Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 46

WAƘA TA 49 Mu Riƙa Faranta Ran Jehobah

ꞌYanꞌuwa Maza​—⁠Kuna Kokari don Ku Zama Bayi Masu Hidima?

ꞌYanꞌuwa Maza​—⁠Kuna Kokari don Ku Zama Bayi Masu Hidima?

“Bayarwa tana sa mutum farin ciki fiye da karɓa.”A. M. 20:​35, NWT.

ABIN DA ZA MU KOYA

An shirya talifin nan ne don a taimaki ꞌyanꞌuwa maza su yi marmarin zama bayi masu hidima, kuma su ƙoƙarta don su cancanta.

1. Mene ne raꞌayin manzo Bulus game da bayi masu hidima?

 BAYI MASU HIDIMA suna da muhimmanci sosai a ikilisiya. Manzo Bulus ya daraja ꞌyanꞌuwan nan masu aminci. Alal misali, a lokacin da ya rubuta wa ꞌyanꞌuwa da suke Filibi wasiƙa, ya aika saƙon gaisuwa ta musamman ga bayi masu hidima da ke ikilisiyar, da kuma dattawansu.—Filib. 1:1.

2. Mene ne raꞌayin Ɗanꞌuwa Luis game da aikinsa a matsayin bawa mai hidima?

2 ꞌYanꞌuwa da yawa suna jin daɗin yin aiki a matsayin bayi masu hidima, komen shekarunsu. Wani matashi mai suna Devan, yana shekara 18 saꞌad da aka naɗa shi bawa mai hidima. Wani ɗanꞌuwa kuma mai suna Luis, ya wuce shekaru 50 saꞌad da aka naɗa shi. Mene ne raꞌayin Ɗanꞌuwa Luis game da hidimar da yake yi? Ya ce: “Yin aikin bawa mai hidima babban gata ne sosai a gare ni. Ina jin daɗin taimaka wa ꞌyanꞌuwa, domin su ma sun nuna min ƙauna a hanyoyi da dama!”

3. Waɗanne tambayoyi ne za mu ga amsoshinsu a wannan talifin?

3 Idan ka yi baftisma amma ba ka zama bawa mai hidima ba tukun, zai yi kyau ka kasance da wannan burin. Me zai taimaka maka ka yi marmarin yin wannan hidimar? Kuma waɗanne halaye ne Littafi Mai Tsarki ya ce kana bukata don ka zama bawa mai hidima? Za mu ga amsoshin tambayoyin nan a wannan talifin. Amma bari mu fara da tattauna aikin da bayi masu hidima suke yi a ikilisiya.

WANE AIKI NE BAYI MASU HIDIMA SUKE YI?

4. Wane aiki ne bayi masu hidima suke yi? (Ka kuma duba hoton.)

4 Bawa mai hidima ɗanꞌuwa ne da ya yi baftisma kuma aka naɗa shi da ruhu mai tsarki, don ya taimaki dattawa wajen yin ayyuka da dama masu muhimmanci a ikilisiya. Wasu bayi masu hidima ne suke tabbatar da cewa ꞌyanꞌuwa sun sami inda za su yi waꞌazi, da littattafan da suke bukata. Wasu suna taimakawa wajen yin shara da kula da Majami’ar Mulki. Wasu kuma suna yin aikin atenda, ko su yi aiki a wurin kunna sauti da nuna bidiyo. Amma abin da ya fi muhimmanci shi ne cewa, bayi masu hidima ꞌyanꞌuwa ne da suke ƙaunar Jehobah, kuma suna yin rayuwar da take faranta masa rai. Suna kuma ƙaunar ꞌyanꞌuwa masu bi sosai. (Mat. 22:​37-39) Idan ɗanꞌuwa ya yi baftisma kuma yana so ya zama bawa mai hidima, me zai yi?

Bayi masu hidima suna yin koyi da Yesu ta wajen yi wa ꞌyanꞌuwa hidima da son ransu, domin amfanin ꞌyanꞌuwa (Ka duba sakin layi na 4)


5. Me za ka yi idan kana so ka zama bawa mai hidima?

5 Littafi Mai Tsarki ya gaya mana halayen da ɗanꞌuwa yake bukata ya kasance da su kafin a naɗa shi bawa mai hidima. (1 Tim. 3:​8-10, 12, 13) Idan kana so ka zama bawa mai hidima, ka san waɗannan halayen sosai, kuma ka yi ƙoƙari ka nuna su a rayuwarka. Amma kafin nan, ka bincika dalilin da ya sa kake so ka zama bawa mai hidima.

