Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 41

Darussan da Wasiku Biyu da Bitrus Ya Rubuta Suka Koya Mana

Darussan da Wasiku Biyu da Bitrus Ya Rubuta Suka Koya Mana

“Zan dinga tuna muku da waɗannan abubuwa.”—2 BIT. 1:12.

WAƘA TA 127 Irin Mutumin da Ya Kamata In Zama

ABIN DA ZA A TATTAUNA a

1. Da manzo Bitrus ya kusan mutuwa, mene ne Jehobah ya sa shi ya yi?

 MANZO Bitrus ya san cewa ya kusan mutuwa. A shekaru da yawa da ya yi yana bauta wa Jehobah, ya yi aiki tare da Yesu. Shi ne ya soma yi wa waɗanda ba Yahudawa ba waꞌazi, kuma ya zama membam hukumar da ke kula da ayyukan Kiristoci a lokacin. Amma ba shi ke nan ba. A wajen shekara ta 62 zuwa 64 bayan haihuwar Yesu, Jehobah ya sa shi ya rubuta wasiƙu biyu, wato littafin Bitrus na 1 da na 2. Bitrus ya sa rai cewa wasiƙun nan za su taimaka wa Kiristoci bayan mutuwarsa.—2 Bit. 1:12-15.

2. Me ya sa za mu ce wasiƙun da Bitrus ya rubuta sun zo daidai lokacin da ake bukatar su?

2 A lokacin da Bitrus ya rubuta wasiƙun nan, ꞌyanꞌuwansa Kiristoci suna “baƙin ciki saboda gwaje-gwaje iri-irin” da suke ciki. (1 Bit. 1:6) Lokacin, mugayen mutane suna ƙoƙarin kawo koyarwar ƙarya da ayyukan kazanta cikin ikilisiya. (2 Bit. 2:1, 2, 14) Kuma lokacin “ƙarshen dukan abu ya yi kusa” a Urushalima, wato lokacin da za a halaka Urushalima da haikalinta. (1 Bit. 4:7) Ba shakka, wasiƙun Bitrus sun taimaka wa Kiristoci su ga yadda za su jimre matsalolin da suke fuskanta da waɗanda za su fuskanta a nan gaba. b

3. Wane amfani za mu samu idan muka bincika wasiƙun manzo Bitrus?

3 Ko da yake ga Kiristoci a ƙarni na farko ne Bitrus ya rubuta wasiƙunsa, Jehobah yana so mu amfana daga wasiƙun nan. Shi ya sa ya sa aka saka su a cikin Littafi Mai Tsarki. (Rom. 15:4) Da yake muna rayuwa a duniyar da ke ɗaukaka halaye marasa kyau, mu ma mukan gamu da jarabobi da suke sa ya yi mana wuya mu bauta wa Jehobah. Ban da haka ma, mun kusa mu shiga ƙunci, wanda ya fi ƙuncin da Kiristoci suka fuskanta saꞌad da aka halaka Urushalima da haikalinta. Akwai wasu abubuwa masu muhimmanci da Bitrus ya tuna mana a wasiƙun nan da za su taimaka mana mu ci gaba da jiran ranar Jehobah, mu daina tsoron mutum kuma mu nuna wa juna ƙauna ta gaskiya. Ban da haka ma, za su taimaka wa dattawa su san yadda za su kula da ꞌyanꞌuwa da kyau.

KA CI GABA DA JIRA

4. Kamar yadda 2 Bitrus 3:3, 4 suka ce, mene ne zai iya sa mu yi shakka?

4 Muna rayuwa da mutanen da ba su yarda da abin da Littafi Mai Tsarki ya ce zai faru ba. Masu adawa da mu suna iya mana dariya don mun yi shekaru da yawa muna cewa ƙarshen duniyar nan zai zo. Wasu ma suna cewa ba zai taɓa zuwa ba. (Karanta 2 Bitrus 3:3, 4.) Idan abokin aikinmu ko wani a iyalinmu ko wani da muka je yi masa waꞌazi ya gaya mana hakan, zai iya sa mu soma shakka. Amma Bitrus ya bayyana abin da zai taimaka mana.

