Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TARIHI

Jehobah Ya Ba Mu Karfin Jimrewa a Lokacin Yaki da Lokacin da Ba A Yaki

Jehobah Ya Ba Mu Karfin Jimrewa a Lokacin Yaki da Lokacin da Ba A Yaki

Paul ya ce: A watan Nuwamba 1985, mun yi farin ciki sosai da aka ce mu je yin waꞌazi a ƙasar Laberiya da ke Afirka ta Yamma. Wannan shi ne karo na farko da za mu je yin waꞌazi a ƙasar waje. Da jirginmu ya ɗan sauka a ƙasar Senegal, sai Anne ta ce, “Nan da awa ɗaya za mu kai Laberiya!” Sai kawai muka ji sanarwa cewa: “Masu zuwa Laberiya su sauka a nan. Ba za mu iya zuwa Laberiya ba domin ana ƙoƙarin yin juyin mulki a ƙasar.” Saboda haka, mun yi kwanaki goma muna zama da masu waꞌazi a ƙasar waje da suke Senegal. Mun ji cewa a Laberiya ana kashe-kashe sosai, kuma gwamnati ta saka dokar hana fita. Ana harbe duk wanda ya taka dokar.

Anne ta ce: Mu ba masu ƙarfin zuciya ba ne. Tun ina ƙarama ake ce da ni Anne Matsoraciya. Ko tsallake titi ma yana ba ni tsoro! Duk da haka, mun ce sai mun je Laberiya, tun da wurin aka aike mu.

Paul ya ce: Kilomita takwas (wato mil 5) ne kawai, ke tsakanin inda aka haife ni da inda aka haifi matata Anne, a kudancin Ingila. Iyayena da mahaifiyar Anne sun yi ta ƙarfafa mu cewa mu yi hidimar majagaba. Don haka, da muka gama makarantar sakandare, sai mu biyu muka zama majagaba. Kuma da suka ji cewa muna so mu yi amfani da rayuwarmu a hidima ta cikakken lokaci, sun ji daɗi sosai. Da na kai shekara 19, sai aka kira ni in soma hidima a Bethel. Saꞌan nan a lokacin da na auri Anne a shekara ta 1982, sai aka ce ita ma ta zo Bethel.

Bikin sauke karatu daga Makarantar Gilead, 8 ga Satumba, 1985

Anne ta ce: Muna son yin hidima a Bethel, amma mun fi so a tura mu yin hidima a ƙasar da ake bukatar masu shela. Kuma da muke Bethel, mun yi aiki da ꞌyanꞌuwa da suka taɓa yin waꞌazi a ƙasar waje. Labaransu sun ƙara mana shaꞌawar yin wannan hidimar. Kowace rana, kafin mu kwanta da dare, idan muna adduꞌa, mukan gaya wa Jehobah cewa za mu so a tura mu yin waꞌazi a ƙasar waje. Mun yi shekaru uku muna haka. Shi ya sa mun yi murna sosai saꞌad da aka gayyace zuwa makarar Gilead a shekara ta 1985! Muna cikin ꞌyan aji na 79. Da muka sauke karatu, sai aka tura mu Laberiya, da ke Afirka ta Yamma.

ƘAUNAR DA ꞌYANꞌUWA SUKA NUNA YA BA MU ƘARFIN JIMREWA

Paul ya ce: Da aka fara barin mutane su shiga Laberiya, sai muka kama hanya. Jirginmu ne na farko. Lokacin mutane suna kan jin tsoro, kuma an hana fita da yamma. Ko da salansar mota ce ta yi ƙara kamar harbin bindiga, sai mutane su yi ihu kuma su kama gudu. Mukan karanta wasu ayoyi a littafin Zabura da dare kowace rana, don su kwantar mana da hankali. Duk da haka, mun so hidimarmu a Laberiya sosai. Lokacin Anne tana zuwa yin waꞌazi kowace rana. Ni kuma ina hidima a Bethel da ke Laberiya. Ina aiki da wani ɗanꞌuwa mai suna John Charuk. a Na koyi abubuwa da yawa daga wurinsa, domin ya daɗe a wurin. Ya san ꞌyanꞌuwan da kuma halin da suke ciki sosai.

