Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 42

WAƘA TA 103 Jehobah Ya Yi Tanadin Makiyaya

Mu Yi Godiya don Mazan da Aka Ba Mu Kyauta

Mu Yi Godiya don Mazan da Aka Ba Mu Kyauta

“Saꞌad da ya haura, ya . . . ba da maza kyauta.”AFIS. 4:​8, NWT.

ABIN DA ZA MU KOYA

Za mu ga yadda bayi masu hidima, da dattawa, da masu kula da daꞌira suke taimaka mana, da kuma yadda za mu nuna godiya don abin da suke yi.

1. Ka ambaci wasu abubuwan da Yesu ya yi mana?

 BABU wani mutum da ya kai Yesu yin alheri. Saꞌad da yake duniya, ya yi amfani da ikonsa sosai wajen yin abubuwan ban-mamaki don ya taimaki mutane. (Luk. 9:​12-17) Kuma kyauta mafi girma da ya bayar shi ne ransa, da ya bayar dominmu. (Yoh. 15:13) Har yau, Yesu yana kan yi mana alheri. Ya roƙi Jehobah ya ba mu ruhunsa don ya koyar da mu kuma ya ƙarfafa mu, kamar yadda ya yi alkawari. (Yoh. 14:​16, 17; 16:13) Ƙari ga haka, ta wurin taron ikilisiya da muke zuwa a yau, Yesu yana koyar da mu don mu iya yin waꞌazi a dukan duniya.—Mat. 28:​18-20.

2. Su waye ne suke cikin mazan da Afisawa 4:​7, 8 suka ambata?

2 Akwai wani abin alheri kuma da Yesu ya yi mana. Allah ya sa manzo Bulus ya rubuta cewa da Yesu ya je sama, ya “ba da maza kyauta.” (Karanta Afisawa 4:​7, 8. a) Bulus ya bayyana cewa Yesu ya ba da mazan nan ne don su taimaka ma ikilisiya a hanyoyi da dama. (Afis. 1:​22, 23; 4:​11-13) A yau mazan da aka ba mu sun haɗa da bayi masu hidima, da dattawa, da masu kula da daꞌira. b ꞌYanꞌuwan nan ajizai ne, don haka wani lokaci sukan yi kuskure. (Yak. 3:2) Duk da haka, Yesu yana taimaka mana ta wurinsu.

3. Ka kwatanta yadda za mu taimaka wa mazan da aka ba mu su cika aikinsu.

3 Yesu ya ba wa mazan nan aikin ƙarfafa waɗanda suke cikin ikilisiya. (Afis. 4:12) Kuma dukanmu za mu iya taimaka musu su cika wannan aiki mai muhimmanci da aka ba su. Za mu iya kwatanta hakan da yadda ake gina Majami’ar Mulki. Wasu ne suke yin ainihin ginin. Wasu kuma sukan taimaka ta wurin dafa abinci, da kai-da-kawowa, da dai sauransu. Mu ma za mu iya taimaka ma bayi masu hidima da dattawa da masu kula da daꞌira su yi aikinsu, ta furucinmu da ayyukanmu. Bari mu ga yadda muke amfana don ayyukan da suke yi, da kuma yadda za mu nuna godiyarmu gare su, da wanda ya ba mu su, wato Yesu.

BAYI MASU HIDIMA SUNA TAIMAKON IKILISIYA

4. Waɗanne ayyuka ne bayi masu hidima suka yi a lokacin Kiristoci na farko?

4 A lokacin Kiristoci na farko, an naɗa bayi masu hidima. (1 Tim. 3:8) Akwai alama cewa su ne manzo Bulus ya ce da su “masu taimako.” (1 Kor. 12:28) Hakan ya nuna cewa bayi masu hidima a dā sun yi ayyuka da dama masu muhimmanci, don dattawa su samu damar yin koyarwa da kuma ƙarfafa ꞌyanꞌuwa. Alal misali, wataƙila bayi masu hidima sun taimaka wajen kofan Nassosi, ko wajen sayan kayan rubutun.

