Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 42

Kana “Son Yin Biyayya”?

Kana “Son Yin Biyayya”?

“Hikimar da ta fito daga wurin Allah . . . mai son yin biyayya ce.”—YAK. 3:​17, New World Translation.

WAƘA TA 101 Mu Riƙa Hidima da Haɗin Kai

ABIN DA ZA A TATTAUNA a

1. Me ya sa yake mana wuya mu yi biyayya a wasu lokuta?

 SHIN yana maka wuya ka yi biyayya a wasu lokuta? Ya yi wa Dauda wuya, shi ya sa ya yi adduꞌa ga Allah cewa: “Ka ba ni ruhun biyayya da zai riƙe ni.” (Zab. 51:12) Dauda yana ƙaunar Jehobah sosai. Amma a wasu lokuta, ya yi masa wuya ya yi biyayya. Haka ma yake da mu. Me ya sa? Na ɗaya, mu ajizai ne kuma hakan yana sa mu yi rashin biyayya. Na biyu, a kowane lokaci Shaiɗan yana ƙoƙarin sa mu yi wa Jehobah rashin biyayya kamar yadda ya yi da Hauwaꞌu. (2 Kor. 11:3) Na uku, muna rayuwa ne tare da mutanen da suke son yin rashin biyayya. Shi ya sa Littafi Mai Tsarki ya ce suna da “ruhun nan da yake zuga zuciyar mutanen da suka ƙi biyayya ga Allah.” (Afis. 2:2) Don haka, dole ne mu yi iya ƙoƙarinmu mu guji jarabar yin zunubi, da kuma matsin da Shaiɗan da mutane a duniyar nan suke mana don su sa mu yi rashin biyayya. Ƙari ga haka, dole ne mu yi iya ƙoƙarinmu mu riƙa yi wa Jehobah biyayya da waɗanda ya naɗa su yi ja-goranci.

2. Mene ne “son yin biyayya” yake nufi? (Yakub 3:17)

2 Karanta Yakub 3:17. b Allah ya sa Yakub ya rubuta cewa masu hikima suna “son yin biyayya.” Me kake gani hakan yake nufi? Yana nufin cewa mu zama masu marmari da kuma niyyar yin biyayya ga waɗanda Jehobah ya ba su iko a kanmu. Amma idan wani ya ce mu taka umurnin Jehobah, Jehobah ba zai so mu yi biyayya ba.—A. M. 4:​18-20.

3. Me ya sa a gun Jehobah, yana da muhimmanci mu yi wa masu iko biyayya?

3 Mai yiwuwa za mu fi son yi wa Jehobah biyayya maimakon ꞌyan Adam. Domin in Jehobah ya faɗi abu, ba ya kuskure. (Zab. 19:7) Amma ba haka yake da ꞌyan Adam masu iko ba, domin su ajizai ne. Duk da haka, akwai ikon da Jehobah ya ba wa iyaye da hukumomin gwamnati da kuma dattawa. (K. Mag. 6:20; 1 Tas. 5:12; 1 Bit. 2:​13, 14) Idan muka yi musu biyayya, kamar Jehobah ne muke wa biyayya. Bari mu ga yadda za mu yi biyayya ga waɗanda Jehobah ya ba wa iko, duk da cewa a wasu lokuta zai iya yi mana wuya mu bi umurnin da suka ba mu.

KA YI WA IYAYENKA BIYAYYA

4. Me ya sa matasa da yawa suke yi wa iyayensu rashin biyayya?

4 Matasa da yawa a yau, “marasa biyayya ga iyayensu” ne, kuma hakan zai iya shafan matasan da suke bauta wa Jehobah. (2 Tim. 3:​1, 2) Amma me ya sa suke rashin biyayya? Wasu suna ganin iyayensu munafukai ne, domin iyayen ba sa yin abin da suke gaya musu. Wasu kuma suna ganin abin da iyayensu suke gaya musu tsohon yayi ne, don haka, ba shi da amfani, ko kuma yana takura musu. Idan kai matashi ne, ka taɓa jin hakan? Yana yi wa matasa da yawa wuya su bi umurnin Jehobah da ya ce: “Saboda Ubangiji ku yi wa iyayenku biyayya, domin wannan shi ne daidai.” (Afis. 6:1) Mene ne zai taimaka maka ka yi hakan?

