Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 47

WAƘA TA 103 Jehobah Ya Yi Tanadin Makiyaya

ꞌYanꞌuwa Maza​—⁠Kuna Kokari don Ku Zama Dattawa?

ꞌYanꞌuwa Maza​—⁠Kuna Kokari don Ku Zama Dattawa?

“Duk wanda yake marmarin zaman mai kula da jamaꞌar masu bi, aikin daraja yake marmarinsa.”1 TIM. 3:1.

ABIN DA ZA MU KOYA

Za mu ga abin da Littafi Mai Tsarki ya ce ana bukata daga wurin ɗanꞌuwa kafin a naɗa shi dattijo.

1-2. Mene ne aikin dattijo ya ƙunsa?

 IDAN kai bawa mai hidima ne, ba mamaki ka riga ka soma nuna halaye da ake bukata dattawa su kasance da su. Za ka so ka ƙara taimaka wa ꞌyanꞌuwa ta wurin yin aikin dattijo?—1 Tim. 3:1.

2 Mene ne aikin dattijo ya ƙunsa? Dattawa suna yin ja-goranci a waꞌazi, suna iya ƙoƙarinsu su kula da ꞌyanꞌuwa a ikilisiya kuma su koyar da su. Kuma suna ƙarfafa ꞌyanꞌuwa su kasance da bangaskiya ta furucinsu da ayyukansu. Shi ya sa ya dace sosai da Littafi Mai Tsarki ya ce dattawa maza ne da aka ba mu “kyauta.”—Afis. 4:​8, NWT.

3. Mene ne za ka yi don ka zama dattijo? (1 Timoti 3:​1-7; Titus 1:​5-9)

3 Me za ka yi don ka zama dattijo? Zama dattijo ba kamar samun aiki a wani wuri ba ne. Domin idan ka je neman aiki, a yawacin lokaci muddin ka iya yin aikin, za a ɗauke ka. Amma idan kana so ka zama dattijo, ba iya yin waꞌazi da koyarwa kawai kake bukata ba. Kana bukatar ka kasance da halayen da Littafi Mai Tsarki ya ambata a 1 Timoti 3:​1-7 da Titus 1:​5-9. (Karanta.) A talifin nan, za mu tattauna wasu daga cikin halayen nan. Za mu ga abin da ɗanꞌuwa zai yi don a san da shi a matsayin mutumin kirki, da yadda zai kula da iyalinsa da kyau, da kuma abin da zai taimake shi ya yi marmarin yi wa ꞌyanꞌuwa hidima.

A SAN KAI A MATSAYIN MUTUMIN KIRKI

4. Me ake nufi da cewa mutum ya “kasance marar laifi a gaban mutane”?

4 Idan kana so ka zama dattijo, dole ka “kasance marar laifi a gaban mutane.” Hakan yana nufi ka zama wanda ꞌyanꞌuwa a ikilisiya suna ganin cewa shi mutumin kirki ne, don halayenka da ayyukanka sun nuna hakan. Ƙari ga haka, ka “kasance wanda yake da shaida mai kyau a gaban mutanen da ba masu bi ba.” Waɗanda ba sa bauta wa Jehobah ba za su yarda da imaninka ba a wasu lokuta, amma bai kamata halinka ya sa su yi shakka cewa kai mutumin kirki ne kuma mai faɗin gaskiya ba. (Dan. 6:​4, 5) Ka tambayi kanka, ‘ꞌYanꞌuwa da waɗanda ba ꞌyanꞌuwa ba sun san ni a matsayin mutumin kirki kuwa?’

5. Ta yaya za ka nuna cewa kai “mai son nagarta” ne?

5 Idan kai “mai son nagarta” ne, za ka fi lura da abubuwa masu kyau da mutane suke yi, kuma za ka riƙa yabon su. Za ka so yi wa mutane kirki, har ma fiye da yadda ake zato. (1 Tas. 2:8) Me ya sa ake bukatar dattawa su zama masu son nagarta? Domin za su riƙa amfani da lokacinsu sosai wajen kula da ꞌyanꞌuwa, da yin ayyukan ikilisiya. (1 Bit. 5:​1-3) Yin hakan ba ƙaramin aiki ba ne, amma yana sa su farin ciki ba kaɗan ba.—A. M. 20:35.

