Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 46

Yadda Jehobah Yake Taimaka Mana Mu Jimre da Farin Ciki

Yadda Jehobah Yake Taimaka Mana Mu Jimre da Farin Ciki

“Yahweh yana jira ya yi muku alheri. A shirye yake ya yi muku jinƙai.”​—ISHA. 30:18.

WAƘA TA 3 Ƙarfinmu, Begenmu da Makiyayinmu

ABIN DA ZA A TATTAUNA a

1-2. (a) Waɗanne tambayoyi ne za mu tattauna? (b) Mene ne ya nuna cewa Jehobah yana marmarin taimaka mana?

 JEHOBAH zai iya taimaka mana mu jimre matsalolin da muke fuskanta, kuma mu yi farin ciki yayin da muke bauta masa. A waɗanne hanyoyi ne yake taimaka mana? Kuma ta yaya za mu amfana sosai daga taimakon da Jehobah yake yi mana? Za a amsa tambayoyin nan a wannan talifin. Amma kafin mu bincika amsoshin tambayoyin, bari mu tattauna wannan tambayar: Da gaske ne Jehobah yake so ya taimaka mana?

2 Kalmar da manzo Bulus ya yi amfani da ita a wasiƙar da ya aika wa Ibraniyawa za ta taimaka mana mu sami amsar. Manzo Bulus ya rubuta cewa: “Ubangiji mai taimakona ne, ba zan ji tsoro ba. Me ɗan Adam zai iya yi mini?” (Ibran. 13:6) Binciken Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa kalmar nan “mai taimako” a wannan ayar, tana nufin mutumin da ba ya jinkirin taimaka wa mabukata. Bisa ga wannan bayanin, ka yi tunanin yadda Jehobah yake hanzarin taimaka ma wanda yake cikin damuwa. Babu shakka za ka yarda cewa Jehobah yana marmarin taimaka mana. Da taimakon Jehobah, za mu iya jimre matsalolinmu da farin ciki.

3. A waɗanne hanyoyi uku ne Jehobah yake taimaka mana mu jimre matsalolinmu da farin ciki?

3 A waɗanne hanyoyi ne Jehobah yake taimaka mana mu jimre matsalolinmu da farin ciki? Don mu sami amsar, bari mu bincika littafin Ishaya. Me ya sa? Domin da yawa daga cikin annabce-annabce da Ishaya ya yi sun shafi bayin Allah a yau. Ƙari ga haka, Ishaya yana yawan kwatanta Jehobah da kalmomi da suke da sauƙin fahimta. Alal misali, ka yi la’akari da Ishaya sura 30. A wannan surar, Ishaya ya yi amfani da wani kwatanci da ya nuna yadda Jehobah yake taimaka wa mutanensa (1) ta wajen saurara da kyau da kuma amsa addu’o’inmu, (2) ta wajen yi mana ja-goranci, (3) ta wajen yi mana albarka yanzu da kuma a nan gaba. Bari mu bincika hanyoyi ukun nan da Jehobah yake taimaka mana.

JEHOBAH YANA SAURARAR MU

4. (a) Ta yaya Jehobah ya kwatanta Yahudawa a zamanin Ishaya, kuma mene ne ya bari ya faru daga baya? (b) Wane bege ne Jehobah ya ba wa masu aminci? (Ishaya 30:​18, 19)

4 A gabatarwar littafin Ishaya sura 30, Jehobah ya kwatanta Isra’ilawa da ‘ꞌyaꞌya masu tayarwa’ waɗanda suke “aikata zunubi a kan zunubi.” Ya ci gaba da cewa: “Su ꞌyaꞌyan tawaye ne, . . . da suka ƙi jin Koyarwar Yahweh.” (Isha. 30:​1, 9) Domin mutanen sun ƙi su saurari Jehobah, Ishaya ya annabta cewa Jehobah zai bar su su sha wahala. (Isha. 30:​5, 17; Irm. 25:​8-11) Kuma kamar yadda ya annabta, Babiloniyawa sun kai su bauta a Babila. Amma a cikinsu, akwai waɗanda suka bauta ma Jehobah da aminci kuma Ishaya ya idar musu da saƙo da zai ba su bege. Ya gaya musu cewa wata rana Jehobah zai yi musu alheri ta wajen maido da su Urushalima. (Karanta Ishaya 30:​18, 19.) Kuma abin da ya faru ke nan. Jehobah ya ba su ꞌyanci daga Babila. Amma ꞌyancin ba zai zo nan tāke ba. Furucin nan “Yahweh yana jira ya yi muku alheri,” ya nuna cewa zai ɗan ɗauki lokaci kafin Jehobah ya ceci bayinsa masu aminci. Israꞌilawan sun yi shekaru 70 suna bauta a Babila kafin aka maido da wasun su zuwa Urushalima. (Isha. 10:21; Irm. 29:10) Saꞌad da Israꞌilawan suke bauta a Babila, sukan yi kuka don baƙin ciki. Amma da suka dawo ƙasarsu, sun yi kuka domin farin ciki.