5. Me zai taimaka mana mu ci gaba da jiran ƙarshen duniyar nan da haƙuri? (2 Bitrus 3:8, 9)

5 Wasu suna ganin kamar Jehobah yana jinkirin kawo ƙarshen wannan zamanin. Amma abin da Bitrus ya rubuta zai iya taimaka mana, don ya tuna mana cewa yadda Jehobah yake ganin lokaci ba ɗaya ba ne da yadda muke ganin sa. (Karanta 2 Bitrus 3:8, 9.) A gun Jehobah, shekaru dubu kamar kwana guda ne. Kuma Jehobah mai haƙuri ne, ba ya so kowa ya halaka. Amma idan ranarsa ta kai, zai kawo ƙarshen zamanin nan. Don haka a yanzu, muna da babbar damar yi wa dukan mutane waꞌazi.

6. Me zai taimake mu mu ci gaba da yin “marmarin zuwan” ranar Ubangiji? (2 Bitrus 3:11, 12)

6 Bitrus ya ce mu yi “marmarin zuwan” ranar Jehobah. (Karanta 2 Bitrus 3:11, 12.) Ta yaya za mu yi hakan? A kowace rana, za mu iya yin tunanin abubuwa masu ban shaꞌawa da za su faru a sabuwar duniya. Ka yi tunanin yadda za ka ji idan kana shaƙar iska mai tsabta, kana cin abinci mai gina jiki, kana marabtar waɗanda kake ƙauna da aka ta da su daga mutuwa, kuma kana koya wa mutanen da suka yi rayuwa a dā yadda annabcin Littafi Mai Tsarki ya cika. Idan kana irin wannan tunanin, zai taimake ka ka ci gaba da yin marmarin zuwan ranar, kuma ba za ka yi shakkar cewa ƙarshen ya yi kusa ba. Idan ‘mun riga mun san da waɗannan’ abubuwa, masu koyarwar ƙarya ba za su ‘kwashi hankalinmu’ ba.—2 Bit. 3:17.

DAINA TSORON MUTUM

7. Me zai iya faruwa da mu idan muna tsoron mutum?

7 Da yake muna marmarin zuwan ranar Jehobah, muna son yi wa mutane waꞌazin labarin nan mai daɗi. Amma wani lokaci, za mu iya jin tsoron yin hakan. Me ya sa? Don ƙila muna jin tsoron abin da mutane za su faɗa ko za su yi mana. Abin da ya faru da Bitrus ke nan a daren da aka kama Yesu. Tsoro ya sa Bitrus ya kasa cewa shi mabiyin Yesu ne, har ya yi mūsun saninsa sau da yawa. (Mat. 26:69-75) Amma daga baya manzo Bitrus ya zama mai ƙarfin zuciya har ya ce: “Kada ku ji tsoron masu yi muku mugunta, kada kuma ku damu da su.” (1 Bit. 3:14) Abin da Bitrus ya faɗa ya tabbatar mana da cewa za mu iya daina jin tsoron mutum.

8. Me zai taimake mu mu daina jin tsoron mutum? (1 Bitrus 3:15)

8 Me zai taimake mu mu daina jin tsoron mutane? Bitrus ya ce: “Ku girmama Almasihu a zukatanku ku yarda shi Ubangiji ne.” (Karanta 1 Bitrus 3:15.) Za mu iya yin hakan ta wajen tuna wa kanmu cewa Yesu Kristi ne Sarkinmu, kuma yana da iko sosai. Idan ka samu damar yin waꞌazi amma kana tunanin me za ka ce, ko kana jin tsoro, ka tuna da Sarkinmu. Ka yi tunanin yadda yake mulki a sama, ga malaꞌiku marasa iyaka kewaye da shi. Ka tuna cewa an ba shi “dukan iko a sama da kuma nan duniya.” Kuma cewa zai kasance ‘tare da kai kullum har ƙarshen zamani.’ (Mat. 28:18-20) Bitrus ya ƙarfafa mu mu “zauna a shirye kullum” don mu iya bayyana imaninmu. Za ka so ka yi waꞌazi a wurin aiki ko a makaranta ko a wani wuri dabam? Tun da wuri, ka yi tunanin lokacin da za ka iya samun damar yin hakan saꞌan nan ka shirya abin da za ka faɗa. Ka roƙi Jehobah ya ba ka ƙarfin zuciya, kuma ka gaskata cewa Jehobah zai taimake ka ka shawo kan tsoron mutum.—A. M. 4:29.

