Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

SHAWARA A KAN YIN NAZARI

Ka Tuna da Muhimman Darussan

Ka Tuna da Muhimman Darussan

Ka taɓa yin nazari amma da ka gama, sai ka kasa tuna ainihin abin da ka yi nazarinsa? Hakan yana iya faruwa da kowa. Me zai taimaka maka? Ka sake yin tunani a kan muhimman darussan.

Yayin da kake nazari, ka riƙa dakatawa ka yi tunani a kan ainihin darasin. Abin da manzo Bulus ya ƙarfafa ꞌyanꞌuwa su yi ke nan idan suna karanta wasiƙarsa. Shi ya sa ya ce: “Manufar maganarmu duka ita ce,” saꞌan nan ya faɗi ainihin darasin. (Ibran. 8:1) Ta haka, ya taimaka musu su fahimci abin da yake nufi, da kuma yadda abubuwan da ya faɗa suka nuna hakan.

Bayan ka gama nazari, ka yin amfani da ɗan lokaci, misali minti goma, don ka yi tunani a kan muhimman darussan da ka koya. Idan ka kasa tuna su, ka sake duba ƙananan jigogin da ke talifin, ko jimla ta farko da ke kowane sakin layi, don ka ga darussan. Idan kuma ka koyi sabon abu, ka yi ƙoƙari ka bayyana shi yadda ka fahimta. Yin abubuwan nan zai sa ka tuna da muhimman darussan, kuma zai taimaka maka ka ga yadda za ka yi amfani da su a rayuwarka.