5. Kamar yadda yake a Luka 2:​46-52, me ya sa yadda Yesu ya yi wa iyayensa biyayya misali ne mai kyau sosai?

5 Yesu ne ya fi kafa misali mai kyau a wannan batun, kuma za ka iya yin koyi da shi. (1 Bit. 2:​21-24) Shi ba ya kuskure, amma iyayensa ajizai ne. Duk da haka, Yesu ya daraja iyayensa ko a lokacin da suka yi kuskure ko ba su fahimce shi ba. (Fit. 20:12) Ka ga abin da ya faru saꞌad da Yesu yake shekara 12. (Karanta Luka 2:​46-52.) Da iyayensa suke dawowa daga Urushalima, ba su lura cewa sun bar shi a baya ba. Hakkin Yusufu da Maryamu ne su tabbata cewa dukan yaransu suna cikin mutanen da za su koma gida. Amma da Yusufu da Maryamu suka samo Yesu, sai Maryamu ta ce Yesu ne ya sa su cikin wannan wahalar. Yesu zai iya nuna musu cewa ba laifinsa ba ne, amma bai yi hakan ba, ya ba su gajeriyar amsa kuma ya yi hakan cikin daraja. Ko da yake Yusufu da Maryamu ba ‘su gane mene ne yake nufi’ ba, Yesu ya “ɗinga biyayya ga iyayensa.”

6-7. Mene ne zai taimaka wa matasa su yi wa iyayensu biyayya?

6 Matasa, ya taɓa muku wuya ku yi wa iyayenku biyayya saꞌad da suka yi kuskure ko saꞌad da ba su fahimce ku ba? Idan amsar e ce, mene ne zai taimaka muku? Na ɗaya, ku yi tunanin yadda Jehobah zai ji. Littafi Mai Tsarki ya ce a duk lokacin da kuka yi wa iyayenku biyayya, “yakan faranta wa Ubangiji rai.” (Kol. 3:20) Jehobah ya san cewa a wasu lokuta iyayenku ba sa fahimtar ku, kuma sukan kafa dokokin da za su yi muku wuyar bi. Amma idan kuka yi ƙoƙarin bin dokokin nan, za ku sa shi farin ciki.

7 Na biyu, ku yi tunanin yadda iyayenku za su ji. Idan kuka yi musu biyayya, za su yi farin ciki kuma za su yarda da ku. (K. Mag. 23:​22-25) Za ku ƙulla dangantaka mai kyau da su. Wani ɗanꞌuwa daga Beljiyam mai suna Alexandre ya ce: “Da na soma bin umurnin iyayena, dangantakata da su ta daɗa yin kyau, kuma mun ƙara ƙaunar juna.” c Na uku, ku yi tunanin yadda yi wa iyayenku biyayya yanzu zai taimaka muku a nan gaba. Wani mai suna Paulo da ke zama a Barazil ya ce: “Yi wa iyayena biyayya ya taimaka min in yi wa Jehobah biyayya, da sauran mutane masu iko.” Kalmar Allah ta ba da dalili mai kyau na yi wa iyayenku biyayya. Ta ce: “Domin ka sami zaman lafiya, ka kuma yi tsawon rai a duniya.”—Afis. 6:​2, 3.

8. Me ya sa matasa da yawa suka zaɓi su yi wa iyayensu biyayya?

8 Matasa da yawa sun ga yadda yi wa iyayensu biyayya ya taimaka musu a rayuwa. Akwai wata ꞌyarꞌuwa daga Barazil mai suna Luiza. Da farko, ta kasa fahimtar dalilin da ya sa iyayenta suka ƙi barin ta ta yi amfani da waya, don yawancin saꞌanninta suna da waya. Amma ta zo ta gano cewa iyayenta sun yi hakan ne don su kāre ta. Yanzu ta ce: “Dokokin da iyayena suke kafawa ba sa takura min, amma bin su yana taimaka min domin abin da nake bukata ke nan.” Akwai wata ꞌyarꞌuwa matashiya daga Amurka mai suna Elizabeth da har yanzu, yana mata wuya ta yi wa iyayenta biyayya a wasu lokuta. Ta ce: “Idan ban fahimci ainihin abin da ya sa iyayena suka kafa wata doka ba, nakan tuna wata doka da suka kafa da ta kāre ni.” Wata ꞌyarꞌuwa mai suna Monica da take zama a Armeniya ta ce ta fi farin ciki a duk lokacin da ta yi wa iyayenta biyayya, fiye da lokacin da ta yi musu rashin biyayya.

