Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TARIHI

“Na Shirya Zan Yi ma Jehobah Hidima”

“Na Shirya Zan Yi ma Jehobah Hidima”

MUN yi ban kwana ke nan da wani ƙaramin rukunin mutane wanda muka ziyarce su kusa da ƙauyen Granbori da ke gandun dajin Suriname. Sai muka kama hanya ta kwalekwale za mu tsallake Kogin Tapanahoni. Ba da daɗewa ba muka isa inda ruwan yake guduwa sosai sai fankar injin kwalekwalenmu ya bugi dutse. Nan da nan sai gaban kwalekwalen ya nutse cikin kogin kuma ya nutse tare da mu. Zuciyata ta tsinke. Ko da yake na daɗe ina tafiya cikin kogi da kwalekwale a matsayin mai kula da daꞌira, ban iya ruwa ba!

Kafin in ci gaba da labarina, bari in gaya muku yadda na soma hidima ta cikakken lokaci.

An haife ni a 1942 a tsibirin Curaçao na Caribbea. Tsibirin yana da kyau sosai. Babana mutumin Suriname ne, amma ya ƙaura zuwa tsibirin don aiki ’yan shekaru kafin a haife ni. Yana ɗaya daga cikin Shaidun Jehobah na farko da suka yi baftisma a Curaçao. a Yakan yi nazarin Littafi Mai Tsarki tare da mu kowane mako ko da yake ba kowane lokaci ne mukan so hakan ba. Da nake shekara 14 mahaifinmu ya koma Suriname tare da mu don ya kula da mahaifiyarsa da ta tsufa.

ABOKAN KIRKI SUN TAIMAKA MIN

A Suriname, na soma tarayya da matasa masu himma a ikilisiya. Sun girme ni da ’yan shekaru kuma suna hidimar majagaba. A duk lokacin da suke magana game da abubuwan da suka faru sa’ad da suke wa’azi, sai in ga yadda suke farin ciki. Bayan an gama taro, ni da abokaina mukan tattauna batutuwa daga Littafi Mai Tsarki. A wasu lokuta, mukan yi hakan sa’ad da muke zaune a waje da dare muna kallon taurari. Waɗannan abokan sun sa na gano abin da nake so a rayuwa, wato in yi wa Jehobah hidima. Don haka na yi baftisma sa’ad da nake shekara 16. Daga baya na soma hidimar majagaba sa’ad da na kai shekara 18.

NA KOYI DARUSSA MASU KYAU

A lokacin da nake hidimar majagaba a Paramaribo

Na koyi darussa da yawa a matsayin majagaba kuma hakan ya taimaka min a hidimar da na yi na cikakken lokaci. Alal misali, ɗaya daga cikin darussa da na fara koya shi ne muhimmancin koyar da wasu. A lokacin da na soma hidimar majagaba, wani mai wa’azi a ƙasar waje mai suna Willem van Seijl ya soma koyar da ni. b Ya koya min yadda zan kula da ayyuka a ikilisiya. A lokacin, ban san cewa zan bukaci koyarwar sosai a gaba ba. Bayan shekara ɗaya, an naɗa ni majagaba na musamman. Na soma taimaka ma ƙananan rukunoni na ’yan’uwa da suke zama a gandun daji na Suriname kuma suke nesa da wasu ikilisiyoyi. Ina godiya sosai don yadda ’yan’uwa kamar Willem suka koyar da ni a lokacin da nake bukata. Kuma tun daga lokacin, ni ma ina ƙoƙari in koyar da wasu.

