Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 43

WAƘA TA 90 Mu Riƙa Ƙarfafa Juna

Ta Yaya Za Ka Kau da Shakka?

Ta Yaya Za Ka Kau da Shakka?

“Ku tabbatar da kome.”1 TAS. 5:​21, NWT.

ABIN DA ZA MU KOYA

Za mu ga abin da zai taimaka mana idan muna shakkar cewa muna da daraja a gun Jehobah.

1-2. (a) Wane irin shakka ne wasu bayin Jehobah suke yi? (b) Me za mu tattauna a wannan talifin?

 DUKANMU mukan yi shakka a a wasu lokuta, ko da mu matasa ne ko tsofaffi. Alal misali, ƙaramin yaro a ƙungiyar Jehobah zai iya yin tunanin cewa Jehobah bai san da zamansa ba. Kuma hakan zai iya sa ya yi jinkirin yin baftisma. Idan kuma ɗanꞌuwa ya yi amfani da rayuwarsa saꞌad da yake matashi wajen bauta wa Jehobah maimakon neman kuɗi, saꞌad da ya manyanta, zai iya soma shakkar ko zaɓin da ya yi ya dace. Musamman idan abubuwa ba sa masa sauƙi sosai. ꞌYarꞌuwar da ta tsufa kuma ƙarfinta yana ƙarewa, za ta iya yin sanyin gwiwa don ba ta iya yin abubuwan da ta saba yi. Kai fa, ka taɓa tunani cewa: ‘Anya, Jehobah ya san da ni kuwa? Ban yi kuskure ba kuwa da na yi sadaukarwa don in sa hidimar Jehobah kan gaba a rayuwata? Zan iya yin wani abin kirki kuma a bautar Jehobah kuwa?’

2 Idan mun ci-gaba da yin shakka a kan abubuwan nan, hakan zai iya sa mu yi sanyin gwiwa, har mu daina bauta wa Jehobah. A talifin nan, za mu ga yadda yin tunani a kan ƙaꞌidodin Littafi Mai Tsarki zai taimaka mana idan muna shakkar cewa (1) Jehobah ya san da mu, (2) zaɓin da muka yi a dā ya dace, ko kuma (3) cewa za mu iya yin abin kirki a bautar Jehobah.

ABIN DA ZAI TAIMAKE MU MU KAU DA SHAKKA

3. Me zai taimaka mana mu daina yin shakka?

3 Wani abin da zai taimaka mana mu daina yin shakka shi ne binciken Kalmar Allah. Yin haka zai sa mu ga tabbacin da zai ƙarfafa mu, zai sa mu ƙara kusantar Jehobah, kuma zai sa mu ‘tsaya sosai cikin bangaskiyarmu.’—1 Kor. 16:13.

4. Ta yaya za mu “tabbatar da kome”? (1 Tasalonikawa 5:21)

4 Karanta 1 Tasalonikawa 5:21. Ka lura cewa Littafi Mai Tsarki ya ce mu “tabbatar da kome.” Ta yaya za mu yi haka? Ta wurin gwada abin da muke tunani da abin da Littafi Mai Tsarki ya ce. Alal misali, idan matashi yana ganin kamar Jehobah bai san da shi ba, zai dace ya kammala cewa hakan gaskiya ne? Aꞌa, zai dace ya “tabbatar da kome” ta wurin bincika Kalmar Allah, don ya ga raꞌayin Jehobah game da shi.

5. Ta yaya za mu san raꞌayin Jehobah game da batun da ke damunmu?

5 Idan muna karanta Kalmar Allah, kamar Jehobah yana magana ne da mu. Amma idan muna so mu san raꞌayinsa game da wani abu, akwai abin da muke bukatar mu yi. Muna bukatar mu nemi nassosin da suka shafi batun, kuma mu yi nazarinsu. Za mu iya yin haka ta wurin yin amfani da kayan bincike da muke da su a ƙungiyar Jehobah. (K. Mag. 2:​3-6) Kuma zai yi kyau mu roƙi Jehobah ya ja-gorance mu saꞌad da muke yin binciken, kuma ya taimaka mana mu ga raꞌayinsa game da batun. Saꞌan nan mu nemi ƙaꞌidodin Littafi Mai Tsarki da kuma bayanan da suka dace da yanayinmu. Ƙari ga haka, ƙila mu amfana sosai idan muka bincika labaran mutanen da suka shiga irin halin da muke ciki a Littafi Mai Tsarki.