Anne ta ce: Abin da ya sa muka so Laberiya sosai shi ne, irin ƙaunar da ꞌyanꞌuwa a wurin suka nuna mana. Ƙari ga haka, suna ƙaunar Jehobah ba kaɗan ba. Mun so su sosai, kuma sun zama kamar ꞌyan iyalinmu. Sun ba mu shawarwari masu kyau kuma sun ƙarfafa mu. Mutanen wurin suna son waꞌazinmu ba kaɗan ba. Har ma idan ka gama yi wa mutum waꞌazi za ka tafi, sai ransa ya ɓace don yana so ku ci-gaba da tattaunawa! A kan titi za ka ji mutane suna muhawwara game da koyarwar Littafi Mai Tsarki. Don haka, ba ya mana wuya mu soma tattaunawa da su. Ɗalibanmu sun yi yawa har ba ma samun isasshen lokacin yin nazari da dukansu. A gaskiya mun ji daɗin wannan wurin!

TSORO YA KAMA MU, AMMA JEHOBAH YA ƘARFAFA MU

Lokacin da muke kula da masu gudun hijira a Bethel da ke Laberiya, a 1990

Paul ya ce: Mun yi shekaru huɗu a Laberiya babu tashin hankali. Amma sai aka soma yaƙi a 1989 kuma kome ya canja. A ranar 2 ga Yuli, 1990, masu ƙoƙarin yin juyin mulki sun mallaki yankin da Ofishinmu yake. Mun yi watanni uku ba ma iya kiran kowa a ƙasar waje, har da ꞌyan iyalinmu da ꞌyanꞌuwa da ke hedkwatarmu. Mugunta da fyaɗe sun zama ruwan dare game gari, ga ƙarancin abinci. An yi shekaru 14 ana cikin wannan halin, kuma ya shafi ƙasar gabaki-ɗaya.

Anne ta ce: Wasu kabilu sun yi ta faɗa da juna, suna kashe juna. Sojoji sun cika koꞌina a titi ɗauke da makamai, kuma sun saka tufafi masu ban tsoro, suna bin gida-gida suna kwasan duk abin da suka ga dama. A gun wasunsu, kashe mutum kamar yanka kaza ne. Sukan tare hanya kuma su kakkashe masu wucewa, saꞌan nan su tara gawakin a kan hanya. Hakan ya faru kusa da ofishinmu. Sun kashe wasu ꞌyanꞌuwa, har da masu waꞌazi a ƙasashen waje guda biyu.

A baƙin ransu, yanꞌuwanmu sun ɓoye ꞌyanꞌuwa daga kabilar da ake nema a kashe. Masu waꞌazi a ƙasar waje da mu da muke Bethel ma, mun yi hakan. Alal misali, da yake a gidan sama muke kwana, wasu ꞌyanꞌuwa da suka gudu suka shigo Bethel sun yi ta kwana a ɗakunan da ke ƙasa, wasu kuma sun kwana a ɗakunanmu. Mutum bakwai ne suka zauna da mu a ɗakinmu.

Paul ya ce: Kowace rana, mayaƙan sukan zo Bethel su ga ko mun ɓoye wani. Idan suka zo, sai ꞌyanꞌuwa maza biyu su je su same su a ƙofar shiga Bethel, biyu kuma su yi ta kallon su ta wundo. Idan waɗanda suka je suka same su suka ga cewa ba matsala, sai su naɗe hannayensu a gaba. Amma idan suka ga cewa akwai matsala, sai su naɗe hannayensu a bayansu. Da zarar ꞌyanꞌuwan da suke kallo ta wundo suka ga haka, sai su yi sauri su ɓoye sauran ꞌyanꞌuwan.

