Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA

Ku Zama Masu Sanin Yakamata Kamar Jehobah

Ku Zama Masu Sanin Yakamata Kamar Jehobah

“Bari kowa ya ga cewa ku masu sanin yakamata ne.”​—FILIB. 4:​5, New World Translation.

WAƘA TA 89 Mu Ji, Mu Yi Biyayya Don Mu Sami Albarka

ABIN DA ZA A TATTAUNA a

Wace irin bishiya ce za ka so ka zama? (Ka duba sakin layi na 1)

1. A wace hanya ce Kiristoci suke bukatar su zama kamar bishiya? (Ka kuma duba hoton.)

 “ISKA ba ta karya bishiyar da take iya lanƙwashewa.” Wannan furucin ya nuna cewa bishiya tana bukatar ta lanƙwashe idan ana iska mai ƙarfi don kada ta karye. Kamar bishiyar, mu ma muna bukatar mu lanƙwashe, wato mu kasance da halin sanin yakamata don mu iya jimre saꞌad da yanayinmu ya canja. Ko kuma don mu iya daraja raꞌayin ꞌyanꞌuwanmu da kuma shawarar da suka yanke.

2. Waɗanne halaye ne za su taimaka mana idan yanayinmu ya canja, kuma me za mu tattauna a wannan talifin?

2 Da yake mu bayin Jehobah ne, muna so mu zama masu sanin yakamata. Ƙari ga haka, muna so mu zama masu sauƙin kai da kuma tausayi. A talifin nan, za mu ga yadda halayen nan suka taimaka ma wasu ꞌyanꞌuwa su jimre saꞌad da yanayinsu ya canja. Za mu kuma ga yadda halayen nan za su taimaka mana. Amma bari mu fara da tattauna yadda Jehobah da Yesu suka nuna halin sanin yakamata don mu koya.

JEHOBAH DA YESU MASU SANIN YAKAMATA NE

3. Ta yaya muka san cewa Jehobah mai sanin yakamata ne?

3 Ana kiran Jehobah “Dutse” domin ya kafu daram. (M. Sha. 32:4) Duk da haka, shi mai sanin yakamata ne. Yayin da abubuwa suke canjawa a wannan duniyar, Jehobah yakan ɗau mataki don ya tabbata cewa dukan abubuwan da ya yi alkawarin su sun cika. Jehobah ya halicce mu a kamanninsa. Don haka, mu ma za mu iya ɗaukan mataki don mu iya jimrewa idan yanayinmu ya canja. Ya ba mu ƙaꞌidodin Littafi Mai Tsarki da suke taimaka mana mu yanke shawarar da ta dace a duk yanayin da muka sami kanmu. Abubuwan da Jehobah ya yi da kuma ƙaꞌidodin Littafi Mai Tsarki da ya ba mu sun tabbatar mana cewa ko da yake shi “Dutse” ne, yana da sanin yakamata.

4. Ka ba da misalin da ya nuna cewa Jehobah mai sanin yakamata ne. (Littafin Firistoci 5:​7, 11)

4 Jehobah ba ya yin kuskure, duk da haka shi mai sanin yakamata ne. Ba ya nacewa a kan abu ɗaya idan yana shaꞌani da ꞌyan Adam. Ka yi laꞌakari da yadda Jehobah ya nuna sanin yakamata ga Israꞌilawa. Bai bukaci talakawa su ba da hadaya daidai da masu arziki ba. A wasu yanayoyi ma, ya bar kowa ya ba da hadaya daidai ƙarfinsa.​—Karanta Littafin Firistoci 5:​7, 11.