6. Ta yaya zuwa taro zai taimaka mana mu sami amsoshin tambayoyinmu?

6 Wata hanya kuma da muke sauraron Jehobah ita ce ta wurin zuwa taro. Idan muna zuwa taro babu fashi, za mu iya jin wani jawabi ko wani kalami da zai amsa tambayar da ke damunmu a zuciya. (K. Mag. 27:17) Bari mu tattauna wasu abubuwan da za su taimaka mana mu sami amsoshin tambayoyin da muke da su.

JEHOBAH YA DAMU DA KAI KUWA?

7. Wane irin tunani ne wasu suke yi?

7 Ka taɓa tunani cewa, ‘Anya Jehobah ya san da ni kuwa?’ Idan kana gani kamar ba ka da daraja, hakan zai sa ka ga kamar ba zai yiwu ka zama abokin Allah ba. Sarki Dauda ma ƙila ya taɓa yin irin tunanin nan. Ya yi mamakin sanin cewa Jehobah ya damu da ꞌyan Adam. Shi ya sa ya ce: “Ya Yahweh, mene ne mutum da har ka damu da shi? Ɗan Adam, da har kana tunaninsa?” (Zab. 144:3) A ina kake ganin za mu sami amsar tambayoyin nan?

8. Bisa ga 1 Samaꞌila 16:​6, 7, 10-12, mene ne Jehobah yake dubawa?

8 Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa Jehobah ya damu da mutanen da ake ganin ba su da wani amfani. Alal misali, akwai lokacin da Jehobah ya aiki Sama’ila ya je gidan Yesse ya naɗa ɗaya daga cikin ꞌyaꞌyansa sarki mai jiran gado. Sai Yesse ya kira ꞌyaꞌyansa guda bakwai amma bai kira autansa Dauda ba. b Duk da haka, Dauda ne Jehobah ya zaɓa. (Karanta 1 Samaꞌila 16:​6, 7, 10-12.) Jehobah ya ga zuciyar Dauda kuma ya san yana ƙaunarsa sosai.

9. Me ya tabbatar maka cewa Jehobah ya damu da kai? (Ka kuma duba hoton.)

9 Ka yi tunanin yadda Jehobah ya nuna cewa ya san da zamanka. Yana ba ka shawarwarin da za su taimaka maka a kowane yanayin da kake ciki. (Zab. 32:8) Hakan ya nuna cewa ya san da zamanka. (Zab. 139:1) Idan ka bi shawarar da Jehobah yake bayarwa kuma ka ga yadda ka amfana, hakan zai tabbatar maka cewa ya damu da kai. (1 Tar. 28:9; A. M. 17:​26, 27) Jehobah yana ganin ƙoƙarin da kake yi. Yana ganin halayenka masu kyau kuma yana so ka zama abokinsa. (Irm. 17:10) Zai yi farin ciki sosai idan kai ma ka yarda ka zama abokinsa.—1 Yoh. 4:19.

“Idan ka neme [Jehobah], zai sa ka same shi.” —1 Tar. 28:9 (Ka duba sakin layi na 9) c


IDAN KANA GANIN ZAƁIN DA KA YI BAI DACE BA

10. Idan muka yi tunani a kan zaɓin da muka yi a dā, wace shakka ce za mu iya yi?

10 A wasu lokuta, wasu sukan ga kamar zaɓin da suka yi a dā bai dace ba. Wataƙila suna irin wannan tunanin ne domin sun bar aikin da ake biyansu albashi mai tsoka, ko wani kasuwanci, don su iya sa bautar Jehobah a kan gaba. Kuma ƙila sun yanke shawarar ne shekaru da dama da suka shige. A-kwana-a-tashi, za su iya ganin yadda mutanen da ba su yi irin zaɓin da suka yi ba, suke jin daɗi kuma suke da arziki. Hakan zai iya sa su soma tunani cewa: ‘Anya sadaukarwar da na yi don ibadata ba kuskure ba ne kuwa? Ko da na yi aiki sosai ne don in zama mai arziki?’

