mai Tsarki mai suna Markus ya yi fama da irin yanayinta a lokacin da aka canja masa hidima, kuma hakan ya taimaka mata. Zaina ta tuna abin da ya faru kuma ta ce: “Misalin Markus ne ya taimaka min in daina sanyin gwiwa.” Kuma Zaina ba ta nisanta kanta da abokanta ba. Ba ta yanke zumunci da ’yan’uwa maza da mata ba kuma ta ci gaba da yin wa’azi tare da su. Ba ta soma jin tausayin kanta ba. Ta gano cewa ruhu mai tsarki ne yake taimaka wa ƙungiyar Jehobah ta yanke shawarwari kuma ’yan’uwan da suke ja-goranci sun damu da ita sosai. Ta gaya wa kanta cewa abu mafi muhimmanci a ƙungiyar Jehobah shi ne a yi aikin Jehobah.
14. Waɗanne canje-canje ne ya yi wa Vlado wuya ya amince da su, kuma me ya taimake shi?
14 Wani dattijo ɗan shekara 73 mai suna Vlado a Slovenia, bai ji daɗi ba sa’ad da aka haɗa ikilisiyarsu da wata ikilisiya dabam, kuma aka rufe Majami’ar Mulki da yake zuwa a dā. Ya ce: “Ban gane dalilin da ya sa za a rufe Majami’ar Mulki mai kyau kamar namu ba. Na yi fushi domin bai daɗe da muka gyara Majami’ar Mulkin ba. Ni kafinta ne, kuma na taimaka wajen yin wasu daga cikin sabbin kujerun. Ƙari ga haka, zuwa sabuwar ikilisiyar ya bukaci mu yi canje-canjen da ba su yi wa mu tsofaffi sauƙi ba.” Mene ne ya taimaka wa Vlado ya bi umurnin da aka bayar. Ya ce: “A kullum, bin canje-canje da ƙungiyarmu take yi yana sa Jehobah ya yi mana albarka. Canje-canjen nan suna taimaka mana mu kasance a shirye don manyan canje-canje da za su auku a nan gaba.” Kana fama da sabon tsarin da aka yi na haɗa ikilisiyarku da wata, ko an canja maka hidima? Ka kasance da tabbaci cewa Jehobah ya san yadda kake ji. Idan ka amince da waɗannan canje-canjen, kuma ka ci gaba da bin Jehobah da kuma ƙungiyar da yake amfani da ita a yau, tabbas, Jehobah zai yi maka albarka.—Zab. 18:25.
KA ZAMA MAI HIKIMA A CIKIN KOWANE YANAYI
15. Ta yaya za mu nuna cewa mu masu hikima ne idan muka fuskanci ƙalubale a cikin ikilisiya?
15 Yayin da muke daɗa kusantar ƙarshen zamanin nan, za mu iya fuskantar ƙalubale a cikin ikilisiya. Waɗannan matsalolin za su iya gwada amincinmu ga Jehobah. Don haka, dole ne mu ci gaba da nuna cewa mu masu hikima ne. Idan kana ganin kamar wani ɗan’uwa ya yi maka rashin adalci, kada ka bar hakan ya sa ka zama mai fushi. Idan aka yi maka horo, kada ka mai da hankali ga kunya da hakan ya jawo maka. Ka karɓi horon kuma ka yi canje-canje da kake bukatar ka yi. Kuma idan ƙungiyar Jehobah ta yi canje-canje da suka shafe ka, ka amince da canje-canjen da dukan zuciyarka kuma ka bi sabon tsarin.
16. Me zai taimake ka ka ci gaba da yarda da Jehobah da kuma ƙungiyarsa?
16 Za ka iya ci gaba da bin Jehobah da ƙungiyarsa a duk lokacin da aka gwada amincinka. Abin da zai taimaka maka ka iya yin hakan shi ne, idan ka nuna cewa kai mai hikima ne, wato, ka natsu, ka yi tunani da kyau kuma ka kasance da ra’ayin Jehobah. Ka ƙudura cewa za ka yi nazari a kan mutanen da suka fuskanci irin yanayinka a cikin Littafi Mai Tsarki kuma ka yi bimbini a kan misalinsu. Ka yi addu’a ga Jehobah don ya taimaka maka kuma kada ka guje wa ’yan’uwa a cikin ikilisiya. Idan ka yi hakan, ko da mene ne ya faru, Shaiɗan ba zai iya raba ka da Jehobah ko ƙungiyarsa ba.—Yak. 4:7.
WAƘA TA 126 Mu Yi Tsaro, Mu Riƙe Aminci, Mu Yi Ƙarfi
a A wasu lokuta zai iya yi mana wuya mu kasance da aminci ga Jehobah da kuma ƙungiyarsa, musamman idan wani abu ya faru a cikin ikilisiya da ba mu ji daɗinsa ba. A wannan talifin za mu tattauna ƙalubale guda uku da za mu iya fuskanta da abin da za mu iya yi don mu ci gaba da zama da aminci ga Jehobah da kuma ƙungiyarsa.
b 2 Timoti 4:5 (NWT): “Amma kai, sai ka zama mai hikima a cikin kowane yanayi, ka jimre cikin wahala, ka yi aikin yaɗa bishara, ka cika hidimarka.”
c An canja wasu sunayen.
d Za ka iya samun ƙarin shawarwari a talifin nan “Ka Taɓa Yin Hidima? Za Ka Iya Yi Kuma?” a Hasumiyar Tsaro ta 15 ga Agusta, 2009.
e Dokar ta umurci iyaye maza da suke so su yanka dabba don iyalansu su ci, su kai dabbar mazauni. Waɗanda suke zama nesa da mazaunin ne kaɗai ba a bukace su su kai dabbar mazauni ba.—M. Sha. 12:21.