Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

1924—Shekaru Dari da Suka Shige

1924—Shekaru Dari da Suka Shige

MUJALLAR Bulletin a ta watan Janairu 1924 ta ce: “Yanzu da muka shiga sabuwar shekara, wannan lokaci ne da ya dace kowane Kirista da ya yi baftisma . . . ya nemi hanyar ƙara ƙwazo a hidimarsa.” Ɗaliban Littafi Mai Tsarki sun bi shawarar nan a shekarar, ta wurin yin waꞌazi da ƙwazo kuma a sabbin hanyoyi.

SUN SOMA YIN WAꞌAZI A REDIYO

ꞌYanꞌuwa da ke Bethel sun yi fiye da shekara guda suna gina gidan rediyo mai suna WBBR a Tsibirin Staten, da ke birnin New York. Sun fara ne da yayyanka bishiyoyin da ke wurin. Bayan haka, sai suka gina inda masu aikin za su zauna, da kuma ainihin gidan rediyon. Da suka gama ginin, sai suka soma harhaɗa kayan watsa labarai ta rediyo. Amma sun yi fama da wasu matsaloli.

Kafa wani eriya (wato antenna) na gidan rediyon ya yi musu wuya sosai. Tsawonsa ƙafa 300 ne (wato, mita 91), kuma za a ɗaura shi a tsakanin pole na katako guda biyu da tsawonsu ya kai ƙafa 200 (wato, mita 61). Da suka fara ɗaurawa, abin bai yiwu ba. Amma sun dogara ga Jehobah kuma sun sāke gwadawa. Wannan karon sun yi nasara. Wani ɗanꞌuwa mai suna Calvin Prosser, da yake cikin masu aikin ya ce: “Da a ce mun yi nasara a karo na farko, da mun yaba wa kanmu.” ꞌYanꞌuwan nan sun miƙa dukan yabo ga Jehobah, don shi ne ya sa suka yi nasara. Amma da sauran aiki.

Lokacin da ake kafa eriyar gidan rediyon WBBR

Lokacin ba a daɗe da soma amfani da gidan rediyo ba, don haka samun kayan yaɗa labarai yana da wuya. Saꞌad da wasu ꞌyanꞌuwa suke neman kayan aikin, sai suka sami wata naꞌurar yaɗa labarai da wani ya haɗa da kansa kuma suka saya. Ban da haka, maimakon su sayi sabon makarufo, sun yi amfani da wanda yake jikin tarho. Wata rana da daddare, sai ꞌyanꞌuwan suka ce bari su gwada yaɗa wani abu su gani. A watan Fabrairu ke nan. Da suka rasa me za su yaɗa, sai suka ce bari su yi waƙoƙinmu kawai. Ɗanꞌuwa Ernest Lowe ya ce da suke waƙar, sai wani abin ban dariya ya faru. Ɗanꞌuwa Judge Rutherford b ya ji waƙar da suke yi a rediyonsa a Brooklyn, da ke wajen mil 15 (wato, kilomita 25) daga inda suke, sai ya kwala musu kira.

Ya ce: “Ku daina wannan abin da kuke yi, ihu kawai kuke!” Kunya ya kama ꞌyanꞌuwan, sai suka daina nan-da-nan. Amma dai, wannan gwajin da suka yi ya tabbatar musu da cewa za su iya soma yaɗa labarai.

A ranar 24 ga Fabrairu, 1924, Ɗanꞌuwa Rutherford ya buɗe gidan rediyon, kuma ya ce za su yi amfani da shi ne wajen yaɗa bisharar da Sarki Yesu Kristi ya ce su yi. Ƙari ga haka, ya ce abin da ya sa suka buɗe gidan rediyon shi ne don su “taimaki mutane su fahimci Littafi Mai Tsarki, kuma su san irin kwanakin da muke rayuwa a ciki.”