Darasi na biyu da na koya shi ne yadda zan sauƙaƙa rayuwata kuma in dinga tsara ayyukana. A farkon kowane wata, ni da ɗan’uwan da muke hidimar majagaba ta musamman tare mukan tattauna abubuwa da za mu bukace su a watan. Sa’an nan ɗaya daga cikin mu zai yi tafiya mai nisa zuwa babban birnin tsibirin don ya saya abubuwan. Ba ma kashe kuɗin alawus namu haka kawai, kuma muna amfani da abubuwan da kyau don su kai mu har ƙarshen wata, domin idan wani abu da muke bukata ya ƙare kafin ƙarshen watan, mutane ƙalilan ne kawai za su iya taimaka mana. Na san cewa koyan yadda zan sauƙaƙa rayuwata da kuma yadda zan tsara ayyukana ne ya taimake ni in mai da hankali ga hidimata ga Jehobah a duk rayuwata.

Darasi na uku da na koya shi ne amfanin koyar da mutane a yarensu. Tun lokacin da nake ƙarami, na koyi yaren Dutch da Turanci da Papiamento da Sranantongo (an kuma san sa da sunan nan Sranan), wanda shi ne yaren da aka fi amfani da shi a Suriname. Amma a gandun dajin, na gano cewa mutane sun fi saurarar wa’azi idan muka yi amfani da yarensu. Ya yi min wuya in yi wasu yaruka kamar yaren Saramaccan, da yake bukatar mutum ya yi magana da babbar murya ko kuma ƙaramar murya. Ko da yake bai yi min sauƙi ba, na yi farin ciki cewa na koyi yaren. Da shigewar lokaci, na iya na koya wa mutane da yawa gaskiya domin na iya yarensu.

Hakika, akwai lokutan da na ba kaina kunya yayin da nake yaren. Alal misali, akwai lokacin da na so in tambayi ɗalibata a yaren Saramaccan yaya jiki, da yake tana ciwon ciki. Amma sai na tambaye ta ko ta yi ciki ne. Ba sai na gaya muku ba, tambayar ya sa ta fushi. Ko da yake nakan yi kuskure kamar haka, na ci gaba da ƙoƙari in koyi duk yaren da ake yi a yankin da nake.

NA KARƁI ƘARIN AYYUKA

An naɗa ni mai kula da da’ira a 1970. A shekarar, na ziyarci rukunoni da dama masu nisa da suke gandun dajin don in nuna musu bidiyon “Visiting the World Headquarters of Jehovah’s Witnesses.” Ni da wasu ’yan’uwa mukan yi amfani da kwalekwale mu yi tafiya a cikin kogi don mu iya samun su. Mukan ɗauki janareto da tanki na gas, da fitilu da kayan da za a nuna bidiyon da su. Idan muka isa ƙauyukan, mukan kwashi kayanmu zuwa cikin daji inda za mu yi taron. Abin da na fi tuna game da waɗannan tafiye-tafiye da muka yi shi ne yadda mutane a ƙauyuka masu nisan nan suke jin daɗin bidiyoyin. Na yi farin ciki sosai don na iya koya wa mutane game da Jehobah da kuma sashen ƙungiyarsa da ke duniya. Ganin yadda mutane suka kusaci Jehobah ya sa na yi farin ciki don hidimar da na yi.

YADDA NA SAƘA IGIYOYI UKU

Ni da Ethel mun yi aure a Satumba 1971

Ko da yake na ga yadda zama marar aure ya taimaka wa hidimata, duk da haka, na so in yi aure. Sai na soma addu’a musamman don in sami mata wadda za ta ji daɗin yin hidima ta cikakken lokaci tare da ni a wannan yanki mai wuya. Bayan shekara ɗaya, na soma fita zance da wata majagaba na musamman mai suna Ethel, wadda take da halin sadaukarwa sosai. Halin manzo Bulus ya burge Ethel tun tana ƙarama kuma hakan ya sa ta so ta yi iya ƙoƙarinta a hidimarta kamar yadda ya yi. Mun yi aure a watan Satumba, 1971 kuma mun ci gaba da hidimar mai kula da daꞌira tare.

