TALIFIN NAZARI NA 30
Bari Kaunarka Ta Ci Gaba da Karuwa
“Cikin ƙauna, mu yi girma cikin alꞌamuranmu duka.”—AFIS. 4:15.
WAƘA TA 2 Jehobah Ne Sunanka
ABIN DA ZA A TATTAUNA a
1. Waɗanne abubuwa ne ka koya da ka soma nazarin Littafi Mai Tsarki?
KA TUNA lokacin da ka soma nazarin Littafi Mai Tsarki? Mai yiwuwa ka yi mamaki da ka koyi cewa Allah yana da suna. Kuma mai yiwuwa hankalinka ya kwanta da ka koyi cewa Allah ba ya azabtar da mutane a cikin wuta. Ƙari ga haka, ba mamaki ka yi farin ciki da ka koyi cewa za ka iya sake ganin ꞌyanꞌuwanka da suka mutu, kuma ka yi rayuwa tare da su a cikin aljanna a duniya.
2. Wane ci gaba ne ka samu bayan ka koyi gaskiyar da ke Littafi Mai Tsarki? (Afisawa 5:1, 2)
2 Yayin da kake ci gaba da nazarin Kalmar Allah, ƙaunar da kake wa Jehobah ma ta ƙaru. Wannan ƙaunar ta sa ka aikata abubuwan da ka koya. Kuma ka soma yanke shawarwarin da suka dace, suka kuma jitu da nufin Allah. Ka kyautata halayenka kuma ka soma tunanin abubuwan da suka dace domin kana so ka faranta wa Allah rai. Kamar yadda ɗa yake yin koyi da ubansa, kai ma ka soma yin koyi da Ubanka na sama.—Karanta Afisawa 5:1, 2.
3. Waɗanne tambayoyi ne za mu iya yi wa kanmu?
3 Zai dace mu tambayi kanmu cewa: ‘Shin ƙaunar da nake yi wa Jehobah yanzu ta ƙaru fiye da lokacin da na yi baftisma? Tun daga lokacin da na yi baftisma zuwa yanzu, tunanina da halina sun ƙara zama kamar na Jehobah, musamman yadda nake nuna ƙauna ga ꞌyanꞌuwana?’ Idan “ƙaunarka ta farko” ta yi sanyi, kada ka karaya. Kiristoci a ƙarni na farko ma sun fuskanci abu kamar haka. Yesu bai yashe su saboda hakan ba, kuma ba zai yashe mu ba. (R. Yar. 2:4, 7) Ya san cewa za mu iya sake kasancewa da ƙaunar nan.
4. Waɗanne abubuwa ne za mu tattauna a talifin nan?
4 Wannan talifin zai tattauna yadda za mu ci gaba da ƙaunar Jehobah da mutane. Bayan haka, za mu ga yadda yin hakan zai amfane mu da kuma mutane.
BARI ƘAUNARKA GA JEHOBAH TA CI GABA DA ƘARUWA
5-6. Waɗanne matsaloli ne manzo Bulus ya fuskanta, amma mene ne ya taimaka masa ya ci gaba da bauta wa Jehobah?
5 Manzo Bulus ya ji daɗin bauta wa Jehobah amma ya fuskanci matsaloli da yawa. Bulus ya yi tafiya zuwa wurare masu nisa sosai kuma yin tafiya a lokacin bai da sauƙi. A tafiye-tafiyen da ya yi, wasu lokuta manzo Bulus ya “gamu da hatsari a koguna” da kuma “hatsari a hannun ꞌyan fashi.” Ƙari ga haka, ya sha dūka a hannun maƙiya. (2 Kor. 11:23-27) Kuma a wasu lokuta, ꞌyanꞌuwan da yake ƙoƙarin taimaka musu ma ba su nuna godiya ba.—2 Kor. 10:10; Filib. 4:15.
6 To, me ya taimaka wa Bulus ya ci gaba da bauta wa Jehobah? Bulus ya koyi abubuwa da dama game da Jehobah daga Nassosi da kuma abubuwan da ya fuskanta. Hakan ya tabbatar masa da cewa Jehobah yana ƙaunar sa. (Rom. 8:38, 39; Afis. 2:4, 5) Sai shi ma ya soma ƙaunar Jehobah sosai. Bulus ya nuna cewa yana ƙaunar Jehobah ta wajen ci gaba da taimaka wa “tsarkaka.”—Ibran. 6:10.
