Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 44

Ka Kara Fahimtar Kalmar Allah

Ka Kara Fahimtar Kalmar Allah

“Ku fahimci . . . faɗinta, da tsawonta, da girmanta, da zurfinta.”—AFIS. 3:18.

WAƘA TA 95 Muna Samun Ƙarin Haske

ABIN DA ZA A TATTAUNA a

1-2. Mene ne zai taimaka mana mu yi nazarin Littafi Mai Tsarki da kyau? Ka ba da misali.

 A CE kana so ka sayi wani gida, za ka gamsu idan hoton gidan ne kawai ka gani kuma ka saye shi? Ba shakka za ka so ka je gidan kuma ka duba shi ciki da waje. Zai kuma dace idan ka tambayi wanda ya san tsarin da aka bi wajen gina gidan. Hakika, za ka so ka san kome da kome game da gidan kafin ka saye shi.

2 Za mu iya bin wannan misalin yayin da muke nazarin Littafi Mai Tsarki. Wani marubuci ya kwatanta Littafi Mai Tsarki da “babban gida da ke da tsayi sosai kuma an gina shi a kan tushe mai ƙarfi sosai.” Don haka, ta yaya za mu iya fahimtar kome da kome da ke Littafi Mai Tsarki da kyau? Idan ka karanta Littafi Mai Tsarki cikin hanzari, “koyarwa mai sauƙi ta kalmar Allah” ce kawai za ka fahimta. (Ibran. 5:12) Amma kamar yadda kake bukatar ka shiga cikin gidan da muka ambata, kana bukatar ka yi nazarin Littafi Mai Tsarki da kyau don ka ƙara fahimtar abubuwa da ke ciki. Wani abin da zai taimaka mana sosai shi ne, neman alaƙar da ke tsakanin abin da Littafi Mai Tsarki ya faɗa a wani wuri, da abin da ya faɗa a wani wuri dabam. Ka yi ƙoƙari ka san abubuwan da ka yi imani da su da kuma dalilin da ya sa ka yi imani da su.

3. Mene ne manzo Bulus ya umurci ꞌyanꞌuwansa Kiristoci su yi, kuma me ya sa? (Afisawa 3:​14-19)

3 Don mu ƙara fahimtar abubuwan da ke Littafi Mai Tsarki, akwai abubuwan da muke bukatar mu fahimce su da kyau. Manzo Bulus ya shawarci ꞌyanꞌuwansa Kiristoci su yi nazarin Kalmar Allah da kyau domin su ‘fahimci . . . faɗinta, da tsawonta, da girmanta, da zurfinta.’ Yin hakan zai sa su “kafu sosai cikin” bangaskiya. (Karanta Afisawa 3:​14-19.) Ya kamata mu ma mu yi hakan. Bari mu ga yadda za mu iya yin nazarin Kalmar Allah da kyau don mu ƙara fahimtar abubuwan da ke ciki.

KA ƘARA FAHIMTAR KOYARWA MASU ZURFI

4. Mene ne za mu iya yi don mu ƙara kusantar Jehobah? Ka ba da misali.

4 A matsayinmu na Kiristoci, ba koyarwa masu sauƙi ne kawai muke so mu fahimta ba. Da taimakon ruhu mai tsarki, muna marmarin koyan “abubuwan Allah masu wuyar ganewa.” (1 Kor. 2:​9, 10) Za ka iya yin nazari mai zurfi da zai sa ka ƙara kusantar Jehobah. Alal misali, za ka iya bincika yadda ya nuna ƙauna ga bayinsa a dā, da kuma yadda hakan ya nuna cewa yana ƙaunar ka. Za ka kuma iya bincika yadda Israꞌilawa suka bauta ma Jehobah a dā, kuma ka kwatanta shi da yadda muke bauta ma Jehobah a yau. Ko kuma za ka iya yin nazari mai zurfi game da annabce-annabce da Yesu ya cika saꞌad da yake duniya.

5. Akwai batu da za ka so ka yi nazarin sa da kanka don ka ƙara fahimta?

5 Wasu ꞌyanꞌuwa da suke son yin nazari mai zurfi sun ambata wasu abubuwa da za su so su ƙara fahimta. An rubuta wasu daga cikin abubuwan da suka ce za su so su ƙara fahimta a akwatin nan, “ Abubuwa da Za Mu Iya Yin Nazari Mai Zurfi a Kansu.” Za ka yi farin ciki sosai idan ka bincika batutuwan nan ta yin amfani da Littafin Bincike Don Shaidun Jehobah. Yin nazari mai zurfi zai ƙarfafa bangaskiyarka kuma zai taimaka maka ka “sami sanin Allah.” (K. Mag. 2:​4, 5) Yanzu, bari mu tattauna wasu koyarwar Littafi Mai Tsarki da za mu iya ƙara fahimtar su.