5. A waɗanne hanyoyi ne bayi masu hidima suke taimakawa a ikilisiyoyinmu?

5 Ka yi tunani a kan hanyoyi masu muhimmanci da bayi masu hidima suke taimakawa a ikilisiyarku. (1 Bit. 4:10) Akan ba su aikin kula da kuɗaɗe a ikilisiya, da shirya yankin da za a yi waꞌazi, da yin odar littattafai, da kula da naꞌurorin sauti da bidiyo, da yin aikin atenda, da kuma taimakawa wajen kula da Majami’ar Mulki. Duka ayyukan nan suna da muhimmanci sosai, domin su suke sa kome ya tafi sumul a ikilisiya. (1 Kor. 14:40) Ƙari ga haka, wasu bayi masu hidima suna yin aiki a taron Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu, kuma suna yin jawabai ga jamaꞌa. Za a iya sa bawa mai hidima ya zama mataimakin mai kula da rukunin masu waꞌazi. Kuma wani lokaci, dattijo zai iya zuwa ziyarar ƙarfafa tare da bawa mai hidima.

6. Me ya sa muke godiya sosai don aikin da bayi masu hidima suke yi?

6 Wane amfani muke samuwa don ayyukan da bayi masu hidima suke yi? Wata ꞌyarꞌuwa mai suna Beberly c a ƙasar Bolibiya ta ce: “Bayi masu hidima suna sa in ji daɗin taro sosai. Aikin da suke yi ne ya sa nake iya yin waƙa, in yi kalami, in saurari jawabai, kuma in iya kallon bidiyoyi da hotuna. Suna tabbatar da tsaron ꞌyanꞌuwa da suke taron, kuma suna kula da waɗanda suke jin taron ta naꞌurorinsu. Idan aka tashi taro, sukan taimaka wajen yin shara, da ƙirga kuɗaɗe, kuma suna tabbatar da cewa mun sami littattafan da muke bukata. Ina alfahari da su!” Wata kuma mai suna Leslie a Kwalambiya, wadda maigidanta dattijo ne, ta ce: “Maigidana yana bukatar taimakon bayi masu hidima wajen yin ayyuka da dama. In ba don su ba, aiki zai yi masa yawa. Ina musu godiya sosai don ƙwazonsu da yadda suke son taimaka wa ikilisiya.” Ba mamaki kai ma haka kake ji game da ꞌyanꞌuwan nan.—1 Tim. 3:13.

7. Ta yaya za mu nuna cewa muna godiya don bayi masu hidima da suke ikilisiyarmu? (Ka kuma duba hoton.)

7 Muna jin daɗin ayyukan da bayi masu hidima suke yi, amma Littafi Mai Tsarki ya ƙarfafa mu mu nuna godiyarmu. (Kol. 3:15) Wani dattijo mai suna Kristofer a ƙasar Finlan, ya bayyana yadda yake nuna godiyarsa. Ya ce: “Nakan yi rubutu a kati in tura ma wani bawa mai hidima, ko in tura masa saƙon tes. Nakan rubuta wata nassi kuma in gaya masa abin da ya yi da ya ƙarfafa ni. Ko in gaya masa abin da ya sa nake jin daɗin aikin da yake yi a ikilisiya.” Wani ɗanꞌuwa mai suna Pascal da matarsa Jael, da suke zama a ƙasar New Caledonia, sukan yi adduꞌa musamman don bayi masu hidima. Pascal ya ce, “Kwanan nan, muna yin adduꞌa sosai a madadin bayi masu hidima da ke ikilisiyarmu. Muna gode wa Jehobah da ya ba mu su, kuma muna roƙonsa ya taimaka musu.” Jehobah yakan amsa irin adduꞌoꞌin nan, kuma dukan ikilisiya sukan amfana.—2 Kor. 1:11.

DATTAWA SUNA ‘FAMA DA AIKI A CIKINMU’

8. Me ya sa manzo Bulus ya ce dattawa a lokacin Kiristoci na farko sun yi “fama da aiki”? (1 Tasalonikawa 5:​12, 13)

8 A lokacin Kiristoci na farko, dattawa sun yi aiki tuƙuru a ikilisiya. (Karanta 1 Tasalonikawa 5:​12, 13; 1 Tim. 5:17) Su ne suke yin ja-goranci, suna gudanar da taron ikilisiya da kuma yanke shawarwari. Suna yi wa ꞌyanꞌuwansu “gargaɗi” cikin ƙauna, don su ci-gaba da riƙe imaninsu. (1 Tas. 2:​11, 12; 2 Tim. 4:2) Ban da haka, dattawa a ƙarni na farko sun yi aiki sosai don su ciyar da iyalansu kuma su ci-gaba da yin kusa da Jehobah.—1 Tim. 3:​2, 4; Tit. 1:​6-9.

