Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 39

Mai Sauƙin Kai Jarumi Ne

Mai Sauƙin Kai Jarumi Ne

“Kada mai hidimar Ubangiji ya zama mai yawan gardama, amma dai ya zama mai kirki ga kowa.”—2 TIM. 2:24.

WAƘA TA 120 Mu Koyi Nuna Sauƙin Kai Kamar Yesu

ABIN DA ZA A TATTAUNA a

1. Wane irin tambaya ne za a iya yi mana a wurin aiki ko a makaranta?

 YAYA kake ji idan abokin aikinka ko ɗan makarantarku ya yi maka tambaya game da imaninka? Hankalinka yakan tashi ne? Yawancinmu ba ya yi mana sauƙi. Amma irin tambayoyin nan za su iya taimaka mana mu san abin da mutumin yake tunani, ko imaninsa, har ma su sa mu iya yi masa waꞌazi. Amma wasu sukan yi mana tambaya don ba su yarda da imaninmu ba, ko don suna so su yi gardama. A yawancin lokaci suna hakan ne don an gaya musu wani abu da ba gaskiya ba game da mu. (A. M. 28:22) Ban da haka, a “kwanakin ƙarshe” muke, don haka mutane da yawa sun zama masu “ƙin yarda da juna” da kuma “marasa tausayi.”—2 Tim. 3:1, 3, New World Translation.

2. Me ya sa yake da kyau mu zama masu sauƙin kai?

2 Ƙila ka ce, ‘Ta yaya zan natsu kuma in amsa wa mutum da alheri idan yana ƙoƙarin ƙaryata abin da na yi imani da shi?’ Abin da zai taimaka maka shi ne, sauƙin kai. Mutum mai sauƙin kai yakan kame kansa idan aka ɓata masa rai ko bai san amsar da zai bayar ba. (K. Mag. 16:32) Kana iya cewa, ‘Amma gaskiya wani lokaci yin hakan ba sauƙi.’ Me zai taimake ka ka zama mai sauƙin kai? Ta yaya za ka amsa wa mutum cikin sauƙin kai idan ya yi ƙoƙarin ƙaryata imaninka? Iyaye, ta yaya za ku taimaki yaranku su kāre imaninsu cikin sauƙin kai? Bari mu bincika.

YADDA ZA KA ZAMA MAI SAUƘIN KAI

3. Me ya nuna cewa mutum mai sauƙin kai jarumi ne ba rago ba? (2 Timoti 2:24, 25)

3 Mai sauƙin kai jarumi ne, ba rago ba. Don idan mutum ya shiga yanayi mai wuya, yana bukatar ƙarfin zuciya kafin ya iya kame kansa. Sauƙin kai ko kuma tawaliꞌu hali ne da “ruhun Allah yake haifar.” (Gal. 5:22, 23) A Helenanci, ana amfani da kalmar nan sauƙin kai don a kwatanta yadda akan sa doki mai ƙarfi sosai ya natsu. Ka yi tunanin wannan, duk da cewa an sa dokin ya natsu, hakan ba ya nufin cewa ya rasa ƙarfinsa. Mu ma ta yaya za mu koyi zama masu ƙarfi da kuma sauƙin kai? Ba za mu iya yin hakan da kanmu ba, muna bukatar mu roƙi Allah ya ba mu ruhunsa don ya taimaka mana mu zama da wannan halin. Mutane da yawa sun iya yin hakan. Misali, akwai ꞌyanꞌuwanmu da yawa da mutane suka so su yi gardama da su ko su ɓata musu rai, amma sun nuna sauƙin kai kuma sun amsa da alheri. Abin da ꞌyanꞌuwan suka yi ya burge wasu mutane. (Karanta 2 Timoti 2:24, 25.) Ta yaya kai ma za ka bi misalinsu?