KA YI TUNANI SOSAI GAME DA NUFIN ALLAH

6. (a) Mene ne bambancin shirin mutum da kuma nufinsa? (b) Me ya sa za mu iya cewa nufin Allah ga duniya “madawwami” ne? (Afisawa 3:11)

6 Ka yi laꞌakari da abin da Littafi Mai Tsarki ya ce game da nufin Allah. Akwai bambanci tsakanin shirin mutum da kuma nufinsa. Za mu iya kwatanta shirin mutum da hanyar da ya zaɓa don ta kai shi inda za shi. Idan wani abu ya faru kuma hanyar ta toshe, mutumin ba zai iya isa wurin ba. Amma nufin mutum, kamar inda mutumin yake so ya je ne. Mun san inda za mu, amma akwai hanyoyi dabam-dabam da za su iya kai mu wurin. Idan hanya ɗaya ta toshe, za mu iya bin wata hanya dabam. Muna godiya don yadda Jehobah ya ci-gaba da bayyana mana ‘madawwamin nufinsa’ a hankali. (Afis. 3:11) Jehobah zai iya amfani da hanyoyi dabam-dabam don ya cim ma nufinsa. Kuma a kullum yakan yi nasara, don “ya halicci kowane abu domin nufin kansa” ne. (K. Mag. 16:4) Nufin Jehobah madawwami ne domin duk abin da Jehobah ya cim ma zai kasance har abada. Mene ne nufin Allah kuma wane canje-canje ne ya yi don ya iya cim ma nufinsa?

7. Bayan iyayenmu na farko sun yi wa Jehobah tawaye, ta yaya Jehobah ya canja hanyar da zai cika nufinsa? (Matiyu 25:34)

7 Allah ya gaya wa iyayenmu na farko nufinsa a gare su. Ya ce: “Ku yi ta haifuwa sosai ku yalwata, ku ciccika duniya ku kuma sha ƙarfinta. Ku yi mulkin . . . kowane abu mai rai” a duniya. (Far. 1:28) Saꞌad da Adamu da Hauwaꞌu suka yi wa Allah tawaye kuma suka jawo zunubi ga dukan ꞌyan Adam, hakan bai hana Jehobah cika nufinsa ba. Ya canja hanyar da zai bi don ya cika nufinsa. Nan take, ya yanke shawarar kafa wata Mulki a sama da za ta sa ya cim ma nufinsa ga ꞌyan Adam da kuma duniya. (Karanta Matiyu 25:34.) Da lokacin da ya shirya ya kai, Jehobah Allahnmu mai ƙauna ya aiko da Ɗansa duniya don ya koyar da mutane game da Mulkin, kuma ya ba da ransa don ya ceto mu daga zunubi da mutuwa. Bayan haka, an ta da Yesu daga mutuwa kuma ya koma sama don ya zama Sarki a Mulkin da Allah ya kafa. Amma akwai wasu abubuwa kuma da za mu iya koya game da nufin Allah.

Ka yi tunanin lokacin da malaꞌiku da ꞌyan Adam za su bauta ma Jehobah da aminci da kuma haɗin kai! (Ka duba sakin layi na 8)

8. (a) Mene ne Littafi Mai Tsarki yake koyarwa a taƙaice? (b) Kamar yadda aka faɗa a Afisawa 1:​8-11, wane abu ne kuma Jehobah zai cim ma? (Ka duba hoton da ke shafin farko.)

8 A taƙaice, ainihin abin da Littafi Mai Tsarki yake koyarwa shi ne cewa, Jehobah zai wanke sunansa daga zargi yayin da yake cika nufinsa ga duniya ta wurin Mulkinsa wanda Yesu ne Sarkin. Ba wanda ya isa ya canja nufin Jehobah. Ya yi alkawari cewa nufinsa zai cika daidai yadda ya faɗa. (Isha. 46:​10, 11; Ibran. 6:​17, 18) Nan gaba, duniya za ta zama aljanna, kuma ꞌyaꞌyan Adamu masu adalci za su yi rayuwa cikin farin ciki “har abada!” (Zab. 22:26) Amma ba shi ke nan ba, akwai wasu abubuwa kuma da Jehobah zai cim ma. Ainihin nufinsa shi ne ya haɗa kan bayinsa da suke sama da waɗanda suke nan duniya. Bayan haka, dukan halittu za su miƙa kansu ga Sarautarsa. (Karanta Afisawa 1:​8-11.) Yadda Jehobah yake cika nufinsa yana burge mu, ko ba haka ba?