9. Ka ambaci wasu ayyukan da dattawa suke yi a yau?

9 A yau ma, dattawa suna aiki sosai. Su masu waꞌazi ne. (2 Tim. 4:5) Suna kafa wa ꞌyanꞌuwa misali mai kyau ta wajen yin waꞌazi da ƙwazo. Su ne suke shirya yadda za a yi waꞌazi a yankin ikilisiyarsu, kuma suna koya mana yadda za mu yi waꞌazi da kyau. Ƙari ga haka, suna yin shariꞌa a ikilisiya, kuma ba sa nuna bambanci. Idan wani a ikilisiya ya yi zunubi mai tsanani, dattawa sukan yi iya ƙoƙarinsu su taimake shi ya gyara dangantakarsa da Jehobah. Kuma suna iya ƙoƙarinsu su sa ikilisiya ta kasance da tsabta. (1 Kor. 5:​12, 13; Gal. 6:1) Aiki mafi muhimmanci da dattawa suke yi shi ne aikin makiyaya. (1 Bit. 5:​1-3) Sukan yi jawabai masu ban ƙarfafa, suna ƙoƙari su san kowa a ikilisiya, kuma suna yin ziyarar ƙarfafa. Wasu dattawa kuma suna yin aikin gini, da yin gyare-gyare a Majami’ar Mulki. Su suke yin shirye-shirye don taron yanki, wasu suna Kwamitin Hulɗa da Asibitoci da Rukunin Ziyartar Majiyyata, da dai wasu ayyuka da dama. A gaskiya, dattawa suna yin aiki sosai a madadinmu!

10. Me ya sa muke godiya don dattawan da Jehobah ya ba mu?

10 Jehobah ya ce makiyayan nan za su kula da mu sosai, kuma ba za mu ‘ƙara jin tsoro ko mu firgita ba.’ (Irm. 23:4) Wata ꞌyarꞌuwa mai suna Johanna a ƙasar Finlan, ta shaida hakan lokacin da mahaifiyarta ta yi rashin lafiya sosai. Johanna ta ce: “Ni ba mai son gaya wa mutane abin da yake damuna ba ne. Amma wani dattijo da ban san shi sosai ba, ya saurare ni da haƙuri, ya yi adduꞌa da ni, kuma ya tabbatar min da cewa Jehobah yana ƙauna ta. Ba zan iya tuna abin da ya gaya min ba, amma na tuna cewa hankalina ya kwanta. A gaskiya Jehobah ne ya aiko shi ya zo daidai lokacin da nake bukatar ƙarfafa.” Kai kuma fa, ta yaya dattawan ikilisiyarku suka taɓa taimaka maka?

11. Ta yaya za mu nuna godiyarmu ga dattawa? (Ka kuma duba hoton.)

11 Jehobah yana so mu nuna godiyarmu ga dattawa “saboda aikinsu.” (1 Tas. 5:​12, 13) Wata mai suna Henrietta a ƙasar Finlan ta ce: “A koyaushe, dattawa suna son taimaka wa ꞌyanꞌuwa. Amma hakan ba ya nufin cewa sun fi sauran mutane ƙarfi da kuma samun lokaci. Kuma hakan ba ya nufin cewa ba su da matsaloli. Don in nuna godiyata, nakan gaya wa dattijo cewa: ‘A gaskiya ɗanꞌuwa, kai dattijo mai kirki ne.’” Wata kuma a ƙasar Türkiye d mai suna Sera ta ce: “Dattawa suna bukatar a ƙarfafa su. Hakan zai sa su ci-gaba da yin aikinsu. Za mu iya rubuta musu saƙon godiya a kati, ko mu kira su su zo mu ci abinci tare, ko mu fita waꞌazi tare da su.” Akwai wani dattijo da yake burge ka don aikin da yake yi a ikilisiya? Ka yi ƙoƙari ka nuna masa cewa kana godiya.—1 Kor. 16:18.

