Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Amsoshin Tambayoyin Masu Karatu

Amsoshin Tambayoyin Masu Karatu

Yaya tsayin zauren de ke gaban haikalin da Sulemanu ya gina?

Akan bi ta zauren ne a shiga Wuri Mai Tsarki na haikalin. A duka juyin New World Translation of the Holy Scriptures da aka fitar kafin 2023, an ce daga farkon zauren zuwa ƙarshensa kamu ko cubit 20 ne (wato kafa 30), daidai da faɗin cikin haikalin. Kuma tsayinsa kamu 120 ne (wato mita 53 ko kafa 175). (2 Tar. 3:4) Wasu juyin Littafi Mai Tsarki su ma sun ce tsayinsa “kamu 120” ne.

Amma, a juyin New World Translation da aka fitar a 2023, an ce tsayin zauren haikalin da Sulemanu ya gina “kamu 20” ne, wato wajen mita 9 ke nan (kafa 30). a Bari mu ga wasu dalilai da suka sa aka yi wannan gyara.

Ba a ambaci tsayin zauren a 1 Sarakuna 6:3 ba. A wannan ayar, Irmiya ya ambaci faɗin zauren da zurfinsa, amma bai yi zancen tsayinsa ba. A sura 7, ya yi bayani sosai a kan abubuwa da dama da suke haikalin, kamar su ƙaton kwano na ƙarfen tagulla, da amalanke guda goma, da ginshiƙan ƙarfe guda biyu da suke a gaban zauren. (1 Sar. 7:​15-37) Da a ce zauren yana da tsayi sosai har ya kai mita 50, ai da Irmiya ya yi magana a kan tsayinsa, domin da zai fi haikalin tsayi ba kaɗan ba. Ƙari ga haka, bayan ɗarurruwan shekaru, masanan tarihin Yahudawa sun rubuta cewa zauren bai fi sauran haikalin tsayi ba.

Masu bincike sun ce zai yi wuya a yi wa haikalin zauren da tsayinsa ya kai mita 50 (kamu 120). A zamanin dā, idan za a yi gini mai tsayi da duwatsu da kuma bulo, akan yi ƙasan ginin da faɗi sosai, sai a yi ta rage faɗin yayin da ake haurawa. Irin abin da aka yi ke nan a ƙofofin haikali a ƙasar Masar. Amma ba haka haikalin da Sulemanu ya gina yake ba. Masu bincike sun ce kaurin bangon haikalin bai wuci mita 2.7 ko kafa 9 ba. Kuma wani masanin tarihin gine-gine mai suna Theodor Busink ya ce: “Da yake kaurin bangon haikalin ke nan, ba za a iya gina masa zaure mai tsayin da ya kai kamu 120 ba.”

Mai yiwuwa an yi kuskure ne lokacin da ake kofan 2 Tarihi 3:4. Ko da yake a waɗansu kofi na rubuce-rubucen hannu na dā “120” aka rubuta a wannan ayar, akwai wasu kofi na rubuce-rubucen hannu na dā da aka yarda da su, da suka ce “kamu 20” ne. Alal misali, wanda ake kira Codex Alexandrinus da aka kofa fiye da shekaru 1,500 da suka wuce, da kuma Codex Ambrosianus da aka kofa fiye da shekaru 1,400 da suka wuce, sun ce “kamu 20” ne. Me zai iya sa a rubuta “120” maimakon “kamu 20”? Dalilin shi ne a Ibrananci, yadda ake rubuta “ɗari,” da “kamu” (cubit), ya yi kama sosai. Don haka, wataƙila mai kofan rubutun ne ya rubuta “ɗari” maimakon “kamu.”

Muna iya ƙoƙarinmu mu fahimci abubuwan nan, kuma mu tabbata cewa abubuwa da muke faɗa game da haikalin da Sulemanu ya gina daidai ne. Amma ya kamata mu fi mai da hankali ga haikalin da ya ɗauki matsayin wannan, wato babban haikali na alama. Mun gode wa Jehobah sosai don yadda ya kira dukanmu bayinsa mu bauta masa a wannan haikalin!—Ibran. 9:​11-14; R. Yar. 3:12; 7:​9-17.

a An sa ƙarin bayani a ayar nan da ya nuna cewa “wasu kofe na rubuce-rubucen hannu na dā sun ce ‘120’ ne, wasu kuma sun ce ‘kamu 20.’ Wasu juyin ma sun ce ‘kamu 20’ ne.”