Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Shawara a Kan Yin Bincike

Shawara a Kan Yin Bincike

Ayyuka don Yara

Hakkin iyaye ne su koyar da yaransu game da Jehobah, kuma wannan babban hakki ne. (Afis. 6:4) Ƙungiyar Jehobah ta wallafa abubuwa da dama don ta taimaka wa iyaye su cika hakkin nan. Ta yaya za ku yi amfani da su wajen koyar da yaranku?

  • Ku shiga JW.ORG. A jw.org/ha, akwai bidiyoyi da yawa da takardu da za a iya saukarwa don yara su yi rubutu ko zane a kai. a Don ku same su, ku rubuta “Yara” ko kuma “Matasa” a inda aka ce “Bincika.”

  • Ku zaɓi wanda ya dace da yaranku. A sashen yara, za ku iya zaɓan bidiyoyi da dai sauransu da kuke ganin za su taimaka ma yaronku. Don ku samo su, ku rubuta “Ayyuka don Ibada ta Iyali” a inda aka ce “Bincika.”

  • Ku tattauna darasin da yaranku. Kar ku riƙa amfani da bidiyoyin ko kuma ayyukan nan don kawai ku ba wa yaranku ayyukan yi. A maimakon haka, ku tattauna bayanin da ke ciki da ɗanku ko ꞌyarku, da niyyar taimaka musu su zama abokan Jehobah.

a A manhajar JW Library®, akwai duka bidiyoyi na matasa da muke da su da Hausa, amma ba a gama fitar da duka takardunsu don zane da rubutu ba.