A gefen hagu: Ɗanꞌuwa Rutherford a cikin gidan rediyonmu na farko

A gefen dama: Kayan yaɗa labarai da suke gidan rediyon

Sun yi nasara wajen yaɗa wannan shirin, kuma shi ne na farko. Bayansa an yi shekaru 33 ana amfani da gidan rediyon WBBR wajen yaɗa shirye-shiryen ƙungiyarmu.

SUN ƘARYATA SHUGABANNIN ADDINI BA TSORO

A watan Yuli 1924, Ɗaliban Littafi Mai Tsarki sun yi wani babban taro a birnin Columbus da ke jihar Ohio. Mutane sun zo taron daga duk faɗin duniya, kuma sun saurari jawabai da Larabci, da Turanci, da Faransanci, da Jamusanci, da Hellenanci, da yaren Hungari, da Italiya, da Lithuania, da Poland, da Rasha, da Ukraine, da kuma yarukan yankin Scandinavia. Ƙari ga haka, an yaɗa wasu sassan taron ta rediyo, kuma an shirya da gidan jarida da ke yankin cewa su riƙa wallafa bayanai game da taron kowace rana.

Babban taron da aka yi a 1924 a birnin Columbus, jihar Ohio

A ranar Alhamis, 24 ga Yuli, ꞌyanꞌuwa fiye da 5,000 da suka zo taron, sun fita yin waꞌazi. Sun rarraba littattafai kusan 30,000, kuma sun soma nazarin Littafi Mai Tsarki da dubban mutane. Mujallar Hasumiyar Tsaro ta ce waꞌazin da ꞌyanꞌuwa suka yi a wannan ranar ne “ya fi sa su farin ciki.”

Wani abin burgewa ya faru kuma a taron a ranar Jummaꞌa, 25 ga Yuli. Ɗanꞌuwa Rutherford ya karanta wata takarda da ta ƙaryata shugabannin addini ba tsoro. Ya ce ꞌyan siyasa, da shugabannin addini, da manyan ꞌyan kasuwa, suna hana mutane sanin gaskiya game da Mulkin Allah, ga shi ta wurin mulkin ne Allah zai yi wa mutane albarka. Ya ƙara da cewa sun yi laifi, domin suna goyon bayan Majalisar Ɗinkin Duniya ta Dā, suna cewa Allah ne yake mulkin duniya ta wurin majalisar. Ɗaliban Littafi Mai Tsarki za su gaya wa mutane wannan saƙon a waꞌazi. Hakika, sai da ƙarfin zuciya za su iya yin haka.

Daga baya, mujallar Hasumiyar Tsaro ta ce babban taron nan da aka yi a birnin Columbus ya ƙarfafa ꞌyanꞌuwan nan masu ƙwazo. Ya ba su ƙarfin zuciyar yin waꞌazi komen tsanantawa. Wani ɗanꞌuwa mai suna Leo Claus da ya je taron ya ce: “Da aka gama taron, mun yi marmarin gaya wa mutane wannan saƙo.”

Warƙar da ke ɗauke da saƙon da ya ƙaryata shugabannin coci

A watan Oktoba, Ɗaliban Littafi Mai Tsarki sun soma rarraba wata warƙa da take ɗauke da saƙon da Ɗanꞌuwa Rutherford ya karanta da ya ƙaryata shugabannin coci. An ba ma wani ɗanꞌuwa mai suna Frank Johnson yankin da zai rarraba warƙar a wani ƙaramin gari da ake kira Cleveland, a jihar Oklahoma. Bayan da ya gama rarraba wa mutane warƙar, yana bukatar ya jira wasu ꞌyanꞌuwa su zo su ɗauke shi a mota. Amma za su yi minti 20 kafin su isa wurinsa, kuma ba dama ya tsaya a inda za a yi saurin ganinsa, domin wasu mazan garin sun yi fushi kuma suna nemansa. Saboda haka, Ɗanꞌuwa Johnson ya gudu ya shiga wani coci ya ɓoye. Da yake ba kowa a ciki, sai ya ajiye warƙa guda a kowane wurin zama, kuma ya sa wasu a Littafi Mai Tsarkin da fasto yake amfani da shi. Ya yi hakan da wuri kuma ya fita. Da ya ga cewa yana da sauran lokaci, sai ya je wasu coci guda biyu. A nan ma, ya sassaka warƙoƙin kamar yadda ya yi a na farkon.

