Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 40

Za Ka Iya Ci Gaba da Yin Kokari Kamar Bitrus

Za Ka Iya Ci Gaba da Yin Kokari Kamar Bitrus

“Rabu da ni, ya Ubangiji! Gama ni mai zunubi ne!”—LUK. 5:8.

WAƘA TA 38 Zai Ƙarfafa Ka

ABIN DA ZA A TATTAUNA a

1. Mene ne Bitrus ya yi da Yesu ya taimaka musu su iya kama kifi a hanya mai ban mamaki?

 BITRUS ya kwana yana ƙoƙarin kama kifi, amma bai kama ko guda ɗaya ba. Don haka, ya yi mamaki saꞌad da Yesu ya ce masa: “Ka ƙara tura jirgin zuwa inda akwai zurfi, ku saki ragar kamun kifinku, ku jawo kifi.” (Luk. 5:4) Bitrus ya yi shakka, amma ya yi abin da Yesu ya ce masa ya yi. Bitrus da abokan aikinsa sun soma kama kifaye da yawa, har ragar kamun kifinsu ta soma yagewa. Da Bitrus da abokan aikinsa suka ga abin ban alꞌajibi da Yesu ya yi, “mamaki ya kama su sosai.” Sai Bitrus ya ce: “Rabu da ni, ya Ubangiji! Gama ni mai zunubi ne!” (Luk. 5:6-9) Da alamar cewa Bitrus yana ganin bai cancanci ya kasance tare da Yesu ba.

2. Ta yaya za mu amfana idan muka yi nazarin labarin Bitrus?

2 Abin da Bitrus ya faɗa cewa shi “mai zunubi ne” gaskiya ne. Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa a wasu lokuta ya yi nadama domin abubuwan da ya furta ko kuma ya yi. Shin hakan yana faruwa da kai a wasu lokuta? Shin kana da wani hali marar kyau da kake ƙoƙarin dainawa? Idan haka ne, nazarin labarin Bitrus zai ƙarfafa ka. Ta yaya? Ka yi tunanin wannan: Jehobah zai iya sa marubutan Littafi Mai Tsarki su cire kurakuran da Bitrus ya yi. Amma ya umurce su su rubuta kurakuran don mu koyi darasi. (2 Tim. 3:16, 17) Idan muka yi nazari a kan abin da Bitrus ya yi ta fama da shi, za mu ga cewa Jehobah ba ya bukatar mu zama kamilai. Amma yana so mu ci gaba da yin ƙoƙari duk da kasawarmu.

3. Me ya sa muke bukatar mu ci gaba da yin ƙoƙari?

3 Me ya sa muke bukatar mu ci gaba da yin ƙoƙari? Domin idan mutum ya ci gaba da ƙoƙarin yin abu, a-kwana-a-tashi, zai ƙware a yin sa. Ga wani misali, idan mutum yana so ya koyi buga ganga, zai yi shekaru yana koya. Saꞌad da yake koya, zai yi kurakure da dama, amma idan ya ci gaba da koya, a-kwana-a-tashi, zai ƙware. Ko da ya zo ya ƙware a buga gangar, zai iya yin kuskure a wasu lokuta. Amma kuskuren ba zai sa ya daina buga ganga ba, zai ci gaba da inganta yadda yake buga ganga. Haka ma, ko da muna ganin mun shawo kan wata kasawa da muke da ita, a wasu lokuta za mu iya sake yin kuskuren. Amma za mu ci gaba da yin iya ƙoƙarinmu don mu shawo kansa. Dukanmu mukan faɗa ko mu yi wasu abubuwa kuma daga baya mu yi nadama. Amma idan ba mu karaya ba, Jehobah zai taimaka mana don mu sami ci gaba. (1 Bit. 5:10) Bari mu yi laꞌakari da yadda Bitrus ya ci gaba da yin ƙoƙari. In muka ga yadda Yesu ya tausaya masa duk da kasawarsa, hakan zai sa mu ci gaba da bauta ma Jehobah.