Anne ta ce: Wata rana, da mayaƙan suka zo, sai suka shiga Bethel da-ƙarfi-da-yaji. Sai ni da wata ꞌyarꞌuwa muka gudu muka shiga ban-ɗaki muka kulle kofa. A ban-ɗakin, muna da wani kabat da ke da wurin da mutum zai iya ɓoyewa a ƙasarsa. A nan ne ꞌyarꞌuwar ta ɓoye. Da mayaƙan suka haura suka zo inda muke, sai suka buga kofa da ƙarfi. Da suka shigo ɗakinmu, maigidana bai so su shiga inda muke ba. Don haka, ya gaya musu cewa su yi haƙuri matarsa tana a ban-ɗaki. Da na rufe wurin da ꞌyarꞌuwar ta ɓoye, abin ya ɗan yi ƙara. Ban da haka, na ɗan ɓata lokaci domin dole in mayar da abubuwan da suke cikin kabat ɗin. Na san cewa mayaƙan za su soma tunanin mene ne nake yi a wannan wurin. Don haka, na ji tsoro sosai, har na fara rawar jiki. Amma kuma dole in natsu kafin in buɗe kofar, don haka na yi adduꞌa a zuciyata. Na roƙi Jehobah ya taimake ni. Sai na sami natsuwa, na buɗe kofar, kuma na gaishe su. Sai ɗaya daga cikinsu ya ture ni gefe guda, ya shiga ban-ɗakin, ya buɗe kabat ɗin ya dudduba. Ya yi mamaki da bai ga mutum a ciki ba. Sai shi da abokansa suka bi sauran ɗakunan ꞌyanꞌuwa suka dudduba koꞌina, har da cikin silin. Amma, ba su ga kome ba.

GASKIYA TA CI-GABA DA HASKAKAWA

Paul ya ce: Sau da yawa ba ma cin abinci da safe domin babu abincin. Amma ibadar safiya da ake yi a Bethel ta ƙarfafa mu. Ba shakka, karanta Littafi Mai Tsarki da nazarinsa zai sa mu sami ƙarfin jimre matsalolinmu kowace rana.

Mun san cewa idan abincinmu da ruwan sha sun kare kwata-kwata kuma mun fita neman abubuwan nan, ba za mu iya kāre ꞌyanꞌuwa da suka ɓoye a wurinmu ba. Mai yiwuwa a kashe su. Amma godiya ga Jehobah, ba su ƙare ba. A yawancin lokaci, Jehobah ya yi mana tanadin abin da muke bukata, a daidai lokacin da muke bukatarsa, kuma a hanya mai ban mamaki. Gaskiya Jehobah ya kula da mu, kuma ya taimaka mana mu sami kwanciyar hankali.

Abubuwa sun yi ta ƙara muni a ƙasar, amma koyarwar Littafi Mai Tsarki ta ƙarfafa dukanmu. ꞌYanꞌuwanmu sun yi ta guje-guje don su ceci rayukansu, amma sun ci-gaba da riƙe amincinsu, kuma ba su ruɗe ba. Wasu sun ce wahalar da suke sha “yana shirya su don ƙunci mai girma ne.” Dattawa da ꞌyanꞌuwa matasa sun yi iya ƙoƙarinsu wajen taimaka wa sauran ꞌyanꞌuwa. A duk inda ꞌyanꞌuwa suka gudu suka je, sukan kasance tare. Sukan soma waꞌazi a wurin, kuma suna amfani da kome da suka samu a daji don su shirya wurin da za su yi taro kuma su yi taron. A wannan lokaci mai wuya, zuwa taro da yin waꞌazi ya ƙarfafa ꞌyanꞌuwa sosai, kuma ya ba su bege. A lokacin da muke raba wa ꞌyanꞌuwa kayan agaji, da yawa daga cikinsu sun ce mu taimaka musu da jakunkunan yin waꞌazi, ba su ma ce a kawo musu rigunan sakawa ba. Hakan ya ƙarfafa mu sosai. Mutane da yawa sun so waꞌazin da muke yi. Sun ga cewa muna ƙaunar juna sosai kuma muna farin ciki a wannan lokacin balaꞌi. Abin ya ba su mamaki. Yanꞌuwanmu sun fita dabam, kamar haske a cikin duhu. (Mat. 5:​14-16) Yadda ꞌyanꞌuwa suka sa ƙwazo wajen yin ayyukan ibada ya sa wasu mayaƙan ma sun juya sun zama Shaidun Jehobah.

