TALIFIN NAZARI NA 40
WAƘA TA 30 Jehobah Ubana, Allahna da Abokina
Jehobah “Yakan Warkar da Masu Fid da Zuciya”
“Yakan warkar da masu fid da zuciya.”—ZAB. 147:3.
ABIN DA ZA MU KOYA
Jehobah yana so ya taimaka wa waɗanda suke cikin damuwa sosai. Wannan talifin zai tattauna yadda Jehobah yake taꞌazantar da mu, da kuma yadda za mu taimaka wa mutane.
1. Mene ne Jehobah yake yi wa bayinsa?
JEHOBAH yana lura da duk wani abin da ke faruwa da bayinsa. Ya san lokacin da muke farin ciki da kuma lokacin da muke cikin damuwa. (Zab. 37:18) Idan ya ga cewa muna cikin damuwa amma muna iya ƙoƙari mu bauta masa, hakan yakan burge shi! Ƙari ga haka, yana so ya taimaka mana.
2. Ta yaya Jehobah yake taimaka wa masu fid da zuciya, kuma me za mu yi don mu amfana?
2 Zabura 147:3 ta ce Jehobah ‘yakan ɗaure raunukan’ masu fid da zuciya. Ayar nan ta nuna yadda Jehobah yake taimaka wa waɗanda suke cikin damuwa sosai. Amma me za mu yi don mu amfana daga taimakon da Jehobah yake mana? Alal misali, likitan da ya ƙware zai iya taimaka wa wanda ya ji rauni ya warke. Amma don marar lafiyan ya warke, wajibi ne ya bi umurnin da likitan ya ba shi. A wannan talifin, za mu ga shawarar da Jehobah ya ba wa waɗanda suke cikin damuwa da kuma yadda za mu bi shawarar.
JEHOBAH YA CE MUNA DA DARAJA A GARE SHI
3. Me ya sa wasu suke ji kamar su ba kome ba ne?
3 Mutane da yawa a duniyar nan ba sa nuna ƙauna. Don haka, mutane da yawa suna shan wulaƙanci, kuma ana sa su ga kamar ba su da daraja. Wata ꞌyarꞌuwa mai suna Helen a ta ce: “Iyayena ba su nuna min ƙauna ba. Mahaifina azzalumi ne, kuma kullum yake gaya min cewa ba ni da wani amfani.” Wataƙila kai ma an zalunce ka, ko ana yawan zagin ka har kana ganin kamar kai ba kome ba ne. Hakan zai iya sa ka ga kamar ba wanda ya damu da kai.
4. Bisa ga Zabura 34:18, wane tabbaci ne Jehobah ya ba wa waɗanda suke cikin damuwa?
4 Ko da an wulaƙanta ka, kar ka damu domin Jehobah yana ƙaunarka kuma kana da muhimmanci a gare shi. Ya ce “yana kusa da” waɗanda suke cikin damuwa. (Karanta Zabura 34:18.) Idan kana ji kamar ba ka da wani amfani, ka tuna cewa kana da hali mai kyau, shi ya sa Jehobah ya jawo ka kusa da shi. (Yoh. 6:44) Jehobah yana ƙaunar ka sosai. Don haka, a koyaushe yana so ya taimaka maka.
5. Mene ne yadda Yesu ya bi da waɗanda ba a darajawa ya koya mana game da Jehobah?
5 Yesu ya nuna mana cewa Jehobah ya damu da waɗanda ake ganin su ba kome ba ne. Saꞌad da Yesu yake duniya, ya damu da irin mutanen nan. (Mat. 9:9-12) Alal misali, da wata mata da take fama da cuta mai tsanani ta zo ta taɓa rigarsa don ta sami lafiya, Yesu ya ƙarfafa ta kuma ya yaba mata don irin bangaskiyar da ta nuna. (Mar. 5:25-34) Yesu yana koyi da Ubansa ne. (Yoh. 14:9) Wannan ya nuna cewa Jehobah yana ɗaukan ka da muhimmanci sosai, kuma yana lura da irin ƙaunar da kake masa, da bangaskiyarka da dai sauran su.
