Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Abin da Zai Taimaka Mana Mu Yi Nazari Kowane Mako

Abin da Zai Taimaka Mana Mu Yi Nazari Kowane Mako

YANA yi maka wuya ka yi nazarin Littafi Mai Tsarki kowane mako, ko ka ji daɗin yin sa? Yana faruwa da dukanmu a wasu lokuta. Amma ka yi laꞌakari da wasu abubuwan da muke yi kowane lokaci, kamar wanka da sauransu. Ba kowane lokaci ne yake da sauƙi mutum ya yi wanka ba, amma idan mutum ya yi, yana jin daɗi! Haka ma yake da nazarin Littafi Mai Tsarki. Idan muka yi ƙoƙari muka yi nazari, za mu ji daɗi sosai. (Afis. 5:26) Ga wasu shawarwari da za su iya taimakawa:

  • Ka zaɓi lokaci. Yin nazarin Littafi Mai Tsarki yana cikin abubuwa da suka “fi muhimmanci” da bai kamata mu yi watsi da su ba. (Filib. 1:​10, NWT) Idan ba ka so ka riƙa mantawa da lokacin nazarinka, ka rubuta lokacin da ranar da ka zaɓa, kuma ka saka shi a inda za ka riƙa gani da wuri. Za ka iya sa alam a wayarka don ta tunasar da kai kafin lokacin nazarin.

  • Ka yi bisa ga yanayinka. Yaya kake so ka yi nazarin? Alal misali, za ka iya yin nazarin har na awa ɗaya? Ko za ka fi so ka riƙa yinsa kaɗan-kaɗan? Kai ne ka fi sanin wanda zai fi maka. Don haka, ka zaɓi abin da zai dace da yanayinka. Idan lokacin nazarinka ya yi kuma ka ji kamar ba ka so, ka yi ƙoƙari ka yi shi ko na minti goma kawai. Yin nazari na minti goma, ya fi babu. Ƙila bayan minti goman ma, za ka ji daɗinsa har ka ci-gaba.—Filib. 2:13.

  • Ka zaɓi batutuwan da za ka yi nazarinsu. Idan a lokacin da za ka yi nazari ne ka soma neman batutuwan da za ka yi nazarinsu, hakan ba zai sa ka yi “amfani da lokacinka” da kyau ba. (Afis. 5:16) Ka yi ƙoƙari ka rubuta jerin batutuwa da za ka so ka yi nazarinsu. Kuma idan ka sami wani batu da za ka so ka nemi ƙarin haske a kai, sai ka rubuta shi a cikin jerin batutuwan da kake da su. Bayan ka gama nazari ma, ƙila ka ga wasu batutuwa da za ka so ka yi nazari a kai. Su ma ka rubuta su.

  • Za ka iya yin canje-canje. Ka tsara yadda za ka iya yin canje-canje idan da bukata. Hakan zai sa ka iya canja tsawon lokacin da kake yin nazari, ko batutuwan da kake nazari a kai, ko kuma ranar da kake yi nazarin. Abin da ya fi muhimmanci shi ne ka riƙa yin nazarin kowane mako.

Idan muna nazari kowane mako, za mu amfana. Za mu kusaci Jehobah sosai, za mu kasance da hikima, kuma nazarin zai ƙarfafa mu.—Yosh. 1:8.