Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 44

WAƘA TA 33 Mu Miƙa Dukan Damuwarmu ga Jehobah

Yadda Za Ka Jimre Rashin Adalci

Yadda Za Ka Jimre Rashin Adalci

“Kada ku bar mugunta ta yi nasara a kanku, a maimakon haka ku yi nasara a kan mugunta ta wurin aikata abin da yake mai kyau.”ROM. 12:21.

ABIN DA ZA MU KOYA

Za mu ga abin da zai taimaka wa mutum idan aka yi masa rashin adalci.

1-2. Su waye ne za su iya yi mana rashin adalci? Ka bayyana.

 YESU ya ba da labarin wata gwauruwa da ta ci-gaba da roƙon wani alƙali ya taimaka mata, domin wani yana wulaƙanta ta. Babu shakka almajiran Yesu sun fahimci labarin nan, domin a lokacin ana wulaƙanta mutane sosai. (Luk. 18:​1-5) Mu ma mun fahimci yadda matar ta ji, domin babu waninmu da ba a taɓa yi masa rashin adalci ba.

2 Mutane a yau suna nuna bambanci, suna wulaƙanta mutane, kuma suna da son kai. Don haka, mun san cewa a-kwana-a-tashi za a yi mana rashin adalci. (M. Wa. 5:8) Amma abin da zai fi damunmu shi ne idan wani ɗanꞌuwa ko ꞌyarꞌuwa ta yi mana rashin adalci. Gaskiyar ita ce, ꞌyanꞌuwanmu ba kamar waɗanda suke tsananta mana ba ne. Ba sa mana rashin adalci da gangan. Ajizanci ne yake sa su yi hakan. Amma, yadda Yesu ya bi da mugaye da suka yi musu rashin adalci, misali ne mai kyau da za mu iya bi. Da yake muna haƙuri da mugayen da suke mana rashin adalci, ya kamata mu yi haƙuri da ꞌyanꞌuwanmu! Amma tambayar ita ce, yaya Jehobah yake ji idan ɗanꞌuwa ko wani da ba ya bauta wa Jehobah ya yi mana rashi adalci? Yana damuwa kuwa?

3. Me ya sa Jehobah yake damuwa idan aka yi mana rashin adalci?

3 Jehobah yana damuwa da abin da ke faruwa da mu, kuma idan mutane suna wulaƙanta mu, yana gani. Littafi Mai Tsarki ya ce, “Yahweh yana ƙaunar shariꞌar gaskiya.” (Zab. 37:28) Kuma Yesu ya tabbatar mana cewa Jehobah zai biya hakkin waɗanda aka yi musu rashin adalci “da sauri-sauri,” a lokacin da ya dace. (Luk. 18:​7, 8) Ƙari ga haka, nan ba da daɗewa ba Jehobah zai cire duk wahalar da muke sha, kuma ba za a sake yi mana rashin adalci ba.—Zab. 72:​1, 2.

4. Ta yaya Jehobah yake taimaka mana idan aka wulaƙanta mu?

4 Wajibi ne mu jira lokacin da Jehobah zai cire dukan matsalolinmu. Amma a yanzu yana taimaka mana idan mutane suna wulaƙanta mu. (2 Bit. 3:13) Alal misali, yana koya mana abin da za mu yi idan aka yi mana rashin adalci. Hanya ɗaya da yake hakan ita ce ta wurin Kalmarsa, inda ya nuna mana abin da ɗansa Yesu ya yi a lokacin da aka yi masa rashin adalci. Kuma yana ba mu shawarwari masu kyau da za mu bi idan aka wulaƙanta mu.

KA YI HATTARA DON KADA KA WUCE GONA DA IRI

5. Me ya sa ya kamata mu yi hattara idan ranmu ya ɓace sakamakon rashin adalci?

5 Idan aka yi mana rashin adalci, hakan zai iya damunmu ba kaɗan ba. (M. Wa. 7:7) Abin da ya faru da wasu bayin Allah masu aminci kamar Ayuba da Habakkuk ke nan. (Ayu. 6:​2, 3; Hab. 1:​1-3) Abin ɓacin rai ne kam, amma zai dace mu yi hattara, in ba haka ba za mu yi abin da bai kamata ba.

