Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 37

Ka Dogara ga Jehobah Kamar Samson

Ka Dogara ga Jehobah Kamar Samson

“Ya Ubangiji Yahweh, bari ka tuna da ni! Ina roƙonka, ya Allah, ka sāke ba ni ƙarfi.”—ALƘA. 16:28.

WAƘA TA 30 Jehobah Ubana, Allahna da Abokina

ABIN DA ZA A TATTAUNA a

1-2. Ta yaya za mu amfana idan muka yi nazarin labarin Samson?

 IDAN ka ji sunan nan Samson, wane tunani ne yake zuwa zuciyarka? Ba mamaki, za ka tuna cewa shi wani mutum ne mai ƙarfi sosai. Hakan gaskiya ne. Amma akwai wani zaɓi marar kyau da Samson ya yi da ya sa ya sha wahala sosai. Duk da haka, Allah ya mai da hankali ga amincinsa ne kuma ya sa an rubuta labarin wannan bawan Allah a Littafi Mai Tsarki don amfanin mu.

2 Jehobah ya yi abubuwan ban mamaki ta wurin Samson don ya ceci mutanensa Israꞌilawa. Ɗarurruwan shekaru bayan mutuwar Samson, Jehobah ya sa manzo Bulus ya rubuta sunansa a cikin mutane masu bangaskiya sosai. (Ibran. 11:32-34) Abubuwan da Samson ya yi za su iya ƙarfafa mu don ya dogara ga Jehobah har a yanayi mai wuya. A wannan talifin, za mu ga abin da za mu koya daga wurin Samson, da kuma yadda labarinsa zai ƙarfafa mu.

SAMSON YA DOGARA GA JEHOBAH

3. Wane aiki ne Jehobah ya ba wa Samson?

3 A lokacin da aka haifi Samson, Filistiyawa ne suke mulki a kan ƙasar Israꞌila, kuma suna wulaƙanta su. (Alƙa. 13:1) Israꞌilawan sun sha wahala sosai don Filistiyawan mugaye ne. Sai Jehobah ya zaɓi Samson, kuma ya ce “shi zai fara ceton mutanen Israꞌila daga hannun Filistiyawa.” (Alƙa. 13:5) Wannan ba ƙaramin aiki ba ne. Sai da taimakon Jehobah ne kaɗai Samson zai iya yin aikin nan.

Samson ya dogara ga Jehobah kuma ya yarda ya yi canji don ya bauta masa da kyau. Ya yi amfani da abin da ya samu don ya yi nufin Jehobah (Ka duba sakin layi na 4-5)

4. Ta yaya Jehobah ya taimaki Samson ya kuɓutar da kansa daga hannun Filistiyawa? (Alƙalai 15:14-16)

4 Bari mu ga yadda Samson ya dogara ga Jehobah kuma ya nemi taimakon sa. Akwai lokacin da sojojin Filistiyawa suka zo su kama Samson a inda ake kira Lehi. Da alama wurin nan a ƙasar Yahuda yake. Da mutanen Yahuda suka gan su, sun ji tsoro, sai suka ce za su ba su Samson. Mutanen Samson ne da kansu suka ɗaure shi da sabbin igiyoyi guda biyu, suka kai wa Filistiyawan. (Alƙa. 15:9-13) Amma sai “ruhun Yahweh ya sauko a kansa,” ya ba shi iko kuma ya tsintsinke igiyoyin. Sai ya samo “sabon ƙashin bakin jakin da bai daɗe da mutuwa ba” ya yi amfani da shi ya kashe Filistiyawa 1000!—Karanta Alƙalai 15:14-16.

5. Ta yaya yadda Samson ya yi amfani da ƙashin bakin jaki ya nuna cewa da Jehobah ya dogara?

5 Ai ƙashin bakin jaki ba abin da mutum zai yi yaƙi da shi ba ne. To, me ya sa Samson ya yi amfani da shi? Domin ya san cewa Jehobah zai ba shi nasara ko da me ya yi amfani da shi. Samson mutum mai bangaskiya ne. Ya yi amfani da abin da ya samu a lokacin don ya yi nufin Jehobah. Kuma Samson ya ci nasara don ya dogara ga Jehobah.

6. Wane darasi ne za mu iya koya daga labarin Samson game da hidimarmu?

6 Mu ma Jehobah zai iya ba mu ƙarfin yin hidimarmu ko da muna ganin ba za mu iya ba. Kuma Jehobah zai iya yin hakan a hanya mai ban mamaki. Don haka, ka tabbata cewa Jehobah, Allahn da ya ba Samson ƙarfi, Zai taimake ka ka yi nufinsa, in dai ka dogara gare Shi.—K. Mag. 16:3.