4. Me labarin Ishaku ya koya mana game da sauƙin kai?

4 Akwai labarai da yawa a Littafi Mai Tsarki da suka nuna muhimmancin sauƙin kai. Misali, da Ishaku yake zama a yankin Filistiyawa, wato a Gerar, mutanen wurin sun yi ƙishin sa sosai da har suka tottoshe rijiyoyin da bayin babansa suka tona. Amma Ishaku bai yi ƙoƙarin kwace hakkinsa ba. A maimako, ya bar musu, sai ya ƙaura da iyalinsa, ya kuma tona wasu rijiyoyin. (Far. 26:12-18) Duk da haka, Filistiyawan sun ce ruwan da ke wannan wurin ma nasu ne. Har ila, Ishaku bai yi faɗa da su ba. (Far. 26:19-25) Me ya taimaka masa ya ci gaba da nuna sauƙin kai duk da cewa mutane sun yi ta ƙoƙarin ɓata masa rai? Ba shakka ya koyi hakan daga wurin iyayensa ne. Don babansa Ibrahim mutum ne mai son zaman lafiya, mamarsa Saratu kuma mace ce mai “sauƙin kai da kuma natsuwa.”—1 Bit. 3:4-6; Far. 21:22-34.

5. Ka ba da misali da ya nuna cewa iyaye Kiristoci za su iya koyar da yaransu su zama masu sauƙin kai.

5 Iyaye, za ku iya koya wa yaranku muhimmancin zama masu sauƙin kai. Abin da iyayen wani mai suna Max b suka yi ke nan. Shekarunsa 17. Yana haɗuwa da mutane masu zafin rai a makaranta da kuma a waꞌazi. Iyayensa sun yi ta ƙoƙari har sai da suka koya masa ya zama mai sauƙin kai. Sun ce, “Yanzu Max ya gane cewa rago ne yake ramawa idan aka ɓata masa rai, don abin da ya fi sauƙi ke nan. Mutum mai ƙarfin zuciya ne yake iya kame kansa.” Daɗin daɗawa, yanzu Max ya zama mai sauƙin kai.

6. Ta yaya yin adduꞌa zai taimaka mana mu ƙara zama masu sauƙin kai?

6 Me zai taimaka mana idan ranmu ya ɓace don wani ya faɗi abin da bai dace ba game da Jehobah ko yana kushe Littafi Mai Tsarki? Mu yi adduꞌa, mu roƙi Jehobah ya ba mu ruhunsa da kuma hikima don mu amsa cikin sauƙin kai. Amma idan mun riga mun yi kuskure kuma mun ga cewa yadda muka amsa wa mutumin bai dace ba fa? Zai dace mu yi adduꞌa game da batun kuma mu yi tunanin yadda za mu ba da amsar da ta dace idan ya sake faruwa. In muka yi hakan, Jehobah zai ba mu ruhu mai tsarki don mu iya kame kanmu kuma mu nuna sauƙin kai.

7. Idan muka haddace wasu ayoyi, ta yaya hakan zai taimake mu saꞌad da aka ɓata mana rai? (Karin Magana 15:1, 18)

7 Akwai Nassosi da yawa da za su taimaka mana mu san abin da ya kamata mu yi idan aka ɓata mana rai. Ruhun Allah zai iya sa mu tuna Nassosin nan. (Yoh. 14:26) Misali, akwai Nassosi a littafin Karin Magana da za su iya taimaka mana mu nuna sauƙin kai. (Karanta Karin Magana 15:1, 18.) Littafin nan ya kuma nuna amfanin kame kanmu idan aka ɓata mana rai.—K. Mag. 10:19; 17:27; 21:23; 25:15.

YADDA HANKALI YAKE SA MU NUNA SAUƘIN KAI

8. Me ya sa ya kamata mu yi tunani a kan dalilin da ya sa mutum yake ƙoƙarin ƙaryata imaninmu?

8 Hankali ko kuma fahimi zai iya taimaka mana. (K. Mag. 19:11) Mutum mai hankali yakan kame kansa in ya ji an faɗi abin da bai dace ba game da imaninsa. Don a yawancin lokaci, idan mutane suka yi mana tambaya ko sun faɗi wani abu, ba ma sanin ainihin dalilin da ya sa suka yi hakan. Don haka, kafin mu ce wani abu, zai dace mu tuna cewa mai yiwuwa ba mu san abin da ya sa mutumin ya kawo zancen ba.—K. Mag. 16:23.