ME YA SA KAKE SO KA ZAMA BAWA MAI HIDIMA?

6. Mene ne ya kamata ya zama dalilinmu na son taimaka wa ꞌyanꞌuwa? (Matiyu 20:28; ka kuma duba shafin farko.)

6 Ka tuna da Yesu, wanda shi ne muke bin gurbinsa. Ƙaunar da yake yi wa Jehobah da mutane, ita ce ta sa ya yi dukan abubuwan da ya yi. Ƙauna ce ta sa ya yi iya ƙoƙarinsa a hidimarsa, har ya yi aiki kamar bawa don amfanin mutane. (Karanta Matiyu 20:28; Yoh. 13:​5, 14, 15) Kai ma idan ƙauna ce ta sa kake so ka zama bawa mai hidima, Jehobah zai yi maka albarka, kuma zai taimake ka ka cancanta.—1 Kor. 16:14; 1 Bit. 5:5.

Yesu ya ƙaskantar da kansa ya yi wa mutane hidima, kuma ya koya wa almajiransa su yi bi halinsa maimakon su yi ta neman matsayi (Ka duba sakin layi na 6)


7. Me ya sa bai dace ɗanꞌuwa ya zama mai neman matsayi ba?

7 A yau, mutane suna son ɗaukaka kansu, kuma masu irin wannan halin suna burge mutane da yawa. Amma ba haka ake yi a ƙungiyar Jehobah ba. Idan ɗanꞌuwa yana ƙaunar mutane kamar Yesu, ba zai nemi yin iko a kansu ko ya ɗaukaka kansa ba. Ƙari ga haka, idan ɗanꞌuwa mai neman matsayi ne, kuma aka naɗa shi bawa mai hidima, zai yi wuya ya ƙasƙantar da kansa ya yi ƙananan ayyukan da ake bukatar ya yi don amfanin tumakin Jehobah. Wataƙila ya ɗauka cewa ya fi ƙarfin yinsu. (Yoh. 10:12) Jehobah ba zai albarkaci mai girman kai ko mai neman matsayi ba, komen ƙoƙarinsa.—1 Kor. 10:​24, 33; 13:​4, 5.

8. Mene ne Yesu ya gaya wa manzanninsa?

8 Akwai lokutan da waɗanda suka fi kusa da Yesu suka nuna halin neman matsayi. Abin da manzanninsa biyu, wato Yakub da Yohanna, suka yi ke nan. Sun ce ma Yesu ya ba su matsayi na musamman a Mulkinsa. Yesu bai yaba masu ba. A maimakon haka, ya gaya musu da sauran manzannin cewa: “Duk wanda yake so ya zama babba a cikinku, dole ne ya zama mai yi wa sauran hidima.” (Mar. 10:​35-37, 43, 44) Idan ꞌyanꞌuwa suka ƙoƙarta don su zama bayi masu hidima da dalili mai kyau, wato da niyyar yi ma ꞌyanꞌuwa hidima, za su amfani ikilisiyarsu sosai.—1 Tas. 2:8.

ME ZAI SA KA SO YI WA ꞌYANꞌUWA HIDIMA?

9. Me zai sa ka so yi wa ꞌyanꞌuwa hidima?

9 Mun san kana ƙaunar Jehobah, kuma kana so ka taimaka wa ꞌyanꞌuwa. Amma wataƙila ba ka so ka zama bawa mai hidima domin yawan ayyukan da suke yi. Me zai iya sa ka so yi wa ꞌyanꞌuwa wannan hidimar? Ka yi tunanin irin farin cikin da za ka yi idan kana taimaka wa ꞌyanꞌuwa. Yesu ya ce: “Bayarwa tana sa mutum farin ciki fiye da karɓa.” (A. M. 20:​35, NWT) Shi ma ya shaida hakan a rayuwarsa. Ya yi wa mutane hidima, kuma hakan ya sa shi farin ciki sosai. Kai ma idan ka yi wa ꞌyanꞌuwanka hidima, za ka yi farin ciki.

