Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 45

WAƘA TA 138 Tsofaffi Masu Aminci Suna da Daraja

Shawara ta Karshe da Maza Masu Aminci Suka Bayar

Shawara ta Karshe da Maza Masu Aminci Suka Bayar

“Ba a wurin tsofaffi ake samun hikima ba? Ba a cikin tsawon kwanaki ne ake samun fahimta ba?”AYU. 12:12.

ABIN DA ZA MU KOYA

Za mu ga cewa idan muka yi biyayya ga Jehobah, zai yi mana albarka kuma zai ba mu rai na har abada.

1. Me ya sa ya kamata mu saurari tsofaffi?

 DUKANMU muna bukatar wanda zai taimaka mana mu yi zaɓi mai kyau a rayuwa. Kuma za mu iya samun wannan taimako daga wurin dattawa da ꞌyanꞌuwan da suka manyanta. Idan ꞌyanꞌuwan nan sun girme mu sosai kuma sun ba mu shawara, kada mu yi saurin ɗauka cewa shawararsu tsohon yayi ne. Jehobah yana so mu saurari tsofaffi. Me ya sa? Sun fi mu shekaru sosai kuma sun ga abubuwa da yawa, don haka ba wuya su fi mu hikima da fahimi.—Ayu. 12:12.

2. Me za mu tattauna a talifin nan?

2 A zamanin dā, Jehobah ya yi amfani da tsofaffi masu aminci wajen ƙarfafa bayinsa da kuma ba su shawara. Alal misali, ya yi amfani da Musa, da Dauda, da kuma manzo Yohanna. Lokacin da mazan nan suka yi rayuwa ba ɗaya ba ne, kuma yanayinsu ya bambanta. Amma da suka kusan mutuwa, sun shawarci waɗanda suke tasowa a bayansu. Kowannensu ya nanata cewa yana da muhimmanci mu yi wa Allah biyayya. Kuma Jehobah ya sa an rubuta kalmomin hikima da suka furta don mu koyi darasi. Za mu amfana sosai idan muka bincika shawarar da suka bayar, ko da mu matasa ne ko tsofaffi. (Rom. 15:4; 2 Tim. 3:16) A talifin nan, za mu tattauna shawara ta ƙarshe da Musa, da Dauda, da Yohanna suka bayar, da kuma darussan da suka koya mana.

“ZAI SA KU YI TSAWON RAI”

3. Waɗanne ayyukan ibada ne Musa ya yi?

3 Musa mai ibada ne sosai. Ya yi aikin annabi, da alƙali, da mai ba mayaƙa umurni, da kuma marubuci. Ya koyi darussa da yawa daga abubuwan da suka faru da shi a rayuwa. Shi ne ya ja-goranci Israꞌilawa saꞌad da suka fita daga ƙasar Masar, kuma a idanunsa Jehobah ya yi abubuwan ban mamaki da yawa. Ƙari ga haka, shi ne Jehobah ya sa ya rubuta littattafai biyar na farko a Littafi Mai Tsarki, da Zabura ta 90. Kuma mai yiwuwa shi na ya rubuta Zabura ta 91 da littafin Ayuba.

4. Su wane ne Musa ya ƙarfafa, kuma me ya sa?

4 Kafin ya mutu, Musa ya kira dukan Israꞌilawa don ya tuna musu abubuwan da Jehobah ya yi musu. A lokacin, shekarunsa 120 ne. Wasu daga cikin Israꞌilawan tun suna matasa sun ga abubuwa masu ban mamaki da Jehobah ya yi, da kuma hukuncin da ya yi wa Masarawa. (Fit. 7:​3, 4) Sun ga lokacin da Jehobah ya raba ruwan Jar Teku, kuma suka haye da kafa. Sun kuma ga yadda Jehobah ya halaka Firꞌauna da sojojinsa. (Fit. 14:​29-31) Sun ga yadda Jehobah ya kiyaye su kuma ya kula da su a daji. (M. Sha. 8:​3, 4) Da suke shirin shiga Ƙasar Alkawari, Musa ya ga zai yi kyau ya ƙarfafa su kuma ya ba su shawara kafin ya mutu. a