9. Ta yaya Gideyon ya nuna hankali ko kuma fahimi da kuma sauƙin kai saꞌad da yake shaꞌani da mutanen Ifrayim?

9 Ka lura da yadda Gideyon ya bi da mutanen Ifrayim, wato Ifraimu. Sun zo suna masa faɗa a kan cewa me ya sa bai kira su tun farko, su bi shi yaƙan magabtan Israꞌilawa ba. Amma mene ne ainihin dalilin da ya sa suke fushi? Ƙila don suna ganin bai kamata a yi ban da su ba. Ko da me dalilinsu, Gideyon ya yi ƙoƙari ya fahimce su kuma ya amsa musu cikin sauƙin kai. Ƙarshenta “sai suka daina fushi.”—Alƙa. 8:1-3.

10. Me zai taimake mu mu san yadda za mu amsa wa mutum idan ya yi mana tambaya game da imaninmu? (1 Bitrus 3:15)

10 Ƙila abokin aikinmu ko ɗan makarantarmu ya tambaye mu wani abu game da imaninmu. Idan hakan ya faru, zai dace mu yi iya ƙoƙarinmu mu kāre imaninmu, amma mu daraja mutumin. (Karanta 1 Bitrus 3:15.) Mu yi amfani da tambaya don mu san abin da yake a zuciyarsa. Ko da mene ne ya sa mutum ya tā da wani batu, zai dace mu amsa masa cikin natsuwa kuma da alheri. Idan muka amsa masa da kyau, hakan zai iya sa ya canja raꞌayinsa. Ko da mutumin ya yi mana baƙar magana ko ya zolaye mu, burinmu shi ne mu amsa masa da alheri.—Rom. 12:17.

Idan ka fara da tunanin ko me ya sa mutum ya gayyace ka zuwa bikin ranar haifuwa, hakan zai sa ka ba da amsa mafi dacewa (Ka duba sakin layi na 11-12)

11-12. (a) Wane tunani ne ya kamata mu yi kafin mu amsa tambaya game da imaninmu? (Ka kuma duba hoton.) (b) Ka ba da misalin yadda yin hakan zai iya ba mu damar bayyana imaninmu a hanya mai gamsarwa.

11 Misali, idan wani abokin aikinmu ya tambaye mu abin da ya sa ba ma bikin zagayowar ranar haifuwa (birthday), ka dakata ka yi tunani. Shin, mutumin yana ganin kamar ba a barin mu mu yi wani abin jin daɗi gabaki ɗaya ne? Ko dai yana tsoron cewa da yake ba ma yin wannan bikin, za mu ɓata dangantaka da ke tsakanin maꞌaikatan kamfanin ne? Mai yiwuwa abin da kawai yake bukata shi ne mu gode masa don yadda ya nuna cewa ya damu da abokan aikinsa, kuma mu tabbatar masa cewa mu ma muna so mu yi zaman lafiya da abokan aikinmu. Ƙila hakan zai sa hankalinsa ya kwanta, kuma ya so jin abin da za mu gaya masa daga Littafi Mai Tsarki game da bikin ranar haifuwa.

12 Za mu iya yin amfani da wannan dabarar idan aka yi mana wata tambaya game da imaninmu. Misali, wani a makarantarmu zai iya cewa ya kamata Shaidun Jehobah su canja raꞌayinsu game da luwaɗi. In ka ji hakan, ka yi tunanin wannan: Mai yiwuwa bai gama gane raꞌayin Shaidun Jehobah game da luwaɗi ba. Mai yiwuwa kuma wani abokinsa ko danginsa ɗan luwaɗi ne shi ya sa. Ban da haka, ƙila yana ganin kamar mun ƙi jinin waɗanda suke irin yin wannan rayuwar ne. Wataƙila muna bukatar mu tabbatar masa da cewa muna ƙaunar kowa, kuma mun san cewa kowa yana da ꞌyancin zaɓan irin rayuwar da zai yi. c (1 Bit. 2:17) Ƙila idan muka yi hakan, za mu samu damar gaya masa abin da Littafi Mai Tsarki ya ce, da kuma yadda bin sa yake inganta rayuwarmu.

