Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 41

WAƘA TA 13 Mu Riƙa Bin Misalin Yesu

Darussa Daga Kwanaki 40 na Ƙarshe da Yesu Ya Yi a Duniya

Darussa Daga Kwanaki 40 na Ƙarshe da Yesu Ya Yi a Duniya

‘Ya yi kwana arbaꞌin, yana magana a kan alꞌamuran Mulkin Allah.’—A. M. 1:3.

ABIN DA ZA MU KOYA

Za mu ga wasu abubuwa masu muhimmanci da Yesu ya yi a kwanaki 40 na ƙarshe da ya yi a duniya, da yadda za mu yi koyi da shi.

1-2. Me ya faru saꞌad da Almajiran Yesu guda biyu suke kan hanyar zuwa Imawus?

 A RANAR 16 ga Nisan, shekara ta 33 bayan haihuwar Yesu, almajiransa suna cike da tsoro da baƙin ciki. Biyu daga cikinsu sun bar Urushalima za su je Imawus, wato wani ƙauye de ke wajen kilomita 11 daga Urushalima. Sun yi sanyin gwiwa domin an kashe Yesu Ubangijinsu. Sun ɗauka cewa Almasihu zai kawo wa Yahudawa ꞌyanci kuma ya taimaka musu a hanyoyi da dama, amma ga shi ya mutu. Suna cikin tafiya sai wani abin ban mamaki ya faru.

2 Wani mutum ya zo ya same su. Da suke kan tafiya, sai suka gaya masa mummunan abin da ya faru da Yesu. Sai mutumin ya soma gaya musu abin da ba za su taɓa mantawa ba. “Daga Koyarwar Musa har zuwa littattafan annabawa duka,” ya bayyana musu dalilin da ya sa Almasihu ya sha wahala kuma ya mutu. Da suka isa Imawus, sai suka gane cewa Yesu ne! Babu shakka, sun yi farin ciki sosai da suka ga cewa Yesu yana da rai!—Luk. 24:​13-35.

3-4. Me Yesu ya yi wa almajiransa, kuma me za mu tattauna a talifin nan? (Ayyukan Manzanni 1:3)

3 Yesu ya yi ta bayyana ga almajiransa cikin kwanaki 40 na ƙarshe da ya yi a duniya. (Karanta Ayyukan Manzanni 1:3.) A wannan lokacin, ya ƙarfafa su har sun daina jin tsoro da baƙin ciki. Sun soma farin ciki, kuma sun yi ƙarfin zuciya suna waꞌazi da kuma koyarwa a game da Mulkin Allah.

4 Akwai darussa da dama da za mu koya idan muka bincika abin da Yesu ya yi a waɗannan kwanaki 40. A talifin nan, za mu ga yadda Yesu ya yi amfani da lokacin nan don ya ƙarfafa almajiransa, ya sa su ƙara fahimtar Nassosi, kuma ya koyar da su don su iya yin wasu ayyuka masu muhimmanci. Za mu tattauna abubuwan nan ɗaya bayan ɗaya, kuma mu ga yadda za mu yi koyi da Yesu.

KA ƘARFAFA MUTANE

5. Me ya sa almajiran Yesu suke bukatar ƙarfafa?

5 Almajiran Yesu suna bukatar ƙarfafa a lokacin. Me ya sa? Domin wasu daga cikinsu sun bar gidajensu, da iyalansu, da kuma sanaꞌoꞌinsu don su bi Yesu. (Mat. 19:27) Wasu kuma sun sha wulaƙanci don sun zama mabiyan Yesu. (Yoh. 9:22) Sun gaskata cewa Yesu ne Almasihun, shi ya sa suka yi waɗannan sadaukarwa. (Mat. 16:16) Amma da aka kashe Yesu, sun ga kamar sun yi biyu babu ke nan, shi ya sa suka shiga damuwa.