6. Me zai taimaka maka idan kana ganin kamar ba ka da amfani?
6 Me zai taimaka maka idan kana ganin kamar ba ka da amfani? Ka karanta ayoyin da suke nuna cewa Jehobah yana ƙaunarka kuma ka yi tunani a kansu. b (Zab. 94:19) Kada ka riƙa gwada kanka da wasu mutane kuma kar ka mai da hankali a kan abin da ba za ka iya yi ba. Jehobah ba ya son ka yi abin da ya fi ƙarfinka. (Zab. 103:13, 14) Idan kuma an taɓa cin zarafin ka, ba laifin ka ba ne. Ka tuna cewa wanda ya yi laifi ne Jehobah zai hukunta, ba wanda aka yi ma laifin ba. (1 Bit. 3:12) An taɓa cin zarafin wata mai suna Sandra. Kuma ga abin da ta ce: “Ina roƙon Jehobah a kullum ya taimaka min in riƙa ganin kaina kamar yadda yake gani na.”
7. Ta yaya abubuwan da muka fuskanta za su taimaka mana a bautarmu ga Jehobah?
7 Ka riƙa tuna cewa Jehobah zai iya taimaka ma wasu ta wurin ka. Ya ba ka damar yin aiki tare da shi, ta wurin yin waꞌazi. (1 Kor. 3:9) Ba mamaki abubuwan da ka yi fama da su a rayuwa sun sa kana saurin fahimtar yadda mutane suke ji, kuma kana tausaya musu. Don haka, za ka iya taimaka wa mutane sosai. An taimaka wa Helen da aka ambata ɗazu, kuma yanzu ita ma tana taimaka ma wasu. Ta ce: “A dā nakan ga kamar ba ni da amfani amma Jehobah ya nuna min cewa yana ƙauna ta, kuma yana taimaka ma wasu ta wurina.” Yanzu Helen tana hidimar majagaba da farin ciki.
JEHOBAH YANA SO MU SAN CEWA YA YAFE MANA
8. Mene ne Jehobah ya gaya mana a Ishaya 1:18?
8 Wasu bayin Jehobah suna damuwa sosai don zunubin da suka yi, wataƙila kafin su yi baftisma ko bayan haka. Amma zai dace mu tuna cewa Jehobah yana ƙaunarmu sosai kuma ya ba da ɗansa don ya iya yafe zunubanmu. Yana so mu amince da kyautar nan. Jehobah ya tabbatar mana cewa bayan mun “shirya tsakaninmu” c da shi, yana yafe mana kwatakwata. (Karanta Ishaya 1:18.) Muna godiya cewa idan Jehobah ya yafe mana, yakan manta da laifin da muka yi masa! Abin farin cikin shi ne, ba ya manta da ayyukan kirki da muka yi.—Zab. 103:9, 12; Ibran. 6:10.
9. Me ya sa bai kamata mu ci-gaba da damuwa a kan zunuban da muka yi a dā ba?
9 Idan abin da ka yi a dā yana damun ka, ka yi ƙoƙari ka mai da hankali a kan abin da kake yi yanzu, da abin da za ka iya yi a nan gaba. Abin da manzo Bulus ya yi ke nan. Ya yi nadama don a dā ya tsananta wa Kiristoci sosai, amma ya san cewa Jehobah ya yafe masa. (1 Tim. 1:12-15) Shin, ya ci-gaba da yin tunani a kan kurakuren da ya yi a dā ne? Aꞌa bai yi hakan ba, kamar yadda bai ci-gaba da tunani a kan tsohon matsayinsa na Ba-farisi ba. (Filib. 3:4-8, 13-15) A maimakon haka, manzo Bulus ya mai da hankali ga yin hidimarsa da ƙwazo da kuma ladan da zai samu. Kai ma ba za ka iya canja abin da ya riga ya wuce ba. Amma za ka iya yin abin da zai faranta ran Jehobah a yanzu, kuma ka sa ran samun ladan da ya maka alkawarinsa.
10. Me zai taimaka mana idan zunubin da muka yi ya shafi wasu?
10 Me zai taimaka idan zunubin da ka yi ya shafi wasu, kuma yana damunka? Ka yi ƙoƙari ka gyara lamarin, sai ka ba su haƙuri. (2 Kor. 7:11) Ka roƙi Jehobah ya taimaki waɗanda zunubinka ya shafa. Jehobah zai iya taimaka wa dukanku ku jimre kuma ku sami kwanciyar hankali.