13. Idan wani ya zolaye ka don ka yi imani da Allah, me za ka iya yi don ka taimaka masa?

13 Idan mutum ya nuna mana cewa shi bai yarda da imaninmu ba, kar mu yi saurin tunanin cewa mun san abin da ke zuciyarsa. (Tit. 3:2) Misali, idan ɗan makarantarku ya ce maka, ‘Jahilai ne suke yin imani da Allah,’ kar ka yi zaton cewa ya yi imani da juyin halitta kuma ya san batun ciki da waje. Gaskiyar ita ce, mai yiwuwa abin da ya ji ana faɗa ne kawai shi ma yake faɗa. Don haka, maimakon ka shiga yi masa bayani game da juyin halitta, zai fi dacewa ka taimaka masa ya yi tunani game da batun bayan rabuwarku. Misali, za ka iya nuna masa wani abu game da juyin halitta a jw.org/ha don ya je ya bincika. Ƙila ka ga cewa daga baya mutumin ya yarda ku tattauna wani talifi ko bidiyo da ya gani. Hakika, idan muka daraja mutum kamar haka, zai iya taimaka masa ya sake tunani.

14. Ta yaya Niall ya yi amfani da dandalinmu don ya nuna wa ɗan ajinsu cewa wani abin da mutane suke faɗa game da mu ba gaskiya ba ne?

14 Wani matashi mai suna Niall ya taɓa amfani da abin da ke dandalinmu don ya nuna cewa abin da mutane suke faɗa game da Shaidun Jehobah ba gaskiya ba ne. Niall ya ce: “Akwai wani ɗan ajinmu da yakan ce na fi so in yarda da littafin ƙage maimakon bayanan da aka tabbatar da su, shi ya sa ba na so in yarda da koyarwar ꞌyan kimiyya.” Da yake yaron bai bar Niall ya gaya masa dalilin imaninsa ba, sai Niall ya nuna masa dandalin jw.org kuma ya ce masa ya duba sashen “Ilimin Kimiyya da Littafi Mai Tsarki.” Daga baya, Niall ya ga cewa ɗan ajinsu ya karanta talifin, har ma sun samu sun tattauna game da yadda rayuwa ta soma. Kai ma za ka iya yin nasara idan ka bi misalin Niall.

KU KOYA WA YARANKU YADDA ZA SU BA DA AMSA

15. Ta yaya iyaye za su taimaka wa yaransu su iya ba da amsa da sauƙin kai idan aka yi musu tambaya game da imaninsu?

15 Iyaye za su iya koya wa yaransu yadda za su ba da amsa cikin sauƙin kai idan aka tambaye su game da imaninsu. (Yak. 3:13) Wasu sukan gwada yadda za su yi hakan saꞌad da suke ibada ta iyali. Sukan zaɓi batutuwan da za a iya yi wa yaransu tambaya a kai a makaranta, sai su tattauna amsar da ta fi dacewa kuma su gwada yadda yaran za su ba da amsar. Saꞌan nan su koya wa yaran yadda za su yi magana mai daɗin ji kuma su yi hakan cikin sauƙin kai.—Ka duba akwatin da ya ce, “ Gwada Yinsa a Gida Zai Taimaka Muku.”

 

16-17. Ta yaya yara za su amfana idan iyaye suka taimaka musu su gwada yadda za su kāre imaninsu?

