Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 38

Matasa, Wane Irin Rayuwa Ne Za Ku Yi?

Matasa, Wane Irin Rayuwa Ne Za Ku Yi?

“Fahimta . . . ta yi ta kiyaye ka.”—K. MAG. 2:11.

WAƘA TA 135 Jehobah Ya Ce: “Ɗana Ka Yi Hikima”

ABIN DA ZA A TATTAUNA a

1. Wane yanayi mai wuya ne Yowash da Uzziya da kuma Josiya suka fuskanta?

 A CE an naɗa ka ka yi mulki a kan mutanen Jehobah saꞌad da kake ƙarami, yaya za ka ji? Yaya za ka yi amfani da ikon da kake da shi? A Littafi Mai Tsarki, akwai labaran yara da yawa da suka zama sarakuna a Yahuda. Alal misali, Yowash yana shekara 7 saꞌad da ya zama sarki, Uzziya 16, Josiya kuma 8. Ba mamaki hakan bai yi musu sauƙi ba. Duk da hakan, taimakon da suka samu daga wurin Jehobah da ma wasu mutane, ya sa sun iya yin abubuwa masu kyau da yawa.

2. Me ya sa yake da kyau mu bincika labarin Yowash da Uzziya da kuma Josiya?

2 Ko da yake mu ba sarakuna ba ne, za mu iya koyan darussa daga mutane ukun nan da muka ambata. Akwai lokutan da suka yanke shawarwari masu kyau, kuma akwai lokutan da suka yanke shawarwari marasa kyau. Daga misalansu, za mu ga dalilin da ya sa yake da kyau mu ci gaba da yin abokan kirki, da nuna sauƙin kai, da kuma neman nufin Jehobah.

KA YI ABOKAN KIRKI

A yau, za mu iya yin koyi da Yowash ta wajen bin shawarar abokan kirki (Ka duba sakin layi na 3, 7) c

3. Ta yaya Yehoyida ya taimaka wa Yowash ya yanke shawarwari masu kyau?

3 Ka yanke shawarwari masu kyau kamar Yowash. Sarki Yowash ya yanke shawarwari masu kyau saꞌad da yake ƙarami. Da yake babansa ya rasu, ya bi umurnin Babban Firist mai suna Yehoyida. Wannan firist ya tarbiyantar da Yowash kamar ɗansa. Saboda tarbiya mai kyau da Yehoyida ya ba wa Yowash, Yowash ya bauta wa Jehobah kuma ya taimaka wa mutane su yi hakan. Ya ma sa an gyara haikalin Jehobah.—2 Tar. 24:1, 2, 4, 13, 14.

4. Ta yaya za mu amfana idan muna son dokokin Jehobah kuma muna bin su? (Karin Magana 2:1, 10-12)

4 Idan ana koya maka ka ƙaunaci Jehobah kuma ka yi irin rayuwar da yake so, abu mai kyau ne ake maka. (Karanta Karin Magana 2:1, 10-12.) Iyaye za su iya koyar da yaransu a hanyoyi da yawa. Ka yi laꞌakari da yadda mahaifin wata ꞌyarꞌuwa mai suna Katya ya taimaka mata ta yanke shawarwari masu kyau. Yayin da mahaifinta yake kai ta makaranta a kowace rana, yakan tattauna nassin yini da ita. Ta ce, “Hakan yana taimaka mini in yi abin da ya dace idan na shiga matsala a makaranta.” Amma idan kana ganin shawarwarin da iyayenka suke ba ka daga Littafi Mai Tsarki ba sa barin ka ka yi abin da kake so kuma fa? Me zai taimake ka ka yi musu biyayya? Wata ꞌyarꞌuwa mai suna Anastasia ta tuna yadda iyayenta suka bayyana mata dalilin da ya sa suka ba ta wani umurni. Ta ce, “Hakan ya taimaka min in ga umurnin a matsayin abin da yake kāre ni, maimakon abin da ke takura min.”

