Shin Ka Sani?
Shin Mordekai ya taɓa rayuwa kuwa?
WANI Bayahude mai suna Mordekai ya yi ayyuka masu muhimmanci da aka rubuta a littafin Esta. Shi Bayahude ne da aka kai bauta kuma ya yi aiki a gidan sarkin Fashiya. Hakan ya faru a shekara ta 496 kafin haihuwar Yesu, a “lokacin da Sarki Ahasuwerus yake mulki.” (A yau, yawancin mutane suna ganin wannan sarkin shi ne Xerxes I.) Mordekai ya fallasa ƙullin da aka yi don a kashe sarkin. Sai sarkin ya nuna godiyarsa ta wurin sa a ɗaukaka Mordekai a fili. Bayan mutuwar Haman, wato maƙiyin Mordekai da kuma Yahudawa, sarkin ya ƙara wa Mordekai matsayi zuwa matsayin firayim minista. Wannan matsayin da aka ba Mordekai ya ba shi izini ya ba da doka don ya ceci Isra’ilawa a daular Fashiya daga kisan kāre dangi.—Esta 1:1; 2:5, 21-23; 8:1, 2; 9:16.
Wasu ꞌyan tarihi sun ce littafin Esta ƙage ne kuma Mordekai bai taɓa wanzuwa ba. Amma a 1941, masu tona kasa sun gano abubuwa da suka tabbatar da abin da Littafi Mai Tsarki ya faɗa game da Mordekai. Me suka gano?
ꞌYan tarihi sun gano wani fasasshen tukunyar laka na Fashiya da aka yi rubutu a kai, da ya ambata wani mutum mai suna Marduka. Ya yi aiki a matsayin jamiꞌin gwamnati, wataƙila mai kula da kasafin kuɗi a birnin Shushan. Arthur Ungnad wani masanin tarihin Gabas ta Tsakiya ya rubuta cewa “wannan ne karo na farko da an rubuta sunan Mordekai a wani littafi da ba Littafi Mai Tsarki ba.”
Tun bayan rahoto da Ungnad ya bayar, masana sun fassara rubutun da ke dubban tukwanen laka na Fashiya. Wasu daga cikin su su ne fasassun tukwanen laka da aka samo a ƙangon Maꞌaji, kusa da katangar birnin. A lokacin sarautar Xerxes I ne aka yi rubutun. An yi rubutun a harshen Elam, kuma yana ɗauke da sunaye da dama da ke cikin littafin Esta. a
Tukwanen laka na Persepolis da dama sun ambata sunan nan Marduka, wanda shi marubuci ne a fadar sarki a Shushan a lokacin da Sarki Xerxes I yake sarauta. Ɗaya daga cikin tukwanen lakar ya ce Marduka mafassari ne. Wannan kwatancin ya jitu da bayanan da Littafi Mai Tsarki ya bayar game da Mordekai. Shi jamiꞌin gwamnati ne da ya yi aiki a fadar Sarki Ahasuwerus, wato Xerxes I, kuma yana jin aƙalla harsuna biyu. A yawancin lokuta, Mordekai yakan zauna a ƙofar shiga fadar sarki a Shushan. (Esta 2:19, 21; 3:3) Ƙofar babban zaure ne da jamiꞌan gwamnati suke aiki.
Akwai alaƙa sosai tsakanin Marduka da aka rubuta a jikin tukwanen lakan da Mordekai da aka ambata a cikin Littafi Mai Tsarki. Sun yi rayuwa a lokaci ɗaya, a ƙasa ɗaya kuma su biyun sun yi aiki a matsayin jamiꞌan gwamnati a wurin aiki ɗaya. Wannan alaƙar ta tabbatar mana cewa Marduka da Mordekai mutum ɗaya ne.
a A 1992, wani farfesa mai suna Edwin M. Yamauchi ya rubuta sunaye goma daga fasassun tukwanen laka da aka samo a Persepolis, kuma sunayen nan suna cikin littafin Esta ma.