7. Wane misali ne ya nuna cewa yana da muhimmanci mu nemi ja-gorancin Jehobah?

7 ꞌYanꞌuwa da yawa da suke aikin gine-gine sun nuna cewa da Jehobah suka dogara. A dā, yawancin sabbin Majamiꞌun Mulki da sauran gine-ginenmu, ꞌyanꞌuwa ne suke zana su, su kuma gina su. Amma saboda yawan mutane da suke yin baftisma, an bukaci a canja wannan tsarin. Don haka, ꞌyanꞌuwan da suke ja-goranci sun roƙi Jehobah ya taimake su kuma suka soma sayan gine-gine, da kuma yi ma wasu kwaskwarima da dai sauransu. Wani ɗanꞌuwa mai suna Robert da ya taimaka a aikin gine-ginenmu a faɗin duniya ya ce: “Da aka zo da wannan sabon tsarin, mutane da yawa ba su so shi ba don ya yi dabam da abin da muka yi shekaru da dama muna yi. Amma ꞌyanꞌuwa sun yi ƙoƙari sun bi sabon tsarin, kuma yanzu muna ganin tabbacin cewa Jehobah yana sa albarka.” Ban da wannan, akwai misalai da yawa da suka nuna yadda Jehobah yake yi wa mutanensa ja-goranci don ya cim ma nufinsa. Zai dace a wasu lokuta mu riƙa tambayar kanmu, ‘Shin, ina neman ja-gorancin Jehobah kuwa? Zan yi canji in da bukata, don in inganta ibadata?’

SAMSON YA YI AMFANI DA ABIN DA JEHOBAH YA TANADAR

8. Da Samson ya ji ƙishi sosai, me ya yi?

8 Wataƙila ka taɓa jin wasu abubuwan ban mamaki da Samson ya yi ban da wannan. Misali, da hannunsa ya kashe zaki. Kuma daga baya ya kashe mayaƙa 30 a birnin Ashkelon na Filistiyawa. (Alƙa. 14:5, 6, 19) Samson ya san cewa in ba da taimakon Jehobah ba, ba zai iya yin abubuwan nan ba. Me ya nuna hakan? Akwai lokacin da ya ji ƙishin ruwa sosai bayan ya kashe Filistiyawa 1,000. Maimakon ya je ya nemi ruwa da kansa, ya yi kira ga Jehobah ya taimaka masa.—Alƙa. 15:18.

9. Ta yaya Jehobah ya amsa roƙon Samson? (Alƙalai 15:19)

9 Jehobah ya ji roƙon Samson kuma ya samo masa ruwa a hanya mai ban mamaki. Da Samson ya sha ruwan, “sai hankalinsa ya komo, ƙarfinsa kuma ya dawo.” (Karanta Alƙalai 15:19.) Da alama cewa an ci gaba da samun ruwa daga wannan wurin da Jehobah ya yi wa Samson tanadi, har lokacin da annabi Sama’ila ya rubuta littafin Alƙalai. Ba mamaki Israꞌilawan da suka yi shekaru suna ganin ruwan nan yana ɓullowa sun yi ta tuna cewa in suna cikin bukata, kuma suka dogara ga Jehobah, zai taimake su.

Da Samson ya sha ruwan da Jehobah ya tanadar, ya samu ƙarfi. Mu ma muna bukatar mu yi amfani da abubuwan da Jehobah yake ba mu don ya ƙara mana bangaskiya (Ka duba sakin layi na 10)

10. Me muke bukatar mu yi idan muna so Jehobah ya taimake mu? (Ka kuma duba hoton.)

10 Mu ma muna bukatar mu dinga dogara ga Jehobah komen baiwarmu, ko kuma abubuwa da yawa da muka cim ma a hidimarsa. Ya kamata mu san kasawarmu kuma mu tuna cewa sai da taimakon Jehobah ne za mu iya yin hidimarmu kuma mu yi nasara. Da Samson ya sha ruwan da Jehobah ya tanadar, ya sami ƙarfin da yake bukata. Mu ma muna bukatar mu yi amfani da abubuwan da Jehobah yake tanada mana don mu ƙarfafa bangaskiyarmu.—Mat. 11:28.