5. Ta yaya shawarwarin da kake yankewa za su shafi iyayenka da kuma Jehobah? (Karin Magana 22:6; 23:15, 24, 25)

5 Iyayenka za su yi farin ciki idan kana yin biyayya da umurnin da suka ba ka daga Littafi Mai Tsarki. Abin da ya fi muhimmanci ma shi ne, za ka sa Jehobah farin ciki kuma za ka zama abokinsa har abada. (Karanta Karin Magana 22:6; 23:15, 24, 25.) Babu shakka, wannan dalili ne mai kyau na yin biyayya kamar Yowash saꞌad da yake ƙarami!

6. Shawarar wa Yowash ya fara bi, kuma wane sakamako ne hakan ya jawo masa? (2 Tarihi 24:17, 18)

6 Ka koyi darasi daga shawarwari marasa kyau da Yowash ya yanke. Bayan Yehoyida ya mutu, Yowash ya soma bin abokan banza. (Karanta 2 Tarihi 24:17, 18.) Ya bi shawarar dattawan Yahuda waɗanda ba sa ƙaunar Jehobah. Ya kamata Yowash ya guji mugayen mutanen nan, ko ba haka ba? (K. Mag. 1:10) A maimako, ya bi shawarwari marasa kyau da suka ba shi. Har Yowash ya sa an kashe Zakariya wanda danginsa ne, domin ya ja masa kunne. (2 Tar. 24:20, 21; Mat. 23:35) Wannan wawanci ne da kuma mugunta! Da farko, Yowash yana ƙaunar Jehobah, amma daga baya ya daina bauta ma Jehobah kuma ya zama mai kisa. A ƙarshe, bayinsa sun kashe shi. (2 Tar. 24:22-25) Da a ce ya ci gaba da bin umurnan Jehobah, da na waɗanda suke ƙaunar Jehobah, da ba haka rayuwarsa ta ƙare ba! Wane abu ne ka koya daga misalin nan?

7. Su wa ya kamata ka yi abokantaka da su? (Ka kuma duba hoton.)

7 Wani darasi da za mu iya koya daga shawara marar kyau da Yowash ya yanke shi ne, muna bukatar mu yi abokan kirki, wato waɗanda suke ƙaunar Jehobah kuma suke so su faranta masa rai. Bai kamata mu ce sai tsaranmu ne kawai za mu yi abokantaka da su ba. Ka tuna cewa Yehoyida ya girmi Yowash sosai, duk da haka sun zama abokai. Ka yi wa kanka tambayoyin nan: ‘Shin abokaina suna taimaka min in kasance da bangaskiya sosai? Suna ƙarfafa ni in yi irin rayuwar da Jehobah yake so? Sukan yi magana game da Jehobah da kuma gaskiyar da yake koya mana? Suna son ƙaꞌidodin Jehobah? Idan na yi abin da bai dace ba, sukan gaya min kuskurena?’ (K. Mag. 27:5, 6, 17) Gaskiyar ita ce, idan abokanka ba sa ƙaunar Jehobah, to ba ka bukatar su. Amma idan abokanka suna ƙaunar Jehobah, kar ka bar su domin za su taimaka maka!—K. Mag. 13:20.

8. Idan muna amfani da hanyoyin sadarwa ta intane, me ya kamata mu yi laꞌakari da shi?

8 A yau, akwai hanyoyi masu kyau da za mu iya tattaunawa da ꞌyanꞌuwanmu da kuma abokan arziki ta intane. Amma wasu suna amfani da wannan hanyar don su burge mutane, ta wurin tura hotuna ko kuma bidiyoyin abubuwan da suka saya ko kuma abubuwan da suka yi. Idan kana amfani da wannan hanyar sadarwa, ka tambayi kanka: ‘Shin ina yin hakan don in burge mutane ne? Shin ina so in taimaka wa mutane ne ko kuma ina so su yaba min? Shin raꞌayoyin mutane da ke amfani da wannan hanyar sadarwar sukan shafi tunanina da furucina da kuma abubuwan da nake yi a hanyar da ba ta dace ba?’ Ɗanꞌuwa Nathan Knorr wanda memban Hukumar da Ke Kula da Ayyukanmu ne a dā ya ce: “Kada ka yi ƙoƙarin burge mutane. Don ƙarshenta ba za ka burge kowa ba. Ka faranta wa Jehobah rai, hakan zai sa ka burge duk waɗanda suke ƙaunar sa.”