Akwai abubuwa da yawa da za ka iya yi don ka ƙarfafa mazan nan su ci-gaba da yin aikinsu (Ka duba sakin layi na 7, 11, 15)


MASU KULA DA DAꞌIRA SUNA ƘARFAFA MU

12. Su wane ne kuma Yesu ya yi amfani da su ya ƙarfafa ꞌyanꞌuwa a lokacin Kiristoci na farko? (1 Tasalonikawa 2:​7, 8)

12 Yesu ya ba ma wasu maza aikin taimaka wa ikilisiya a wata hanya dabam. Shi ne ya sa dattawan da suke Urushalima su aiki Bulus, da Barnaba, da kuma wasu, a matsayin masu kai wa ikilisiyoyi ziyara. (A. M. 11:22) Me ya sa? Domin su ƙarfafa ꞌyanꞌuwa, kamar yadda dattawa da bayi masu hidima suke yi. (A. M. 15:​40, 41) ꞌYanꞌuwan nan sun yi sadaukarwa sosai. Akwai ma lokutan da suka sa ransu a cikin haɗari don su koyar da ꞌyanꞌuwa kuma su ƙarfafa su.—Karanta 1 Tasalonikawa 2:​7, 8.

13. Ka ba da misalin ayyukan da mai kula da daꞌira yake yi?

13 A zamaninmu, masu kula da daꞌira suna tafiye-tafiye a kullum. Wasu sukan yi tafiya mai nisa sosai kafin su kai wata ikilisiya. Kuma kowane mako, mai kula da daꞌira yakan yi jawabai da dama, ya kai ziyarar ƙarfafa, ya gudanar da taron majagaba, da taron dattawa, da kuma taron fita waꞌazi. Yakan shirya jawabai, kuma ya tsara ayyukan da za a yi a taron daꞌira da kuma taron yanki. Yana koyarwa a makarantar majagaba, kuma ya shirya taro na musamman da majagaban da suke daꞌirar gabaki-ɗaya. Ban da haka, yakan yi wasu ayyukan da rashen ofishinmu suke ba shi, kuma wani lokaci ana bukatar sa ya yi su da gaggawa.

14. Me ya sa muke ƙaunar masu kula da daꞌira?

14 Ta yaya ikilisiyoyi suke amfana daga aikin da masu kula da daꞌira suke yi? Wani ɗanꞌuwa daga Türkiye ya ce: “Zuwan mai kula da daꞌira yakan sa in ƙara ƙwazo wajen taimaka wa ꞌyanꞌuwa da ke ikilisiyarmu. Na haɗu da masu kula da daꞌira dabam-dabam, kuma duk da yawan ayyukan da suke yi, a koyaushe sukan ba ni lokacinsu kuma su saurare ni.” ꞌYarꞌuwa Johanna da muka ambata a baya ta taɓa yin waꞌazi tare da wani mai kula da daꞌira. Ranar ba su sami kowa a gida ba. Amma ta ce: “Duk da haka, ba zan taɓa mantawa da wannan ranar ba. Don a lokacin bai daɗe ba da ꞌyanꞌuwana mata biyu suka ƙaura zuwa wani yanki. Na yi kewarsu sosai. Mai kula da daꞌirar ya ƙarfafa ni, kuma ya bayyana min cewa wani lokaci ba za mu iya kasancewa tare da ꞌyan iyalinmu ko abokanmu ba, amma a aljanna, za mu sami damar kasancewa tare da su yadda muka ga dama.” Ba shakka, dukanmu muna ƙaunar masu kula da daꞌira don yadda suke taimaka mana.—A. M. 20:37–21:1.

15. (a) Ta ya za mu nuna godiyarmu don masu kula da daꞌira kamar yadda 3 Yohanna 5-8 suka ce? (Ka kuma duba hoton.) (b) Me ya sa ya kamata mu gode wa matan ꞌyanꞌuwa da suke yin aiki sosai a ikilisiya, kuma ta yaya za mu yi haka? (Ka duba akwatin da ya ce, “ Ku Tuna da Matansu.”)