KA YI WA “SHUGABANNIN GWAMNATI” BIYAYYA

9. Mene ne raꞌayin mutane game da bin doka?

9 Mutane da yawa sun yarda cewa ana bukatar “shugabannin gwamnati” kuma ya kamata mu yi biyayya ga wasu dokokin da suka kafa. (Rom. 13:1) Amma waɗannan mutanen su ma sukan ƙi bin doka idan suna ganin rashin adalci ne, ko idan ba sa son dokar. Alal misali biyan haraji. A wata ƙasa a Turai, mutane da yawa sun yarda cewa “ba laifi ba ne ka ƙi biyan haraji in kana ganin harajin bai dace ba.” Shi ya sa a wannan ƙasar, mutane ba sa biyan dukan harajin da gwamnati ta ce a biya.

Mene ne labarin Yusufu da Maryamu ya koya mana game da yin biyayya? (Ka duba sakin layi na 10-12) d

10. Me ya sa muke yin biyayya ko da dokar ba ta kwanta mana a rai ba?

10 Littafi Mai Tsarki ya ce gwamnatocin ꞌyan Adam suna sa mutane wahala, a ƙarƙashin ikon Shaiɗan suke, kuma nan ba da daɗewa ba, Allah zai halaka su. (Zab. 110:​5, 6; M. Wa. 8:​9, Mai Makamantu[n] Ayoyi; Luk. 4:​5, 6) Ƙari ga haka, ya gaya mana cewa duk wanda ya “ƙi yin biyayya ga shugabannin gwamnati, ya ƙi yin biyayya da abin da Allah ya kafa ne.” A yanzu, Jehobah ya ƙyale ꞌyan Adam su yi mulki a kan mu domin su sa abubuwa su tafi a kan tsari, kuma yana so mu yi musu biyayya. Saboda haka, dole ne mu ‘biya wa kowa duk abin da yake bin mu,’ wato mu biya haraji, mu daraja su, kuma mu yi musu biyayya. (Rom. 13:​1-7) Muna iya ganin cewa wata doka tana takura mana, ko ba adalci ba ne, ko kuma bin sa zai sa mu kashe kuɗi sosai. Amma muna yin biyayya domin abin da Jehobah ya ce mu yi ke nan.—A. M. 5:29.

11-12. Kamar yadda Luka 2:​1-6 suka nuna, mene ne Yusufu da Maryamu suka yi don su bi doka, kuma wane sakamako ne suka samu? (Ka kuma duba hoton.)

11 Za mu iya koyan darasi daga gun Yusufu da Maryamu, domin sun yi biyayya ga hukumomin gwamnati duk da cewa hakan bai yi musu sauƙi ba. (Karanta Luka 2:​1-6.) Saꞌad da Maryamu ta yi wata tara da juna biyu, gwamnati ta umurce su su yi wani abu mai wuya sosai. A lokacin, Augustus ne yake mulkin Daular Roma kuma ya ba da umurni cewa a ƙirga mutanen da ke Daular. Don haka, ya zama dole Yusufu da Maryamu su je Baiꞌtalami, kuma tafiyar ta kai kilomita 150. Ban da haka, za su yi ta hawa a kan tuddai da yawa. Hakika, tafiyar za ta yi musu wuya sosai, musamman ma Maryamu. Wataƙila sun damu da yadda tafiyar za ta shafi lafiyar Maryamu da kuma ɗanta. Me zai faru idan ta soma nakuɗa a hanya? Jaririn da ke cikinta shi ne Almasihu da aka yi alkawarin sa. Shin dalilan nan sun sa sun ƙi yin biyayya ga shugabannin gwamnati ne?

12 Yusufu da Maryamu ba su bar dalilan nan su hana su bin umurnin ba. Jehobah ya yi musu albarka don sun yi biyayya. Maryamu ta isa Baiꞌtalami cikin ƙoshin lafiya kuma babu abin da ya samu ɗan da ta haifa!—Mik. 5:2.

13. Ta yaya ꞌyanꞌuwanmu za su amfana idan muka yi biyayya ga gwamnati?

13 Idan mun yi biyayya ga hukumomin gwamnati, za mu amfana kuma mutane ma za su amfana. Ta yaya? Hanya ɗaya ita ce, za mu guji sakamako marar kyau da ƙin yin biyayya zai iya jawowa. Idan muka yi biyayya ga hukumomin gwamnati, za su ga cewa Shaidun Jehobah mutane ne masu biyayya. (Rom. 13:4) Misali, shekaru da yawa da suka shige, sojoji sun shiga Majamiꞌar Mulki a Najeriya suna neman waɗanda suke adawa da biyan haraji. Amma jamiꞌin da ke ja-gorantar sojojin ya gaya musu su bar Majamiꞌar Mulkin, kuma ya ce: “Shaidun Jehobah suna biyan haraji a kullum.” A duk lokacin da ka bi doka, kana ƙara sa mutanen Jehobah su yi suna mai kyau. Kuma a-kwana-a-tashi, wannan sunan zai kāre ꞌyanꞌuwanka.—Mat. 5:16.