11. Mene ne ya dami marubucin Zabura ta 73?

11 Idan kana fama da irin tunanin nan, ka yi laꞌakari da abin da Littafi Mai Tsarki ya ce game da marubucin Zabura ta 73. Ya ga cewa mutanen da ba sa bauta wa Jehobah suna da koshin lafiya, da arziki, kuma kamar ba su da matsala. (Zab. 73:​3-5, 12) Da ya ga yadda suke samun ci-gaba, sai ya ga kamar ƙoƙarin da yake yi wajen bauta wa Jehobah bai da amfani. Yakan yini yana damuwa a kan abubuwan nan, kuma sun sa shi sanyin gwiwa. (Zab. 73:​13, 14) Me ya yi don ya daina irin tunanin nan?

12. Bisa ga Zabura 73:​16-18, mene ne mai Zaburar ya yi don ya daina damuwa?

12 Karanta Zabura 73:​16-18. Marubucin Zaburar ya je wuri mai tsarki na Jehobah. A wurin ya iya ya yi tunani da kyau. Kuma ya gano cewa ko da yana ganin kamar mugaye suna jin daɗin rayuwa, ba su da wani bege a nan gaba. Hakan ya sa hankalinsa ya kwanta, kuma ya fahimci cewa bautar Jehobah ce zaɓi mafi kyau da mutum zai iya yi. Don haka, ya ƙudiri niyyar ci-gaba da bauta wa Jehobah.—Zab. 73:​23-28.

13. Me za ka yi idan kana ganin zaɓin da ka yi bai dace ba? (Ka kuma duba hoton.)

13 Kai ma, Kalmar Allah za ta taimaka maka ka sami kwanciyar hankali. Ta yaya? Idan ka yi tunani a kan albarkun da kake samu daga wurin Jehobah. Ka kuma tuna cewa Jehobah ba zai taimaki waɗanda ba sa bauta masa ba. Irin mutanen nan, suna gani kamar jin daɗin rayuwa ne ya fi muhimmanci, don ba su da wani bege. Amma Jehobah ya yi alkawari cewa ban da albarkun da kake samu yanzu, za ka mori wasu har abada a aljanna. (Zab. 145:16) Abin shi ne, ba ka san yadda rayuwarka za ta kasance ba da a ce wani abu dabam ka zaɓa. Ƙari ga haka, idan ka yi zaɓin da ya nuna cewa kana ƙaunar Jehobah da kuma mutane, ba za ka rasa kome ba, kuma za ka yi farin ciki sosai.

Ka riƙa tunani a kan albarkun da Jehobah zai yi maka nan gaba (Ka duba sakin layi na 13) d


IDAN KANA GANIN BA KA DA AMFANI A GUN JEHOBAH

14. Mene ne wasu bayin Jehobah suke fama da shi, kuma wane tunani ne za su iya yi?

14 Wasu bayin Jehobah suna fama da rashin lafiya ko tsufa ko kuma wata naƙasa. Hakan zai iya sa su ga kamar ba su da amfani a gun Jehobah. Wataƙila ma su soma tunani cewa, ‘Anya ina da wani amfani a gun Jehobah kuwa?’

15. Wane tabbaci ne marubucin Zabura ta 71 yake da shi?

15 Marubucin Zabura ta 71 ya yi irin wannan tunanin. Ya roƙi Allah cewa, lokacin “da ƙarfina ya ƙare, kada ka manta da ni.” (Zab. 71:​9, 18) Duk da irin tunanin da ya yi, ya kasance da tabbaci cewa Jehobah zai taimaka masa idan ya ci-gaba da bauta masa da aminci. Marubucin Zaburar ya gane cewa Jehobah yana amincewa da waɗanda suke bauta masa duk da fama da suke yi.—Zab. 37:​23-25.