6. Ta yaya za ka nuna cewa kai “mai karɓar baƙi” ne? (Ibraniyawa 13:​2, 16; ka kuma duba hoton.)

6 Ta yaya za ka nuna cewa kai “mai karɓar baƙi” ne? Ta wurin marabtar mutane da kuma yi musu alheri, har da waɗanda ba ka saba da su ba. (1 Bit. 4:9) Wani littafi da ke bayyana Littafi Mai Tsarki ya ce mai karɓar baƙi, yana yi wa mutane alheri ko da bai san su ba, kuma yana son gayyatarsu su zo gidansa. Ka tambayi kanka, ‘An san ni a matsayin mai karɓar baƙi?’ (Karanta Ibraniyawa 13:​2, 16.) Mai karɓar baƙi yakan ba baƙinsa abin da yake da shi hannu sake. Alal misali, yana hakan ga talakawa, da baƙi da suka zo ba da jawabi a ikilisiyarsu, da masu kula da da’ira, da dai sauransu.—Far. 18:​2-8; K. Mag. 3:27; Luk. 14:​13, 14; A. M. 16:15; Rom. 12:13.

Wani ɗanꞌuwa da matarsa sun marabci mai kula da daꞌira da matarsa, kuma sun ba su wurin kwana (Ka duba sakin layi na 6)


7. Me ake nufi da cewa kada mutum ya zama “mai son kuɗi”?

7 “Ba mai son kuɗi ba.” Wato, kada kuɗi da abin duniya su fi kome muhimmanci a rayuwarka. Ko da kai talaka ne ko mai kuɗi, ka sa bautar Jehobah farko a rayuwarka. (Mat. 6:33) Ka dinga amfani da lokacinka, da ƙarfinka, da duk wani abin da kake da shi wajen bauta wa Jehobah, da kula da iyalinka, da kuma yi wa ikilisiya hidima. (Mat. 6:24; 1 Yoh. 2:​15-17) Ka tambayi kanka: ‘Samun kuɗi ne ya fi muhimmanci a gare ni? Idan na sami abin da nake bukata, ina gamsuwa kuwa? Ko dai na fi mai da hankali ga neman kuɗi da ƙarin dukiya?’—1 Tim. 6:​6, 17-19.

8. Me ake nufi da cewa mutum ya zama “mai hankali” da kuma “mai horar da kansa”?

8 Idan kai “mai hankali” ne, kuma “mai horar da kansa,” za ka riƙa nuna sanin ya kamata a duk abin da kake yi. Alal misali, idan kana cin abinci, ko shan giya, ko yin ado, ko shakatawa, ba za ka riƙa wuce gona da iri ba. Kuma ba za ka zama mai bin halin mutanen da ba sa bauta wa Jehobah ba. (Luk. 21:34; Yak. 4:4) Ka zama mai haƙuri ko da an ɓata maka rai. Kada ka zama “mai buguwa.” Kuma kada a san ka a matsayin mashayi, wato wanda yake shan giya da yawa. Ka tambayi kanka, ‘Yadda nake yin abubuwa yana nuna cewa ni mai hankali ne, da kuma mai horar da kansa?’

9. Me ake nufi da cewa mutum ya zama “mai natsuwa” da mai tsari?

9 Idan kai “mai natsuwa” ne, za ka riƙa neman sanin abin da Littafi Mai Tsarki ya ce a kowane fannin rayuwarka. Idan wani batu ya taso, za ka bincika shawarar da ke Littafi Mai Tsarki don ka fahimci batun, kuma ka tsai da shawarar da ta dace. Ba za ka zama mai tsai da shawara da garaje ba. A maimakon haka, za ka tabbata ka fahimci batun da kyau. (K. Mag. 18:13) Hakan zai sa ka yi zaɓi mai kyau kuma bisa ƙaꞌida. Kana kuma bukatar ka zama “mai kamun kai,” wato mai tsari. Hakan yana nufi ka riƙa tsara ayyukanka da kyau kuma ka yi su a kan lokaci. Ka zama wanda ba ya fasa yin abin da aka sa shi, kuma mai bin umurni. ꞌYanꞌuwa za su so ka idan kana da halayen nan. Yanzu bari mu tattauna abin da ake bukata daga wurin magidanci da ke so ya zama dattijo.

KA KULA DA IYALINKA DA KYAU

10. Me ake nufi da cewa mutum ya “kasance wanda ya iya bi da iyalinsa da kyau”?

10 Idan kai magidanci ne kuma kana so ka zama dattijo, iyalinka suna bukatar su kasance da halin kirki. Don haka dole ne ka “kasance wanda ya iya bi da iyalinsa da kyau.” Hakan yana nufi ka riƙa nuna wa iyalinka ƙauna, ka biya bukatunsu, kuma ka yi musu ja-goranci mai kyau. Hakan ya haɗa da yin ibada ta iyali, da zuwa taro, da kuma tabbatar da cewa iyalinka suna fita waꞌazi. Me ya sa abubuwan nan suke da muhimmanci? Domin manzo Bulus ya ce: “In har wani bai san yadda zai bi da iyalinsa ba, to, yaya zai iya lura da jamaꞌar masu bin Allah?”—1 Tim. 3:5.