Bayan hakan sai ya ruga da gudu ya koma inda ꞌyanꞌuwan za su ɗauke shi. Ya ɓoye a bayan wani gidan mai, kar masu neman shi su kama shi. Kuma mutanen sun zo sun wuce a mota, amma ba su gan shi ba. Bayan da suka wuce, sai ꞌyanꞌuwan da Frank yake jira suka zo suka ɗauke shi suka tafi.

Ɗaya daga cikin ꞌyanꞌuwan ya ce, “Da muke wucewa, mun bi ta gaban coci guda ukun da Ɗanꞌuwa Frank ya ajiye warƙoƙinmu a ciki. Kuma mun ga mutane wajen 50 a gaban kowannensu, wasu suna karanta warƙar, wasu kuma suna nuna wa fastonsu ya gani. A gaskiya, mun tsallake rijiya da baya! Amma mun gode wa Allahnmu Jehobah da ya kiyaye mu, kuma ya ba mu hikimar yin waꞌazin nan ba tare da mun shiga cikin matsala ba.”

A WASU ƘASASHE MA SUN YI WAꞌAZI BA TSORO

Józef Krett

Ɗaliban Littafi Mai Tsarki da suke wasu ƙasashe su ma sun yi waꞌazi ba tsoro. Alal misali, a arewacin ƙasar Faransa, wani ɗanꞌuwa mai suna Józef Krett ya yi wa masu hakkar maꞌadanai waꞌazi. Kuma an shirya cewa zai yi wani jawabi mai jigo, “The Resurrection of the Dead Soon,” (wato, An Kusan Ta da Matattu). Da ake gayyatar mutane zuwa taron, wani fada ya ce wa ꞌyan cocinsa kada su je taron. Amma maimakon hakan ya hana su zuwa, mutane fiye da 5,000 sun zo taron, har da fadan karan-kansa! A taron, Ɗanꞌuwa Krett ya ce wa fadan ya zo ya kāre imaninsa, amma ya ƙi. Bayan jawabin, Ɗanꞌuwa Krett ya rarraba wa mutanen littattafan da yake da su, har sun ƙare kaf, domin mutanen suna son sanin koyarwar Kalmar Allah sosai.—Amos 8:11.

Claude Brown

A Afirka kuma, Ɗanꞌuwa Claude Brown ne ya soma waꞌazi a ƙasar Ghana, wadda ake kira Gold Coast a lokacin. Mutane da yawa a wurin sun ji koyarwar gaskiya domin ya yi jawabai da yawa kuma ya rarraba wa mutane littattafai sosai. A lokacin, wani ɗan jamiꞌa mai suna John Blankson, da ke karatu a fannin magunguna, ya je inda Ɗanꞌuwa Brown yake jawabi. Da ya ji jawabin, sai ya ga cewa wannan ita ce gaskiya. John ya ce: “Gaskiyar da na koya ta burge ni sosai, kuma na yi ta ba wa ꞌyan makarantarmu labarin abin da na ji.”

John Blankson

John ya koyi cewa Littafi Mai Tsarki bai goyi bayan koyarwar Allah-uku-cikin-ɗaya ba. Don haka, wata rana ya je wani cocin Angilika don ya yi wa fadansu tambaya game da batun. Sai fadan ya kore shi, yana cewa: “Kai ba kirista ba ne, kai Shaiɗan ne. Ka bar nan!”

