Amsoshin Tambayoyin Masu Karatu
Saꞌad da Israꞌilawa suke daji, suna da wani abinci ban da manna da kajin-daji?
Manna ne abincin da Israꞌilawa suka ci a yawancin lokuta saꞌad da suke daji. (Fit. 16:35) Jehobah ya kuma ba su kajin-daji har sau biyu. (Fit. 16:12, 13; L. Ƙid. 11:31) Amma ban da manna da kuma kajin-daji, akwai wasu abubuwa dabam da Israꞌilawan suka ci.
Alal misali, akwai lokutan da Jehobah ya kai mutanensa “wurin da za su huta,” kuma akwai ruwan sha da abin da za su ci a wurin. (L. Ƙid. 10:33) Ɗaya daga cikin wuraren shi ne “Elim, inda akwai maɓuɓɓugar ruwa 12, da itatuwan dabino 70.” (Fit. 15:27) Wani littafi mai suna Plants of the Bible, ya ce itatuwan dabino “sukan yi girma a wurare da yawa kuma an fi amfani da ꞌyaꞌyansu a matsayin abinci da kuma māi. Ƙari ga haka, suna ba da inuwa ga miliyoyin mutane.”
Da alama Israꞌilawan sun tsaya a wani babban wurin hutawa da a yau ake kira Feiran, kuma yana a wurin da ake kira Wadi Feiran. a Littafin nan Discovering the World of the Bible, ya ce daga inda wadi ɗin, (wato kwarin da ke da ruwa) ya soma zuwa iyakarsa, ya kai “kilomita 130. Shi ne wadi da ya fi tsayi da kuma kyau, kuma shi ne wadi da aka fi sani a yanki Sinai.” Littafin ya kuma ce: “Idan mutum ya yi tafiya na kilomita 45 daga inda kwarin ya haɗu da teku, zai isa wani wurin hutawa da ke da ruwa da kuma itatuwa. Ana kiran wurin Feiran Oasis. Wurin yana a hawan da ya kai wajen kafa 2,000 daga teku, kuma tsayinsa ya kai kilomita 4.8. Akwai itatuwan dabino da yawa a wurin, kuma wurin yana da kyau sosai har akan kwatanta shi da gonar Adnin. Mutane sun yi dubban shekaru suna zuwa wurin domin dubban itatuwan dabino da ke wurin.”
Saꞌad da Israꞌilawa suke barin Masar, sun ɗauki fulawa da suka riga suka kwaɓa, da abin da za su riƙa amfani da shi su kwaɓa fulawa. Da alama sun kuma ɗauko hatsi da kuma māi. Hakika, abubuwan nan sun ƙare ba da jimawa ba. Mutanen sun kuma tafi da “garkunansu na tumaki, da awaki, da na shanu masu yawa.” (Fit. 12:34-39) Amma saboda yanayin zafi da kuma rashin ruwa a dajin, da alama wasu daga cikin dabbobin sun mutu. Wataƙila wasu Israꞌilawan sun yanka wasu dabbobin sun ci, wasu kuma sun yi hadaya da su ga Jehobah da kuma allolin ƙarya. b (A. M. 7:39-43) Duk da haka, Israꞌilawan sun yi kiwon wasu dabbobi. Mun gano hakan ta abin da Jehobah ya gaya wa Israꞌilawan don rashin bangaskiyarsu. Ya ce: “ꞌYaꞌyanku kuma za su zama makiyaya a cikin jeji har shekara arbaꞌin.” (L. Ƙid. 14:33) Don haka, mai yiwuwa sun riƙa samun madara da kuma nama daga dabbobin. Amma madarar da naman ba za su iya ciyar da mutane wajen miliyan uku har na shekaru 40 ba. c
To ta yaya dabbobin suka sami ruwan sha da kuma abinci? d Da alama a lokacin ana yin ruwan sama sosai, kuma hakan na sa ciyayi su yi girma a dajin. Talifi mai suna Arabia, a littafin Insight on the Scriptures na 1, ya ce shekaru 3,500 da suka shige, “ana ruwan sama sosai a yankin da Israꞌilawa suke, fiye da yadda ake yi a yau. Mun san da hakan domin akwai kwaruruwa da dama da suka bushe. A dā, rafuffuka ne. Hakan ya nuna cewa a dā ana ruwan sama sosai a yankin.” Duk da haka, dajin a bushe yake kuma yana da ban tsoro. (M. Sha. 8:14-16) Da ba don ruwan da Jehobah ya tanadar musu ta wajen muꞌujiza ba, da dukan Israꞌilawan da dabbobinsu sun mutu.—Fit. 15:22-25; 17:1-6; L. Ƙid. 20:2, 11.
Musa ya gaya wa Israꞌilawan cewa Jehobah ya tanada musu manna ne “domin [su] sani cewa ba da abinci kaɗai mutum zai rayu ba, amma ta kowace maganar da take fitowa daga bakin Yahweh.”—M. Sha. 8:3.
a Ka duba Hasumiyar Tsaro ta 1 ga Mayu, 1992, shafuffuka na 24-25 na Turanci.
b Littafi Mai Tsarki ya ambata lokuta biyu da Israꞌilawan suka yi hadaya da dabbobi ga Jehobah a daji. Ƙaro na farko da aka yi hadayan shi ne lokacin da aka naɗa firistoci. Na biyun kuma shi ne lokacin bikin Ƙetarewa. An yi hadayu biyun a shekara ta 1512 kafin haihuwar Yesu, wato shekaru biyu bayan da Israꞌilawa suka bar Masar.—L. Fir. 8:14–9:24; L. Ƙid. 9:1-5.
c Da Israꞌilawan suka kusan cika shekaru 40 a daji, sun ci wasu ƙasashe da yaƙi kuma sun kwashi dabbobi da yawa a matsayin ganima. (L. Ƙid. 31:32-34) Amma duk da hakan sun ci-gaba da cin manna har sai da suka shiga ƙasar da aka yi musu alkawari.—Yosh. 5:10-12.
d Babu abin da ya nuna cewa dabbobin ma sun ci manna, domin Jehobah ya gaya wa mutanensa cewa su ɗibi mannar daidai da yadda kowane mutum zai iya ci, amma bai ce har da dabbobi ba.—Fit. 16:15, 16.