11-12. Idan ɗanꞌuwa yana so ya zama dattijo, me ya sa yake da muhimmanci ya lura da halin yaransa? (Ka kuma duba hoton.)

11 Idan kana da yara da ba su kai shekaru 18 ba, dole su ‘zama masu biyayya da ban girma gare ka ta kowace hanya.’ Kana bukatar ka koyar da su cikin ƙauna. Mun san kana so su ma su riƙa yin wasa da dariya kamar sauran yara. Amma kana bukatar ka koya musu yin biyayya, da girmama mutane, kuma su zama yaran kirki. Ƙari ga haka, dole ka yi iya ƙoƙarinka wajen taimaka musu su ƙaunaci Jehobah, su bi ƙaꞌidodinsa, kuma su zama da burin yin baftisma.

12 “ꞌYaꞌyansa masu gaskiya ne, kuma ba a zarginsu da halin iskanci ko rashin biyayya.” Idan dattijo ko bawa mai hidima yana da yaro da ya yi baftisma ko yana so ya yi baftisma, kuma yaron ya yi zunubi mai tsanani, dattawa za su bincika lamarin. Idan suka ga cewa mahaifin ne ya yi sakaci, hakan zai iya sa a sauƙe shi.—Ka duba Hasumiyar Tsaro na 1 ga Nuwamba, 1996, shafi na 14, sakin layi na 6-7.

Maza za su iya koyar da yaransu ta wurin yin ayyukan ibada dabam-dabam tare da su (Ka duba sakin layi na 11)


KA YI WA IKILISIYA HIDIMA

13. Ta yaya za ka nuna cewa kai “mai tawaliꞌu” ne, kuma ba “mai nuna iko” ba?

13 ꞌYanꞌuwa maza masu halayen kirki suna da amfani sosai a ikilisiya. Mutum “mai tawaliꞌu” yana iya ƙoƙari ya zauna lafiya da mutane, kuma yana taimaka wa mutane su zauna lafiya da juna. Don haka, ka riƙa sauraron mutane, kuma ka yi ƙoƙari ka fahimce su. Hakan zai nuna cewa kai mai tawaliꞌu ne. Alal misali, idan yawancin dattawa suka yarda da wata shawara da ba ta saɓa wa ƙaꞌidodin Littafi Mai Tsarki ba, za ka goyi bayansu ko da kana da wani raꞌayi dabam? “Kada ya zama mai nuna iko,” wato kada ka dinga dagewa cewa sai an bi raꞌayinka. Kuma ka zama mai son jin raꞌayin wasu, domin hakan yana da muhimmanci. (Far. 13:​8, 9; K. Mag. 15:22) “Ba mai gardama ba” ko “mai saurin fushi.” Hakan yana nufin cewa ba za ka riƙa magana cikin fushi ko ka yi gardama da mutane ba. Amma ka riƙa magana da alheri kuma cikin basira. A matsayinka na mai son zaman lafiya, ka riƙa saurin warware matsala da ke tsakaninka da mutane ko da yin haka na da wuya. (Yak. 3:​17, 18) Idan kana yi wa mutane magana da alheri, hakan zai kwantar musu da hankali, ko da su masu tsananta mana ne.—Alƙa. 8:​1-3; K. Mag. 20:3; 25:15; Mat. 5:​23, 24.

14. Me ake nufi da cewa kada mutumin “ya zama sabon tuba,” kuma ya zama “mai tsarki”?

14 Bai kamata ɗanꞌuwa da zai zama dattijo “ya zama sabon tuba” ba. Ko da yake ba sai ka yi shekaru da yawa da yin baftisma kafin a naɗa ka dattijo ba, kana bukatar lokaci don ka zama Kirista da ya manyanta. Kafin ka zama dattijo, sai ka yi koyi da halin Yesu. Hakan yana nufin cewa za ka zama mai sauƙin kai, kuma ba za ka yi fushi idan ya ɗau lokaci kafin aka ba ka ƙarin ayyuka a ikilisiya ba. (Mat. 20:23; Filib. 2:​5-8) Ka nuna cewa kai “mai tsarki” ne ta wurin yin rayuwar da ta dace a gaban Allah, da kuma bin umurnan da yake ba mu ta wurin ƙungiyarsa.—1 Tim. 4:15.