6. Mene ne Yesu ya yi bayan da ya tashi daga mutuwa?

6 Yesu ya san cewa ba rashin bangaskiya ba ne ya sa almajiransa baƙin ciki ba, mutuwarsa ce. Saboda haka, rana-ranar da ya tashi daga mutuwa, ya soma ƙarfafa mabiyansa. Alal misali, ya bayyana ga Maryamu Magadaliya lokacin da take kuka a kabarinsa. (Yoh. 20:​11, 16) Ya kuma bayyana ga almajirai biyun nan da za su Imawus. Ban da haka ma, ya bayyana ga Bitrus. (Luk. 24:34) Mene ne Yesu ya koya mana? Bari mu ga abin da ya faru lokacin da ya bayyana ga Maryamu.

7. Bisa ga Yohanna 20:​11-16, mene ne Yesu ya ga Maryamu take yi da sassafe ranar 16 ga Nisan, kuma me ya yi? (Ka kuma duba hoton.)

7 Karanta Yohanna 20:​11-16. Da sassafe ranar 16 ga Nisan, wasu mata masu aminci sun je inda aka binne Yesu. (Luk. 24:​1, 10) Maryamu Magadaliya tana cikinsu. Da ta je inda aka binne Yesu kuma ta ga ba ya nan, sai ta gudu ta je ta gaya wa Bitrus da Yohanna, kuma su ukun suka dawo inda aka binne Yesu a guje. Da Bitrus da Yohanna suka ga cewa gaskiya ne, sai suka koma gida. Amma Maryamu ba ta bi su ba, ta zauna a wurin ta ci-gaba da yin kuka. Ashe Yesu yana kallon ta, ba ta sani ba. Ya ga cewa ta damu sosai kuma ya so ya ƙarfafa ta. Sai ya bayyana a gabanta, kuma ya yi wani abin da ya kwantar mata da hankali sosai. Ya yi mata magana, kuma ya ba ta saƙo na musamman ta je ta gaya wa almajiransa, cewa yana da rai.—Yoh. 20:​17, 18.

Ka yi koyi da Yesu ta wajen lura da ꞌyanꞌuwanmu da suke cikin damuwa, kuma idan da hali, ka taimaka musu (Ka duba sakin layi na 7)


8. Ta yaya za mu yi koyi da Yesu?

8 Ta yaya za mu yi koyi da Yesu? Ta wurin ƙarfafa ꞌyanꞌuwanmu su ci-gaba da bauta wa Jehobah. Mu riƙa lura don mu ga lokacin da suke cikin damuwa. Saꞌan nan mu yi ƙoƙari mu fahimce su, kuma mu ƙarfafa su. Ga abin da ya faru da wata ꞌyarꞌuwa mai suna Jocelyn. Ƙanwarta ta yi hatsari kuma ta rasu. Jocelyn ta yi watanni da yawa tana baƙin ciki. Ana haka sai wani ɗanꞌuwa da matarsa suka gayyace ta gidansu, suka saurare ta da kyau, kuma suka tabbatar mata da cewa Jehobah yana ƙaunar ta. Ta ce: “Yanayina ya sa na ji kamar na faɗi ne cikin teku, amma Jehobah ya yi amfani da ɗanꞌuwan nan da matarsa ya ceto ni. Sun taimaka mini in ci-gaba da bauta wa Jehobah.” Mu ma za mu ƙarfafa mutane idan muna sauraran su saꞌad da suke gaya mana abin da yake damunsu. Ta haka, za mu taimaka musu su ci-gaba da bauta wa Jehobah.—Rom. 12:15.

KA TAIMAKI MUTANE SU ƘARA FAHIMTAR NASSOSI

9. Wace matsala ce almajiran Yesu suka fuskanta, kuma ta yaya Yesu ya taimaka musu?

9 Almajiran Yesu sun yi imani da Kalmar Allah kuma sun yi iya ƙoƙarinsu su bi ta. (Yoh. 17:6) Duk da haka, sun kasa gane abin da ya sa aka kashe Yesu a matsayin mai laifi. Yesu ya san almajiransa suna da bangaskiya kuma suna ƙaunar Jehobah, abin da suke bukata shi ne ƙarin fahimtar Nassosi. (Luk. 9:​44, 45; Yoh. 20:9) Saboda haka, ya taimaka musu su fahimci abin da suka karanta a Kalmar Allah. Ka lura da yadda ya yi hakan saꞌad da ya bayyana ga almajirai biyun nan da za su Imawus.