5. Wane tabbaci ne Ishaya 30:19 ta ba mu?

5 A yau, za mu iya samun ƙarfafa daga kalmomin nan: “Zai yi muku alheri sa’ad da kuka yi kuka gare shi.” (Isha. 30:19) Ishaya ya tabbatar mana da cewa Jehobah zai saurare mu idan mun yi kuka gare Shi, kuma zai amsa mana ba tare da ɓata lokaci ba. Ishaya ya ƙara cewa: “Da zarar kukanku na neman taimako ya kai kunnensa, zai amsa muku.” Kalmomin nan sun tabbatar mana cewa Ubanmu na sama yana marmarin taimaka wa mabukata. Sanin hakan yana taimaka mana mu ci gaba da jimrewa.

6. Ta yaya abin da Ishaya ya faɗa ya nuna cewa Jehobah yana sauraron adduꞌar kowane ɗaya daga cikin bayinsa?

6 Wane ƙarin tabbaci ne ayar nan ta ba mu game da adduꞌoꞌinmu? Jehobah yana saurarar adduꞌar kowannenmu. Me ya sa muka faɗi hakan? A sashen farko na Ishaya 30, Jehobah yana magana da bayinsa gabaki ɗaya ne. Amma a asalin yare da aka rubuta Littafi Mai Tsarki, an yi amfani da ‘kai’ maimakon ‘ku’ a aya ta 19. Hakan yana nufin cewa Jehobah yana magana ga kowannenmu ne. Don haka, saꞌad da Ishaya ya ce: “Ba za ku sāke yin kuka ba”; “Lallai kuwa zai yi muku alheri”; “Zai amsa muku,” yana nufin yadda Jehobah yake sauraron kowannenmu ne. Da yake Jehobah Ubanmu ne mai ƙauna, ba ya gwada mu da sauran bayinsa a lokacin da muke baƙin ciki. A maimakon haka, yana ƙaunar kowannenmu kuma yana sauraron adduꞌoꞌin kowannenmu.​—Zab. 116:1; Isha. 57:15.

Mene ne Ishaya yake nufi saꞌad da ya ce: “Kada kuma ku ba Yahweh hutu”? (Ka duba sakin layi na 7)

7. Ta yaya Ishaya da Yesu suka nuna muhimmancin nacewa a yin adduꞌa?

7 Idan muka yi adduꞌa ga Jehobah kuma muka gaya masa abubuwan da suke damun mu, Jehobah zai amsa mana ba tare da ɓata lokaci ba kuma zai ba mu ƙarfin da muke bukata don mu jimre. Kuma idan matsalolinmu ba su ƙare a lokacin da muke tsammani ba, za mu bukaci mu ci gaba da roƙon Jehobah don ya ba mu ƙarfi da muke bukata don mu iya jimrewa. Ya gaya mana mu yi hakan. Abin da Ishaya yake nufi ke nan saꞌad da ya ce: “Kada kuma ku ba Yahweh hutu.” (Isha. 62:7) Mene ne hakan yake nufi? Zai dace mu ci gaba da yin adduꞌa babu fashi har ya zama kamar ba ma barin Jehobah ya huta. Abin da Ishaya ya faɗa ya tuna mana da kwatanci da Yesu ya yi a Luka 11:​8-10, 13. A wurin, Yesu ya ƙarfafa mu mu yi ta yin adduꞌa da naciya kuma mu yi ta roƙon Jehobah ya ba mu ruhunsa. Za mu kuma iya roƙon Jehobah ya ja-gorance mu don mu iya yanke shawarar da ta dace.