5. Ka ba da misalan da suka nuna cewa Jehobah mai sauƙin kai ne da kuma tausayi.

5 Da yake Jehobah mai sauƙin kai ne da kuma tausayi, yana nuna sanin yakamata. Alal misali, Jehobah ya nuna sauƙin kai saꞌad da yake so ya halaka birnin Saduma ko kuma Sodom. Ko da yake malaꞌikunsa sun gaya wa Lot, wato Lutu cewa ya gudu zuwa yankunan tuddai, Lutu ya ji tsoron zuwa wurin. Don haka, ya roƙa cewa a bar shi da iyalinsa su gudu zuwa wani ƙaramin gari mai suna Zowar, ko da yake Jehobah yana so ya halaka garin. Jehobah zai iya nace cewa Lutu ya yi daidai abin da ya gaya masa. Amma ya amince da roƙon da Lutu ya yi kuma ya fasa halaka garin Zowar. (Far. 19:​18-22) Ɗarurruwan shekaru bayan hakan, Jehobah ya tausaya wa mutanen Nineba. Ya aiki annabi Yona, wato Yunana, ya sanar cewa za a halaka birnin da kuma mugayen mutanen da ke cikinsa. Amma da mutanen Nineba suka tuba, Jehobah ya tausaya musu kuma ya fasa halaka birnin.​—Yona 3:​1, 10; 4:​10, 11.

6. Ka ba da misalan da suka nuna cewa Yesu yana da sanin yakamata kamar Jehobah.

6 Yesu ma ya nuna sanin yakamata kamar Jehobah. An aiko shi zuwa duniya don ya yi waꞌazi ga “tumakin Israꞌila waɗanda suka ɓata.” Amma ya nuna sanin yakamata saꞌad da yake yin aikin nan da aka ba shi. Akwai lokacin da wata mata da ba Ba-israꞌiliya ba ce ta roƙe shi ya warkar da ꞌyarta domin ‘wani aljani yana wahalar da ꞌyarta.’ Yesu ya tausaya wa matar kuma ya warkar da ꞌyarta. (Mat. 15:​21-28) Ga wani misali kuma. Saꞌad da Yesu ya soma waꞌazi, ya ce: “Duk wanda ya yi musun sanina . . . , ni ma zan yi musun saninsa.” (Mat. 10:33) Amma da Bitrus ya yi musun sanin Yesu har ma sau uku, Yesu ya yi musun sanin Bitrus ne? Aꞌa. Yesu ya san cewa Bitrus ya tuba da gaske kuma shi mai bangaskiya ne. Bayan an ta da Yesu daga mutuwa, ya bayyana ga Bitrus. Da alama ya yi hakan ne don ya tabbatar wa Bitrus cewa ya yafe masa kuma yana ƙaunar sa.​—Luk. 24:​33, 34.

7. Kamar yadda Filibiyawa 4:5 ta nuna, wane hali ne muke so a san mu da shi?

7 Mun koyi cewa Jehobah da Yesu masu sanin yakamata ne. Mu kuma fa? Jehobah yana so mu zama masu sanin yakamata. (Karanta Filibiyawa 4:5. b) Ku yi abubuwan da za su sa mutane su ga cewa ku masu sanin yakamata ne. Za mu iya yi wa kanmu tambayoyin nan: ‘Shin mutane suna gani na a matsayin mai sanin yakamata? Ba na nacewa a kan raꞌayina kuma ina haƙuri da mutane? Ko dai suna gani na a matsayin mai tsattsauran raꞌayi, marar tausayi kuma mai taurin kai? Ina nace cewa sai mutane sun yi abubuwa yadda nake gani ya dace a yi? Ko dai ina sauraran mutane kuma in bin shawararsu idan hakan ya dace?’ Yadda muke nuna sanin yakamata zai nuna ko muna yin koyi da Jehobah da Yesu. Bari mu tattauna hanyoyi biyu da za mu iya nuna sanin yakamata, wato saꞌad da yanayinmu ya canja ko kuma saꞌad da raꞌayin ꞌyanꞌuwanmu ko kuma shawarar da suka yanke ya yi dabam da namu.