5. Wane tabbaci ne Musa ya ba wa Israꞌilawa a Maimaitawar Shariꞌa 30:​19, 20?

5 Mene ne Musa ya ce? (Karanta Maimaitawar Shariꞌa 30:​19, 20.) Ya tuna ma Israꞌilawan irin rayuwar da Allah ya ce zai ba su. Ya kuma tabbatar musu da cewa idan suka yi biyayya ga Jehobah, za su yi tsawon rai a ƙasar da ya yi musu alkawari. Ƙasar tana da kyau sosai kuma ana samun amfanin gona sosai! Musa ya ce musu: “Ƙasa ce mai manyan birane masu kyau waɗanda ba ku ne kuka gina ba. Tana da gidaje cike da abubuwa masu kyau waɗanda ba ku ne kuka cika su ba, da rijiyoyin da ba ku ne kuka haƙa ba, da gonakin inabi da na itatuwan zaitun waɗanda ba ku ne kuka shuka ba.”—M. Sha. 6:​10, 11.

6. Me ya sa Jehobah ya bar wasu ƙasashe su ci Israꞌilawa da yaƙi?

6 Musa ya kuma yi wa Israꞌilawa gargaɗi. Ya ce idan suna so su ci-gaba da zama a wannan ƙasa mai albarka, dole su yi wa Jehobah biyayya. Musa ya ce musu su “zaɓi rai,” kuma ya gaya musu yadda za su yi haka. Ya ce su yi wa Allah biyayya, kuma su “manne masa.” Amma, Israꞌilawan sun yi wa Jehobah taurin kai. Hakan ya sa Allah ya bar Assuriyawa da Babiloniyawa sun ci su da yaƙi kuma sun kai su zaman bauta.—2 Sar. 17:​6-8, 13, 14; 2 Tar. 36:​15-17, 20.

7. Mene ne abin da Musa ya faɗa ya koya mana? (Ka kuma duba hoton.)

7 Wannan ya koya mana cewa yin biyayya ne zai sa mu rayu har abada. A lokacin da Musa ya yi wa Israꞌilawa wannan gargaɗin, suna dab da shiga Ƙasar Alkawari. Mu ma muna dab da shigan sabuwar duniyar da Allah ya yi mana alkawarin ta, inda koꞌina zai zama aljanna. (Isha. 35:1; Luk. 23:43) Za a cire Shaiɗan da aljanunsa. (R. Yar. 20:​2, 3) Ba za a sake yin wani addini da zai koya wa mutane abin da ba daidai ba. (R. Yar. 17:16) Gwamnatocin ꞌyan Adam da suke wulaƙanta talakawansu za su zama labari. (R. Yar. 19:​19, 20) Jehobah ba zai bar wani ya kawo tashin hankali a cikin aljanna ba. (Zab. 37:​10, 11) Mutane a koꞌina za su bi dokokin Allah, kuma hakan zai sa a sami haɗin kai da zaman lafiya. Mutane za su yarda da juna kuma su ƙaunaci juna. (Isha. 11:9) Kuma idan muka yi wa Jehobah biyayya, za mu ci-gaba da rayuwa a aljanna har abada. Muna marmarin ganin wannan lokacin!—Zab. 37:29; Yoh. 3:16.

Idan muka yi wa Jehobah biyayya, za mu ci-gaba da rayuwa a aljanna har abada! (Ka duba sakin layi na 7)


8. Ta yaya alkawarin yin rayuwa har abada ya taimaka ma wani mai waꞌazi a ƙasar waje? (Yahuda 20, 21)

8 Idan muka ci-gaba da yin tunani a kan alkawarin aljanna da Allah ya yi mana, hakan zai taimaka mana mu yi masa biyayya ko da wace matsala ce muke ciki. (Karanta Yahuda 20, 21.) Za mu kuma sami karfin shawo kan kasawarmu. Alal misali, wani ɗanꞌuwa da ya daɗe sosai yana waꞌazi a ƙasar waje a Afirka, ya ce ya yi fama da jarabar yin wani abin da bai dace ba. Amma ya ƙara da cewa: “Na tuna cewa idan ban yi wa Jehobah biyayya ba, ba zan sami rai na har abada ba. Wannan tunanin ya sa na ci-gaba da yin iya ƙoƙarina kar in yi zunubin, kuma na ƙara roƙon Jehobah ya taimake ni. Da taimakonsa, na shawo kan wannan kasawar.”