ƘOƘARIN DA BITRUS YA YI DA ALBARKUN DA YA SAMU

Me za ka yi idan irin abin da ya faru da Bitrus ya faru da kai? (Ka duba sakin layi na 4)

4. Mene ne Bitrus ya ce game da kansa a Luka 5:5-10, amma wane tabbaci ne Yesu ya ba shi?

4 Littafi Mai Tsarki bai gaya mana dalilin da ya sa Bitrus ya ce shi “mai zunubi ne” ko kuma zunubin da ya yi ba. (Karanta Luka 5:5-10.) Amma mai yiwuwa Bitrus ya yi manyan kurakure. Yesu ya san cewa yana tsoro ne domin a ganinsa shi mai kasawa ne. Yesu ya kuma san cewa Bitrus zai iya bauta ma Jehobah da aminci. Don haka, Yesu ya gaya wa Bitrus cewa “kada ka ji tsoro.” Yadda Yesu ya yarda da Bitrus ya taimaka wa Bitrus har iya rayuwarsa. Daga baya, Bitrus da ɗanꞌuwansa Andarawus sun bar kamun kifi, kuma sun soma yin waꞌazi tare da Yesu. Don haka, Jehobah ya albarkace su a hanyoyi da dama.—Mar. 1:16-18.

5. Wace albarka ce Bitrus ya samu don ya iya daina tsoron da yake ji da farko, kuma ya soma bin Yesu?

5 Bitrus ya shaida abubuwa da dama yayin da yake bin Yesu. Ya ga yadda Yesu ya warkar da marasa lafiya, ya kori aljanu, har ma ya ta da matattu. b (Mat. 8:14-17; Mar. 5:37, 41, 42) Bitrus ya kuma ga wahayi mai ban mamaki game da yadda Yesu zai yi mulki a Mulkin Allah. Bitrus bai manta da abin da ya gani ba har iya rayuwarsa. (Mar. 9:1-8; 2 Bit. 1:16-18) Bitrus ya ga abubuwa da dama, da a ce bai bi Yesu ba, da bai gan su ba. Ba mamaki, Bitrus ya yi farin ciki sosai domin ya iya daina tunani marar kyau da yake yi game da kansa, kuma ya iya shaida waɗannan abubuwa!

6. Shin Bitrus ya yi saurin shawo kan kasawarsa? Ka bayyana.

6 Duk da abubuwan da Bitrus ya gani kuma ya ji, ya ci gaba da fama da kasawarsa. Bari mu ga wasu misalai. Da Yesu ya bayyana yadda zai sha wahala kuma ya mutu kamar yadda aka annabta, Bitrus ya gaya masa cewa hakan ba zai faru ba. (Mar. 8:31-33) Bitrus da sauran manzannin sun yi ta gardama da juna a kan wane ne mafi girma. (Mar. 9:33, 34) A dare na ƙarshe kafin Yesu ya mutu, Bitrus ya kai ma wani mutum hari kuma ya yanke kunnensa. (Yoh. 18:10) A daren, tsoron mutane ya sa Bitrus ya yi mūsun sanin Yesu har sau uku. (Mar. 14:66-72) Bitrus ya yi kuka sosai saboda kuskuren da ya yi.—Mat. 26:75.

7. Wace dama aka ba wa Bitrus bayan an tashi Yesu daga mutuwa?

7 Yesu bai yashe manzonsa da ya yi sanyin gwiwa ba. Bayan an tashi Yesu daga mutuwa, ya sake ba wa Bitrus dama don Bitrus ya nuna masa cewa yana ƙaunarsa. Yesu ya gaya wa Bitrus ya yi kiwon tumakinsa. (Yoh. 21:15-17) Kuma Bitrus ya yarda. Yana Urushalima a ranar Fentakos kuma yana cikin mutane na farko da aka ba su ruhu mai tsarki.