KA CI GABA DA NUNA SAUƘIN KAI

9. Mene ne Jehobah ya taimaka ma Uzziya ya iya yi? (2 Tarihi 26:1-5)

9 Ka yanke shawarwari masu kyau kamar Uzziya. Saꞌad da Sarki Uzziya yake ƙarami, ya nuna sauƙin kai. Ya koyi jin “tsoron Allah.” Ya yi rayuwa na shekaru 68 kuma Jehobah ya albarkace shi a yawancin shekarun. (Karanta 2 Tarihi 26:1-5.) Uzziya ya ci yawancin maƙiyan ƙasarsa da yaƙi, kuma ya kāre birnin Urushalima sosai. (2 Tar. 26:6-15) Babu shakka, Uzziya ya ji daɗi sosai don abubuwan da Jehobah ya taimaka masa ya yi.—M. Wa. 3:12, 13.

10. Yaya rayuwar Uzziya ta ƙare?

10 Ka koyi darasi daga kuskuren da Uzziya ya yi. Sarki Uzziya ya saba ba wa mutane umurni kuma su bi. Mai yiwuwa hakan ya sa yana ganin zai iya yin duk abin da yake so. Wata rana, Uzziya ya shiga haikalin Jehobah, kuma ya so ya kona turare a kan bagaden Jehobah, duk da cewa sarakuna ba su da izinin yin hakan. (2 Tar. 26:16-18) Babban Firist mai suna Azariya ya gargaɗe shi, amma hakan ya sa Uzziya fushi sosai. Uzziya bai riƙe amincinsa ga Jehobah ba, kuma hakan abin baƙin ciki ne. Saboda rashin amincinsa, Jehobah ya sa ya kamu da cutar kuturta. (2 Tar. 26:19-21) Da a ce ya ci gaba da nuna sauƙin kai, da ba haka rayuwarsa ta ƙare ba!

Kada mu yi takama da abubuwan da muke iya yi a ibadarmu, a maimako, mu miƙa yabo ga Jehobah (Ka duba sakin layi na 11) d

11. Me zai taimaka mana mu ci gaba da nuna sauƙin kai? (Ka kuma duba hoton.)

11 Da Uzziya ya zama mai iko sosai, sai ya manta cewa Jehobah ne ya ba shi wannan ikon. Mene ne hakan ya koya mana? Zai dace mu ci gaba da tuna cewa Jehobah ne ya ba mu dukan abubuwan da muke morewa a rayuwarmu, da hidimarmu. Maimakon mu yi takama a kan abubuwan da muka cim ma, zai dace mu gode wa Jehobah domin shi ne yake taimaka mana. b (1 Kor. 4:7) Zai dace mu tuna cewa mu ajizai ne kuma muna bukatar Jehobah ya riƙa yi mana gyara. Wani ɗanꞌuwa da ya ba wa shekaru 60 baya ya rubuta cewa: “Wani darasin da na koya shi ne, kada in yi fushi ko kuma in yi sanyin gwiwa idan an nuna min kuskurena. Idan aka yi min gyara saboda kuskuren da na yi, nakan yi iya ƙoƙarina don kada in sake yin kuskuren, kuma in ci gaba da bauta ma Jehobah iya gwargwadon ƙarfina.” Gaskiyar ita ce, idan muna biyayya ga Jehobah, kuma muna da sauƙin kai, za mu ji daɗin rayuwa sosai.—K. Mag. 22:4.

KA CI GABA DA NEMAN NUFIN JEHOBAH

12. Ta yaya Josiya ya nemi nufin Jehobah saꞌad da yake matashi? (2 Tarihi 34:1-3)

12 Ka yanke shawarwari masu kyau kamar Josiya. Shekarun Josiya 16 ne kawai saꞌad da ya soma neman nufin Jehobah. Yana so ya san nufin Jehobah kuma ya yi abin da Jehobah yake so. Amma abubuwa ba su yi wa wannan sarkin sauƙi ba. A lokacin, yawancin mutane suna bauta ma allolin ƙarya. Don haka, Josiya yana bukatar ƙarfin zuciya don ya hana su. Kuma abin da ya yi ke nan! Kafin Josiya ya kai shekaru 20, ya soma kawar da bautar gumaka daga ƙasar.—Karanta 2 Tarihi 34:1-3.

