Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

SHAWARA A KAN YIN NAZARI

Ka Nemi Wuri Mai Kyau don Yin Nazari

Ka Nemi Wuri Mai Kyau don Yin Nazari

Za ka so ka amfana sosai saꞌad da kake yin nazari? Ga wasu shawarwarin da za su iya taimakawa:

  • Ka zaɓi wurin da ya dace. Ka yi ƙoƙari ka nemi wuri da yake da tsabta da kuma haske. Ka zauna a kujera da teburi a gabanka, ko kuma ka nemi wuri mai kyau ka zauna a waje.

  • Ka nemi wurin da za ka zauna kai kaɗai. Yesu ya yi adduꞌa “da sassafe,” kuma a “inda ba kowa.” (Mar. 1:35) Idan zai yi wuya ka sami wurin da za ka zauna kai kaɗai, ka gaya wa ꞌyan iyalinku ko waɗanda kuke zama tare cewa kana so ka yi nazari kuma su yi ƙoƙari kar su dame ka.

  • Kada ka bar wani abu ya raba hankalinka. Idan kana nazari da wayarka, ka saita ta yadda kira ko saƙonni ba za su dame ka ba. Idan kuma ka tuna da wani abin da kake so ka yi, ka rubuta shi don ka iya yinsa daga baya. Idan ka gagara mai da hankali ga nazarinka, ka tashi ka ɗan zagaya ko ka mimmiƙe.