14. Me ya taimaka ma wata ꞌyarꞌuwa ta soma yin biyayya ga gwamnati?

14 Duk da haka, a wasu lokuta zai iya mana wuya mu yi biyayya ga gwamnati. Wata ꞌyarꞌuwa a Amurka mai suna Joanna ta ce: “Ya yi min wuya sosai in yi biyayya ga gwamnati domin ta yi ma wasu a iyalina rashin adalci sosai.” Amma Joanna ta yi ƙoƙari don ta canja raꞌayinta. Ta fara da daina karanta abubuwan da ake yaɗawa a dandalin sada zumunta da ke sa mutane su ƙi jinin gwamnati. (K. Mag. 20:3) Na biyu, ta roƙi Jehobah ya taimaka mata ta dogara gare shi maimakon ta sa rai cewa za a magance matsalarta in aka yi canjin gwamnati. (Zab. 9:​9, 10) Na uku, ta karanta wasu talifofi da suka nuna cewa bai kamata mu sa hannu a harkokin siyasa ba. (Yoh. 17:16) A yanzu, Joanna ta ce tana “farin ciki kuma tana samun kwanciyar hankali,” domin tana biyayya da kuma daraja gwamnati.

KA BI UMURNIN DA ƘUNGIYAR JEHOBAH TA BAYAR

15. Me ya sa a wasu lokuta zai iya mana wuya mu bi umurnin da ƙungiyar Jehobah ta ba mu?

15 Jehobah ya umurce mu mu yi biyayya ga waɗanda suke ja-goranci a ikilisiya. (Ibran. 13:17) Ko da yake Shugabanmu Yesu Kristi kamili ne, yana amfani da ajizai a nan duniya ya yi mana ja-goranci. Zai iya yi mana wuya mu yi musu biyayya musamman idan suka ce mu yi abin da ba ma so. Akwai lokacin da aka ba wa manzo Bitrus umurni kuma bai so ya yi biyayya ba. Hakan ya faru ne saꞌad da malaꞌika ya gaya masa ya ci naman dabbar da Dokar Musa ta haramta, amma Bitrus ya ƙi har sau uku. (A. M. 10:​9-16) Me ya sa ya ƙi? Domin a ganinsa sabon umurnin bai dace ba. Bai taɓa cin naman ba. Idan ya yi ma Bitrus wuya ya bi umurnin da malaꞌika ya ba shi, tabbas, mu ma a wasu lokuta zai yi mana wuya mu bi umurnin da ꞌyanꞌuwanmu ajizai suka ba mu.

16. Ko da yake Bulus zai iya ce umurnin da aka ba shi bai dace ba, mene ne ya yi? (Ayyukan Manzanni 21:​23, 24, 26)

16 Manzo Bulus ya nuna cewa shi mai “son yin biyayya” ne, kuma ya yi hakan ko a lokacin da aka ba shi umurnin da a ganinsa bai dace ba. Kiristoci Yahudawa sun ji cewa manzo Bulus yana gaya wa mutane su “yar da Koyarwar Musa” kuma ba ya bin Dokar. (A. M. 21:21) Don haka, dattawa da ke Urushalima sun gaya wa Bulus cewa ya je haikali da maza guda huɗu kuma ya tsarkake kansa, don ya nuna cewa yana bin Dokar Musa. Amma Bulus ya san cewa Kiristoci ba sa bin Dokar Musa, kuma bai yi laifi ba. Duk da haka, Bulus ya yi biyayya ba tare da ɓata lokaci ba. “Washegari, Bulus ya ɗauki mutanen nan suka tsabtace tare.” (Karanta Ayyukan Manzanni 21:​23, 24, 26.) Yadda Bulus ya yi biyayya ya sa ꞌyanꞌuwan sun ci gaba da kasancewa da haɗin kai.—Rom. 14:​19, 21.