13. Idan ka yi alkawarin bauta ma Jehobah, yaya hakan zai shafi rayuwarka?

13 Ko da kai yaro ƙarami ne, za ka iya koya game da Jehobah da kuma halayensa masu kyau kamar yadda Josiya ya yi. Yin hakan zai sa ka yi alkawarin bauta ma Jehobah. Yaya hakan zai shafi rayuwarka? Wani mai suna Luke ya yi baftisma saꞌad da yake shekara 14. Bayan da ya yi alkawarin bauta wa Jehobah, ya ce: “Daga yanzu, bautar Jehobah ce za ta zama abu mafi muhimmanci a rayuwata. Kuma zan yi iya ƙoƙarina don in sa shi farin ciki.” (Mar. 12:30) Idan kai ma ka yi hakan, za ka sami albarku sosai!

14. Ka ba da misalin yadda wasu matasa suke yin koyi da Sarki Josiya.

14 Waɗanne matsaloli ne matasa da suke bauta ma Jehobah za su iya fuskanta? Johan ya yi baftisma saꞌad da yake shekara 12, kuma ya ce ꞌyan makarantarsu sun matsa masa ya sha sigari na lantarki. Don ya guji jarabar, Johan ya tuna wa kansa cewa shan taba zai iya shafan lafiyar jikinsa, kuma zai iya ɓata dangantakarsa da Jehobah. Rachel ta yi baftisma saꞌad da take shekara 14, kuma ta bayyana abin da ya taimaka mata ta iya jimre matsalolin da ta fuskanta a makaranta. Ta ce: “Nakan nemi abubuwan da suke tuna min game da Jehobah da kuma Littafi Mai Tsarki. Alal misali, idan muna tattaunawa game da tarihi a makaranta, hakan yana sa in tuna da wani labari ko kuma wani annabci a Littafi Mai Tsarki. Ko kuma saꞌad da nake magana da wani, nakan tuna nassin da zan nuna masa.” Mai yiwuwa matsalolin da za ka fuskanta za su yi dabam da na Sarki Josiya, amma za ka iya nuna hikima, kuma ka yi aminci kamar yadda ya yi. Idan kana iya jimre matsalolin da kake fuskanta yanzu da kake matashi, hakan zai taimaka maka ka jimre matsalolin da za ka fuskanta a gaba.

15. Me ya taimaka wa Josiya ya bauta ma Jehobah cikin aminci? (2 Tarihi 34:14, 18-21)

15 Saꞌad da Sarki Josiya ya kai shekaru 26, ya soma gyara haikalin Jehobah. Saꞌad da ake aikin, an “sami Littafin Koyarwar Yahweh, wanda aka bayar ta bakin Musa.” Da aka karanta wa sarkin littafin, nan da nan ya bi abin da aka rubuta a ciki. (Karanta 2 Tarihi 34:14, 18-21.) Za ka so ka riƙa karanta Littafi Mai Tsarki a kullum? Idan kana ƙoƙarin yin hakan, shin kana jin daɗin sa? Shin kana mai da hankali ga ayoyin da za su taimaka maka? Luke da muka ambata ɗazu, yakan rubuta darussa masu kyau da ya koya. Yin hakan zai taimake ka ka tuna darussa ko kuma nassin da kake so. Yayin da kake ci gaba da yin nazarin Littafi Mai Tsarki kuma kake jin daɗin sa, hakan zai ƙara maka niyyar bauta wa Jehobah. Kuma kamar yadda Kalmar Allah ta taimaka wa Josiya ya yi abin da ya dace, kai ma za ta taimaka maka.

16. Me ya sa Josiya ya yi babban kuskure, kuma mene ne hakan ya koya mana?

16 Ka koyi darasi daga kuskuren da Josiya ya yi. Saꞌad da Josiya yake wajen shekara 39, ya yi wani kuskuren da ya yi ajalinsa. Maimako ya nemi nufin Jehobah, ya dogara ga kansa. (2 Tar. 35:20-25) Wannan ya koya mana cewa komen tsufanmu ko kuma yawan shekaru da muka yi muna nazarin Littafi Mai Tsarki, dole ne mu ci gaba da neman nufin Jehobah. Hakan yana nufin cewa za mu riƙa roƙan sa ya yi mana ja-goranci, da yin nazarin Kalmarsa, da kuma bin shawarar Kiristoci da suka manyanta. Hakan zai taimaka mana mu guji yin kuskure mai tsanani, kuma ya taimaka mana mu yi farin ciki a rayuwa.—Yak. 1:25.