6. Mene ne muka koya daga labarin Absalom? (Ka kuma duba hoton.)

6 Idan an yi mana rashin adalci ko an yi ma wani namu, za mu so mu rama. Amma ramako zai iya ƙara ɓata lamarin. Bari mu tattauna labarin Absalom ɗan Sarki Dauda. Ya yi fushi sosai saꞌad da Amnon, wani ɗanꞌuwansa da mamarsu ba ɗaya ba, ya yi wa ƙanwarsa Tamar fyaɗe. Bisa ga Dokar Musa, ya kamata a kashe Amnon don abin da ya yi. (L. Fir. 20:17) Amma bai kamata Absalom ya kashe Amnon da kansa ba, duk da cewa abin ɓacin rai ne sosai.—2 Sam. 13:​20-23, 28, 29.

Absalom ya yi fushi sosai kuma bai kame kansa ba saꞌad da aka yi wa ꞌyarꞌuwarsa Tamar fyaɗe (Ka duba sakin layi na 6)


7. Yaya wani mai zabura ya ji saꞌad da ya ga rashin adalci da ke faruwa?

7 Idan ba a hukunta waɗanda suka yi rashin adalci ba, mai yiwuwa mu soma gani kamar yin abin da ya dace ba amfani. Irin tunanin da mai zabura ya yi ke nan da ya ga cewa mugaye suna cutar da masu adalci, amma ba abin da yake samunsu. Ya ce “kullum a kwanciyar rai suke.” (Zab. 73:12) Rashin adalcin ya ɓata masa rai sosai har ya ga kamar ba amfani ya ci-gaba da bauta wa Jehobah. Ya ce: “Da na yi ƙoƙarin gane wannan, ya zama mini da wuya sosai.” (Zab. 73:​14, 16) Ya ƙara da cewa: “Amma ni dai, ƙafafuna sun yi santsi, har tafin ƙafata yana gab da faɗuwa.” (Zab. 73:2) Irin abin da ya faru da wani ɗanꞌuwa mai suna Alberto a ke nan.

8. Mene ne wani ɗanꞌuwa ya yi da aka yi masa rashin adalci?

8 Wasu ꞌyanꞌuwa sun ce Alberto ya saci kuɗin ikilisiya. Hakan ya sa an sauƙe shi daga zama dattijo, kuma da yawa daga cikin ꞌyanꞌuwa da suka ji abin da ya faru sun daina daraja shi. Ɗanꞌuwa Alberto ya ce, “Na yi fushi sosai don abin da aka yi min bai kamata ba.” A sakamakon haka, ya yi shekaru biyar ba ya zuwa taro. Wannan labarin ya nuna abin da zai iya faruwa idan aka yi mana rashin adalci kuma ba mu kame kanmu ba.

KA YI KOYI DA YESU IDAN AKA YI MAKA RASHIN ADALCI

9. Wane irin rashin adalci ne aka yi wa Yesu? (Ka kuma duba hoton.)

9 Yesu ya nuna mana abin da ya kamata mu yi idan aka yi mana rashin adalci. Shi ma mutane da yawa sun yi masa rashin adalci, har da ꞌyan iyalinsa. ꞌYanꞌuwansa sun ce ya haukace. Shugabannin addini sun ce aljanu ne suke ba shi ikon yin abubuwan ban mamaki. Sojojin Roma kuma sun yi masa baꞌa, da dūka, a ƙarshe kuma suka kashe shi. (Mar. 3:​21, 22; 14:55; 15:​16-20, 35-37) Duk da haka, Yesu ya jimre kuma bai rama ba. Me wannan ya koya mana?

Yesu ya nuna mana abin da za mu yi idan aka yi mana rashin adalci (Ka duba sakin layi na 9-10)


10. Me ya taimaka wa Yesu ya jimre rashin adalci da aka yi masa? (1 Bitrus 2:​21-23)

10 Karanta 1 Bitrus 2:​21-23. b Yesu ya kafa mana misali mai kyau da za mu bi idan aka yi mana rashin adalci. Ya san lokacin da ya dace ya yi magana da kuma lokacin da bai dace ya yi hakan ba. (Mat. 26:​62-64) Akwai wasu lokuta da mutane suka yi ƙarya a kansa, amma bai ce kome ba. (Mat. 11:19) A lokacin da ya amsa wa maƙiyansa ma, bai laꞌanta su ba. Me ya taimaka wa Yesu ya kame kansa kuma ya jimre? “Ya dogara ga Allah wanda yake yin shariꞌar gaskiya.” Yesu ya san cewa Jehobah yana ganin rashin adalcin da ake masa. Kuma ya tabbata cewa Jehobah zai yi maganin kome a lokacin da ya dace.