8. Wane babban kuskure ne Bitrus ya yi a Antakiya?

8 Har bayan ya zama shafaffen Kirista, Bitrus ya ci gaba da fama da kasawarsa. A shekara ta 36 bayan haifuwar Yesu, Allah ya aiki Bitrus zuwa wurin Karniliyus kuma a wurin Allah ya ba wa Karniliyus ruhu mai tsarki. Hakan ya nuna cewa “Allah ba ya nuna bambanci” kuma waɗanda ba Yahudawa ba za su iya zama Kiristoci. (A. M. 10:34, 44, 45) Bayan haka, Bitrus ya soma cin abinci da waɗanda ba Yahudawa ba. Hakan abu ne da ba ya yi a dā. (Gal. 2:12) Amma wasu Kiristoci da Yahudawa ne suna ganin bai kamata Kiristoci Yahudawa su ci abinci da waɗanda ba Yahudawa ba. Saꞌad da wasu Kiristoci Yahudawa da suke da irin wannan raꞌayin suka zo Antakiya, Bitrus ya daina cin abinci da ꞌyanꞌuwansa da ba Yahudawa ba. Da alama ya yi hakan ne domin ba ya so ya ɓata wa Kiristoci Yahudawa rai. Manzo Bulus ya ga abin da Bitrus ya yi, kuma ya yi masa gyara a gaban sauran ꞌyanꞌuwan. (Gal. 2:13, 14) Duk da wannan kuskuren da Bitrus ya yi, ya ci gaba da yin ƙoƙari. Me ya taimaka masa?

MENE NE YA TAIMAKI BITRUS YA CI GABA DA YIN ƘOƘARI?

9. Ta yaya littafin Yohanna 6:68, 69 suka nuna cewa Bitrus mai aminci ne?

9 Bitrus mai aminci ne, don haka bai bar wani abu ya hana shi bin Yesu ba. Alal misali, akwai lokacin da Yesu ya faɗi wani abu da almajiransa ba su fahimta ba. (Karanta Yohanna 6:68, 69.) Maimakon su jira Yesu ya bayyana abin da yake nufi ko su tambaye shi, mutane da yawa sun daina bin shi. Amma Bitrus bai yi hakan ba. Ya nuna aminci, kuma ya ce Yesu ne kaɗai yake da “magana mai ba da rai na har abada.”

Me ya sa yadda Yesu ya yarda da Bitrus yake ƙarfafa ka? (Ka duba sakin layi na 10)

10. Ta yaya Yesu ya nuna cewa ya yarda da Bitrus? (Ka kuma duba hoton.)

10 Yesu bai yashe Bitrus ba. A dare na ƙarshe kafin Yesu ya mutu, ya san cewa Bitrus da sauran manzanninsa za su yashe shi. Duk da haka, Yesu ya gaya wa Bitrus cewa yana da tabbaci Bitrus zai dawo kuma ya kasance da aminci. (Luk. 22:31, 32) Yesu ya fahimci cewa “ruhun [yana marmari] amma jikin ba ƙarfi.” (Mar. 14:38) Don haka, duk da cewa Bitrus ya yi mūsun sanin Yesu, Yesu bai yashe shi ba. Yesu ya bayyana ga Bitrus bayan tashiwarsa daga mutuwa, kuma da alama ya yi hakan saꞌad da Bitrus yake shi kaɗai. (Mar. 16:7; Luk. 24:34; 1 Kor. 15:5) Ba mamaki hakan ya ƙarfafa Bitrus, domin yana baƙin ciki don kuskuren da ya yi!

11. Ta yaya Yesu ya tabbatar wa Bitrus cewa Jehobah zai taimaka masa?

11 Yesu ya tabbatar wa Bitrus cewa Jehobah zai kula da shi. Yesu ya sake taimaka wa manzo Bitrus da kuma sauran manzannin su iya kama kifi a hanya mai ban mamaki. (Yoh. 21:4-6) Ba shakka, wannan alꞌajibi ya sa Bitrus ya gaskata cewa Jehobah zai tanada masa abubuwan da yake bukata. Mai yiwuwa manzannin sun tuna abin da Yesu ya faɗa cewa Jehobah zai iya tanada musu abubuwan da suke bukata muddin sun sa Mulkin Allah farko a rayuwarsu. (Mat. 6:33) Abubuwan nan sun taimaka wa Bitrus ya sa Mulkin Allah farko a rayuwarsa maimakon kamun kifi. Ya yi waꞌazi da ƙarfin zuciya a ranar Fentakos na shekara ta 33, kuma hakan ya sa dubban mutane sun zama almajiran Yesu. (A. M. 2:14, 37-41) Bayan haka, ya taimaka wa Samariyawa da waɗanda ba Yahudawa ba su koya game da Yesu kuma su zama almajiransa. (A. M. 8:14-17; 10:44-48) Hakika, Jehobah ya yi amfani da Bitrus sosai domin ya jawo mutane iri-iri zuwa ƙungiyarsa.