“KU ƘAUNACI JUNA DA ƘAUNA TA AINIHI”

Bitrus ya amince da gyaran da Bulus ya yi masa, kuma wasiƙu biyu da Bitrus ya rubuta sun koya mana muhimmancin nuna wa ꞌyanꞌuwanmu ƙauna (Ka duba sakin layi na 9)

9. Ta yaya Bitrus ya kasa nuna ƙauna ga waɗanda ba Yahudawa ba? (Ka kuma duba hoton.)

9 Bitrus ya ci gaba da koyan yadda zai nuna ƙauna ta gaskiya. Yana a wurin lokacin da Yesu ya ce: “Sabon umarni nake ba ku, ku ƙaunaci juna. Kamar yadda na ƙaunace ku, haka ku ma ku ƙaunaci juna.” (Yoh. 13:34) Duk da haka, daga baya Bitrus ya ƙi cin abinci da mutanen da ba Yahudawa ba don yana tsoron abin da Kiristoci Yahudawa za su ce. Manzo Bulus ya ce abin da Bitrus ya yi “munafunci” ne. (Gal. 2:11-14) Bitrus ya amince da gargaɗin Bulus kuma ya yi gyara. Shi ya sa a wasiƙu biyu da ya rubuta, ya nanata muhimmancin nuna wa ꞌyanꞌuwanmu ƙauna ta ayyukanmu, ba kawai mu ƙaunace su a zuciya ba.

10. Mene ne yake sa mu nuna wa ꞌyanꞌuwanmu “ƙauna ta ainihi”? Ka bayyana. (1 Bitrus 1:22)

10 Bitrus ya ce mu ƙaunaci ‘ꞌyanꞌuwanmu da ƙauna ta ainihi.’ (Karanta 1 Bitrus 1:22.) Muna bin “gaskiya,” shi ya sa muke da irin wannan ƙaunar. Kuma gaskiyar nan ta haɗa da koyarwar nan cewa “Allah ba ya nuna bambanci.” (A. M. 10:34, 35) Idan wasu ne kawai muke nuna wa ƙauna a ikilisiya saꞌan nan ba ma ƙaunar wasu, to ba ma bin umurnin da Yesu ya bayar game da nuna ƙauna ke nan. Gaskiya ne cewa za mu fi kusa da wasu a ikilisiya fiye da wasu kamar yadda Yesu ya yi. (Yoh. 13:23; 20:2) Amma Bitrus ya tuna mana cewa ya kamata mu “ƙaunaci” dukan ꞌyanꞌuwanmu, domin dukansu ꞌyan iyalinmu ne.—1 Bit. 2:17.

11. Ta yaya za mu nuna ƙauna “da zuciya ɗaya”?

11 Bitrus ya ce mu ƙaunaci “juna da zuciya ɗaya.” Wannan yana nufin mu nuna wa mutum ƙauna ko da hakan yana yi mana wuya. Alal misali, idan wani ɗanꞌuwa ya yi abin da ya ɓata mana rai, abin da zai fara zuwa zuciyarmu shi ne mu rama. Amma Yesu ya koya wa Bitrus cewa Allah ba ya son ramako, kuma Bitrus ya fahimci hakan. (Yoh. 18:10, 11) Shi ya sa Bitrus ya rubuta cewa: “Kada ku rama mugunta da mugunta, ko zagi da zagi. Ku rama dai da albarka.” (1 Bit. 3:9) Bari ƙauna ta ainihi ta sa ka yi wa mutane alheri kuma ka nuna musu halin ganewa idan suka ɓata maka rai.

12. (a) Wane abu ne kuma ƙauna ta ainihi za ta sa mu yi? (b) Me za ka so ka yi iya ƙoƙarinka ka yi, kamar yadda aka nuna a bidiyon nan, Ku Kāre Haɗin Kanmu?