10. Mene ne Yesu ya yi da ya nuna cewa ya ji daɗin yi wa mutane hidima? (Markus 6:​31-34)

10 Ga wani misali da ya nuna cewa Yesu ya ji daɗin yi wa mutane hidima. (Karanta Markus 6:​31-34.) Akwai lokacin da shi da manzanninsa suka gaji sosai. Sai suka kama hanya za su je inda babu kowa don su huta. Amma sai jamaꞌa suka riga su zuwa wurin. Sun je suna jiran Yesu ya iso ya koyar da su. Da Yesu ya ga dama, da ya ce ba zai koyar da su ba. Domin shi da manzanninsa sun sha aiki, har “ba su sami damar cin abinci ba.” Ko kuma, da ya koya musu abu ɗaya ko biyu kawai, sai ya ce su tafi. Amma Yesu bai yi haka ba don yana ƙaunarsu. Ya “koya musu abubuwa da yawa.” Kuma ya ci-gaba da koyar da su har “kusan fāɗuwar rana.” (Mar. 6:35) Me ya sa Yesu ya yi hakan? Don ya zama masa dole ne? Aꞌa. Ya “ji tausayinsu” shi ya sa. Da son ransa ya koyar da su, don yana ƙaunarsu. A gun Yesu, yin aiki don amfanin mutane, abin farin ciki ne sosai!

11. Ta yaya Yesu ya taimaka wa mutane da abin da suke bukata? (Ka kuma duba hoton.)

11 Yesu ya taimaka wa mutanen ta wurin koyar da su. Amma ba shi ke nan ba, ya kuma kula da bukatunsu. Ya samo musu abinci, kuma ya ce ma almajiransa su raba musu su ci. (Mar. 6:41) Ta haka, ya koya wa almajiransa su ma su zama masu yi wa mutane hidima. Irin aikin da bayi masu hidima suke yi ke nan. Yesu ya nuna wa almajiransa cewa irin wannan aikin yana da muhimmanci. Ba ka ganin almajiran Yesu sun yi farin ciki sosai da suka taimaka masa wajen rarraba abincin har “duka . . . suka ci suka ƙoshi”? (Mar. 6:42) Wannan ɗaya ne kawai daga cikin lokuta da yawa da Yesu ya sa bukatun mutane gaba da nasa. Hidima ya yi ta yi wa mutane a dukan rayuwarsa. (Mat. 4:23; 8:16) Koyar da mutane da kuma biyan bukatunsu sun sa Yesu farin ciki. Don haka, kai ma za ka yi farin ciki sosai idan ka yarda ka yi wa ꞌyanꞌuwa hidima a matsayin bawa mai hidima.

Idan kana ƙaunar Jehobah kuma kana so ka yi wa ꞌyanꞌuwa hidima, za ka yi duk wani abin da za ka iya don ka taimaka musu (Ka duba sakin layi na 11) a


12. Me ya sa bai kamata waninmu ya ɗauka cewa ba zai iya taimaka wa ꞌyanꞌuwa a ikilisiya ba?

12 Idan kuma kana gani kamar ba ka da wata baiwa ta musamman, kada ka karaya. Kai ma za ka iya taimaka wa ꞌyanꞌuwa a ikilisiya. Ka yi tunani a kan abin da Bulus ya ce a 1 Korintiyawa 12:​12-30, kuma ka roƙi Jehobah ya taimake ka ka ga yadda bayanin ya shafe ka. Kalmomin Bulus sun nuna cewa kai ma kana da muhimmanci sosai a ikilisiya, kuma ana bukatarka kamar yadda ake bukatar sauran ꞌyanꞌuwa. Idan har ila kana bukatar ka koyi wasu halaye don ka cancanci zama bawa mai hidima, kada ka fid da rai. A maimako, ka bauta wa Jehobah kuma ka taimaka wa ꞌyanꞌuwa iya ƙarfinka. Dattawa za su lura da kai, kuma za su ba ka ayyukan da ba za su fi ƙarfinka ba.—Rom. 12:​4-8.