MU NUNA SANIN YAKAMATA IDAN YANAYINMU YA CANJA

8. Me zai taimaka mana mu nuna sanin yakamata idan yanayinmu ya canja? (Ka kuma duba ƙarin bayani.)

8 Muna bukatar mu nuna sanin yakamata idan yanayinmu ya canja. Irin canjin nan zai iya jawo mana matsalolin da ba mu zata ba. Alal misali, za mu iya soma rashin lafiya kwatsam. Faɗuwar tattalin arziki ko kuma wasu canje-canje a gwamnati za su iya sa rayuwa ta yi mana wuya. (M. Wa. 9:11; 1 Kor. 7:31) Ƙari ga haka, zai iya yi mana wuya idan ƙungiyarmu ta canja mana hidima, ko kuma ta ce mu koma yin hidima a wani wuri. Ko da yaya yanayin yake, za mu iya jimrewa idan muka bi abubuwa guda huɗun nan: (1) ka amince cewa yanayinka ya canja, (2) ka mai da hankali ga abin da za ka iya yi yanzu ba abin da ka yi a dā ba, (3) ka mai da hankali ga abubuwan da kake morewa yanzu, (4) ka taimaka wa mutane. c Bari mu tattauna labaran wasu ꞌyanꞌuwa da suka nuna yadda abubuwa huɗun nan za su taimaka mana.

9. Ta yaya wasu maꞌaurata da suke waꞌazi a ƙasar waje suka jimre matsalar da suka fuskanta ba zato?

9 Ka amince cewa yanayinka ya canja. An tura Ɗanꞌuwa Emanuele da matarsa Francesca waꞌazi a wata ƙasa. Yayin da suke ƙoƙarin sabawa da ꞌyanꞌuwa a ikilisiyar kuma su koyi yaren da ake yi a ƙasar, sai aka soma annobar korona kuma sun bukaci su killace kansu. Jim kaɗan bayan haka, mahaifiyar Francesca ta rasu. Francesca ta so ta koma gida don ta kasance da iyalinta, amma ba ta iya yin hakan ba don annobar. Me ya taimaka mata ta iya jimre yanayin? Da farko, Emanuele da matarsa Francesca sun roƙi Jehobah ya ba su hikima don su iya jimre matsalar da kowace rana za ta kawo. Jehobah ya tanada musu abubuwan da suke bukata a kan lokaci don su iya jimrewa. Abin da wani ɗanꞌuwa ya faɗa a wani bidiyo ya ƙarfafa su. Ɗanꞌuwan ya ce: “Idan muka yi saurin amincewa da yanayin da muke ciki, zai yi mana sauƙi mu sake yin farin ciki kuma mu yi amfani da yanayin da muke ciki don mu bauta wa Jehobah.” d Na biyu, sun yanke shawara cewa za su ƙara koyan yadda za su yi waꞌazi ta naꞌura. Kuma hakan ya sa sun fara gudanar da nazarin Littafi Mai Tsarki. Na uku, sun yarda ꞌyanꞌuwa da ke ikilisiyar su taimaka musu, kuma sun yi farin ciki don ƙaunar da ꞌyanꞌuwan suka nuna musu. Wata ꞌyarꞌuwa mai kirki ta riƙa aika musu saƙo da ayar Littafi Mai Tsarki kowace rana na tsawon shekara ɗaya. Mu ma idan muka fahimci cewa yanayinmu ya canja, za mu yi farin ciki domin muna bauta wa Jehobah iya gwargwadon ƙarfinmu.