10. Ta yaya Yesu ya tabbatar wa almajiransa cewa shi ne Almasihun da ake jira? (Luka 24:​18-27)

10 Karanta Luka 24:​18-27. Ka lura cewa Yesu bai yi saurin gaya musu ko shi waye ne ba. A maimakon haka, ya yi musu tambayoyi. Me ya sa? Mai yiwuwa ya so su faɗi abin da ke zuciyarsu ne. Kuma sun yi hakan. Sun ce sun yi zaton cewa Yesu zai zama sarki kuma ya cece su daga hannun Romawa. Bayan da suka faɗi raꞌayinsu, sai Yesu ya yi amfani da Nassosi don ya taimaka musu su fahimci abin da ya faru. b A ranar da yamma, Yesu ya bayyana ga sauran almajiransa kuma ya bayana musu maꞌanar annabce-annabce da dama. (Luk. 24:​33-48) Me muka koya daga wannan labarin?

11-12. (a) Wane darasi ne Yesu ya koya mana ta yadda ya yi koyarwarsa? (Ka kuma duba hotunan.) (b) Ta yaya wani ɗanꞌuwa ya taimaka wa ɗalibinsa?

11 Ta yaya za ka yi koyi da Yesu? Saꞌad da kake nazari da ɗalibanka, ka yi musu tambayoyi da za su sa su faɗi raꞌayinsu. (K. Mag. 20:5) Idan ka ji raꞌayinsu, sai ka nuna musu yadda za su nemi Nassosin da za su taimaka musu a wannan yanayin. Kada ka gaya musu abin da za su yi. A maimakon haka, ka taimaka musu su yi tunani a kan abin da Littafi Mai Tsarki ya ce, kuma su bi ƙaꞌidodinsa a rayuwarsu. Abin da aka yi ma wani ɗanꞌuwa mai suna Nortey a ƙasar Ghana ke nan.

12 Nortey yana shekara 16 saꞌad da ya soma nazarin Littafi Mai Tsarki. Ba da daɗewa ba, sai ꞌyan iyalinsa suka soma tsananta masa. Me ya taimaka masa ya ci-gaba da nazarin? Kafin wannan lokacin, ɗanꞌuwan da ke nazari da shi ya yi amfani da Matiyu sura 10 don ya nuna masa cewa za a tsananta wa Kiristoci na gaske. Nortey ya ce, “Don haka, da aka soma tsananta min, na ga tabbacin cewa wannan shi ne addini na gaskiya.” Ɗanꞌuwan ya kuma taimaka masa ya yi tunani a kan abin da ke Matiyu 10:​16, don idan zai yi magana da danginsa game da imaninsa, ya yi amfani da basira kuma ya daraja su. Bayan da ya yi baftisma, Nortey ya ce zai yi hidimar majagaba, amma babansa yana so ya je jamiꞌa. Ɗanꞌuwan da ke nazari da shi bai gaya masa abin da zai yi ba. Maimakon haka, ya yi masa tambayoyin da za su taimaka masa ya yi tunani a kan abin da Littafi Mai Tsarki ya ce. Hakan ya sa Nortey ya tsai da shawarar yin hidimar majagaba da kansa. Babansa ya kore shi daga gidansu. Duk da haka, Nortey bai ja da baya ba. Ya ce, “Na tabbata cewa wannan zaɓin da na yi, shi ne ya fi.” Mu ma idan muna taimaka wa mutane su yi tunani a kan abin da Littafi Mai Tsarki ya ce, hakan zai sa su tsaya daram a kan bangaskiyarsu.—Afis. 3:​16-19.

