TARIHI
Nuna Cewa Mun Damu da Mutane Yana Kawo Albarka
AKWAI ran da kakata ta ce wa mahaifiyata: “Cocin Anglican ba sa koya wa mutane gaskiya. Don haka, ki ci gaba da neman sanin gaskiya.” Tun daga ranar, mahaifiyata ta soma neman addini na gaskiya. Amma ba ta so Shaidun Jehobah ba, takan ce min in ɓoye duk lokacin da suka zo gidanmu da ke birnin Toronto a Kanada. Amma a 1950, ƙanwar mamata ta soma nazari da Shaidun Jehobah, sai mamata ta bi ta. A gidan ƙanwarta suka yi ta nazarin har su biyun suka yi baftisma.
Babanmu kuma dattijo ne a wani coci da ake kira United Church of Canada. Don haka kowane mako, yakan sa ni da ꞌyarꞌuwata mu je inda ake koyar da yara a cocin, wato Sunday school. Bayan haka sai mu bi shi tasu sujadar wajen ƙarfe 11:00 na safe. Da rana kuma sai mu bi mahaifiyata Majamiꞌar Mulki. Nan da nan mun ga bambanci tsakanin cocin babana da Shaidun Jehobah.
Akwai wasu maꞌaurata da tun dā abokan mamarmu ne, wato Bob Hutcheson da matarsa Marion. Sun saurari waꞌazin mamarmu har sun zama Shaidun Jehobah. Ɗanꞌuwa Hutcheson da matarsa ne suka kai ni taron ƙasashe na kwana takwas da aka yi a 1958, mai jigo, Divine Will. Tare da yaransu maza uku muka je taron a Birnin New York a Amirka. Yanzu ne na gane cewa ba ƙaramin ƙoƙari suka yi da suka kai ni taron nan ba. Kuma a gaskiya, taron nan ya taimaka min sosai.
TAIMAKON ꞌYANꞌUWA YA SA NA ƘARA ƘWAZO
Da nake tasowa, a wani gona ne gidanmu yake kuma na ji daɗin yin kiwon dabbobi. Na so in zama likitan dabbobi. Da mamata ta ga haka, sai ta gaya ma wani dattijo a ikilisiyarmu. Dattijon ya tuna min cewa a “kwanakin ƙarshe” muke, kuma ya ce ba na ganin zuwa yin karatu na shekaru da yawa a jamiꞌa zai shafi dangantakata da Jehobah? (2 Tim. 3:1) Da na yi tunani a kan hakan, sai na fasa zuwa jamiꞌa.
Duk da haka, na yi ta tunanin abin da zan yi idan na gama makarantar sakandare. Ko da yake lokacin ina zuwa waꞌazi kowane ƙarshen mako, ba na jin daɗinsa kuma ban yi tsammanin cewa zan iya zama majagaba ba. Lokacin kuma babana da kawuna waɗanda ba Shaidu ba ne, sun so in soma aiki da wani kamfanin inshora a birnin Toronto. Kawuna yana da babban matsayi a wurin, don haka na yarda.
Da na soma aikin, yawancin lokaci ina a wurin aiki kuma ina tare da mutanen da ba Shaidun Jehobah ba. Har abin ya sa ba na yawan zuwa taro da waꞌazi. A lokacin, da kakana nake zama kuma shi ma ba mashaidi ba ne. Da ya rasu, sai na soma neman gida.
Ɗanꞌuwa Bob da matarsa da suka kai ni taron da aka yi a 1958 kamar iyaye suke a gare ni. Sun ce in zo in zauna da su, kuma sun taimaka mini in ƙara kusantar Jehobah. A 1960, na yi baftisma tare da ɗansu mai suna John. Bayan haka, John ya zama majagaba, kuma hakan ya sa ni ma na ƙara ƙwazo a hidimata. Sai ꞌyanꞌuwa suka ga cewa na samu ci gaba sosai, har daga baya aka naɗa ni mai kula da taron da a yanzu ake kira taron Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu.
NA SAMU MACEN KIRKI KUMA NA ZAMA MAJAGABA
A 1966, na auri wata majagaba mai ƙwazo da take son yin hidima a inda ake da bukata. Sunanta Randi Berge. Mai kula da daꞌirarmu a lokacin ya so mu sosai, kuma ya ƙarfafa mu mu je mu taimaka ma wata ikilisiya a garin Orillia, da ke Ontario. Sai muka tattara kayanmu muka ƙaura.