JEHOBAH YANA MANA JA-GORANCI

8. Ta yaya abin da ke Ishaya 30:​20, 21 suka cika a zamanin dā?

8 Karanta Ishaya 30:​20, 21. A lokacin da sojojin Babila suka kewaye Urushalima na tsawon shekara ɗaya da rabi, mutanen sun sha wahala sosai, kuma hakan ya zama musu kamar abinci da ruwa. Amma bisa ga ayoyi 20 da 21, Jehobah ya yi wa Yahudawan alkawari cewa idan sun tuba kuma suka canja halayensu, zai taimaka musu. Ishaya ya kira Jehobah ‘Malaminsu,’ kuma ya yi musu alkawari cewa Jehobah zai koya musu yadda za su bauta masa a hanyar da ta dace. Annabcin nan ya cika saꞌad da aka saki Israꞌilawa daga bauta. Jehobah ya nuna cewa shi Babban Malaminsu ne da gaske domin a ƙarƙashin ja-gorancinsa sun yi nasarar maido da bauta ta gaskiya. Muna farin ciki sosai domin Jehobah ne Babban Malaminmu a yau.

9. Ta wace hanya ce Jehobah yake yi mana ja-goranci a yau?

9 A waɗannan ayoyin, Ishaya ya ce Jehobah yana koyar da mu ɗalibansa a hanyoyi biyu. Da farko, Ishaya ya ce: “Za ku ga Malaminku Ubangiji da idanunku.” A wannan kwatanci, Ishaya ya ce Malamin yana tsaye a gaban ɗalibansa. Babban gata ne a gare mu mu koya daga wurin Jehobah. Ta yaya Jehobah yake koyar da mu? Yana yin hakan ta wajen ƙungiyarsa. Muna farin ciki sosai domin umurnai da muke samuwa daga wurin Jehobah! Umurnai da ake ba mu a taron ikilisiya da taron yanki, da kuma littattafanmu da Tashar JW da wasu hanyoyi da dama suna taimaka mana mu iya jimre matsaloli da farin ciki.

10. Ta yaya muke jin ‘murya a bayanmu’?

10 Ishaya ya rubuta hanya ta biyu da Jehobah yake yi mana ja-goranci, ya ce: “Kunnenka zai ji murya a bayanka.” Ishaya ya kwatanta Jehobah a matsayin malamin da yake bin ɗalibansa a baya yana lura da su da kyau kuma yana nuna musu hanyar da za su bi. A yau, muna jin muryar Allah a bayanmu. Ta yaya? An rubuta Kalmomin Allah a cikin Littafi Mai Tsarki shekaru da yawa kafin a haife mu. Don haka, idan muka karanta Littafi Mai Tsarki yana kamar muna jin Kalmar Allah a bayanmu ne.​—Isha. 51:4.

11. Don mu iya jimre da farin ciki, waɗanne abubuwa ne muke bukatar mu yi, kuma me ya sa?

11 Ta yaya za mu iya amfana daga ja-goranci da Jehobah yake yi mana ta wurin ƙungiyarsa da kuma Kalmarsa? Ka lura cewa Ishaya ya faɗi abubuwa guda biyu. Da farko, ya ce “ga hanyar.” Sai ya ƙara da cewa, “yi tafiya a cikinta.” (Isha. 30:21) Ba sanin “hanyar” ne kawai muke bukatar mu yi ba, muna bukatar mu “yi tafiya a cikinta.” Muna sanin abin da Jehobah yake bukata a gare mu ta hanyar da ƙungiyarsa take bayyana mana Kalmarsa. Muna kuma koyan yadda za mu aikata abin da muka koya. Don mu ci gaba da farin ciki yayin da muke jimrewa a hidimarmu ga Jehobah, muna bukatar mu yi dukansu biyun. Idan mun yi hakan, za mu iya kasance da tabbaci cewa Jehobah zai albarkace mu.