11. Ta yaya za mu nuna kamun kai kamar Yesu? (Ka kuma duba hotunan.)

11 Kamar Yesu, idan aka yi mana rashin adalci, mu nuna kamun kai ta wurin yin tunani kafin mu faɗi wani abu. Wani lokaci ma, zai fi kyau mu ƙyale abin da aka yi mana idan bai taƙa-kara-ya-ƙarya ba. Ko kuma mu yi shiru kawai, idan muka ga cewa yin magana zai daɗa ɓata lamarin. (M. Wa. 3:7; Yak. 1:​19, 20) A wasu lokuta kuma, zai dace mu yi magana. Alal misali idan muka ga ana wulaƙanta wani, ko muna bukatar mu kāre imaninmu. (A. M. 6:​1, 2) Amma idan za mu yi magana, mu yi iya ƙoƙarinmu mu yi ta cikin natsuwa da bangirma.—1 Bit. 3:15. c

Idan aka yi mana rashin adalci, mu bi halin Yesu ta wurin yin tunani don mu san lokacin da zai dace mu yi magana ko mu yi shiru (Ka duba sakin layi na 11-12)


12. Ta yaya za mu “dogara ga Allah wanda yake yin shariꞌar gaskiya”?

12 Wata hanya kuma da za mu yi koyi da Yesu ita ce, ta wurin “dogara ga Allah wanda yake yin shariꞌar gaskiya.” Ta yaya za mu yi hakan? Idan aka zarge ka a kan abin da ba ka yi ba, ko an wulaƙanta ka, ka tuna cewa Jehobah ya san ainihin abin da ya faru. Irin tunanin nan zai taimaka mana mu jimre rashin adalci domin mun san cewa a-kwana-a-tashi, Jehobah zai gyara abubuwa. Barin kome a hannun Jehobah zai taimaka mana mu daina yin fushi, kuma ba za mu riƙe mutane a zuciya ba. Me ya sa hakan yake da muhimmanci? Domin ci-gaba da yin fushi zai iya sa mu yi abin da za mu zo muna da-na-sani, mu ƙasa yin farin ciki, kuma mu ɓata abokantakarmu da Jehobah.—Zab. 37:8.

13. Idan muna fama don rashin adalci, me zai taimaka mana mu ci-gaba da yin haƙuri kuma mu jimre?

13 A gaskiya, ba za mu iya bin misalin Yesu ba kuskure ba. Wani lokaci mukan yi kuskure a maganarmu ko ayyukanmu. (Yak. 3:2) Kuma wani lokaci rashin adalci da aka yi mana zai dame mu har iya rayuwarmu. Idan yanayin da kake ciki ke nan, ka tuna cewa Jehobah ya san irin halin da kake ciki. Yesu ma ya san yadda kake ji, domin shi ma ya yi fama da rashin adalci. (Ibran. 4:​15, 16) Jehobah ya sa an rubuta labarin Yesu don mu yi koyi da shi, kuma ya ba mu shawarwari masu kyau da za su taimaka mana idan muna fama da rashin adalci. Bari mu tattauna ayoyi biyu daga littafin Romawa da za su taimaka mana.

“KU BAR WA ALLAH YA RAMA MUKU”

14. Idan aka ce mu bar wa Allah ya rama mana, me ake nufi? (Romawa 12:19)

14 Karanta Romawa 12:19. Manzo Bulus ya shawarci Kiristoci cewa su bar Allah ya rama musu. Hakan yana nufin cewa mu bar kome a hannun Jehobah, domin ya yi abin da ya dace a lokacin da ya dace. Wani ɗanꞌuwa mai suna John da aka yi wa rashin adalci ya ce: “A gaskiya abin bai da sauƙi, sai da na yi ta ƙoƙarin kame kaina don kar in yi abin da bai dace ba. Abin da ke Romawa 12:19 ya taimaka min in dogara ga Jehobah.”