Ka yi koyi da Yesu ta wajen taimaka wa mutane su fahimci Nassosi da kyau (Ka duba sakin layi na 11) e


DATTAWA, KU TAIMAKA WA ꞌYANꞌUWA MAZA SU ƘWARE

13. Me Yesu ya yi don ya tabbatar da cewa an ci-gaba da yin waꞌazi bayan ya koma sama?

13 A lokacin da Yesu yake duniya, ya yi dukan abubuwan da Ubansa ya ce ya yi. (Yoh. 17:4) Amma Yesu bai yi tunani cewa in ba shi ba, ba wanda zai iya yin abin da Jehobah ya ce. Shi ya sa a shekaru uku da rabi da ya yi yana waꞌazi, ya koya wa almajiransa yadda za su yi abubuwa. Duk da cewa wataƙila wasu almajiran Yesu ba su kai shekaru 30 ba, ya danƙa musu aikin kula da tumakin Jehobah da kuma yin waꞌazi. Manzo Bulus ya ce su maza ne da Yesu ya ba wa ikilisiya “kyauta.” (Afis. 4:​8, NWT) Da Yesu yake tare da su, sun riƙe aminci kuma sun yi aiki tuƙuru. Don haka kafin ya tafi sama, ya taimaka musu su daɗa ƙwarewa a yin aikin da ya bar musu. Ta yaya ya yi hakan?

14. Me Yesu ya koya wa almajiransa kafin ya tafi sama? (Ka kuma duba hoton.)

14 Yesu ya yi wa almajiransa gargaɗin da zai taimaka musu, amma ya yi hakan cikin ƙauna. Alal misali, da ya ga cewa wasunsu suna shakka, ya gargaɗe su. (Luk. 24:​25-27; Yoh. 20:27) Ya kuma ce musu su fi mai da hankali ga kula da bayin Jehobah maimakon neman kuɗi. (Yoh. 21:15) Ya koya musu cewa kada su damu da gatan da wasu suke da shi a ƙungiyar Jehobah. (Yoh. 21:​20-22) Da Yesu ya ga cewa akwai kuskure a tunanin da suke yi game da zuwan Mulkin Allah, ya yi musu gyara. Kuma ya taimaka musu su mai da hankali ga yin waꞌazi. (A. M. 1:​6-8) Mene ne hakan ya koya wa dattawa?

Ku yi koyi da Yesu ta wajen taimaka wa ꞌyanꞌuwa maza su iya yin ayyuka a ƙungiyar Jehobah (Ka duba sakin layi na 14)


15-16. (a) Ta yaya dattawa za su yi koyi da Yesu? (b) Ta yaya Patrick ya amfana daga gargaɗin da aka yi masa?

15 Ta yaya dattawa za su yi koyi da Yesu? Ta wajen taimaka wa ꞌyanꞌuwa maza su iya yin ayyuka a ƙugiyar Jehobah, har da matasa. c Bai kamata dattawa su yi zaton cewa waɗanda ake koyar da su za su riƙa yin kome daidai ba. Suna bukatar su koyar da matasa cikin ƙauna, domin su koyi yadda za su zama masu sauƙin kai, da aminci, da masu son taimaka wa mutane.—1 Tim. 3:1; 2 Tim. 2:2; 1 Bit. 5:5.

16 Akwai wani ɗanꞌuwa mai suna Patrick da ya amfana sosai daga gargaɗin da aka yi masa. Da yake tasowa, yana yawan gasa wa mutane magana, kuma ba ya mutunta mutane, har da ꞌyanꞌuwa mata. Wani dattijo ya lura cewa Patrick yana bukatar taimako don ya canja halinsa, sai ya gargaɗe shi cikin ƙauna. Patrick ya ce, “Na ji daɗin yadda dattijon ya gaya mini gaskiya. Ina ganin ana ba wa wasu ꞌyanꞌuwa ƙarin ayyuka a ikilisiya, amma ba a ba ni, kuma hakan yana damu na. Sai da dattijon ya gargaɗe ni ne na ga cewa abin da ya kamata in mai da hankali a kai shi ne, yadda zan yi wa ꞌyanꞌuwa hidima cikin sauƙin kai, ba neman matsayi ba.” Hakan ya sa Patrick ya sami ci-gaba sosai har an naɗa shi dattijo yana shekara 23.—K. Mag. 27:9.