10. Me ya taimaka ma wata ꞌyarꞌuwa ta jimre saꞌad da yanayinta ya canja?

10 Ka mai da hankali ga abin da kake iya yi yanzu da abubuwan da kake morewa. Wata ꞌyar Romaniya mai suna Christina da ke zama a ƙasar Jafan ba ta ji daɗi ba saꞌad da aka rufe ikilisiyarsu ta Turanci. Amma ba ta ci gaba da yin tunani a kan abin da ya faru ba. Maimakon haka, ta soma halartan taro a ikilisiyar da ake yaren Jafan kuma tana yin iya ƙoƙarinta a waꞌazi a yaren. Ta roƙi abokiyar aikinta ta dā ta koya mata yaren. Matar ta yarda ta yi amfani da Littafi Mai Tsarki da ƙasidar nan, Ka Ji Daɗin Rayuwa Har Abada! don ta koya wa Christina yaren Jafan. Hakan ya taimaka wa Christina ta ƙara iya yaren Jafan. Abu mafi muhimmanci ma shi ne matar ta soma marmarin koya game da Littafi Mai Tsarki. Idan muka mai da hankali ga abubuwan da muke iya yi a yanzu kuma muka kasance da raꞌayin da ya dace, matsalolin da suka canja rayuwarmu, za su iya jawo mana albarku da ba mu yi tsammanin su ba.

11. Ta yaya wasu maꞌaurata suka jimre saꞌad da suka shiga matsalar kuɗi?

11 Ka taimaka ma wasu. Wasu maꞌaurata da ke zama a wata ƙasa da aka hana mu yin waꞌazi sun shiga matsalar kuɗi saꞌad da tattalin arzikin ƙasar ya faɗi. Ta yaya suka jimre? Da farko, sun ɗau matakin sauƙaƙa rayuwarsu. Na biyu, maimakon su mai da hankali a kan matsalolinsu, sun yanke shawarar mai da hankali a kan yadda za su taimaka wa mutane ta wajen yin waꞌazi da ƙwazo. (A. M. 20:35) Maigidan ya ce: “Da yake muna yin waꞌazi sosai, ba ma yawan tunani a kan matsalolinmu. Amma mun fi mai da hankali ga yin nufin Allah.” Idan yanayinmu ya canja, zai dace mu tuna da muhimmancin taimaka ma mutane, musamman ma ta wurin yin waꞌazi.

12. Ta yaya misalin Bulus zai taimaka mana mu yi waꞌazi ga kowane mutum bisa ga bukatunsa?

12 Muna yin waꞌazi ga mutane da suke da imani dabam-dabam, kuma inda suka fito ya bambanta. Manzo Bulus ya kasance da raꞌayin da ya dace don ya iya yin waꞌazi ga kowa, kuma za mu iya yin koyi da shi. Yesu ya naɗa Bulus manzo ga “waɗanda ba Yahudawa ba.” (Rom. 11:13) Don haka, Bulus ya yi waꞌazi ga Yahudawa da Helenawa da masu ilimi da ƙauyawa da hukumomin gwamnati da kuma sarakuna. Don ya iya yin waꞌazi ga mutanen nan, Bulus ya “zama kowane irin abu ga ko waɗanne irin mutane.” (1 Kor. 9:​19-23) Da yake yin waꞌazi ga mutane, ya yi tunani a kan inda suka fito da kuma imaninsu, hakan ya taimaka masa ya san yadda zai tattauna da kowannensu don ya taimaka musu su yi kusa da Allah. Mu ma za mu iya kyautata yadda muke yin waꞌazi idan muna tattaunawa da kowanne mutum bisa ga bukatunsa.

KA DARAJA RAꞌAYIN MUTANE

Idan muna da sanin yakamata, za mu daraja raꞌayi da kuma shawarar da ꞌyanꞌuwanmu suka yanke (Ka duba sakin layi na 13)