ZA KA YI NASARA

9. Waɗanne matsaloli ne Dauda ya yi fama da su?

9 Dauda sarki ne mai aminci. Shi mawaƙi ne, da marubuci, da mayaƙi, da kuma annabi. Ya yi fama da matsaloli da yawa. Ya yi shekaru da dama yana gudun hijira, domin Sarki Saul ya so ya kashe shi. Bayan da Dauda ya zama sarki, ya sake guduwa don ɗansa Absalom ya so ya kashe shi ya kwace mulkin. Duk da famar da Dauda ya yi da kuma kurakuransa, ya ci-gaba da bauta wa Jehobah da aminci har ƙarshen rayuwarsa. Jehobah ya ce: “Dawuda ɗan Yesse, mutum ne mai zuciya irin tawa.” Hakika, zai dace mu bi shawarar da Dauda ya bayar!—A. M. 13:22; 1 Sar. 15:5.

10. Me ya sa Dauda ya shawarci ɗansa Sulemanu?

10 A lokacin da Jehobah ya zaɓi Sulemanu ya gina masa haikali inda za a bauta masa, Dauda ya ba shi shawara. (1 Tar. 22:5) Me ya sa? Domin wannan ba ƙaramin aiki ba ne, kuma yin mulki ba zai yi wa Sulemanu sauƙi ba. Don haka yana bukatar taimakon Jehobah. Wace shawara ce Dauda ya ba shi?

11. Bisa ga 1 Sarakuna 2:​2, 3, mene ne Dauda ya tabbatar wa Sulemanu, kuma me ya faru saꞌad da Sulemanu ya bi abin da Dauda ya gaya masa? (Ka kuma duba hoton.)

11 Mene ne Dauda ya ce? (Karanta 1 Sarakuna 2:​2, 3.) Dauda ya gaya wa ɗansa cewa, idan ya yi wa Jehobah biyayya zai yalwata cikin dukan abin da zai yi, wato zai yi nasara. Kuma Sulemanu ya yi shekaru da yawa yana yin nasara. (1 Tar. 29:​23-25) Ya gina haikalin, ya rubuta wasu littattafan Littafi Mai Tsarki, kuma marubutan Littafi Mai Tsarki da dama sun yi amfanin da kalmominsa. Ya yi suna sosai don hikimarsa da arzikinsa. (1 Sar. 4:34) Amma Dauda ya bayyana cewa idan Sulemanu ya daina yi wa Jehobah biyayya, zai daina yin nasara. Kuma abin baƙin cikin shi ne, da Sulemanu ya tsufa, ya soma bauta wa wasu alloli. Jehobah bai ji daɗi ba, don haka ya daina ba wa Sulemanu hikimar yin mulki yadda ya dace.—1 Sar. 11:​9, 10; 12:4.

Shawara ta ƙarshe da Dauda ya ba wa Sulemanu ya nuna mana cewa idan muka yi wa Jehobah biyayya, zai ba mu hikimar tsai da shawarwari masu kyau a rayuwarmu (Ka duba sakin layi na 11-12) b


12. Mene ne abin da Dauda ya faɗa ya koya mana?

12 Wannan ya koya mana cewa yi wa Jehobah biyayya zai sa mu sami albarkarsa. (Zab. 1:​1-3) Jehobah bai yi mana alkawari cewa zai sa mu yi suna ko mu yi arziki kamar Sulemanu ba. Amma idan muka yi masa biyayya, zai ba mu hikimar tsai da shawarwari masu kyau. (K. Mag. 2:​6, 7; Yak. 1:5) Shawarar da ke Kalmarsa za ta taimaka mana mu yi zaɓi mai kyau a batun neman ilimi, da nishaɗi, da kuma neman kuɗi. Idan muka bi shawararsa, zai ci-gaba da ƙaunar mu kuma za mu sami rai na har abada. (K. Mag. 2:​10, 11) Za mu sami abokan kirki, kuma za mu ji daɗin zaman iyalinmu.