13. Wane dalili ne kuma ya sa ya kamata ka yi ƙoƙari ka cancanci zama bawa mai hidima?

13 Ga wani dalili kuma da ya sa ya kamata ka yi ƙoƙari ka cancanci zama bawa mai hidima. Dalilin shi ne: Yawancin halaye da ake bukata, halaye ne da dukan Kiristoci suke bukatar su kasance da su. Dukan Kiristoci suna bukatar su kusaci Jehobah, su yi rayuwar da za ta gamshe shi, kuma su zama masu bayarwa da farin ciki. Yanzu bari mu tattauna abin da ake bukata daga wurin ɗanꞌuwa kafin ya zama bawa mai hidima.

ME ZA KA YI DON KA CANCANCI ZAMA BAWA MAI HIDIMA?

14. Me ake nufi da cewa mutum ya ‘kasance mai hankali’? (1 Timoti 3:​8-10, 12)

14 Littafin 1 Timoti 3:​8-10, 12, (Karanta) sun faɗi abin da ake bukata daga wurin wanda yake so ya zama bawa mai hidima. Dole bawa mai hidima ya ‘kasance mai hankali.’ Hakan yana nufin ya zama mai natsuwa, kuma ya riƙa yin abubuwa yadda mutane ba za su rena shi ba. Wannan ba ya nufin cewa idan kana so ka zama bawa mai hidima, ba za ka riƙa wasa da mutane ba. (M. Wa. 3:​1, 4) Abin da ake nufi shi ne, ka zama wanda yake sa ƙwazo don ya cika aikin da aka ba shi. Idan kana yin ayyukan da aka ba ka da kyau, ꞌyanꞌuwa ba za su yi shakkar ka ba, kuma za su girmama ka.

15. Me ake nufi da cewa kada mutum ya zama mai “baki biyu a magana,” da kuma mai “cuta a fannin kuɗi”?

15 “Ba masu baki biyu a magana ba.” Hakan yana nufin cewa ka zama mai faɗin gaskiya, wato wanda za a iya yarda da shi. Ka riƙa cika alkawarinka, kuma kar ka zama mai munafunci. (K. Mag. 3:32) “Ba … masu cuta a fannin kuɗi ba.” Wannan yana nufin ka zama mai yin gaskiya a kasuwancinka, da duk wani abin da ya shafi kuɗi. Ba za ka yi amfani da mutunci da ke tsakaninka da ꞌyanꞌuwa ka yaudare su don ka sami kuɗi ba.

16. (a) Me ake nufi da cewa kada mutum ya zama mai “yawan shan ruwan inabi”? (b) Me ake nufi da cewa ‘tunaninsa ya tabbatar masa ba shi da laifi’?

16 “Ba … masu yawan shan ruwan inabi … ba.” Hakan yana nufin cewa kada ka zama wanda idan ya tashi shan giya, sai ya sha da yawa, ko a san ka a matsayin mashayi. ‘Tunaninsu ya tabbatar musu ba su da laifi.’ Hakan yana nufin cewa ka riƙa yin rayuwar da za ta gamshi Allah. Ko da yake kai ajizi ne, za ka zama da dangantaka mai kyau da Allah kuma ka sami kwanciyar hankali.

17. Ta yaya ɗanꞌuwa zai nuna cewa za a iya yarda da shi lokacin da ake “gwada” shi? (1 Timoti 3:10; ka kuma duba hoton.)

17 “Sai an gwada su tukuna.” Hakan yana nufin cewa dattawa suna bukatar su ga cewa kana yin aikin da aka ba ka da kyau, kuma za su iya yarda da kai. Don haka, idan dattawa suka ba ka wani aiki, ka yi shi daidai yadda suka gaya maka, kuma ka bi umurnan da ƙungiyarmu ta bayar game da yin aikin. Ka tabbata ka fahimci abin da ake so ka yi, da kuma lokacin da ake so ka gama shi. Idan kana yin aikinka da kyau kuma da himma, ꞌyanꞌuwa a ikilisiya za su ga cewa kana samun ci-gaba. Dattawa, kada ku yi wasa da koyar da ꞌyanꞌuwa maza da suka yi baftisma. (Karanta 1 Timoti 3:10.) A ikilisiyarku, akwai matasa da suka yi baftisma kuma suna ƙasa da shekaru 15? Suna nazari da kansu kuma suna yin shiri kafin su zo taro? Suna yin kalami sosai kuma suna zuwa waꞌazi? Idan akwai su, ku ba su aikin da za su iya yi daidai da shekarunsu. Yadda za ku “gwada su” ke nan. Hakan zai taimake su su cancanci zama bayi masu hidima da wuri, wataƙila saꞌad da suka kai shekaru 17.