7. Ka bayyana abu ɗaya da zai taimaka mana mu ƙara ƙaunar Jehobah.
7 Idan muna nazarin Kalmar Allah sosai, hakan zai taimaka mana mu ƙara ƙaunar sa. Yayin da kake karanta Littafi Mai Tsarki, ka yi ƙoƙari ka ga abin da nassin yake koya maka game da Jehobah. Ka yi wa kanka tambayoyin nan: ‘Ta yaya nassin nan ya nuna cewa Jehobah yana ƙauna ta? Ta yaya hakan ya nuna cewa Jehobah ya cancanci in bauta masa?’
8. Ta yaya adduꞌa take taimaka mana mu ƙara ƙaunar Allah?
8 Wani abu kuma da zai sa mu ƙara ƙaunar Jehobah shi ne, yin adduꞌa ga Jehobah a kullum da bayyana masa yadda muke ji. (Zab. 25:4, 5) Jehobah zai amsa adduꞌarmu. (1 Yoh. 3:21, 22) Wata ꞌyarꞌuwa mai suna Khanh a Asiya ta ce: “Da farko, ina ƙaunar Jehobah ne saboda abubuwan da na koya game da shi, amma na ƙara ƙaunar sa da na ga yadda yake amsa adduꞌoꞌina. Hakan ya sa ina son yin abubuwan da za su faranta masa rai.” b
BARI ƘAUNARKA GA MUTANE TA CI GABA DA ƘARUWA
9. Ta yaya Timoti ya nuna cewa ƙaunar da yake wa ꞌyanꞌuwa tana ƙaruwa?
9 Bayan Bulus ya yi wasu shekaru da zama Kirista, ya haɗu da wani matashi mai kirki. Sunansa Timoti, kuma yana ƙaunar Jehobah da mutane. Bayan wasu shekaru, Bulus ya gaya wa Filibiyawa cewa: “Ba ni da wani kamar [Timoti] wanda ya damu da ku sosai.” (Filib. 2:20) Ba wai Bulus yana yaba wa Timoti don ya iya koyarwa ko tsara abubuwa ba ne, amma ya ga cewa yana ƙaunar mutane sosai. Ba mamaki, ikilisiyoyin da Timoti ya ziyarta sun dinga marmarin zuwansa.—1 Kor. 4:17.
10. Ta yaya ꞌyarꞌuwa Anna da mijinta suka nuna irin ƙaunar da suke yi wa ꞌyanꞌuwansu?
10 Mu ma yana da kyau mu nemi hanyoyin taimaka wa ꞌyanꞌuwanmu maza da mata. (Ibran. 13:16) Ga misalin wata ꞌyarꞌuwa mai suna Anna da muka yi zancenta a talifin da ya gabata. Da aka yi wata guguwa mai ƙarfin gaske, ita da mijinta sun ziyarci wasu ꞌyanꞌuwa kuma suka ga cewa iskar ta lalata rufin gidansu. Hakan ya sa tufafin ꞌyanꞌuwan sun yi datti sosai. ꞌYarꞌuwa Anna ta ce: “Mun kwashe rigunansu, muka wanke, muka yi musu guga, saꞌan nan muka dawo musu da kayan. Ko da yake abin da muka yi musu ƙaramin abu ne, amma ya kawo zumunci mai ƙarfi a tsakaninmu har a yau.” Ƙaunar da ꞌyarꞌuwa Anna da maigidanta suke yi wa ꞌyanꞌuwan nan ita ce ta sa suka ba su taimakon da suke bukata.—1 Yoh. 3:17, 18.
11. (a) Yaya mutane suke ji idan muka nuna musu ƙauna? (b) Bisa ga Karin Magana 19:17, mene ne Jehobah yake yi idan muka nuna wa mutane ƙauna?