13. Wane abu ne aka ambata a 1 Korintiyawa 8:9 da za mu iya guje wa idan muna daraja raꞌayin ꞌyanꞌuwanmu?

13 Idan muna da sanin yakamata, za mu daraja raꞌayin mutane. Alal misali, wasu ꞌyanꞌuwanmu mata suna son kwalliya, wasu kuma ba sa so. Wasu Kiristoci suna jin daɗin shan giya daidai gwargwado, wasu kuma ba sa so. Dukan Kiristoci suna son ƙoshin lafiya, amma sukan zaɓi hanyoyin jinya dabam-dabam. Idan muna ganin zaɓinmu ne ya fi dacewa kuma muna ƙoƙarin tilasta wa ꞌyanꞌuwanmu su bi namu raꞌayin, za mu iya raba kan ꞌyanꞌuwa kuma mu sa wasu tuntuɓe. Hakika, ba za mu so mu yi hakan ba! (Karanta 1 Korintiyawa 8:9; 10:​23, 24) Bari mu tattauna misalai guda biyu da suka nuna yadda bin ƙaꞌidodin Littafi Mai Tsarki zai iya taimaka mana mu kasance da raꞌayin da ya dace kuma mu sa ꞌyanꞌuwa su zauna lafiya.

Idan muna da sanin yakamata, za mu daraja raꞌayi da kuma shawarar da ꞌyanꞌuwanmu suka yanke (Ka duba sakin layi na 14)

14. Wace ƙaꞌidar Littafi Mai Tsarki ce ya kamata mu tuna yayin da muke zaɓan tufafi ko kuma irin askin da za mu yi?

14 Tufafi da ado. Jehobah bai gaya mana irin tufafin da za mu riƙa sakawa ba, amma ya ba mu ƙaꞌidodi da za mu bi. Ya kamata mu riƙa saka “rigunan da suka dace,” kuma mu yi ado da zai daraja Allah. Ƙari ga haka, rigunanmu da adonmu su nuna cewa muna da sanin yakamata da kuma sauƙin kai. (1 Tim. 2:​9, 10; 1 Bit. 3:3) Don haka, ba ma so mu yi adon da zai sa mutane su riƙa mai da hankali ga shigenmu. Ƙaꞌidodin Littafi Mai Tsarki za su taimaka wa dattawa kada su riƙa kafa dokoki bisa ga nasu raꞌayi game da tufafi da kuma aski. Alal misali, dattawa a wata ikilisiya sun so su taimaka ma wasu ꞌyanꞌuwa matasa da suka yi aski da ake yayinsa kuma yake kama da na ꞌyan iska. Ta yaya dattawan za su taimaka musu ba tare da kafa musu doka ba? Mai kula da daꞌira ya shawarci dattawan su gaya wa matasan cewa idan suna ba da jawabi, kuma ꞌyanꞌuwa suka mai da hankali ga shigensu maimakon abin da suke faɗa, hakan na nufin cewa tufafi ko kuma askin da suka yi yana da matsala. Wannan bayani mai sauƙi ya taimaka wa matasan su san abin suke bukatar su yi kuma dattawan ba su kafa musu doka ba. e

Idan muna da sanin yakamata, za mu daraja raꞌayi da kuma shawarar da ꞌyanꞌuwanmu suka yanke (Ka duba sakin layi na 15)

15. Waɗanne dokoki da kuma ƙaꞌidodin Littafi Mai Tsarki ne suke taimaka mana mu san irin jinyar da ta dace mu yi? (Romawa 14:5)

15 Jinya. Kowane Kirista yana da hakkin zaɓan irin jinyar da yake so. (Gal. 6:5) Yayin da Kirista yake zaɓan irin jinyar da zai yi, dole ne ya bi dokar Littafi Mai Tsarki cewa mu guje wa jini da kuma sihiri. (A. M. 15:20; Gal. 5:​19, 20) Kirista zai iya zaɓan irin jinyar da yake so, muddin zai guje wa abubuwa biyun nan. Wasu a asibiti ne kawai suke yin jinya, wasu kuma suna amfani da wasu hanyoyi. Ko da muna ganin cewa wata jinya tana da haɗari sosai, zai dace mu bar ꞌyanꞌuwa su yi zaɓin da suke so. Don haka, zai dace mu tuna da abubuwa huɗun nan: (1) Mulkin Allah ne kawai zai kawo cikakken ƙoshin lafiya. (Isha. 33:24) (2) Kowane Kirista yana da hakkin zaɓan irin jinyar da ta dace da shi. (Karanta Romawa 14:5.) (3) Ba ma shariꞌanta ꞌyanꞌuwanmu, ko mu yi abin da zai dami zuciyarsu. (Rom. 14:13) (4) Kiristoci suna ƙaunar juna kuma sun fahimci cewa haɗin kan ikilisiya na da muhimmanci fiye da ꞌyancinsu na yin zaɓi. (Rom. 14:​15, 19, 20) Idan muna tuna da abubuwa guda huɗun nan, za mu kasance da dangantaka mai kyau da ꞌyanꞌuwanmu. Ƙari ga haka, za mu sa ꞌyanꞌuwa su zauna lafiya kuma su kasance da haɗin kai.