15. Dole ne mutum ya iya yin jawabi mai daɗi sosai kafin ya zama dattijo? Ka bayyana.

15 Littafi Mai Tsarki ya ce dole dattawa su zama masu “iya koyarwa sosai.” Hakan yana nufin cewa dole ne ka iya yin jawabi mai daɗi sosai? Aꞌa. Wasu dattawa ba su iya yin jawabai masu daɗi sosai ba, amma sun iya yin amfani da Littafi Mai Tsarki wajen ƙarfafa ꞌyanꞌuwa, da kuma koyar da mutane a waꞌazi. (Ka ga abin da ke 1 Korintiyawa 12:​28, 29 da Afisawa 4:11.) Ko da yake ba dole ba ne ka iya yin jawabi mai daɗi sosai, kana bukatar ka ci-gaba da inganta yadda kake koyarwa. Ta yaya za ka yi hakan?

16. Ta yaya za ka inganta yadda kake koyarwa? (Ka kuma duba hoton.)

16 “Yana riƙe da tabbatacciyar maganar nan ta Allah daidai kamar yadda aka koyar.” Idan kana so ka riƙa koyarwa da kyau, ka tabbata cewa duk abin da za ka gaya wa ꞌyanꞌuwa ya jitu da abin da Littafi Mai Tsarki ya ce. Me zai taimaka maka? Yin nazarin Littafi Mai Tsarki da littattafanmu. (K. Mag. 15:28; 16:23) Yayin da kake nazari, ka lura da yadda aka bayyana nassosi da batun da suka shafa. Hakan zai sa ka iya yin amfani da su da kyau. Idan kana koyarwa, ka taimaka wa mutane su ƙara ƙaunar Jehobah, kuma ka sa su so bin abin da suka koya. Ƙari ga haka, za ka inganta koyarwarka idan kana neman shawarar dattawa da suka ƙware kuma kana bin ta. (1 Tim. 5:17) Dattawa suna bukatar su iya “ƙarfafa” ꞌyanꞌuwa; amma a wasu lokuta, dole ne su “ƙaryata kuskuren waɗanda suke gāba da koyarwar.” Sai dai su yi hakan da alheri. Idan kana koyarwarka da alheri kuma bisa ga abin da ke Littafi Mai Tsarki, koyarwarka za ta ƙara yin kyau. Kana bin misalin Yesu ke nan, wanda shi ne Babban Malami.—Mat. 11:​28-30; 2 Tim. 2:24.

Wani bawa mai hidima yana tare da wani kwararan dattijo, yana koyan yadda zai yi amfanin da Littafi Mai Tsarki wajen ƙarfafa ꞌyanꞌuwa. Bawa mai hidimar yana gwada yin jawabinsa a gaban madubi (Ka duba sakin layi na 16)


KA CI-GABA DA YIN ƘOƘARI

17. (a) Me zai taimaki bayi masu hidima su ci-gaba da yin ƙoƙari? (b) Me ya kamata dattawa su tuna saꞌad da suke duba ko ɗanꞌuwa ya cancanci zama dattijo? (Ka duba akwatin nan “ Saꞌad da Dattawa Suke Duba Ko Ɗanꞌuwa Ya Cancanci Zama Dattijo.”)

17 Idan wasu bayi masu hidima suka ga abin da ake bukata daga wurin mutum kafin ya zama dattijo, wataƙila su ga kamar ba za su iya ba. Amma ka tuna cewa Jehobah ba ya bukatar ka nuna duka halayen nan babu kuskure, haka ma ƙungiyarsa. (1 Bit. 2:21) Kuma ruhun Jehobah ne zai taimake ka ka koyi halayen. (Filib. 2:13) Shin, ka lura da wani fanni da za ka so ka ƙara ƙoƙari? Ka roƙi Jehobah ya taimake ka. Ka yi bincike a kan batun, kuma ka gaya wa wani dattijo ya ba ka shawara don ka sami ci-gaba.

18. Me ake ƙarfafa dukan bayi masu hidima su yi?

18 Bari dukan ꞌyanꞌuwa maza, har da dattawa, su ci-gaba da ƙoƙarin nuna halayen da aka tattauna a talifin nan. (Filib. 3:16) Idan kai bawa mai hidima ne, ka yi ƙoƙari don ka zama dattijo! Ka roƙi Jehobah ya koya maka yadda za ka yi masa hidima kuma ka taimaki ꞌyanꞌuwa a ikilisiya. (Isha. 64:8) Jehobah zai albarkace ka don duk ƙoƙarin da kake yi ka zama dattijo.

WAƘA TA 101 Mu Riƙa Hidima da Haɗin Kai