11 Idan muka nuna wa mutane ƙauna kuma muka yi musu alheri, za su ga cewa muna ƙoƙarin yin koyi da Jehobah. Idan muka yi musu alheri, zai sa su yi farin ciki fiye da yadda muka yi tsammani. ꞌYarꞌuwa Khanh da muka ambata ɗazu takan yi farin ciki idan ta tuna da waɗanda suka taimaka mata. Ta ce: “Ina godiya sosai ga ꞌyanꞌuwa mata masu aminci da suka ɗauke ni don in je waꞌazi da su. Sukan zo su ɗauke ni, su gayyace ni in ci abinci tare da su kuma su sake mai da ni gida lafiya. Yanzu na fahimci cewa ba ƙaramin taimako suka yi mini ba, kuma sun yi hakan da zuciya ɗaya.” Gaskiyar ita ce, ba kowa ne zai gode mana don alherin da muka yi masa ba. Ga abin da Khanh ta ce game da waɗanda suka taimaka mata: “Da ma a ce zan iya sāka musu don alherin da suka min, da na ji daɗi. Sai dai yanzu ban ma san inda suke ba. Amma Jehobah ya san inda suke kuma fatana shi ne ya yi musu albarka.” Abin da Khanh ta faɗa gaskiya ne. Domin Jehobah yana lura da alherin da muke yi wa mutane komen ƙanƙantar sa. Hakan yana da daraja a gunsa kuma yana ɗaukan sa a matsayin bashi da yake bukatar ya biya.—Karanta Karin Magana 19:17.
12. Me ya kamata ꞌyanꞌuwa maza su yi don su nuna ƙauna a ikilisiya? (Ka kuma duba hoton.)
12 Idan kai ɗanꞌuwa ne, ta yaya za ka nuna wa mutane ƙauna kuma ka ba da kanka don ka taimaka musu? Wani ɗanꞌuwa matashi mai suna Jordan ya tambayi wani dattijo yadda zai iya taimakawa a ikilisiya. Dattijon ya yaba masa don ci gaban da ya riga ya samu kuma ya ba shi shawara a kan yadda zai iya taimakawa a ikilisiya. Alal misali, ya shawarci Jordan ya riƙa zuwa taro da wuri don ya iya gai da ꞌyanꞌuwa, ya riƙa yin kalami a taro, da yin waꞌazi tare da rukunin waꞌazinsa. Ya kuma gaya masa ya nemi wasu hanyoyin da zai taimaka wa mutane. Da Jordan ya bi shawarar da aka ba shi, ya koyi sabbin abubuwa. Mafi muhimmanci ma, ƙaunar da yake yi wa ꞌyanꞌuwansa ta ƙaru. Jordan ya koyi cewa ba sai ɗanꞌuwa ya zama bawa mai hidima ne zai soma taimaka wa mutane ba, amma ya kamata ya soma tun kafin nan kuma ya ci gaba bayan ya zama bawa mai hidima.—1 Tim. 3:8-10, 13.
13. Ta yaya ƙauna ta sa wani ɗanꞌuwa ya sake zama dattijo?
13 Idan kuma a dā kai bawa mai hidima ne ko kuma dattijo fa? Jehobah ba zai manta da ayyukan da ka yi a dā da kuma ƙaunar da ya sa ka yi ayyukan ba. (1 Kor. 15:58) Yana kuma lura da ƙaunar da kake nunawa. Wani ɗanꞌuwa mai suna Christian ya yi baƙin ciki saꞌad da aka sauƙe shi daga dattijo. Duk da haka ya ce: “Na yanke shawara cewa zan yi iya ƙoƙarina don in bauta wa Jehobah domin ina ƙaunar sa, ko da ni dattijo ne ko ba dattijo ba.” A-kwana-a-tashi, an sake naɗa shi dattijo. Christian ya ce: “Na ɗan ji tsoro da aka sake naɗa ni dattijo. Amma na gaya wa kaina cewa, idan Jehobah yana so in sake yin hidimar dattijo a ikilisiya, zan yi hakan domin ina ƙaunar sa da ꞌyanꞌuwana.”
14. Mene ne ka koya daga abin da wata ꞌyarꞌuwa daga Georgia ta faɗa?
14 Bayin Jehobah suna kuma nuna ƙauna ga maƙwabtansu. (Mat. 22:37-39) Alal misali, wata ꞌyarꞌuwa mai suna Elena a ƙasar Georgia ta ce: “Da farko, ƙaunar da nake yi wa Jehobah ce kawai take sa in yi waꞌazi, amma yayin da nake ƙara ƙaunar Jehobah, ƙaunata ga mutane ta ƙaru. Sai na soma tunani a kan matsalolin da suke fuskanta da kuma abubuwan da za su so su yi magana a kai. Irin tunanin nan ya sa na ƙara kasancewa da niyyar taimaka musu.”—Rom. 10:13-15.