16. A waɗanne hanyoyi ne tsofaffi suke da amfani? (Zabura 92:​12-15)

16 ꞌYanꞌuwanmu tsofaffi, ku riƙa tunani a kan yadda Jehobah yake ganin ku. Zai taimaka muku ku bauta masa da aminci duk da cewa kuna fama da tsufa. (Karanta Zabura 92:​12-15.) Maimakon ka riƙa tunani a kan abin da ba za ka iya yi ba, ka mai da hankali a kan abin da za ka iya yi. Alal misali, za ka iya ƙarfafa wasu ta warin nuna musu cewa ka damu da su, da kuma ta wurin halayenka masu kyau. Za ka iya gaya wa mutane yadda Jehobah ya taimaka maka cikin shekarun da ka yi kana bauta masa, da kuma abin da kake marmarin ganin cikarsa a nan gaba. Ƙari ga haka, kada ka manta cewa mutane za su amfana daga adduꞌoꞌinka. (1 Bit. 3:12) Ko da a wane yanayi ne muke ciki, akwai abin da za mu iya yi a bautar Jehobah, kuma za mu iya taimaka wa mutane.

17. Me ya sa bai kamata mu gwada kanmu da wasu ba?

17 Idan kana so ka ƙara yin wasu ayyuka a bautar Jehobah amma ka kasa, kar ka damu. Ka kasance da tabbaci cewa Jehobah yana ɗaukan duk abin da kake yi da muhimmanci. Wasu sukan gwada abin da suke yi da abin da wasu ꞌyanꞌuwa suke yi. Amma yin hakan bai dace ba. Domin Jehobah ba ya gwada abin da kake yi da na wasu. (Gal. 6:4) Alal misali, Maryamu ta ba wa Yesu turare mai tsada sosai. (Yoh. 12:​3-5) Wata gwauruwa kuma ta ba da gudummawar anini biyu. (Luk. 21:​1-4) Duk da haka, Yesu ya nuna cewa dukansu masu bangaskiya ne kuma sun bayar daga zuciyarsu. Jehobah ma yana daraja kome da muke yi da bangaskiya don mu nuna cewa muna ƙaunarsa, komen ƙanƙantarsa.

18. Me zai taimaka mana mu kau da shakka? (Ka kuma duba akwatin nan, “ Jehobah Zai Taimaka Mana Mu Kau da Shakka.”)

18 Dukanmu, mukan yi shakka a wasu lokuta. Amma kamar yadda muka gani a wannan talifin, Littafi Mai Tsarki zai iya taimaka mana mu kawar da duk wata shakka da muke yi. Saboda haka, mu yi ƙoƙari mu tabbatar da duk wani abin da muke shakkarsa. Yin hakan zai sa mu kau da shakka. Hakika, Jehobah ya san da zamanka. Yana alfahari da kai don sadaukarwar da kake yi, kuma zai albarkace ka. Bari mu kasance da tabbaci cewa Jehobah yana ƙaunar mu, kuma yana kula da dukan bayinsa masu aminci.

WAƘA TA 111 Dalilan da Suke Sa Mu Murna

a MAꞌANAR WASU KALMOMI: A wannan talifin, muna magana ne game da shakkar da take iya sa mu ga kamar zaɓin da muka yi a dā bai dace ba, ko kuma mu ga kamar ba mu da amfani a gun Jehobah. Wannan ba irin shakkar da Littafi Mai Tsarki ya ce alamar rashin bangaskiya ba ne.

b Ko da yake Littafi Mai Tsarki bai gaya mana shekarun Dauda a lokacin da aka naɗa shi sarki ba, wataƙila bai kai shekara 20 ba.—Ka duba Hasumiyar Tsaro na 1 ga Satumba, 2011, shafi na 29, sakin layi na 2.

c BAYANI A KAN HOTUNA : Wata ꞌyarꞌuwa matashiya tana bincika Kalmar Allah don ta san raꞌayin Jehobah game da batun da ke damunta.

d BAYANI A KAN HOTO: Wani ɗanꞌuwa yana aiki don ya sami kuɗin biyan bukatun iyalinsa, amma ya fi mai da hankali ga yadda za su kasance a aljanna.