15. Idan aka yi mana rashin adalci, me ya sa zai fi mu bar kome a hannun Jehobah?

15 Idan akwai matsala kuma muka bar kome a hannun Jehobah, za mu amfana sosai. Za mu ceci kanmu daga damuwar da ke tattare da ƙoƙarin magance matsalar. Ban da haka ma, Jehobah yana so ya taimaka mana. Shi ne ya ce mu bar kome a hannunsa, mu jira mu ga yadda zai yi adalci. Jehobah ya ce “ni kuwa zan rama.” Idan mun yarda da wannan maganar, za mu ƙyale batun da tabbaci cewa zai yi abin da ya dace. Abin da ya taimaki Ɗanꞌuwa John da muka ambata a baya ke nan. Ya ce: “Idan na bar Jehobah ya magance matsalar a nasa lokaci, zai yi hakan a hanyar da ba zan taɓa iya yi ba.”

“KU YI NASARA A KAN MUGUNTA TA WURIN AIKATA ABIN DA YAKE MAI KYAU”

16-17. Ta yaya yin adduꞌa zai taimaka mana mu “yi nasara a kan mugunta”? (Romawa 12:21)

16 Karanta Romawa 12:21. Bulus ya kuma shawarci Kiristoci cewa su “yi nasara a kan mugunta ta wurin aikata abin da yake mai kyau.” A koyarwar da Yesu ya yi a kan dutse, ya ce: “Ku ƙaunaci waɗanda ba sa ƙaunarku, ku yi wa masu tsananta muku adduꞌa.” (Mat. 5:44) Abin da shi ma ya yi ke nan. Ka tuna da irin wahalar da ya sha lokacin da sojojin Roma suka rataya shi a kan gungume? Sojojin su wulaƙanta shi sosai, kuma ya sha azaba. Zai yi wuya mu fahimci irin wahalar da Yesu ya sha.

17 Yesu ya riƙe amincinsa kuma ya ci-gaba da ƙaunar Jehobah duk da wannan rashin adalcin. Maimakon ya laꞌanta sojojin, ya yi adduꞌa ya ce: “Uba, bari ka gafarta musu, gama ba su san abin da suke yi ba.” (Luk. 23:34) Idan muka yi adduꞌa a madadin waɗanda suka wulaƙanta mu, hakan zai taimaka mana mu daina yin fushi da su har ma mu soma yi musu fatan alheri.

18. Ta yaya yin adduꞌa ya taimaki Alberto da John su jimre rashin adalci?

18 Yin adduꞌa ya taimaka wa ꞌyanꞌuwa biyu da aka ambata a talifin nan su jimre da rashin adalci da aka yi musu. Ɗanꞌuwa Alberto ya ce: “Na yi adduꞌa a madadin ꞌyanꞌuwa da suka yi min rashin adalcin. Kuma na yi ta roƙon Jehobah ya taimaka min in daina fushi a kan batun.” Godiya ga Jehobah, yanzu Alberto ya komo kuma yana bauta wa Jehobah da aminci. Ɗanꞌuwa John kuma ya ce: “Na yi adduꞌa a madadin ɗanꞌuwan da ya ɓata min rai, sau da yawa. Hakan ya taimaka min in daina fushi da shi. Ƙari ga haka, na sami kwanciyar hankali.”

19. Me zai taimaka mana mu ci-gaba da jimrewa har ƙarshe? (1 Bitrus 3:​8, 9)

19 Muddin muna rayuwa a wannan zamanin, za a iya yi mana rashin adalci. Amma ko da me ya faru, mu ci-gaba da roƙon Jehobah ya taimake mu. Ƙari ga haka, idan aka yi mana rashin adalci, mu yi koyi da Yesu kuma mu bi shawarwari da Jehobah ya ba mu a Kalmarsa. Idan muka yi haka, ba shakka Jehobah zai albarkace mu.—Karanta 1 Bitrus 3:​8, 9.

WAƘA TA 38 Zai Ƙarfafa Ka

a An canja wasu sunayen.

b A littafin Bitrus na ɗaya sura 2 da 3, manzo Bitrus ya yi magana game da wulaƙanci da wasu Kiristoci suka sha a hannun uban gidansu, da kuma mazajensu da ba sa bauta wa Jehobah.—1 Bit. 2:​18-20; 3:​1-6, 8, 9.

c Ka kalli bidiyon nan mai jigo, Yadda Ƙauna Take Kawo Salama, a jw.org/ha.