13. Me ya taimaki ꞌyarꞌuwa Carmen ta tsai da shawara mafi kyau a rayuwa?

13 Wata ꞌyarꞌuwa mai suna Carmen a ƙasar Mozambik, ta ɗauka cewa zuwa jamiꞌa ne zai sa ta yi nasara a rayuwa. Sai ta je jamiꞌa kuma ta soma karatu a fannin gine-gine. Ta ce: “Na ji daɗin abin da nake koya, amma yana gajiyar da ni kuma yana cinye lokacina. Ina zuwa makaranta ƙarfe 7:30 na safe, kuma sai 6:00 na yamma muke tashiwa. Da kyar nake zuwa taro, kuma dangantakata da Jehobah ta yi sanyi. Na ga cewa shugabanni biyu nake ƙoƙarin bauta wa.” (Mat. 6:24) ꞌYarꞌuwar ta roƙi Jehobah ya taimake ta kuma ta yi bincike a littattafanmu don ta san abin da za ta yi. Ta ce: “Na saurari shawarar da dattawa da mahaifiyata suka ba ni. Sai na daina makarantar kuma na soma hidima ta cikakken lokaci. Yanzu na ga cewa shawara mafi kyau ne na yanke, kuma ba na da-na-sani.”

14. Mene ne Musa da Dauda suka ƙarfafa mutane su yi?

14 Musa da Dauda masu ƙaunar Jehobah ne, kuma sun san muhimmancin bin abin da Jehobah ya ce. Don haka, sun ƙarfafa mutane su bi misalinsu kuma su bauta wa Jehobah da aminci. Sun kuma gargaɗi mutane cewa, idan sun yi wa Jehobah rashin biyayya zai yi fushi da su kuma ba zai yi musu albarka ba. Shawarar nan da suka bayar tana da amfani a yau. Ɗarurruwan shekaru bayan mutuwarsu, wani bawan Jehobah ya sake nanata muhimmancin bauta wa Jehobah da aminci.

“ABIN DA YA FI SA NI FARIN CIKI”

15. Waɗanne abubuwa ne manzo Yohanna ya gani a rayuwarsa?

15 Yesu ya ƙaunaci manzo Yohanna ba kaɗan ba. (Mat. 10:2; Yoh. 19:26) Yohanna ya yi waꞌazi sosai tare da Yesu. Ya ga muꞌujizai da dama da ya yi, kuma bai bar binsa ba har a lokuta masu wuya. A idonsa aka kashe Yesu, kuma ya ga Yesu lokacin da ya tashi daga mutuwa. Ƙari ga haka, ya ga yadda ikilisiyar Kirista ta ci-gaba da ƙaruwa, har lokacin “da aka yi shelar [labarin nan mai da daɗi] ga kowace halitta a ƙarƙashin sama.”—Kol. 1:23.

16. Su wane ne suka amfana daga wasiƙun da Yohanna ya rubuta?

16 Saꞌad da Yohanna ya tsufa sosai, Jehobah ya ba shi damar rubuta littafin Ruꞌuyar da Aka Yi wa Yohanna. (R. Yar. 1:1) Shi ne ya rubuta Linjilar Yohanna. Ban da haka, ya rubuta wasiƙu uku da suke ɗauke da sunansa. Ya rubuta wasiƙarsa ta uku ne zuwa ga wani Kirista mai aminci mai suna Gayus. Yohanna ya ƙaunace shi kamar ɗan cikinsa. (3 Yoh. 1) A lokacin, ba mamaki akwai ꞌyanꞌuwa da yawa da Yohanna ya ɗauke su kamar ꞌyaꞌyansa da yake ƙauna. Abin da Yohanna ya rubuta ya ƙarfafa dukan mabiyan Yesu, kuma yana kan ƙarfafa mu.

17. Bisa ga 3 Yohanna 4, mene ne ya fi kawo farin ciki?

17 Mene ne Yohanna ya ce? (Karanta 3 Yohanna 4.) A wasiƙarsa ta uku, Yohanna ya ce abin da ya fi sa shi farin ciki shi ne, idan ya ga ꞌyanꞌuwansa suna yin biyayya ga Allah. A lokacin da ya rubuta wasiƙar, wasu a cikin ikilisiya suna yaɗa koyarwar ƙarya, kuma suna raba kan ꞌyanꞌuwa. Duk da haka, wasu sun ci-gaba da ‘bin gaskiya.’ Sun “bi umarnan Allah.” (2 Yoh. 4, 6) Yadda suka riƙe amincinsu ya faranta ran Yohanna da kuma Jehobah.—K. Mag. 27:11.