17. Mene ne ka koya daga abin da ya faru da ꞌyarꞌuwa Stephanie?

17 Ya yi ma wata ꞌyarꞌuwa mai suna Stephanie wuya ta amince da shawarar da ꞌyanꞌuwa da ke ja-goranci a ƙasarsu suka yanke. A lokacin, ita da maigidanta suna jin daɗin hidimar da suke yi a rukunin da ke wani yare dabam da nasu. Sai ꞌyanꞌuwa a ofishin da ke ƙasarsu suka dakatar da rukunin, kuma aka umurci maꞌauratan su koma ikilisiyar da ke yarensu. Stephanie ta ce: “Ban ji daɗi ba ko kaɗan. Hakan ya sa ni baƙin ciki sosai. Ban yarda cewa an fi bukatar mu a ikilisiyar da ake yarenmu ba.” Duk da haka, ta ce za ta bi umurnin. Ta ce: “A-kwana-a-tashi, na soma ganin amfanin umurnin da aka ba mu. Mun zama kamar iyaye ga ꞌyanꞌuwa a ikilisiyarmu waɗanda iyayensu ba sa bauta wa Jehobah. Yanzu ina nazari da wata ꞌyarꞌuwa da bai jima da aka sake maido da ita ikilisiya ba, kuma ina samun lokacin yin nawa nazarin Littafi Mai Tsarki fiye da dā. Yanzu zuciyata ba ta damu na domin na san cewa na yi iya ƙoƙarina in yi biyayya.”

18. Ta yaya muke amfana idan muka yi biyayya?

18 Za mu iya zama masu yin biyayya. Yesu ya “koyi yin biyayya ta hanyar azabar da ya sha.” (Ibran. 5:8) Kamar Yesu, mu ma mukan koyi yin biyayya saꞌad da muka shiga yanayi mai wuya. Alal misali, saꞌad da aka soma annobar korona, an umurce mu mu daina yin taro a Majamiꞌar Mulki, kuma mu daina zuwa waꞌazi gida-gida. Mai yiwuwa ya yi maka wuya ka bi umurnin, amma biyayyar da ka yi ta kāre ka. Ta sa ikilisiya ta kasance da haɗin kai, kuma Jehobah ya yi farin ciki. Hakan ya koya mana yadda za mu bi umurnan da za a ba mu a lokacin ƙunci mai girma. Yin biyayya ne zai sa mu tsira.—Ayu. 36:11.

19. Me ya sa kake so ka zama mai yin biyayya?

19 Mun koyi cewa yin biyayya yana sa mu amfana sosai. Amma ainihin dalilin da ya sa muke biyayya ga Jehobah shi ne, muna ƙaunar sa kuma muna so mu sa shi farin ciki. (1 Yoh. 5:3) Jehobah ya yi mana abubuwa da dama da ba za mu taɓa iya biyan sa ba. (Zab. 116:12) Amma za mu iya yin biyayya ga Jehobah da kuma masu iko. Yin biyayya zai nuna cewa mu masu hikima ne. Kuma masu hikima suna faranta ran Jehobah.—K. Mag. 27:11.

WAƘA TA 89 Mu Ji, Mu Yi Biyayya Don Mu Sami Albarka

a Da yake mu ajizai ne, yana mana wuya mu yi biyayya a wasu lokuta ko da wanda ya ba mu umurnin yana da ikon yin hakan. Wannan talifin zai tattauna albarkun da za mu samu idan muka yi biyayya ga iyayenmu da “shugabannin gwamnati” da kuma masu ja-goranci a ikilisiya.

b Yakub 3:17 (NWT) ta ce: “Amma hikimar da ta fito daga wurin Allah, da farko dai mai tsarki ce, saꞌan nan mai salama ce, mai sanin yakamata ce, mai son yin biyayya ce, mai yawan tausayi ce da kuma alheri, ba ta nuna bambanci, ba ta munafunci.”

c Ka duba talifin nan How Can I Talk to My Parents About Their Rules?” a Turanci, don ka ga shawarwarin da aka bayar a kan yadda za ka iya tattauna da iyayenka game da dokokin da suke maka wuyar bi.

d BAYANI A KAN HOTO: Yusufu da Maryamu sun yi biyayya ga umurnin Kaisar ta wajen zuwa Baiꞌtalami don a ƙirga su. A yau ma, Kiristoci suna yin biyayya ga umurnin da aka kafa game da tuki, da ­biyan haraji, da kuma gargaɗi da “shugabannin gwamnati” suke yi game da kiwon lafiya.