Da John ya koma gida, sai ya rubuta wa fadan wasiƙa ya gayyace shi ya zo wani taro da za a yi, don su tattauna wannan batun Allah-uku-cikin-ɗaya. Sai fadan ya umurci John ya same shi a ofishin babban malamin makarantarsu. Da John ya je, sai malamin ya tambaye shi cewa da gaske ya rubuta wa fadan irin wannan wasiƙa?

Sai John ya amsa da cewa: “E na rubuta, Sir.”

Babban malamin nasu ya ba wa John takarda da abin rubutu, ya umurce shi ya rubuta wa fadan wasiƙa, ya ba shi haƙuri. Sai John ya rubuta cewa:

“Sir, malamina ya ce in rubuta maka wasiƙa in ba ka haƙuri. Zan ba ka haƙurin, amma sai ka yarda cewa kana koyar da abubuwan da ba gaskiya ba.” Da ya gama, sai ya miƙa wa malamin wasiƙar.

Da malamin ya karanta wasiƙar, ya yi mamaki sosai! Sai ya ce wa John, “Abin da za ka rubuta ke nan?”

John ya ce, “E, Sir. Gaskiya abin da zan iya rubutawa ke nan.”

Sai malamin ya ce, “To za ka bar makarantar nan. Ba yadda za a yi ka ci-gaba da zama a makarantar nan, bayan kana yi wa fadan cocin da gwamnati take goya wa baya baƙar magana.”

Sai John ya ce masa: “Amma, Sir, . . . idan ka koya mana wani abu kuma ba mu gane ba, ai muna maka tambaya, ko ba haka ba?”

Malamin ya ce: “Haka ne.”

Sai John ya ce: “Sir, abin da na yi masa ke nan. Mutumin ya zo yana koya mana abin da ke Littafi Mai Tsarki, sai na yi masa tambaya. Idan ba zai iya amsa tambayar ba, don me za a ce in ba shi haƙuri?”

Ƙarshenta, ba a kori John daga makarantar ba, duk da cewa bai ba wa fadan haƙuri ba.

SAI GABA-GABA SUKE YI

A batun abubuwan da suka faru a 1924, mujallar Hasumiyar Tsaro ta kammala da cewa: “Kamar Dauda, mu ma za mu iya cewa: ‘Kai ka ba ni ƙarfi don in yi yaƙi.’ (Zab. 18:39) Abubuwan da suka faru a shekarar nan sun ƙarfafa mu sosai, don mun ga yadda Jehobah ya taimaka mana mu cika hidimarsa. Bayinsa sun yi waꞌazin labari mai daɗin nan da farin ciki.”

A ta ƙarshen shekarar, ꞌyanꞌuwa sun soma shirin gina wani gidan rediyo. Kuma a birnin Chicago a Amurka aka gina shi. Sunan da aka ba wa sabon gidan rediyon shi ne WORD. Kuma kayan yaɗa labarai da suka yi amfani da su a wannan karon, sun fi na dā inganci, don mutane su iya jin saƙon Mulkin Allah ko da suna a wuri mai nisa sosai. Har a can yankin Kanada da ke arewacin Amerika ma ana kama wannan tashar.

A shekara ta 1925 Jehobah ya taimaki mutanensa su fahimci wasu abubuwan da ke Ruꞌuyar da Aka Yi wa Yohanna sura 12. Ƙarin hasken ya sa wasu sun daina bauta wa Jehobah. Amma ꞌyanꞌuwa da yawa sun ji daɗin bayanin da aka yi game da abubuwan da suka faru a sama, da yadda suka shafi bayin Allah a nan duniya.

a Shi ake kira Littafin Taro Don—Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu.

b A lokacin, Ɗanꞌuwa J. F. Rutherford ne yake ja-gorantar Ɗaliban Littafi Mai Tsarkin. Kuma ana kiransa Judge Rutherford. Me ya sa ake kiransa “Judge”? Domin kafin ya soma hidima a Bethel, ya taɓa yin aiki a matsayin alƙali na musamman a wani kotu da ake kira Eighth Judicial Circuit Court of Missouri.