12 A wasiƙar Bitrus ta fari, Bitrus ya ce: “Ƙauna ta ainihi” takan sa mu “yafe laifofi masu ɗumbun yawa.” (1 Bit. 4:8) Wataƙila Bitrus ya tuna abin da Yesu ya koya masa game da yafewa shekarun baya shi ya sa. A lokacin, Bitrus ya zata shi mutumin kirki ne sosai da ya ce zai yafe wa ɗanꞌuwansa “sau bakwai.” Amma Yesu ya koya masa da mu ma a yau, cewa mu yafe, “ba sau bakwai ba, amma dai bakwai sau sabaꞌin,” wato ba iyaka. (Mat. 18:21, 22) Idan yana maka wuya ka yi hakan, kada ka karaya! Duka bayin Allah ajizai ne, kuma akwai lokacin da bai yi musu sauƙi su yafe ba. Abin da ya fi muhimmanci yanzu shi ne ka yi duk abin da za ka iya don ka yafe ma ɗanꞌuwanka kuma ku zauna lafiya. c

DATTAWA, KU KULA DA TUMAKIN JEHOBAH

13. Me zai iya sa ya yi wa dattawa wuya su kula da ꞌyanꞌuwa a ikilisiya?

13 Bayan da Yesu ya tashi daga mutuwa, ya ce wa Bitrus: “Ka yi kiwon tumakina.” (Yoh. 21:16) Ba shakka Bitrus bai manta da wannan umurnin ba. Idan kai dattijo ne, ka san kana bukatar ka bi wannan umurnin. Amma zai iya yi wa dattijo wuya ya samu lokacin yin wannan hidimar. Dole dattawa su soma da tabbatar da cewa sun biya bukatun iyalinsu, su nuna ma iyalinsu ƙauna, kuma su taimaka musu su kusaci Jehobah. Ban da haka ma, dole dattawa su zama kan gaba a yin waꞌazi, su shirya kuma su gudanar da ayyuka a taron ikilisiya da manyan taronmu. Wasu dattawa mambobin Kwamitin Hulɗa da Asibitoci ne, wasu kuma suna aiki da Sashen Zane-zane da Gine-gine da ke ofishinmu. Hakika, dattawa suna yin ayyuka da yawa.

Duk da cewa dattawa suna da ayyuka da yawa, suna iya ƙoƙarinsu su kula da tumakin Allah, don suna ƙaunar tumakin (Ka duba sakin layi na 14-15)

14. Me zai iya ƙarfafa dattawa su kula da tumakin Jehobah? (1 Bitrus 5:1-4)

14 Bitrus ya gaya wa ꞌyanꞌuwansa dattawa cewa: “Ku yi kiwon garken Allah.” (Karanta 1 Bitrus 5:1-4.) Idan kai dattijo ne, mun san kana ƙaunar ꞌyanꞌuwa da ke ikilisiya, kuma kana so ka kula da su. Amma wani lokaci, kana iya ji kamar ba za ka iya yin hakan ba domin ka gaji sosai ko kuma ayyuka sun yi maka yawa. Me zai taimaka maka? Ka gaya wa Jehobah damuwarka da kuma yadda kake so ka taimaki ꞌyanꞌuwa. Bitrus ya rubuta cewa: “Duk wanda baiwarsa ta yin hidima ce, to, sai ya yi hidimar da ƙarfin da Allah ya bayar.” (1 Bit. 4:11) Wataƙila matsalolin da wasu ꞌyanꞌuwa suke fuskanta, ba za a iya magance su a wannan zamanin ba. Don haka, ka tuna cewa ‘Babban Makiyayi,’ wato Yesu Kristi zai iya taimakon su fiye da kai. Zai iya yin hakan a yau da kuma a sabuwar duniya. Abin da kawai Jehobah yake so dattawa su yi shi ne su ƙaunaci ꞌyanꞌuwansu, su kula da su kuma su ‘zama gurbi’ ga ꞌyanꞌuwansu.