17. Me ya nuna cewa Yesu ya san almajiransa za su iya yin aikin da ya ba su?

17 Yesu ya ba wa almajiransa aikin yin waꞌazi da kuma koyar da mutane. (Mat. 28:20) Wataƙila almajiransa sun ga kamar ba za su iya wannan aikin ba. Amma Yesu ya san cewa za su iya. Kuma ya gaya musu cewa za su iya. Shi ya sa ya ce: “Kamar yadda Uba ya aiko ni haka ni ma na aike ku.”—Yoh. 20:21.

18. Ta yaya dattawa za su yi koyi da Yesu?

18 Ta yaya dattawa za su yi koyi da Yesu? Dattawa masu hikima sukan ba wa mutane aiki su yi. (Filib. 2:​19-22) Alal misali, zai yi kyau dattawa su sa matasa cikin masu yin shara da kuma kula da Majami’ar Mulki. Kuma idan sun ba wa ꞌyanꞌuwa aiki, su koya musu yadda za su yi aikin da kyau, kuma kada su yi shakka cewa za su iya yin sa. Wani ɗanꞌuwa mai suna Matthew da bai daɗe da zama dattijo ba, ya ji daɗin yadda dattawa suka koya masa yin ayyuka dabam-dabam a ikilisiya kuma sun yarda cewa zai yi su da kyau. Ya ce, “Idan na yi kuskure suna taimaka mini in yi gyara, kuma hakan ya sa na sami ci-gaba.” d

19. Me ya kamata ya zama niyyarmu?

19 Yesu ya yi amfani da kwanaki 40 na ƙarshe da ya yi a duniya don ya ƙarfafa almajiransa, ya fahimtar da su, kuma ya koya musu yadda za su yi wasu ayyuka masu muhimmanci. Bari mu kasance da niyyar yin koyi da Yesu sosai. (1 Bit. 2:21) Ba shakka, Yesu zai taimaka mana mu yi hakan. Domin ya ce: “Ina tare da ku kullum har ƙarshen zamani.”—Mat. 28:20.

WAƘA TA 15 Mu Yabi Ɗan Allah!

a A littattafan Linjila da ma wasu littattafai, an yi magana game da lokacin da Yesu ya bayyana ga mutane dabam-dabam. Alal misali: Maryamu Magadaliya (Yoh. 20:​11-18); wasu mata (Mat. 28:​8-10; Luk. 24:​8-11); almajiransa 2 (Luk. 24:​13-15); Bitrus (Luk. 24:34); almajiransa ban da Toma (Yoh. 20:​19-24); almajiransa tare da Toma (Yoh. 20:26); almajiransa 7 (Yoh. 21:​1, 2); almajiransa fiye da 500 (Mat. 28:16; 1 Kor. 15:6); ɗanꞌuwansa Yaƙub (1 Kor. 15:7); dukan manzaninsa (A. M. 1:4); manzaninsa kusa da Betani. (Luk. 24:​50-52) Wataƙila ma ba a rubuta wasu wuraren da ya bayyana ba.—Yoh. 21:25.

b Don ka ga annabce-annabce da aka yi game da Almasihu, ka duba talifin jw.org/ha mai jigo, “Annabce-annabce Game da Almasihu Sun Nuna Cewa Yesu Ne Almasihu Kuwa?

c A wasu lokuta, akan naɗa dattijon da ke tsakanin shekaru 25-30 ya zama mai kula da daꞌira. Amma, yana bukatar ya ƙware a aikin dattijo kafin hakan ya yiwu.

d Don samun shawarwari a kan yadda za a taimaka wa ꞌyanꞌuwa maza matasa su cancanci samun ƙarin ayyuka, ka duba Hasumiyar Tsaro ta Agusta 2018, shafi na 11-12, sakin layi na 15-17, da kuma Hasumiyar Tsaro ta 15 ga Afrilu, 2015, shafi na 3-13.

e BAYANI A KAN HOTO: Wani ɗanꞌuwa ya taimaka wa ɗalibinsa ya yi tunani a kan wasu Nassosi, kuma hakan ya sa ɗalibin ya zubar da abubuwan Kirsimati da yake da su.