KA YI TUNANI MAI ZURFI A KAN ABIN DA ZAI FARU A NAN GABA

9. Idan muna karanta Littafi Mai Tsarki, waɗanne abubuwa ne za mu iya sani game da nan gaba?

9 Ka yi laꞌakari da annabcin da ke Farawa 3:15 da Jehobah ya yi a lambun Adnin. b Annabcin ya yi magana game da abubuwan da za su faru don nufinsa ya cika. Amma zai ɗauki dubban shekaru kafin abubuwan nan su cika. Alal misali, Jehobah ya gaya wa Ibrahim cewa wani daga zuriyarsa zai zama Kristi. (Far. 22:​15-18) A shekara ta 33 bayan haifuwar Yesu, an sari diddigen ƙafar Yesu kamar yadda aka annabta. (A. M. 3:​13-15) Amma kafin zuriyar ya murƙushe kan Shaiɗan kamar yadda aka annabta, zai ɗauki fiye da shekaru dubu daga yanzu. (R. Yar. 20:​7-10) Littafi Mai Tsarki ya gaya mana ƙarin abubuwa da za su faru saꞌad da ƙiyayya da ke tsakanin duniyar Shaiɗan da ƙungiyar Jehobah ta daɗa yin tsanani.

10. (a) Waɗanne abubuwa ne za su faru nan ba da jimawa ba? (b) Ta yaya za mu shirya kanmu don abubuwa da za su faru? (Ka duba ƙarin bayani.)

10 Ka yi tunani a kan abubuwan nan masu muhimmanci da Littafi Mai Tsarki ya annabta cewa za su faru. Da farko, ƙasashe za su yi shelar “zaman lafiya da salama!” (1 Tas. 5:​2, 3) “Sai kawai” a soma ƙunci mai girma. Ƙuncin zai soma da harin da ƙasashen duniya za su kai wa addinan ƙarya. (R. Yar. 17:16) Bayan haka, za a ga alama mai ban mamaki na “Ɗan Mutum yana zuwa a cikin girgije da iko da ɗaukaka mai yawa.” (Mat. 24:30) Yesu zai yi shariꞌa, kuma zai ware awaki daga tumaki. (Mat. 25:​31-33, 46) A wannan lokacin, Shaiɗan ba zai yi zaman kashe wando ba, zai ci-gaba da yin gāba da Jehobah domin ya tsani bayin Jehobah sosai. Zai zuga haɗin gwiwar ƙasashe da Littafi Mai Tsarki ya kira Gog na ƙasar Magog su kai wa bayin Jehobah hari. (Ezek. 38:​2, 10, 11) A yayin da ake ƙunci mai girma, za a tattara dukan shafaffun Kiristoci zuwa sama domin su haɗa kai da Yesu da malaꞌikunsa su yi yaƙi a Armageddon. Hakan zai kawo ƙarshen ƙunci mai girma. c (Mat. 24:31; R. Yar. 16:​14, 16) Bayan haka, Yesu zai soma yin sarauta a duniya na shekara dubu.—R. Yar. 20:6.

Yaya dangantakarka da Jehobah za ta kasance bayan ka yi biliyoyin shekaru kana koya game da shi? (Ka duba sakin layi na 11)

11. Waɗanne abubuwa ne za ka mora saꞌad da kake rayuwa har abada? (Ka kuma duba hoton.)

11 Yanzu, ka yi tunanin abubuwa da za su faru bayan Yesu ya yi sarauta na shekara dubu. Littafi Mai Tsarki ya ce Mahaliccinmu “ya sa burin yin rayuwa har abada a zuciyar[mu].” (M. Wa. 3:​11, New World Translation) Ka yi tunanin yadda za ka amfana da kuma yadda hakan zai shafi dangantakarka da Jehobah. Shafi na 319 na littafin nan Ka Kusaci Jehovah, ya faɗi yadda za mu amfana, ya ce: ‘Bayan mun rayu na ɗarurruwan shekaru, dubbai, miliyoyi, har ma biliyoyin shekaru, za mu san Jehobah Allah sosai, fiye da yadda muka yi a yanzu. Amma za mu ga cewa har ila akwai abubuwa masu ban mamaki marasa iyaka da za mu koya. . . . Rai madawwami zai yi daɗi sosai. Kuma a kullum, kusantar Jehobah ne abin da zai fi sa mu farin ciki.’ Idan muka ci-gaba da nazarin Kalmar Allah, wane abu ne kuma za mu iya ƙara fahimta?

KA DUBA CAN CIKIN SAMMAI

12. Ta yaya za mu iya duba can cikin sammai? Ka ba da misali.

12 Kalmar Allah ta ɗan gaya mana abin da ke faruwa “a sama” inda Jehobah yake. (Isha. 33:5) Littafi Mai Tsarki ya gaya mana abubuwa masu ban mamaki game da Jehobah da kuma sashen ƙungiyarsa da ke sama. (Isha. 6:​1-4; Dan. 7:​9, 10; R. Yar. 4:​1-6) Alal misali, za mu iya yin nazari a kan abubuwa masu ban mamaki da Ezekiyel ya gani lokacin da “sammai suka buɗe, [ya] kuwa ga ruꞌuyoyin Allah.”—Ezek. 1:1.