11. Me muka koya daga labarin Yunana? (Ka kuma duba hoton.)
11 Ka ɗauki darasi daga kuskuren da ka yi, kuma ka amince da duk wani aikin da Jehobah ya ba ka. Ka tuna da labarin annabi Yunana. Jehobah ya aike shi ya je Nineba, amma ya gudu ya je wani wuri dabam. Jehobah ya yi ma Yunana horo, kuma ya ɗauki darasi. (Yona 1:1-4, 15-17; 2:7-10) Jehobah bai ƙi shi don ya yi hakan ba. Amma ya sake ba shi dama ya je Nineba, kuma ba tare da ɓata lokaci ba, Yunana ya je. Duk da cewa Yunana ya yi da-na-sanin laifin da ya yi, ya yarda ya yi aikin da Jehobah ya ba shi.—Yona 3:1-3.
JEHOBAH YANA TAꞌAZANTAR DA MU TA WAJEN RUHU MAI TSARKI
12. Ta yaya Jehobah yake ba mu salamarsa idan muna cikin damuwa? (Filibiyawa 4:6, 7)
12 Idan wani mugun abu ya faru da mu, Jehobah yakan taꞌazantar da mu ta wajen ruhunsa mai tsarki. Abin da ya yi wa Ɗanꞌuwa Ron da matarsa Carol ke nan. Ɗansu ya kashe kansa. Sun ce: “Wannan shi ne abu mafi muni da ya taɓa faruwa da mu. Sau da yawa ba ma iya barci da dare. Idan hakan ya faru mukan yi adduꞌa, kuma Jehobah yana ba mu salamarsa kamar yadda ya ce a Filibiyawa 4:6, 7.” (Karanta.) Idan akwai abin da ke ci maka tuwo a ƙwarya, ka yi ta yin adduꞌa kuma ka gaya ma Jehobah kome-da-kome. (Zab. 86:3; 88:1) Ka roƙe shi ya ba ka ruhunsa mai tsarki. Ba zai taɓa yin watsi da kai ba.—Luk. 11:9-13.
13. Ta yaya ruhu mai tsarki zai taimaka maka ka ci-gaba da bauta wa Jehobah da aminci? (Afisawa 3:16)
13 Shin, akwai mummunan abin da ya same ka kwanan nan da ya sa ka sanyin gwiwa? Ruhu mai tsarki zai iya sa ka sami ƙarfin ci-gaba da bauta wa Jehobah da aminci. (Karanta Afisawa 3:16.) Ga abin da ya faru da wata ꞌyarꞌuwa mai suna Flora. Ita da maigidanta masu waꞌazi a ƙasar waje ne. Suna kan hidimarsu, sai maigidanta ya ci amanarta kuma suka kashe aurensu. Ta ce: “Abin da ya yi ya dame ni sosai har na rikice. Na roƙi Jehobah ya ba ni ruhunsa don in iya jimrewa. Jehobah ya ƙarfafa ni har na iya na jimre wannan yanayin da ya yi kamar ya fi ƙarfina.” Taimakon da Jehobah ya yi wa Flora ya sa ta ƙara dogara gare shi, kuma ta tabbata cewa zai taimaka mata a kowane hali. Ta ƙara da cewa: “Kamar marubucin Zabura 119:32 ni ma zan ce: ‘Da ƙwazo nake bin hanyar umarnanka, gama ka ƙara mini ganewa.’”
14. Ban da adduꞌa, me ya kamata mu yi don mu sami ruhu mai tsarki?
14 Me ya kamata ka yi bayan ka roƙi Jehobah ya ba ka ruhu mai tsarki? Ka yi ayyukan da za su sa ka ƙara samun ruhu mai tsarki, wato ayyuka kamar zuwa taro da yin waꞌazi. Ka riƙa karanta Littafi Mai Tsarki kowace rana, hakan zai sa ka yi ta tunani a kan abubuwa masu kyau. (Filib. 4:8, 9) Yayin da kake karatun, ka mai da hankali ga labaran mutanen da suka yi fama da matsaloli, kuma ka yi tunani a kan yadda Jehobah ya taimaka musu. Sandra, da aka ambata a baya, ta yi fama da matsaloli iri-iri. Ga abin da ta ce: “Labarin Yusufu ne ya fi ƙarfafa ni. Duk da cewa ya sha wuya kuma an yi masa rashin adalci, ya ci-gaba da bauta wa Jehobah da aminci.”—Far. 39:21-23.