ME MUKA KOYA?

12. Ta yaya labarin Bitrus zai taimaka mana idan muna fama da wata kasawa?

12 Jehobah zai taimaka mana mu ci gaba da yin ƙoƙari. Mai yiwuwa yin hakan ba zai yi mana sauƙi ba musamman idan mun jima muna fama da wata kasawa. A wasu lokuta, ƙila mu ga kamar kasawarmu ta fi na Bitrus wuya. Amma Jehobah zai ba mu ƙarfi da muke bukata don mu ci gaba da yin ƙoƙari. (Zab. 94:17-19) Alal misali, akwai wani ɗanꞌuwa da a dā shi ɗan luwaɗi ne, kuma ya yi hakan na shekaru da yawa kafin ya zama Mashaidin Jehobah. Ya canja salon rayuwarsa gaba ɗaya kuma ya soma yin rayuwa bisa ƙaꞌidodin Littafi Mai Tsarki. A wasu lokuta, yakan yi fama da shaꞌawoyi marasa kyau. Me ya taimaka masa ya ci gaba da yin ƙoƙari? Ya bayyana cewa: “Jehobah ne yake ba mu ƙarfi.” Ya ƙara da cewa: “Da taimakon ruhun Jehobah . . . , na san zan iya ci gaba da yin abin da yake so . . . Jehobah yana amfani da ni don in yi nufinsa, kuma duk da kasawata Jehobah bai daina ƙarfafa ni ba.”

A ranar 1 ga Janairu 1950 ne Ɗanꞌuwa Horst Henschel ya fara hidimar majagaba. Kana ganin ya yi da-na-sani domin ya yi amfani da rayuwarsa ya bauta ma Jehobah? (Ka duba sakin layi na 13, 15) d

13. Ta yaya za mu yi koyi da abin da Bitrus ya yi a Ayyukan Manzanni 4:13, 29, 31? (Ka kuma duba hoton.)

13 Kamar yadda muka gani, Bitrus ya yi manyan kurakure saboda tsoron mutum. Amma da ya roƙi Jehobah ya ba shi ƙarfin zuciya, Bitrus ya kuwa yi ƙarfin zuciya. (Karanta Ayyukan Manzanni 4:13, 29, 31.) Mu ma za mu iya daina jin tsoro. Ga abin da ya faru da wani ɗanꞌuwa mai suna Horst. Shi matashi ne a Jamus a lokacin Yaƙin Duniya na Biyu. A lokacin, idan mutane za su yi gaisuwa, sukan ce “Heil Hitler,” wato Hitler zai cece mu. Ko da yake Horst ya san cewa bai kamata ya furta waɗannan kalmomin ba, ya yi hakan a wasu lokuta domin yana tsoron malamansa da kuma ꞌyan ajinsu. Maimakon iyayen Horst su tsauta masa, sun yi adduꞌa da shi kuma sun roƙi Jehobah ya ba shi ƙarfin zuciya. Saboda taimakon iyayensa, da kuma yadda ya dogara ga Jehobah, ɗanꞌuwan ya riƙe amincinsa. Daga baya ya ce: “Jehobah bai taɓa yashe ni ba.” c