13. Mene ne yake burge ka game da abin da Yesu yake yi a sama kamar yadda aka bayyana a Ibraniyawa 4:​14-16?

13 Ka kuma yi tunanin abin da Yesu yake yi mana a sama a matsayin Sarkinmu da kuma Babban Firist mai tausayi. Ta wurinsa ne muke zuwa “kujerar mulkin Allah, wato wurin alheri.” Muna yin hakan ne ta wajen yin adduꞌa don mu roƙe shi ya yi mana gafara kuma ya “taimake mu a lokacin bukata.” (Karanta Ibraniyawa 4:​14-16.) A kowace rana, muna bukatar mu yi tunani a kan abin da Jehobah da Yesu suka yi mana da waɗanda suke yi mana a yanzu. Bari ƙaunar da suke mana ta taɓa zuciyarmu kuma ta sa mu ci-gaba da bauta ma Jehobah da ƙwazo.—2 Kor. 5:​14, 15.

Ka yi tunanin irin farin cikin da za ka yi a sabuwar duniya domin ka taimaka wa mutane su zama Shaidun Jehobah da kuma mabiyan Yesu! (Ka duba sakin layi na 14)

14. Wane abu mai muhimmanci ne za mu iya yi don mu nuna godiya ga Jehobah da kuma Yesu? (Ka kuma duba hoton.)

14 Wata hanya mafi kyau da za mu iya nuna godiya ga Jehobah da kuma Ɗansa ita ce mu taimaka wa mutane su zama Shaidun Jehobah da kuma mabiyan Yesu. (Mat. 28:​19, 20) Abin da manzo Bulus ya yi ke nan don ya nuna godiya ga Jehobah da Yesu. Ya san cewa nufin Jehobah ne “dukan mutane su sami ceto, su kuma kai ga sanin gaskiya.” (1 Tim. 2:​3, 4) Ya sa ƙwazo sosai a hidimarsa domin ya taimaka wa mutane da yawa, kuma ‘ko ta yaya ya cece waɗansu.’—1 Kor. 9:​22, 23.

KA YI MARMARIN ƘARA FAHIMTAR ABUBUWAN DA KE KALMAR ALLAH

15. Bisa ga Zabura 1:​2, mene ne zai sa mu farin ciki?

15 Marubucin zabura ta ɗaya ya ce wanda yake “jin daɗi ya kiyaye Koyarwar Yahweh, yana tunanin Koyarwar dare da rana,” shi ne zai yi farin ciki kuma ya yi nasara. Abin da marubucin ya faɗa gaskiya ne. (Zab. 1:​1-3) Wani mafassarin Littafi Mai Tsarki mai suna Joseph Rotherham, ya ce ya kamata mutum ya “so ja-gorancin Allah sosai, har hakan ya sa shi ya nemi nufin Allah, ya yi nazarinsa kuma ya ɗauki lokaci yana tunani a kansa.” Ya kuma ƙara da cewa “idan mutum ya bar rana ɗaya ta wuce bai karanta Kalmar Allah ba, to bai yi wani abin amfani a ranar ba ke nan.” Za ka iya jin daɗin yin nazarin Littafi Mai Tsarki ta wajen mai da hankali ga dukan abubuwa masu muhimmanci da aka rubuta a ciki, da kuma bincika yadda suke da alaƙa da juna. Abin farin ciki ne mutum ya san Kalmar Allah ciki da waje!

16. Me za mu tattauna a talifi na gaba?

16 Fahimtar abubuwa masu kyau da Jehobah yake koya mana ba za ta gagare mu ba. A talifi na gaba, za mu tattauna ɗaya daga cikin koyarwa masu zurfi da ke Kalmar Allah, wato haikali na alama da manzo Bulus ya bayyana a wasiƙar da ya aika wa Ibraniyawa. Fatanmu shi ne nazarin wannan batun ya sa ka farin ciki sosai.

WAƘA TA 94 Muna Godiya Jehobah Don Kalmarka

a Nazarin Littafi Mai Tsarki zai sa mu yi farin ciki har iya rayuwarmu, zai sa mu amfana kuma ya sa mu yi kusa da Ubanmu na sama. A wannan talifin, za mu ga yadda za mu fahimci Kalmar Allah sosai, wato “faɗinta, da tsawonta, da girmanta, da zurfinta.”

b Ka duba talifin nan “Annabcin da Aka Yi Tun Dā da Ya Shafe Ka” a Hasumiyar Tsaro ta Yuli, 2022.

c Don ka san yadda za ka yi shiri don abubuwan da za su faru nan ba da jimawa ba, ka duba shafi na 230 na littafin nan Mulkin Allah Yana Sarauta!