JEHOBAH YANA YI MANA ALBARKA

12. Bisa ga Ishaya 30:​23-26, ta yaya Jehobah zai albarkace mutanensa?

12 Karanta Ishaya 30:​23-26. Ta yaya wannan annabcin ya cika a kan waɗanda suka koma Urushalima daga bauta a Babila? Jehobah ya ba su abubuwa da dama da suke bukata don su ci gaba da rayuwa kuma su ci gaba da bauta masa. Jehobah ya albarkaci mutanensa da abinci mai yawa. Amma mafi muhimmanci shi ne, ya ba su abubuwan da suke bukata don su kusace shi, kuma su bauta masa a hanyar da ta dace. A lokacin, bayin Allah ba su taɓa samun abubuwa da yawa daga wurinsa kamar haka ba. Aya ta 26 ta nuna cewa Jehobah ya ba su ƙarin haske, wato ya taimaka musu su daɗa fahimtar Kalmarsa. (Isha. 60:2) Albarkun da Jehobah ya ba wa mutanensa ya taimaka musu su ji daɗin bauta masa domin suna da “farin ciki a zuciyarsu.”​—Isha. 65:14.

13. Ta yaya annabcin da aka yi game da maido da bauta ta gaskiya yake cika a yau?

13 Shin annabci da aka yi game da maido da bauta ta gaskiya ya shafe mu a yau? Ƙwarai kuwa! A wace hanya? Tun daga 1919 bayan haihuwar Yesu, miliyoyin mutane sun sami ꞌyanci daga bautar da suke yi wa Babila Babba, wato daular addinan ƙarya na dukan duniya. An ja-gorance su zuwa wurin da ya fi Ƙasar Alkawari na Israꞌila daraja. Wurin da aka kai su shi ne aljanna ta ruhu. (Isha. 51:3; 66:8) Mece ce aljanna ta ruhu?

14. Mene ne aljanna ta ruhu, kuma su waye ne suke ciki a yau? (Ka duba Ma’anar Wasu Kalmomi.)

14 Tun daga 1919, shafaffun Kiristoci suna jin daɗin kasancewa a aljanna ta ruhu. b Da shigewar lokaci, “waɗansu tumaki” ma sun shiga aljanna ta ruhun, kuma su ma suna moran albarkun Jehobah.​—Yoh. 10:16; Isha. 25:6; 65:13.

15. A ina ne aljanna ta ruhu take?

15 A ina ne aljanna ta ruhun take a yau? Bayin Jehobah suna koꞌina a duk faɗin duniya. Don haka, aljanna ta ruhu da suke ciki tana koꞌina a faɗin duniya. Ƙari ga haka, a duk inda muke a duniya a yau, za mu iya kasancewa cikin aljanna ta ruhu, muddin muna bauta ma Jehobah a hanyar da yake so.

Mene ne kowannenmu ya kamata ya yi don aljannarmu ta ruhu ta daɗa kasancewa da kyau? (Ka duba sakin layi na 16-17)

16. Ta yaya za mu ci gaba da mai da hankali ga yadda aljannarmu ta ruhu take da kyau?

16 Don mu ci gaba da zama a aljanna ta ruhu, ɗaya daga cikin abubuwan da muke bukatar mu yi shi ne mu ci gaba da nuna godiya don ꞌyanꞌuwa da muke da su a dukan faɗin duniya. Ta yaya za mu yi hakan? Za mu iya yin hakan ta wajen mai da hankali ga yadda aljannar take da kyau, maimakon mai da hankali ga ajizancin ꞌyanꞌuwanmu. (Yoh. 17:​20, 21) Me ya sa hakan yake da muhimmanci? Ka yi laꞌakari da wannan kwatanci. Idan muka je wurin shaƙatawa ko lambu, za mu so mu ga itatuwa dabam-dabam masu kyau. Haka ma, a aljannarmu ta ruhu, akwai ꞌyanꞌuwa maza da mata da suke kama da itatuwa masu kyau. (Isha. 44:4; 61:3) Muna bukatar mu ci gaba da mai da hankali ga yadda lambun gabaki ɗaya take da kyau, maimakon aibin da ke kowane “itace” da ke kusa da mu. Ba zai dace mu bar ajizancinmu ko kuma ajizancin ꞌyanꞌuwanmu a ikilisiya ya ɗauke hankalinmu daga yadda muke amfana domin haɗin kai da muke da shi da ꞌyanꞌuwanmu a duk faɗin duniya ba.