11. Me za mu yi don mu nuna cewa muna dogara ga Jehobah? Ta yaya wasu maꞌaurata suka yi hakan?

11 Ga misalin wani ɗanꞌuwa mai suna Aleksey, wanda ake tsananta masa sosai a ƙasar Rasha. Me ya ba shi ƙarfin jimre yanayoyi masu wuya da ya fuskanta? Shi da matarsa sun saba yin nazari da kuma ibada ta iyali babu fashi. Ɗanꞌuwan ya ce: “Na yi iya ƙoƙarina na ci gaba da yin nazari kuma ina karanta Littafi Mai Tsarki kowace rana. Kowace safiya ni da matata muna tattauna nassin yini kuma mu yi adduꞌa tare.” Me wannan ya koya mana? Maimakon mu dogara ga kanmu, mu dogara ga Jehobah ta wurin yin abubuwan da za su ƙara mana bangaskiya, wato, yin nazarin Littafi Mai Tsarki, da yin adduꞌa, da zuwa taro, da kuma yin waꞌazi da dai sauransu. Idan muka yi hakan, Jehobah zai ba mu ƙarfin da muke bukata don mu ci gaba da bauta masa. Shi ya ba Samson ƙarfi, don haka wannan ƙaramin alhaki ne a gare Shi.

SAMSON BAI FID DA RAI BA

12. Me ya sa soyayyar Samson da Delila ta yi dabam da wadda ya yi da ꞌyan matan Filistiyawa?

12 Samson ajizi ne kamar mu kuma akwai lokutan da ya yi kuskure. Akwai wani kuskure da ya yi da ya jefa shi cikin matsala sosai. Yayin da yake hidimarsa na alƙali, “Samson ya fara son wata macen da ake kiranta Delila, wadda take zama a Kwarin Sorek.” (Alƙa. 16:4) Dā ma ya taɓa yin alkawarin aure da wata ꞌyar Filistiya, amma ‘Allah ne ya bi da Samson domin ya yi haka,’ don “yana neman hanyar da zai hukunta Filistiyawa.” Ban da haka, ya taɓa kwana a gidan wata ƙaruwa a birnin Gaza na Filistiyawa. A lokacin ne Jehobah ya ba shi ƙarfi kuma ya tumbuke ƙofar birnin don cin su da yaƙi ya zo da sauƙi. (Alƙa. 14:1-4; 16:1-3) Amma da alama cewa Delila ꞌyar Israꞌila ce, don haka, soyayyarsa da ita ba don ya yaƙi Filistiyawa ba ne, son zuciyarsa ne ya kai shi.

13. Ta yaya Delila ta sa Samson cikin matsala?

13 Delila ta yarda Filistiyawa su ba ta kuɗi mai yawa don ta ci amanar Samson. Mai yiwuwa son da yake mata ne ya sa ya kasa ganin makircin da take ƙullawa. Ko ma mene ne ya sa, mun dai san cewa Delila ta yi ta matsa masa ya gaya mata sirrin ƙarfinsa, har sai da ya gaya mata. Abin baƙin ciki, Samson ya sa kansa a cikin yanayin da ƙarshenta, ya rasa ƙarfinsa kuma ya ɓata wa Jehobah rai.—Alƙa. 16:16-20.

14. Me ya faru da Samson don ya yarda da Delila?

14 Samson ya sha wuya sosai domin ya yarda da Delila maimakon ya dogara ga Jehobah. Filistiyawa sun kama shi kuma sun ƙwaƙule masa idanu. Sun sa shi a kurkuku a birnin Gaza, inda ya taɓa tumbuke ƙofar birninsu. A wurin, sun mai da shi bawa mai yi musu niƙa. A-kwana-a-tashi, sai suka kawo shi inda suke yin wani biki, suka yi hadaya ga allahnsu mai suna Dagon, don suna ganin shi ne ya sa suka iya kama Samson. Sai suka kawo shi daga kurkuku “ya yi musu wasa” don su yi masa dariya.—Alƙa. 16:21-25.

Jehobah ya ba wa Samson ƙarfi don Ya hukunta Filistiyawa (Ka duba sakin layi na 15)

15. Ta yaya Samson ya sake nuna cewa ya dogara ga Jehobah? (Alƙalai 16:28-30) (Ka duba hoton da ke shafin farko.)

15 Ba ƙaramin kuskure ne Samson ya yi ba, duk da haka, bai fid da rai ba. Ya nemi yadda zai cim ma aikin da Jehobah ya ba shi na yaƙar Filistiyawa. (Karanta Alƙalai 16:28-30.) Samson ya roƙi Jehobah ya taimake shi ya “rama a kan Filistiyawa.” Jehobah ya ji adduꞌarsa kuma ya sake ba shi ƙarfi. Hakan ya sa Samson ya yi babban nasara a kan Filistiyawa, fiye ma da waɗanda ya yi a baya.