Dattawa za su iya “gwada” ꞌyanꞌuwa maza da suka yi baftisma ta wurin ba su wasu ayyuka (Ka duba sakin layi na 17)


18. Me ake nufi da cewa mutum ya tabbata ba shi da laifi?

18 A “tabbata ba su da laifi.” Wato, ya zama cewa ba wanda zai iya zargin ka da yin abin da bai dace ba. Wani lokaci akan zargi Kiristoci a kan abin da ba su yi ba. Saꞌad da Yesu yake duniya, shi ma an yi masa irin wannan zargin, kuma ya ce hakan zai faru da mabiyansa. (Yoh. 15:20) Amma idan ka ci-gaba da yin abu mai kyau, ꞌyanꞌuwa a ikilisiya za su san cewa kai mutumin kirki ne.—Mat. 11:19.

19. Me ake nufi da cewa mutum “ya kasance da mace ɗaya”?

19 “Ya kasance da mace ɗaya.” Jehobah ya shirya aure ya kasance tsakanin namiji ɗaya da mace ɗaya, kuma dole dukan Kiristoci su bi wannan ƙaꞌidar. (Mat. 19:​3-9) Bai kamata Kirista ya yi lalata ba, sam! (Ibran. 13:4) Amma ba shi ke nan ba. Dole ka guji yin duk wani abin da zai nuna cewa kana shaꞌawar wata da ba matarka ba.—Ayu. 31:1.

20. Me ake nufi da cewa mutum ya “bi da yaransa da sauran iyalinsa a hanyar da ta dace”?

20 “Yana kuma bi da yaransa da sauran iyalinsa a hanyar da ta dace.” Hakan yana nufin cewa idan kai magidanci ne, kada ka yi wasa da kula da ꞌyan iyalinka. Ka tabbata kuna yin ibada ta iyali babu fashi. Ka riƙa yin waꞌazi tare da matarka da kowanne cikin yaranka iya gwargwado. Ka taimaki yaranka su ƙaunaci Jehobah kuma su zama abokansa. (Afis. 6:4) Idan mutum yana kula da ꞌyan iyalinsa da kyau, hakan zai nuna cewa zai iya kula da ꞌyanꞌuwa a ikilisiya.—Ka kuma duba 1 Timoti 3:5.

21. Idan ba ka riga ka zama bawa mai hidima ba, me ake ƙarfafa ka ka yi?

21 ꞌYanꞌuwa maza, idan ba ku riga kun zama bayi masu hidima ba, don Allah ku karanta wannan talifin kuma ku roƙi Jehobah ya taimake ku. Ku bincika abubuwan da ake bukata daga wurin bayi masu hidima, kuma ku yi iya ƙoƙarinku don ku cancanci yin wannan hidimar. Ka tuna cewa kana ƙaunar Jehobah sosai, kuma kana ƙaunar ꞌyanꞌuwa. Don haka ka yi abubuwan da za su sa ka ƙara ƙaunar ꞌyanꞌuwa, kuma ka so taimaka musu. (1 Bit. 4:​8, 10) Ka yi ƙoƙari ka zama bawa mai hidima, don hidimar da za ka yi wa ꞌyanꞌuwanka za ta sa ka yi farin ciki sosai. Bari Jehobah ya yi maka albarka, yayin da kake iya ƙoƙarinka don ka zama bawa mai hidima!—Filib. 2:13.

WAƘA TA 17 “Na Yarda”

a BAYANI A KAN HOTUNA: A gefen hagu, Yesu yana taimaka wata mata; a gefen dama, wani bawa mai hidima yana taimaka ma wani ɗanꞌuwa da ya tsufa.