17. Mene ne kowannenmu zai iya yi don a daɗa samun haɗin kai a ikilisiya?

17 Mene ne kowannenmu zai iya yi don a daɗa samun haɗin kai a ikilisiya? Za mu iya sa a yi hakan ta wajen zama masu sada zumunci. (Mat. 5:9; Rom. 12:18) A duk lokacin da mun yi iya ƙoƙarinmu don mu sada zumunci da ꞌyanꞌuwanmu a ikilisiya, muna daɗa sa aljannarmu ta ruhu ta yi kyau. Muna bukatar mu riƙa tuna cewa Jehobah ne ya jawo kowannenmu zuwa cikin aljanna ta ruhu don mu bauta masa a hanyar da yake so. (Yoh. 6:44) Ka yi tunanin irin farin cikin da Jehobah zai yi yayin da yake ganin irin ƙoƙarin da muke yi don mu sa salama ta kasance a tsakanin bayinsa, waɗanda ke da daraja a idanunsa!​—Isha. 26:3; Hag. 2:7.

18. Mene ne ya kamata mu riƙa yin tunani a kai, kuma me ya sa?

18 Jehobah yana ba wa bayinsa abubuwa masu kyau da yawa. Ta yaya za mu amfana daga abubuwan nan? Za mu iya yin tunani mai zurfi a kan abubuwan da muka karanta daga Littafi Mai Tsarki da kuma littattafanmu. Yin nazarin Littafi Mai Tsarki da kuma bimbini zai taimaka mana mu kasance da halayen Kirista kuma mu nuna wa juna “ƙauna irin ta ’yan’uwa” a ikilisiya. (Rom. 12:10) Yayin da muke tunani a kan albarku da Jehobah ya yi mana a yanzu, dangantakarmu da shi za ta daɗa danƙo. Kuma idan muka yi tunani game da alkawura masu kyau da Allah ya yi mana, hakan zai sa mu daɗa marmarin bauta masa har abada. Ƙari ga haka, zai sa mu daɗa farin ciki yayin da muke bauta ma Jehobah a yanzu.

KA ƘUDIRI NIYYAR CI GABA DA JIMREWA

19. (a) Bisa ga Ishaya 30:​18, wane tabbaci ne muke da shi? (b) Mene ne zai taimaka mana mu yi farin ciki yayin da muke jimrewa?

19 A shirye Jehobah yake ya cece mu a lokacin da zai hallaka wannan muguwar duniya. (Isha. 30:18) Muna da tabbaci cewa Jehobah wanda shi ne Allah “mai yin gaskiya,” ba zai bar duniyar Shaiɗan ta ci gaba da kasancewa ko na kwana ɗaya fiye da lokacin da ya shirya ba. (Isha. 25:9) Za mu ci gaba da yin haƙuri yayin da muke jiran lokacin da Jehobah zai cece mu. Amma kafin lokacin, mun ƙudiri niyyar ci gaba da nuna godiya domin gata da muke da shi na yin adduꞌa da nazarin Kalmar Allah, da aikata abubuwan da muke koya da kuma yin bimbini a kan albarkun da Allah ya yi mana. Yayin da muke yin hakan, Jehobah zai taimaka mana mu jimre da farin ciki yayin da muke bauta masa.

WAƘA TA 142 Mu Jimre, Aljanna Ta Kusa

a A wannan talifin, za mu tattauna hanyoyi uku da Jehobah yake taimaka wa bayinsa su iya jimre matsaloli da farin ciki. Za mu ga hanyoyin nan da Jehobah yake taimaka mana ta wajen bincika littafin Ishaya 30. Yayin da muke tattauna wannan surar, za mu ga muhimmancin yin adduꞌa ga Jehobah da yin nazarin Kalmarsa Littafi Mai Tsarki, da kuma yin bimbini a kan albarkun da Allah ya ba mu a yanzu da waɗanda za mu samu a nan gaba.

b MA’ANAR WASU KALMOMI: “Aljanna ta ruhu” tana nufin yadda muke bauta ma Jehobah cikin kwanciyar hankali da kuma haɗin kai. Jehobah yana koya mana dukan abubuwan da muke bukata don mu iya bauta masa ba tare da bin ƙaryace-ƙaryace da addinai suke koyarwa ba, kuma muna farin cikin yin wa’azi game da Mulkin Allah, wato aikin da ke gamsar da mu. Muna farin ciki domin muna da dangantaka mai kyau da Jehobah kuma muna zaman lafiya da ꞌyan’uwanmu, waɗanda suke taimaka mana mu jimre matsalolin da muke fuskanta da farin ciki. Mun shiga aljanna ta ruhu saꞌad da muka soma bauta ma Jehobah a hanyar da ta dace kuma saꞌad da muka yi iya ƙoƙarinmu mu yi koyi da shi.