16 Idan iyaye suna sa yaransu su gwada yadda za su amsa tambaya, hakan zai taimaka ma yaran su ba da amsa mai gamsarwa. Kuma zai sa yaran da kansu su ƙara gaskata cewa imaninsu gaskiya ne. Akwai jerin talifofin nan, “Tambayoyin Matasa,” da kuma “Fallayen Rubutu don Matasa” a jw.org/ha. An shirya fallayen nan ne don a taimaki matasa su ƙara gaskata da abubuwan da suka yi imani da su, kuma su shirya amsar da za su bayar in aka yi musu tambaya. Idan muka bincika talifofin da ke sashen nan a iyalinmu, hakan zai taimaka ma dukanmu mu san yadda za mu kāre imaninmu cikin sauƙin kai, kuma a hanya mai kayatarwa.

17 Wani matashi mai suna Matthew ya amfana sosai don tun daga gida ya gwada yadda zai kāre imaninsa. A ibada ta iyalinsu, iyayensa sukan bincika batutuwan da za su iya tasowa a aji tare da shi. Matthew ya ce: “Mukan yi tunanin tambayar da za a iya yi min, saꞌan nan mu gwada yadda zan ba da amsa bisa ga bincike da muka yi. Idan na fahimci dalilin da ya sa na yi imani da abu sosai, yana ba ni ƙarfin zuciya, kuma yana taimaka min in ba wa mutane amsa cikin sauƙin kai.”

18. Bisa ga Kolosiyawa 4:6, wane abu mai muhimmanci ne ake so mu yi?

18 A wani lokaci, ko da mun bayyana imaninmu da kyau, ba kowa ne zai yarda ba. Amma idan muna yi wa mutane magana cikin hikima da sauƙin kai, za mu ga amfanin sa. (Karanta Kolosiyawa 4:6.) Idan muna bayyana imaninmu ga wani, kamar muna jefa masa kwallo ne. Za mu iya jefa masa a hankali, ko kuma mu jefa masa da ƙarfi. Idan muka jefa masa a hankali, zai kama cikin sauƙi kuma zai so ya ci gaba da wasan. Haka ma idan muna yi wa mutane magana cikin hikima da sauƙin kai, zai iya sa su so jin mu kuma su so tattaunawar. Idan duk da hakan, mutumin yana so ya yi gardama ne ko ya zolaye mu, za mu iya ƙyale shi. (K. Mag. 26:4) Amma yawancin mutane ba za su yi hakan ba, za su so su saurare mu.

19. Me ya sa yake da kyau mu nuna sauƙin kai a duk saꞌad da muke kāre imaninmu?

19 Hakika, za mu amfana sosai idan muka zama masu sauƙin kai. Ka roƙi Jehobah ya ba ka ƙarfin kame kanka don ka amsa cikin sauƙin kai idan aka yi maka tambaya ko an kushe ka don imaninka. Ka tuna cewa idan ka amsa da alheri, hakan zai taimaka kar tattaunawar ta koma ta zama gardama. Kuma idan ka amsa cikin sauƙin kai da ban girma, hakan zai iya sa wasu su canja raꞌayinsu game da mu da kuma koyarwar Littafi Mai Tsarki. Ka “zauna a shirye kullum” don ka bayyana imaninka, kuma ka “yi shi da sauƙin kai da ban girma.” (1 Bit. 3:15) Bari sauƙin kanka ya nuna cewa kai jarumi ne!

WAƘA TA 88 Ka Koya Mini Hanyoyinka

a Talifin nan zai ba da shawarwari a kan yadda za mu nuna sauƙin kai saꞌad da muke kāre imaninmu, ko da an ɓata mana rai ko an zolaye mu.

b An canja sunan.

c Talifin nan mai jigo, “Mene ne Littafi Mai Tsarki Ya Ce Game da Luwaɗi?” zai iya taimaka maka. Yana a jw.org/ha.

d Akwai talifofi da za su iya taimaka maka a jw.org/ha. Ka duba jerin talifofin nan, “Tambayoyin Matasa” da kuma “Tambayoyin da Ake Yawan Yi Game da Shaidun Jehobah.”