14. Ta yaya dattawa za su iya ƙarfafa waɗanda suka yi sanyin gwiwa?

14 Jehobah da Yesu ba za su daina taimaka mana ba. Bayan Bitrus ya yi mūsun sanin Yesu, yana bukatar ya yanke shawara mai muhimmanci. Shin zai ci gaba da bin Yesu ko dai zai daina yin hakan? Yesu ya riga ya roƙi Jehobah ya taimaka wa Bitrus ya ci gaba da kasancewa da bangaskiya. Yesu ya gaya wa Bitrus game da adduꞌar da ya yi, kuma ya nuna cewa yana da tabbaci Bitrus zai dawo ya ƙarfafa ꞌyanꞌuwansa. (Luk. 22:31, 32) Babu shakka, Bitrus ya sami ƙarfafa da ya tuna abin da Yesu ya gaya masa! A lokacin da muke bukatar mu yanke shawara mai muhimmanci a rayuwarmu, Jehobah zai iya yin amfani da dattawa da suke ƙaunar mu don su ƙarfafa mu kuma su taimaka mana mu ci gaba da nuna bangaskiya. (Afis. 4:8, 11) Abin da wani ɗanꞌuwa mai suna Paul da ya daɗe da zama dattijo yake yi ke nan. Yakan gaya ma waɗanda suke ganin ba za su iya ci gaba da bauta ma Jehobah ba, su yi tunanin yadda Jehobah ya jawo su zuwa ƙungiyarsa da farko. Bayan haka, sai ya gaya musu cewa saboda ƙauna marar canjawa da Jehobah yake da ita, ba zai taɓa fid da rai a kan su ba. Ya ƙarasa da cewa, “Na ga yadda mutane da yawa da suka yi sanyin gwiwa suka ci gaba da yin ƙoƙarin bauta wa Jehobah da taimakonsa.”

15. Ta yaya misalin Bitrus da kuma Horst suka nuna cewa abin da ke Matiyu 6:33 gaskiya ne?

15 Kamar yadda Jehobah ya biya bukatun manzo Bitrus da sauran manzannin, mu ma zai biya bukatunmu idan muka sa yin hidimarsa farko a rayuwarmu. (Mat. 6:33) Bayan Yaƙin Duniya na Biyu, Ɗanꞌuwa Horst da muka ambata ɗazu ya soma yin hidimar majagaba. Amma shi talaka ne sosai. Don haka, ya ɗauka ba zai iya kula da kansa kuma ya yi hidimar majagaba ba. Mene ne ya yi? Ya gwada Jehobah don ya ga ko Jehobah zai biya bukatunsa. Ya yi hakan ta wajen fita waꞌazi a dukan ranaku a makon da mai kula da daꞌira ya ziyarce su. A ƙarshen makon, ya yi mamaki sosai saꞌad da mai kula da daꞌira ya miƙa masa kuɗi, amma bai gaya masa wanda ya ba shi kuɗin ba. Kuɗin zai ishe shi har na watanni da yawa yayin da yake hidimar majagaba. A gun Horst, wannan kyautar tabbaci ne cewa Jehobah zai biya bukatunsa. Ya ci gaba da sa Mulkin Allah farko a dukan rayuwarsa.—Mal. 3:10.

16. Me ya sa yake da muhimmanci mu yi nazari game da Bitrus da kuma wasu abubuwa da ya rubuta a wasiƙunsa?

16 Bitrus ya yi farin ciki sosai cewa Yesu bai rabu da shi ba, ko da yake abin da Bitrus ya roƙa da farko ke nan! Yesu ya ci gaba da koyar da manzo Bitrus ya zama manzo mai bangaskiya, kuma ya kafa misali mai kyau ga Kiristoci. Za mu iya koyan darussa da yawa daga koyarwar da Yesu ya yi wa Bitrus. Bitrus ya bayyana wasu daga cikin abubuwan da Yesu ya koya masa a wasiƙu guda biyu da ya tura wa ikilisiyoyi a ƙarni na farko. Talifi na gaba zai tattauna wasu abubuwa daga wasiƙun nan, kuma zai nuna mana yadda za mu bi su a yau.

WAƘA TA 126 Mu Yi Tsaro, Mu Riƙe Aminci, Mu Yi Ƙarfi

a An shirya wannan talifin ne don a ƙarfafa waɗanda suke fama da wata kasawa, don su san cewa za su iya shawo kanta kuma su ci gaba da yin ƙoƙarin bauta ma Jehobah.

b Yawancin nassosin da aka ambata a wannan talifin daga littafin Markus ne. Da alama cewa abubuwan da ya ji daga wurin Bitrus ne ya rubuta. Bitrus kuwa ya ga abubuwan da suka faru da idanunsa.

c Ka kalli bidiyon nan, “Horst Henschel: Jehobah Shi Ne Ƙarfina” a jw.org/ha.

d BAYANI A KAN HOTO: Hoton nan ya kwatanta yadda iyayen Horst Henschel suka yi adduꞌa da shi, kuma suka ƙarfafa shi ya riƙe amincinsa.