18. Mene ne kalmomin Yohanna suka koya mana?

18 Wannan ya koya mana cewa riƙe aminci yana kawo farin ciki. (1 Yoh. 5:3) Alal misali, za mu yi farin ciki don mun san cewa muna faranta ma Jehobah rai. Jehobah yana farin ciki sosai idan ya ga mun ƙi yin abin da bai dace ba, kuma muka bi maganarsa. (K. Mag. 23:15) Malaꞌiku ma sukan yi farin ciki. (Luk. 15:10) ꞌYanꞌuwanmu ma sukan yi farin ciki idan suka ga mun riƙe amincinmu, musamman saꞌad da aka tsananta mana, ko aka jarrabce mu. (2 Tas. 1:4) A-kwana-a-tashi, za a halaka wannan duniyar Shaiɗan. Saꞌad da hakan ya faru, za mu yi farin ciki sosai cewa mun riƙe amincinmu ga Jehobah har ƙarshe.

19. Mene ne ꞌYarꞌuwa Rachel ta ce game da koya wa mutane gaskiya? (Ka kuma duba hoton.)

19 Mukan yi farin ciki sosai idan muna koya wa mutane gaskiya game da Jehobah. Wata ꞌyarꞌuwa mai suna Rachel a Jamhuriyar Dominika, ta ce koya wa mutane game da Jehobah babban gata ne. Ta taimaki mutane da yawa su soma bauta ma Jehobah. ꞌYarꞌuwar ta ce: “Ba zan iya kwatanta irin farin cikin da nake yi ba idan na ga ɗalibaina sun ƙaunaci Jehobah, sun dogara gare shi da dukan zuciyarsu, kuma sun gyara rayuwarsu don su gamshe shi. Farin cikin yakan sa in manta da duk wahalar da na sha lokacin da nake koyar da su.”

Muna farin ciki saꞌad da muke koyar da mutane su ƙaunaci Jehobah kuma su bi maganarsa (Ka duba sakin layi na 19)


KA BI SHAWARA TA ƘARSHE DA MAZAN NAN SUKA BAYAR

20. Ta yaya muke kama da Musa, da Dauda, da Yohanna?

20 Musa, da Dauda, da Yohanna sun rayu a lokacin da ya bambanta da namu. Amma muna kama da su a hanyoyi da yawa. Alal misali, su bayin Jehobah ne, kuma mu ma bayin Jehobah ne. Muna yin adduꞌa ga Jehobah, da shi muka dogara, kuma muna neman shawararsa, kamar yadda suka yi. Ƙari ga haka, kamarsu, mun tabbata cewa Jehobah zai yi mana albarka idan muka bi maganarsa.

21. Me za mu samu idan muka bi shawarar Musa da Dauda da Yohanna?

21 Bari mu bi shawarar da mazan nan suka bayar, wato mu yi biyayya ga Jehobah. Idan muka yi haka, Jehobah zai sa mu yi nasara a rayuwa. Za mu “yi tsawon rai,” wato za mu rayu har abada! (M. Sha. 30:20) Kuma za mu yi farin ciki, domin mun san muna yin abin da ya gamshi Ubanmu na sama, wanda zai ba mu lada fiye da yadda muke tunani.—Afis. 3:20.

WAƘA TA 129 Za Mu Riƙa Jimrewa

a Yawancin Israꞌilawa da suka ga abin ban-mamaki da Jehobah ya yi a Jar Teku ba su shiga Ƙasar Alkawarin ba. (L. Ƙid. 14:​22, 23) Jehobah ya ce waɗanda suka kai shekaru 20 kuma an yi musu rijista, za su mutu a jeji. (L. Ƙid. 14:29) Amma, yawancin waɗanda ba su kai shekaru 20 ba sun tsira. Kuma su da Joshua, da Kaleb, da ꞌyaꞌyan Lawi da yawa, sun haye Kogin Urdun tare, kuma sun shiga ƙasar Kanꞌana.—M. Sha. 1:​24-40.

b BAYANI A KAN HOTUNA: Gefen hagu: Dauda yana ba wa Sulemanu shawara ta ƙarshe. Gefen dama: ꞌYanꞌuwa maza da mata a Makarantar Hidima ta Majagaba, suna samun koyarwa mafi kyau.