15. Mene ne wani dattijo yake yi don ya kula da tumakin Jehobah? (Ka kuma duba hoton.)

15 Akwai wani ɗanꞌuwa mai suna William da ya daɗe da zama dattijo. Ɗanꞌuwan ya san muhimmancin kula da ꞌyanꞌuwa. Da annobar korona ta soma, sai shi da sauran dattawa da ke rukunin waꞌazinsu suka ce ko ta yaya, za su riƙa kiran kowane ɗanꞌuwa ko ꞌyarꞌuwa da ke rukuninsu a kowane mako. Kuma ya faɗi dalilin, ya ce: “Yawancin ꞌyanꞌuwan su kaɗai ne a gidajensu, kuma hakan zai iya sa su soma tunani marar kyau.” Idan ɗanꞌuwa ko ꞌyarꞌuwa tana fama da wata matsala, ɗanꞌuwa William yakan saurare ta don ya fahimci mene ne matsalar kuma me take bukata. Saꞌan nan ya samo wani abin da zai taimaka wa ɗanꞌuwan ko ꞌyarꞌuwar. Yawancin lokaci, bidiyoyi yake samowa daga dandalinmu. Ɗanꞌuwa William ya ce: “ꞌYanꞌuwanmu suna bukatar kulawarmu yanzu fiye da dā. Ba ƙaramin ƙoƙari muke yi ba don mu taimaka wa mutane su zo su bauta wa Jehobah. Ya kamata mu yi ƙoƙari sosai wajen kula da tumakin nan don su ci gaba da bauta wa Jehobah.”

KA BAR JEHOBAH YA HORAR DA KAI

16. Ta yaya za mu iya bin darussan da muka koya daga misalin Bitrus?

16 Darussa biyu ne kawai muka tattauna daga wasiƙun da Bitrus ya rubuta. Ƙila yanzu ka ga wasu wuraren da ya kamata ka ƙara yin ƙoƙari. Misali, za ka so ka ƙara yin tunani mai zurfi a kan albarkun da Mulkin Allah zai kawo? Kana da burin yin waꞌazi a wurin aiki ko a makaranta ko a wani wuri dabam? Ka lura da wasu hanyoyi da za ka ƙara nuna wa ꞌyanꞌuwa ƙauna ta ainihi? Dattawa, kuna da niyyar kula da tumakin Jehobah da son ranku? Idan ka bincika kanka kuma ka ga cewa kana bukatar gyara, kada ka yi sanyin gwiwa. Ubangijinmu Yesu mai alheri ne, kuma zai taimake ka. (1 Bit. 2:3) Bitrus ya tabbatar mana da cewa: Allah “shi da kansa zai mai da ku cikakku, zai kafa ku, zai kuma ƙarfafa ku.”—1 Bit. 5:10.

17. Wane sakamako za mu samu idan muka ci gaba da yin ƙoƙari kuma muka bar Jehobah ya koyar da mu?

17 Da farko, Bitrus ya ɗauka cewa bai cancanci ya kasance tare da Ɗan Allah ba. (Luk. 5:8) Amma da taimakon Jehobah da Yesu, Bitrus ya ci gaba da ƙoƙarin bin Yesu. Don haka, Jehobah ya amince da Bitrus ya “shiga cikin madawwamin mulki na Ubangijinmu Yesu Almasihu Mai Cetonmu.” (2 Bit. 1:11) Wannan ba ƙaramin lāda ba ne! Idan ka ci gaba da yin ƙoƙari kamar Bitrus, kuma ka bar Jehobah ya koyar da kai, kai ma za ka samu ladar rai na har abada. Za ka samu ‘ceton ranka wanda shi ne manufar bangaskiyarka.’—1 Bit. 1:9.

WAƘA TA 109 Mu Kasance da Ƙauna ta Gaske

a A wannan talifin, za mu ga yadda darussa da suke wasiƙu da Bitrus ya rubuta za su taimaka mana mu jimre matsaloli. Ƙari ga haka, talifin zai taimaka wa dattawa su ga yadda za su cika hakkinsu na kula da tumakin Allah.

b Akwai alamar cewa Kiristoci da suke zama a yankin Falasɗinu sun samu wasiƙu biyu da Bitrus ya rubuta kafin a kai wa Urushalima hari a shekara ta 66 bayan haifuwar Yesu.

c Ka kalli bidiyon nan mai jigo, Ku Kāre Haɗin Kanmu, da ke jw.org/ha.