JEHOBAH ZAI YI MANA ALBARKA IDAN MUKA NUNA WA MUTANE ƘAUNA
15-16. Kamar yadda aka kwatanta a hoton, ta yaya mutane za su amfana idan muka nuna ƙauna?
15 Idan muka nuna wa mutane ƙauna, ba su kaɗai ne za su amfana ba. Da annobar korona ta soma, wani ɗanꞌuwa mai suna Paolo da matarsa sun taimaka wa ꞌyanꞌuwa mata da suka tsufa su iya yin waꞌazi da naꞌurori. Akwai wata ꞌyarꞌuwa a cikinsu da abin ya yi mata wuya da farko amma ta yi nasara a ƙarshe. Har ta iya ta gayyaci danginta zuwa Taron Tunawa da Mutuwar Yesu. Danginta guda sittin sun halarci taron ta naꞌura. ꞌYarꞌuwar da danginta sun amfana daga taimakon da Paolo da matarsa suka yi mata. Daga baya, ꞌyarꞌuwar ta rubuta saƙo ga Paolo ta ce: “Na gode da yadda kuka taimaka mana tsofaffi. Ba zan taɓa manta da yadda Jehobah ya kula da mu da yadda kuka taimaka mana ba.”
16 Wannan abin da ya faru ya koya wa Paolo darasi mai muhimmanci. Ya koyi cewa ƙauna tana da muhimmanci fiye da ilimi ko kuma baiwa. Ya ce: “A dā ni mai kula da daꞌira ne. Yanzu na gano cewa, ko da yake ꞌyanꞌuwa sun manta da jawaban da na yi, ba su manta da taimakon da na yi musu ba.”
17. Wane ne kuma zai amfana idan muka nuna ƙauna?
17 Idan muka nuna wa mutane ƙauna, mu ma za mu amfana a hanyar da ba mu yi tsammani ba. Ɗanꞌuwa Jonathan da ke zama a ƙasar New Zealand ya shaida hakan. Ya ga wani majagaba yana waꞌazi shi kaɗai a cikin zafin rana. Sai Jonathan ya ce zai riƙa bin ɗanꞌuwan zuwa waꞌazi kowace Asabar da rana. A lokacin, bai san cewa zai amfana daga alherin da yake yi wa ɗanꞌuwan ba. Jonathan ya ce: “A lokacin, ba na son yin waꞌazi, amma da na ga yadda majagaban yake koyarwa, kuma na ga yadda Jehobah yake masa albarka a hidimarsa, sai na soma son yin waꞌazi. Ɗanꞌuwan ya kuma zama babban abokina. Ya taimaka min in ji daɗin yin waꞌazi kuma in yi kusa da Jehobah.”
18. Mene ne Jehobah yake so mu yi?
18 Jehobah yana so ƙaunar da muke yi masa da ꞌyanꞌuwanmu ta yi ta ƙaruwa. Kamar yadda muka koya, karanta Littafi Mai Tsarki da yin tunani mai zurfi a kan abin da muka koya, da yin adduꞌa za su sa mu ƙara ƙaunar sa. Za mu kuma iya ƙara ƙaunar ꞌyanꞌuwanmu idan muna yin abubuwan da za su taimaka musu. Yayin da ƙaunarmu take ƙaruwa, za mu daɗa yin kusa da Jehobah da ꞌyanꞌuwanmu. Kuma za mu ji daɗin abokantakar nan har abada.
WAƘA TA 109 Mu Kasance da Ƙauna ta Gaske
a Ko da mun daɗe muna bauta wa Jehobah, ko ba mu daɗe ba, dukanmu za mu iya samun ci gaba. Talifin nan zai nuna mana hanya mai muhimmanci da za mu yi hakan, wato ta wajen ƙara yadda muke ƙaunar Jehobah da kuma mutane. Yayin da muke tattauna wannan talifin, ka yi laꞌakari da ci gaban da ka riga ka samu da kuma yadda za ka ƙara samun ci gaba a wasu hanyoyi.
b An canja wasu sunayen.