Idan muna da sanin yakamata, za mu daraja raꞌayi da kuma shawarar da ꞌyanꞌuwanmu suka yanke (Ka duba sakin layi na 16)

16. Ta yaya dattijo zai iya nuna sanin yakamata saꞌad da yake shaꞌani da sauran dattawa? (Ka kuma duba hoton.)

16 Ya kamata dattawa su zama kan gaba a nuna sanin yakamata. (1 Tim. 3:​2, 3) Alal misali, bai kamata wani dattijo ya ɗauka cewa sauran dattawan za su amince da shawararsa domin ya girme su ba. Amma ya san cewa ruhu mai tsarki zai iya taimaka ma kowanne ɗaya daga cikin dattawan ya faɗi abin da zai taimaka wa dattawan su tsai da shawarar da ta dace. Kuma idan yawancin dattawan sun yarda da wata shawarar da ba ta saɓa wa ƙaꞌidodin Littafi Mai Tsarki ba, dattijon mai sanin yakamata zai amince da shawarar ko da ba abin da ya so ba ne.

AMFANIN NUNA SANIN YAKAMATA

17. Waɗanne albarku ne Kiristoci suke samu don suna da sanin yakamata?

17 Kiristoci suna amfana sosai don suna nuna sanin yakamata. Hakan yana sa mu kasance da dangantaka mai kyau da ꞌyanꞌuwanmu kuma salama takan kasance a ikilisiya. Muna jin daɗin halaye dabam-dabam da alꞌadu dabam-dabam na ꞌyanꞌuwanmu. Kuma abin farin ciki ne cewa duk da bambance-bambancenmu, muna bauta ma Allah a matsayin iyali ɗaya. Mafi muhimmanci ma, muna farin cikin sanin cewa muna yin koyi da Allahnmu mai sanin yakamata.

WAƘA TA 90 Mu Riƙa Ƙarfafa Juna

a Jehobah da Yesu masu sanin yakamata ne, kuma suna so mu kasance da wannan halin. Idan muna da sanin yakamata, zai yi mana sauƙi mu jimre idan yanayinmu ya canja, wataƙila don rashin lafiya, ko kuma matsalar kuɗi. Ƙari ga haka, halin zai sa furucinmu da ayyukanmu su sa ꞌyanꞌuwa a ikilisiya su zauna lafiya kuma su kasance da haɗin kai.

b Filibiyawa 4:5 (NWT): “Bari kowa ya ga cewa ku masu sanin yakamata ne. Zuwan Ubangiji ya yi kusa.”

c Ka duba talifin nan, How to Deal With Change a Awake! Na 4 2016.

d Ka kalli bidiyon nan, Ganawa da Aka Yi da Ɗanꞌuwa Dmitriy Mikhaylov da ke talifin nan, “Jehobah Ya Sa Tsanantawa ta Buɗe Hanyar Yin Waꞌazi” a Littafin Taro Don​—Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu na Maris-Afrilu 2021.

e Don ƙarin bayani game da tufafi da kuma ado, ka duba darasi na 52 na littafin nan, Ka Ji Daɗin Rayuwa Har Abada!