Iyalin su Ethel ba masu arziki ba ne, don haka yin hidima a gandun dajin bai zama mata matsala ba. Alal misali, idan muna shirin ziyartar ikilisiyoyi, ba ma kwasan kaya da yawa. Mukan yi wanka da kuma wanke kayanmu a koguna. Mun zo mun saba da cin duk abin da ’yan’uwan suka ba mu, kamar damo da wani irin kifi mai suna piranha, ko dai duk wani abin da sun yi farautarsa ko sun kama a rafi. In babu kwanoni, mukan yi amfani da ganyen ayaba. In babu cokula kuma mukan ci abinci da hannu. Ni da Ethel mun san cewa yin sadaukarwar nan tare a hidimarmu ga Jehobah ya taimaka mana mu zama kamar igiyoyi uku da aka saƙa su zama ɗaya. (M. Wa. 4:12) Ba mu taɓa yin da-na-sani don waɗannan sadaukarwar da muka yi ba.

Wata rana da muke dawowa daga ziyartar ’yan’uwan da ke gandun dajin ne muka fuskanci yanayin da na ambata a farkon labarin nan. Da kwalekwalen ya kai inda ruwa yake guduwa sosai, sai ya nutse amma nan da nan ya fito. Abin godiya shi ne, muna sanye da riguna da za su hana mu nutsewa a cikin ruwa kuma ba mu faɗi daga kwalekwalen ba, amma ruwa ya cika kwalekwalen. Mun zubar da abincin da ke cikin tukwanenmu a kogin, sa’an nan mun yi amfani da tukwanen don mu yashe ruwan da ya shiga kwalekwalen.

Da yake mun zubar da abincinmu, mun soma ƙoƙarin kama kifi yayin da muke tafiya amma ba mu kama kome ba. Saboda haka, mun yi addu’a ga Jehobah kuma mun roƙe shi ya tanadar mana da abinci na ranar. Bayan da mun yi addu’a, ɗaya daga cikin ’yan’uwan ya jefa igiyar kama kifi kuma ya kama babban kifi wanda zai ishe dukanmu biyar har mu ci mu ƙoshi.

NA ZAMA MAIGIDA DA MAHAIFI DA MAI KULA DA DA’IRA DUK A LOKACI ƊAYA

Bayan shekaru biyar a hidimarmu na masu kula da daꞌira, ni da Ethel mun sami wani albarka da ba mu yi tsammani ba. Mun sami labari cewa Ethel ta yi juna biyu. Na yi farin ciki da na ji hakan, amma ban san yadda hakan zai shafi rayuwarmu ba. Ni da Ethel mun so mu ci gaba da hidima ta cikakken lokaci, idan zai yiwu. A 1976, matata ta haifi ɗanmu na fari kuma mun ba shi suna Ethniël. Shekaru biyu da rabi da ya biyo baya, sai aka haifi ɗanmu na biyu, wato, Giovanni.

Na je inda ake yi ma wani ɗan’uwa baftisma a Kogin Tapanahoni kusa da Godo Holo a Gabashin Suriname, a 1983

Da yake ana bukatar masu kula da da’ira sosai a Suriname, ofishinmu na ƙasar ta ba ni dama in ci gaba da hidimar mai kula da da’ira yayin da muke renon yaranmu. Sa’ad da yaranmu suke ƙanana, an ba ni damar kula da daꞌira da ba ta da ikilisiyoyi da yawa. Hakan ya sa na iya ziyartar ikilisiyoyi na ꞌyan makonni a matsayin mai kula da daꞌira, sa’an nan sauran kwanakin za mu yi hidimar majagaba a ikilisiyar da aka kai mu. Ethel da yaranmu sukan bi ni idan na ziyarci ikilisiyoyi da suke kusa da gidanmu. Amma nakan yi tafiya ni kaɗai idan na je ziyartar ikilisiyoyi ko manyan taro a gandun dajin.