15 Manzo Yohanna ya ƙarfafa Gayus ya karɓi ꞌyanꞌuwan da suke kawo ziyara hannu bibbiyu, kuma ya “ci gaba da taimakon irin mutanen nan a tafiye-tafiyensu, kamar yadda ya cancanci yin hidima ga Allah.” (Karanta 3 Yohanna 5-8.) Za mu iya yin haka ta wurin kiran mai kula da daꞌira ya zo mu ci abinci tare, kuma mu fita yin waꞌazi a makon ziyarar. ꞌYarꞌuwa Leslie da muka ambata a baya ta ce: “Nakan roƙi Jehobah ya biya bukatun masu kula da daꞌira. Ni da maigidana mukan rubuta musu wasiƙa mu gaya musu yadda suka ƙarfafa mu saꞌad da suka ziyarce mu.” Mu tuna cewa masu kula da daꞌira su ma suna fama kamar mu. A wasu lokuta, sukan yi fama da rashin lafiya ko tsoro, har ma da sanyin gwiwa. Wataƙila idan ka gaya musu abin da zai ƙarfafa su, ko ka yi musu kyauta, za su yi murna sosai!—K. Mag. 12:25.

 

MUNA BUKATAR ƘARIN MAZA DA ZA SU YI AIKI

16. Bisa ga Karin Magana 3:​27, waɗanne tambayoyi ne zai yi kyau ꞌyanꞌuwa maza su yi tunani a kai?

16 A koꞌina a duniya, akwai bukatar ꞌyanꞌuwa maza da za su yi ayyuka a ikilisiya. Idan kai namiji ne da ya yi baftisma, za ka iya taimakawa? (Karanta Karin Magana 3:27.) Za ka so ka zama bawa mai hidima? Idan kuma kai bawa mai hidima ne, za ka iya ƙara ƙoƙari don ka zama dattijo? e Za ka iya yin canje-canjen da kake bukata don ka iya cika fom na zuwa Makarantar Masu Yaɗa Bisharar Mulki? Makarantar za ta horar da kai sosai don Yesu ya iya yin amfani da kai a hanya ta musamman a ƙungiyar Jehobah. Idan ma kana ganin kamar ba za ka iya ba, ka roƙi Jehobah ya taimake ka. Ka roƙe shi ya ba ka ruhunsa don ka iya yin duk wani aikin da aka ba ka.—Luk. 11:13; A. M. 20:28.

17. Mene ne yadda ꞌyanꞌuwa maza da Yesu ya ba mu suke taimaka mana ya nuna?

17 Yadda ꞌyanꞌuwa maza da Yesu ya ba mu suke taimaka mana, ya nuna cewa shi ne yake mana ja-goranci a waɗannan kwanakin ƙarshe. (Mat. 28:20) Muna godiya sosai don Sarkinmu yana ƙaunarmu kuma ya ba mu waɗanda za su taimaka mana, ko ba haka ba? Don haka, bari mu nemi yadda za mu nuna godiya ga waɗannan ꞌyanꞌuwa maza. Kuma kada mu manta mu gode wa Jehobah, don shi ne yake ba mu “kowace baiwa mai kyau, da kowace cikakkiyar kyauta.”—Yak. 1:17.

WAƘA TA 99 Miliyoyin ꞌYanꞌuwa

a Afisawa 4:​7, 8, (NWT) sun ce: 7 Amma an ba kowannenmu baiwarsa gwargwadon yawan alherin Almasihu. 8 Gama Kalmar Allah ta ce, “Saꞌad da ya haura, ya ɗauki waɗanda ya kama, ya kuma ba da maza kyauta.”

b Dattawan da suke hidima a matsayin membobin Hukumar da Ke Kula da Ayyukanmu, da mataimakansu, da waɗanda suke Kwamitin da Ke Kula da Ofishin Shaidun Jehobah, da dai sauransu, suna cikin mazan nan da Yesu ya ba mu kyauta.

c An canja wasu sunayen.

d A dā ana kiran ƙasar Turkey.

e Don ƙarin bayani a kan abin da mutum zai yi don ya cancanci zama bawa mai hidima ko dattijo, ka karanta talifofin nan, “ꞌYanꞌuwa Maza—Kuna Ƙoƙari don Ku Zama Bayi Masu Hidima?” da “ꞌYanꞌuwa Maza—Kuna Ƙoƙari don Ku Zama Dattawa?” a Hasumiyar Tsaro ta Nuwamba 2024.