BARIN ꞌYANꞌUWANMU BAI YI MANA SAUƘI BA

Paul ya ce: Akwai lokutan da ya zama mana dole mu bar ƙasar. Mun bar ƙasar na ɗan lokaci sau uku. Akwai kuma wasu lokuta biyu da muka bar ƙasar na tsawon shekara guda. Abin bai yi mana sauƙi ba. Wata ꞌyarꞌuwa mai waꞌazi a ƙasar waje ta ce: “A Makarantar Gilead, an koya mana cewa duk inda aka tura mu, mu ƙaunaci ꞌyanꞌuwan da muka samu da dukan zuciyarmu. Kuma abin da muka yi ke nan. Don haka, lokacin da za mu rabu da ꞌyanꞌuwanmu da ke Laberiya, abin ya yi mana zafi sosai!” Amma mun ji daɗi da muka ga cewa ko mun bar ƙasar, za mu iya taimaka wa ꞌyanꞌuwanmu da suke Laberiya.

Mun yi farin ciki da muka sami damar komawa Laberiya, a 1997

Anne ta ce: A watan Mayu 1996, mun yi shirin barin ƙasar. Sai mu huɗu muka shiga motar Bethel. Kuma mun kwashi takardu da suke ɗauke da bayanai masu muhimmanci game da aikinmu a ƙasar. Niyyarmu ita ce mu tuka motar zuwa wani gefen garin, inda rikicin yake da sauƙi. Wurin yana da nisan kilomita 16 (mil 10). Muna fitowa ke nan sai aka kawo hari a yankin. Mayaƙan sun zo da ransu a ɓace, sun yi ta harbin bindiga, sun fitar da mu uku daga motar. Sai suka ɗauki motar suka ƙara gaba, da Paul a ciki. Mun tsaya cik a wurin, mun rasa na yi. Ana nan sai ga Paul yana zuwa da kafa, kuma da jini a goshinsa. Mun ce ko an harbe shi ne a kai, amma da muka sake tunani sai muka ce, ai da harbi aka yi masa a kai, da ba zai iya yin tafiya ba! Ashe ɗaya daga cikin mayaƙan ne ya buge shi a kai, lokacin da ya yake ƙoƙarin ture shi ya fita daga motar. Allah ya sa bai ji masa ciwo sosai ba.

A kusa da mu, akwai wata babbar motar sojoji cike da mutane, motar tana shirin tashiwa. Da yake babu wurin shiga, sai muka hau gefen motar kawai, kuma kowa ya riƙe inda ya iya riƙewa. Da direban ya tashi gudu, sauran kaɗan mu faɗi. Mun roƙe shi ya tsaya, amma ya ƙi ji, domin shi ma tsoro ya shiga jikinsa. Mun riƙe motar da iya ƙarfinmu don kar mu faɗi. Da muka kai inda za mu, mun sauka a gajiye, kuma jikinmu sai rawa yake yi.