A lokacin da nake hidimar mai kula da da’ira, kuma sau da yawa nakan ziyarci ’yan’uwa a ikilisiyoyi masu nisa a cikin kwalekwale

Nakan tsara ayyukana da kyau don in cika dukansu, kuma in tabbata cewa mun yi ibada ta iyali kowane mako. A duk lokacin da na ziyarci ikilisiyoyi a gandun dajin, Ethel takan yi ibada ta iyali da yaranmu. Amma muna iya ƙoƙarinmu don mu riƙa yin abubuwa tare a matsayin iyali. Ni da Ethel da yaranmu mukan yi wasanni tare kuma mu ziyarci wuraren shaƙatawa kusa da gidanmu. Ina yawan yin dare ina shirya ayyukan da aka ba ni a ikilisiya. Kuma Ethel, kamar mace mai kirki da aka ambata a Karin Magana 31:​15, takan tashi da sassafe don ta tabbatar cewa za mu iya karanta nassin yini kuma mu karya tare kafin yaranmu su je makaranta. Ina godiya sosai domin na sami mataimakiya mai dacewa, wadda take taimaka mini in iya yin hidimomin da Jehobah ya ba ni.

A matsayin iyaye, mun yi iya ƙoƙarinmu don mu taimaka wa yaranmu su ƙaunaci Jehobah kuma su so yin wa’azi. Mun so yaranmu su zaɓi yin hidima ta cikakken lokaci ba domin mu muka yi musu zaɓin ba, amma don abin da suke so su yi ke nan. Muna yawan gaya musu yadda hidima ta cikakken lokaci zai sa su farin ciki sosai. Ko da yake mun gaya musu ƙalubalen da ke tattare da hidima ta cikakken lokaci, ba mu fasa gaya musu yadda Jehobah ya taimaka da kuma albarkace mu saꞌad da muka fuskanci matsaloli ba. Mun kuma tabbatar cewa yaranmu sun ƙulla abota da ’yan’uwa da suka sa ibada farko a rayuwarsu.

Jehobah ya tanadar mana da dukan bukatun iyalinmu kuma na yi iya ƙoƙarina in cika hakkina. Yin hidima a matsayin marar aure a gandun dajin ya koya min yadda zan riƙa yin amfani da kuɗi yadda ya kamata. Amma ko da yake mukan yi iya ƙoƙarinmu, ba kowane lokaci ne muke samun abin da muke bukata ba. A lokutan nan, na san cewa Jehobah ne ya taimaka mana. Alal misali, daga 1986 zuwa 1992, an yi yaƙin basasa a Suriname. A shekarun nan ya yi mana wuya mu sami abubuwan da muke bukata, ko da ƙanana abubuwa ne. Duk da haka, Jehobah ya ba mu abin da muke bukata.​—Mat. 6:32.

YIN TUNANI A KAN RAYUWATA

Daga hagu zuwa dama: Tare da matata, Ethel

Ɗan farinmu, Ethniël, tare da matarsa, Natalie

Ɗanmu Giovanni tare da matarsa, Christal

A dukan rayuwarmu, Jehobah ya lura da mu kuma ya taimaka mana mu kasance da gamsuwa. Yaranmu suna sa mu farin ciki sosai kuma muna godiya cewa mun rene su su bauta wa Jehobah. Muna farin ciki cewa su ma sun zaɓi su yi hidima ta cikakken lokaci a rayuwarsu. Ethniël da Giovanni sun gama makarantar da yanzu ake kira Makarantar Masu Yaɗa Bisharar Mulki kuma yanzu suna hidima a ofishinmu da ke Suriname tare da matansu.

Ni da Ethel mun yi tsufa yanzu, amma muna kan aiki tuƙuru a matsayin majagaba na musamman. Tsabagen hidimar da muke yi, har yanzu ban iya na koyi iyo ba! Amma ba na da-na-sani. Idan na tuna baya, ina ganin cewa shawarar da na yanke na soma hidima ta cikakken lokaci tun ina matashi ita ce shawara mafi muhimmanci da na taɓa yi a rayuwata.

b Labarin Willem van Seijl ya fito a Awake! na 8 ga Oktoba, 1999. Jigon shi ne “Reality Has Exceeded My Expectations.”