16. Me muka koya daga abin da Samson ya yi duk da kuskurensa?

16 Duk da cewa Samson ya yi fama da sakamakon kuskuren da ya yi, bai daina ƙoƙarin yin nufin Jehobah ba. Mu ma ko da mun yi kuskure kuma an yi mana gyara, ko mun rasa hidimar da muke yi, kada mu fid da rai. Mu tuna cewa Jehobah yana so ya yi mana gafara, komen kuskuren da muka yi. (Zab. 103:8-10) Jehobah zai iya amfani da mu mu yi nufinsa kamar yadda ya yi da Samson.

Ba mamaki kuskuren da Samson ya yi ya dame shi sosai, amma bai fid da rai ba. Mu ma kada mu fid da rai (Ka duba sakin layi na 17-18)

17-18. Wane ƙarfafa ne ka samu daga labarin Michael? (Ka kuma duba hoton.)

17 Ga abin da ya faru da wani ɗanꞌuwa mai suna Michael. Yana hidima da ƙwazo, shi bawa mai hidima ne kuma majagaba ne. Ana nan, sai ya yi wani kuskure kuma aka dakatar da shi daga hidimomin da yake yi a ikilisiya. Ɗanꞌuwan ya ce: “Kafin wannan lokacin, ina hidimata da ƙwazo sosai, sai kawai na rasa kome. Na ji kamar na yi karo da bango. Ko da yake na san Jehobah ba zai yashe ni ba, na damu don ina ganin kamar dangantakata da Jehobah ba za ta taɓa zama kamar dā ba, kuma na ji kamar ba zan sake iya yin hidima a ikilisiya kamar dā ba.”

18 Abin farin cikin shi ne, Michael bai fid da rai ba. Ya ce: “Na mai da hankali ga yadda zan gyara dangantakata da Jehobah. Na yi ta yin adduꞌa, da nazari, da kuma tunani mai zurfi.” A-kwana-a-tashi, an sake naɗa Michael ya yi hidimomin da yake yi a dā. Yanzu shi dattijo ne, da kuma majagaba. Ya ce: “Taimako da kuma ƙarfafa da na samu, musamman daga wurin dattawa, sun sa na ga cewa har ila, Jehobah yana ƙauna ta. Yanzu zan iya bauta wa Jehobah a ikilisiya da zuciya mai tsabta. Abin da ya faru da ni ya koya min cewa Jehobah zai yafe wa duk wanda ya tuba da gaske.” Mu ma tabbas, Jehobah zai yi amfani da mu, kuma zai yi mana albarka ko da mun yi kuskure, muddin mun yi iya ƙoƙarinmu mu yi gyara kuma mun ci gaba da dogara da shi.—Zab. 86:5; K. Mag. 28:13.

19. Wane ƙarfafa ne ka samu daga labarin Samson?

19 A wannan talifin, mun ga wasu abubuwan ban mamaki da Samson ya yi, kuma mun ga cewa shi ma ya yi kuskure. Amma duk da kuskuren da ya yi dangane da Delila, ya ci gaba da yin ƙoƙarin bauta ma Jehobah, kuma Jehobah bai yasar da shi ba. Allah ya sake yin amfani da shi a hanya mai ban mamaki. Kuma Jehobah ya amince da shi a matsayin mutum mai bangaskiya sosai, har ya sa sunansa a cikin masu bangaskiya da aka ambata a Ibraniyawa sura 11. Hakika, abin ban ƙarfafa ne mu san cewa Ubanmu na sama wanda muke bauta wa, mai ƙauna ne kuma yana so ya taimaka mana idan muna cikin matsala! Don haka, kamar Samson, bari kowannenmu ya dinga roƙon Jehobah yana cewa: “Ka tuna da ni! Ina roƙonka, ya Allah, ka sāke ba ni ƙarfi.”—Alƙa. 16:28.

WAƘA TA 3 Ƙarfinmu, Begenmu da Makiyayinmu

a Samson sunan wani ne a Littafi Mai Tsarki da mutane da yawa suka sani, har da waɗanda ba su san Nassosi sosai ba. Mutane sun yi waƙoƙi da wasanni da kuma fina-finai game da Samson. Amma ban da cewa labarinsa yana da daɗi, akwai darussa da yawa da za mu iya koya daga mutumin nan mai bangaskiya.