Paul ya ce: Sai muka kalli juna, muna mamakin yadda Jehobah ya taimaka mana muka tsira. Rigunanmu duk sun yi datti kuma sun yayyage. A wurin muka kwana, a wani fili inda aka faka wani jirgin sama mai saukar ungulu, wato helicopter. An yi wa jirgin kaca-kaca da harsasai, kamar ba zai iya tashiwa ba. Washe-gari, jirgin ne ya kai mu ƙasar Saliyo. Da muka kai, mun gode ma Jehobah da ya kiyaye mu. Amma mun yi ta damuwa a kan ꞌyanꞌuwanmu da suke Laberiya.

MUN JIMRE WASU MATSALOLI KUMA DA TAIMAKON JEHOBAH

Anne ta ce: Mun isa Bethel da ke birnin Freetown, a ƙasar Saliyo lafiya, kuma ꞌyanꞌuwa a wurin sun kula da mu. Amma sai munanan abubuwa da na gani a Laberiya suka yi ta dawowa zuciyata. Kullum ina ji kamar wani mugun abu zai faru da mu. Na bi na kasa yin tunani da kyau. Nakan farka da dare ina rawan jiki. Yin numfashi ma kamar zai gagare ni. Maigidana yakan riƙe ni, sai mu yi adduꞌa. Bayan haka, sai mu yi ta yin waƙoƙinmu har sai jikina ya daina rawa. Abin ya dame ni sosai har na ɗauka hauka ne yake damu na. Kuma na zata ba zan iya ci-gaba da aikin yin waꞌazi a ƙasar waje ba.

Ba zan taɓa manta da wani abin da ya faru a lokacin ba. Ƙungiyarmu ta wallafa wasu mujallu biyu da suka taimaka mini sosai. Ɗaya ita ce Awake! na 8 ga Yuni, 1996. Tana ɗauke da wani talifi mai jigo, Coping With Panic Attacks,” wato, “Abin da Zai Taimake Ka Idan Tsoro Ya Shiga Jikinka.” Talifin ya sa na fahimci abin da ya sa ni cikin wannan yanayin. Ta biyun kuma ita ce Hasumiyar Tsaro ta 15 ga Mayu, 1996, wadda ke da talifi mai jigo, Where Do They Get Their Strength? wato, “A Ina Ne Suke Samun Ƙarfi?” A talifin, akwai hoton wani malam-buɗe-littafi da yake da rauni a fikafikansa. An bayyana cewa malam-buɗe-littafi zai iya ci-gaba da tashi sama ko da yana da rauni a fikafikansa. Mu ma haka muke, ko da muna ji ba mu da ƙarfi don abubuwan da suka faru da mu a rayuwa, Jehobah zai iya taimaka mana mu ci-gaba da yin hidimarmu. Ta wurin talifofin nan, Jehobah ya ƙarfafa ni a daidai lokacin da nake bukatar hakan. (Mat. 24:45) Na nemi talifofi kamar waɗannan, kuma na adana su. Talifofin sun taimaka min sosai, kuma a-kwana-a-tashi, na ji sauƙi.

DA TAIMAKON JEHOBAH, MUN YI WANI BABBAN CANJI

Paul ya ce: A duk lokacin da aka ce mu je ƙasar Laberiya, mukan ji daɗi ba kaɗan ba. A shekara ta 2004 ne muka cika shekaru 20 muna taimaka wa ꞌyanꞌuwanmu da ke Laberiya. A lokacin an daina yaƙin, muna a ƙasar Laberiya, kuma ana shirin yin wasu gine-gine a Bethel da ke wurin. Sai kawai aka ce mu je yin hidima a Ghana.

Ba mu ji daɗi ba ko kaɗan, don mun saba da ꞌyanꞌuwanmu da suke Laberiya, kuma muna ƙaunar su sosai. Amma da muka tuna yadda Jehobah ya yi mana albarka saꞌad da muka bar ꞌyan iyalinmu muka je Makarantar Gilead, sai muka dogara gare shi, kuma muka amince. Ƙasar Ghana inda za mu je, tana kusa da Laberiya.