MATASA, ZA KU IYA YIN RAYUWA MAI KYAU

17. Wane darasi mai muhimmanci ne muka koya daga labarin sarakuna uku na Yahuda?

17 Akwai abubuwa masu kyau da mutum zai iya yi saꞌad da yake matashi. Misalin Yowash da Josiya da Uzziya sun nuna cewa matasa za su iya yanke shawarar da ta dace kuma su sa Jehobah farin ciki. Gaskiya ne cewa matasan nan sun yi kurakure, kuma hakan ya jawo musu munanan sakamako. Amma idan ka yanke shawarwari masu kyau kamar yadda suka yi, kuma ka guji kurakuran da suka yi, za ka yi rayuwa mai kyau.

Dauda ya kusaci Jehobah saꞌad da yake matashi. Jehobah ya ƙaunace shi kuma ya yi rayuwa mai kyau (Ka duba sakin layi na 18)

18. Waɗanne misalai a Littafi Mai Tsarki ne suka nuna cewa za ka iya yin farin ciki a rayuwa? (Ka kuma duba hoton.)

18 Ban da sarakuna ukun nan, akwai labaran wasu matasa a Littafi Mai Tsarki da suka yi kusa da Jehobah, suka sami amincewarsa, kuma suka yi rayuwa mai kyau. Dauda yana ɗaya daga cikinsu. Saꞌad da yake matashi, ya bauta ma Jehobah. Kuma da ya girma ya zama sarki, ya bauta ma Jehobah da aminci. Dauda ya yi kurakure a wasu lokuta, amma a gun Jehobah shi mai aminci ne. (1 Sar. 3:6; 9:4, 5; 14:8) Idan ka yi nazari game da Dauda, labarinsa zai taimaka maka ka bauta ma Jehobah da aminci. Ko kuma za ka iya yin nazari game da Markus ko Timoti. Za ka ga cewa sun bauta ma Jehobah tun suna matasa. Hakan ya sa Jehobah farin ciki kuma su ma sun yi farin ciki.

19. Wane irin rayuwa ne za ka iya morewa?

19 Yadda kake yin rayuwa a yanzu zai sa rayuwarka ta ƙare da kyau ko kuma aꞌa. Idan ka dogara ga Jehobah ba kanka ba, zai taimaka maka ka yanke shawarwari masu kyau. (K. Mag. 20:24) Za ka yi farin ciki a rayuwa kuma Jehobah zai albarkace ka. Ka tuna cewa Jehobah yana farin ciki domin yadda kake bauta masa. Hakika, babu abin da ya fi kyau ka yi da rayuwarka in ba bauta ma Jehobah ba.

WAƘA TA 144 Mu Riƙa Ɗokin Samun Ladan!

a Matasa, Jehobah ya san cewa a wasu lokuta, yakan yi muku wuya ku yi abin da yake da kyau kuma ku ci gaba da zama abokansa. Ta yaya za ku yanke shawarar da ta dace don ku faranta wa Ubanku na sama rai? Za mu tattauna misalan yara guda uku da suka zama sarakuna a Yahuda. Ku lura da abin da za ku iya koya daga shawarwarin da suka yanke.

b Ka duba akwatin nan “Kar Ka Nuna Girman Kai da Wayo” da ke talifin nan “Yana da Muhimmanci Mutum Ya Sami Ɗimbin Abokai a Shafin Sada Zumunta?” da ke dandalin jw.org/ha.

c BAYANI A KAN HOTUNA: Wata ꞌyarꞌuwa da ta manyanta tana ba wata matashiya shawara.

d BAYANI A KAN HOTUNA: Wata ꞌyarꞌuwa da aka gana da ita a taron daꞌira, ta dogara ga Jehobah don ta iya yin hakan, kuma da aka yabe ta, ta miƙa yabon ga Jehobah.