JEHOBAH YANA ƘARFAFA MU TA WAJEN ꞌYANꞌUWANMU
15. Su waye ne za su iya ƙarfafa mu, kuma ta yaya suke taꞌazantar da mu? (Ka kuma duba hoton.)
15 Idan muna cikin yanayi mai wuya, ꞌyanꞌuwanmu a ikilisiya za su iya “zama abin taꞌaziyya a gare” mu. (Kol. 4:11) Jehobah yana nuna mana ƙauna ta wajen ꞌyanꞌuwanmu maza da mata. Idan muna cikin damuwa sukan saurare mu, su tausaya mana, kuma hakan yana ƙarfafa mu. Wani lokaci sukan karanta mana wata aya mai ban-ƙarfafa, ko su yi adduꞌa tare da mu. d (Rom. 15:4) ꞌYanꞌuwanmu za su iya tuna mana da raꞌayin Jehobah game da wani batu, kuma hakan zai iya kwantar mana da hankali. Za su iya taimaka mana ta wurin ba mu abin da muke bukata, kamar abinci da dai sauransu.
16. Wani lokaci, me muke bukatar mu yi don ꞌyanꞌuwa su taimaka mana?
16 Wani lokaci sai mun nemi taimakon ꞌyanꞌuwanmu ne za su taimaka mana. ꞌYanꞌuwa suna ƙaunarmu kuma suna so su taimaka mana. (K. Mag. 17:17) Amma wataƙila ba su san damuwarmu ko abin da muke bukata ba. (K. Mag. 14:10) Don haka, idan kana cikin damuwa, zai yi kyau ka gaya wa ꞌyanꞌuwan da suka manyanta. Kuma ka gaya musu abin da kake bukata. Za ka iya gaya ma wani dattijo ko dattawa biyu da ka saba da su. Wasu ꞌyanꞌuwa mata kuma sukan sami ƙarfafa sosai idan suka gaya ma wata ꞌyarꞌuwar da ta manyanta damuwarsu.
17. Me zai iya hana mu samun ƙarfafa daga ꞌyanꞌuwanmu, kuma ta yaya za mu magance wannan matsalar?
17 Ka guji yawan zama kai kaɗai. Wani lokaci ba za ka so yin magana da kowa ba don damuwar da kake ciki. Wani lokaci kuma ꞌyanꞌuwa ba za su fahimce ka ba, ko su yi maganar da bai kamata ba. (Yak. 3:2) Amma kada ka bar abubuwan nan su sa ka guji ꞌyanꞌuwa, don Jehobah zai iya ƙarfafa ka ta wajen su. Wani dattijo mai suna Gavin da ke fama da ciwon damuwa ya ce: “A wasu lokuta, ba na so in yi hira ko in kasance tare da abokai na.” Duk da haka, Gavin yakan yi ƙoƙari ya kasance tare da ꞌyanꞌuwa, kuma yakan sami ƙarfafa. Wata ꞌyarꞌuwa mai suna Amy ta ce: “Abubuwan da suka faru da ni sun sa yana min wuya in yarda da mutum. Amma ina iya ƙoƙarina in ƙaunaci ꞌyanꞌuwa kuma in yarda da su kamar yadda Jehobah yake yi. Yin hakan yana sa ni farin ciki kuma na san cewa yana sa Jehobah farin ciki.”
ALKAWARIN DA JEHOBAH YA YI MANA ZAI IYA ƘARFAFA MU
18. Mene ne Jehobah zai yi mana a nan gaba, kuma me za mu yi don mu sami ƙarfafa a yanzu?
18 Nan ba da daɗewa ba Jehobah zai cire duk wani abin da yake damunmu. (R. Yar. 21:3, 4) Kuma a lokacin, tunanin wahalolin da muka sha ma ba zai zo zuciyarmu ba. (Isha. 65:17) Kamar yadda muka gani, ko a yanzu ma Jehobah yana kula da mu idan muna cikin damuwa. Mun ga hanyoyi da dama da Jehobah yake ƙarfafa mu. Don haka, kada ka bar wata damar samun ƙarfafa ta wuce ka. A koyaushe, ka tuna cewa Jehobah ‘ne mai lura da kai.’—1 Bit. 5:7.
WAƘA TA 7 Jehobah Ne Ƙarfinmu
a An canja sunayen.
b Ka duba akwatin nan, “ Kana da muhimmanci a wurin Jehobah.”
c Idan muna so mu “shirya tsakaninmu” da Jehobah, wajibi ne mu tuba ta wajen roƙon sa ya gafarta mana zunubanmu kuma mu daina abin da muke yi da bai dace ba. Idan mun yi zunubi mai tsanani, muna bukatar mu nemi taimakon dattawa.—Yak. 5:14, 15.