Anne ta ce: Mun yi kuka da za mu bar Laberiya. Wani ɗanꞌuwa mai suna Frank da ya manyanta sosai, ya gaya mana cewa: “Dole ku cire mu daga zuciyarku!” Mun yi mamaki da ya gaya mana haka, amma sai ya bayyana cewa: “Mun san ba za ku taɓa manta da mu ba, amma kuna bukatar ku ƙaunaci ꞌyanꞌuwan da ke Ghana ma da dukan zuciyarku. Jehobah ne ya ce ku je wurin. Don haka, ku kula da ꞌyanꞌuwa da suke wurin sosai.” Maganarsa ta taimaka mana mu yi shirin yin rayuwa a wannan sabon wuri, inda ba a san mu sosai ba.

Paul ya ce: Amma ba da jimawa ba, mun shaƙu da ꞌyanꞌuwanmu da ke Ghana. Akwai Shaidun Jehobah da yawa a ƙasar! ꞌYanꞌuwan suna ƙaunar Jehobah sosai, kuma suna da bangaskiya. Bayan da muka yi shekaru 13 muna hidima a Ghana, sai aka sake cewa mu ƙaura. An ce mu je yin hidima a rashen ofishinmu na Gabashin Afirka, da ke ƙasar Kenya. Da muka bar Ghana, mun yi kewar abokanmu da suke wurin. Amma ba da jimawa ba, sai muka ƙulla zumunci da ꞌyanꞌuwan da ke Kenya. A Kenya ma, ana bukatar masu waꞌazi sosai.

Mu da abokanmu a yankin rashen ofishinmu na Gabashin Afirka, a 2023

ABIN DA MUKA KOYA

Anne ta ce: Na ga abubuwan ban tsoro a rayuwata. Yin rayuwa a inda ake tashin hankali sosai zai iya sa mu yi rashin lafiya, kuma tsoro ya shiga jikinmu. Wani lokaci, Jehobah ba ya hana irin abubuwan nan faruwa da mu. Ko a yanzu ma, idan na ji harbin bindiga sai in ji cikina ya yi ruwa. Amma na koyi cewa yana da muhimmanci mu amince da hanyoyi dabam-dabam da Jehobah yake ƙarfafa mu. Yakan yi hakan ta wurin ꞌyanꞌuwanmu maza da mata. Na kuma ga cewa idan muka ci-gaba da yin nazari, da adduꞌa, da zuwa taro, da kuma yin waꞌazi, Jehobah zai ba mu ƙarfin ci-gaba da yin hidimarmu.

Paul ya ce: Wasu sukan tambaye mu cewa, “Kuna son wannan wurin da kuke hidima?” Gaskiyar ita ce, ko da ka je ƙasa mai kyau sosai, abubuwa za su iya lalacewa farat ɗaya. Don haka, ꞌyanꞌuwan da suke ƙasar da muke hidima ne suke a ranmu, ba ƙasar karan-kanta ba. Duk da cewa mun fito daga wurare dabam-dabam, tunaninmu ɗaya ne, dukanmu muna ƙaunar Jehobah. Mu ne aka aika mu je mu ƙarfafa ꞌyanꞌuwa, amma a gaskiya, su ma sun ƙarfafa mu.

A duk lokacin da muka je sabon wuri, muna ganin yadda dukanmu muke kamar ꞌyan iyali ɗaya. Wannan abin ban mamaki ne! Kuma Jehobah ne ya sa hakan ya yiwu. Muddin muna cikin ikilisiya, muna da ꞌyanꞌuwa da suke ƙaunarmu. Kuma tabbas, idan muka ci-gaba da dogara ga Jehobah, zai ba mu ƙarfin jimre duk wani abin da zai faru da mu.—Filib. 4:13.

a Ka ga tarihin Ɗanꞌuwa John Charuk a Hasumiyar Tsaro ta 15 ga Maris, 1973. Jigon labarinsa shi ne, I Am Grateful to God and Christ,” wato, “Ina Godiya ga Allah da Kuma Kristi.”