Muna isowa Orillia, sai ni ma na soma hidimar majagaba na kullum. Ni ma na soma marmarin yin waꞌazi kamar matata! Da na sa zuciyata wajen yin hidimar majagaba, na yi farin ciki sosai, domin na ga yadda nake amfani da Littafi Mai Tsarki ina taimaka wa mutane su san gaskiya. Na ji daɗi sosai da muka taimaka ma wasu maꞌaurata a Orillia su gyara rayuwarsu kuma su soma bauta wa Jehobah.
MUN KOYI SABON YARE KUMA MUN CANJA RAꞌAYINMU
Akwai lokacin da muka je birnin Toronto, sai na haɗu da wani ɗanꞌuwa mai suna Arnold MacNamara.
Yana cikin masu yin ja-goranci a Bethel. Sai ya tambaye mu ko za mu so mu yi hidimar majagaba na musamman. Nan da nan na ce: “Ƙwarai kuwa! Amma fa ba a Quebec ba.” Na faɗi hakan ne domin ꞌyan Kanada da suke yin Turanci ba sa son waɗanda suke yankin Quebec inda Farasanci ake yi, kuma wannan raꞌayin ya shafe ni. A lokacin, mutanen Quebec suna zanga-zangar neman ꞌyancin kansu.Amma sai Ɗanꞌuwa Arnold ya ce min: “Quebec ne kaɗai ake tura majagaba na musamman yanzu.” Nan da nan sai na yarda zan je. Na san dā ma matata Randi za ta so yin hidima a wurin. Daga baya ne na gano cewa ɗaya daga cikin zaɓi mafi kyau da muka yi a rayuwarmu ke nan!
Mun yi makonni biyar muna koyan Faransanci. Bayan haka, sai ni da matata da wasu maꞌaurata muka ƙaura zuwa birnin Rimouski, da ke da nisan kilomita 540. Wurin yana arewa maso gabashin Montreal. Mun zata mun ɗan iya yaren, sai da na yi wata sanarwa ne muka gano cewa da saura. Sanarwar game da wani babban taro ne da ake shirin yi. Maimako in ce za mu yi baƙi da yawa daga ƙasar “Ostiriya,” sai na ce “jimina” da yawa za su zo taron, domin a yarensu, kalmomi biyun sun yi kama.
Ana nan, sai ꞌyanꞌuwa mata huɗu majagaba masu ƙwazo sosai suka ƙauro zuwa Rimouski. Har da wani ɗanꞌuwa mai suna Huberdeaus da matarsa da yaransu mata guda biyu. Ɗanꞌuwa Huberdeaus ya yi hayar babban gida, saꞌan nan dukanmu majagaba da muke zama a wurin mukan haɗa hannu mu biya kuɗin hayar tare. Muna kiran gidan “White House,” domin farin fanti aka yi wa gaban gidan da ginshiƙansa, wato pillars ɗinsa. Wani lokaci mukan kai 12 ko 14 a gidan. Da yake ni da matata majagaba na musamman ne, muna zuwa waꞌazi da safe da rana da kuma yamma. Mun ji daɗinsa don ba ma rasa wanda zai bi mu waꞌazi, ko a yammar da ake sanyi sosai.
Akwai zumunci sosai tsakaninmu da sauran majagaban, har mun zama kamar iyali. Wani lokaci mukan taru mu hura wuta muna girke-girke tare. Ɗaya daga cikin ꞌyanꞌuwan ya iya kiɗa, don haka ran Asabar da yamma, mukan yi waƙoƙi muna rawa.
Mutane da yawa a birnin Rimouski sun so bishararmu! Cikin shekaru biyar, ɗaliban Littafi Mai Tsarki da yawa sun samu ci gaba har suka yi baftisma. Har mun kai masu shela 35 a ikilisiyar. Wannan ya faranta mana rai.
Hidimar da muka yi a Quebec ya horar da mu sosai a fannin waꞌazi. Mun kuma ga yadda Jehobah ya yi ta taimaka mana saꞌad da muke waꞌazi, kuma ya biya bukatunmu. Ya kuma sa mun soma ƙaunar mutanen da suke Faransanci, da yarensu, da kuma alꞌadarsu. Da haka muka soma ƙaunar mutane masu alꞌadu dabam-dabam.—2 Kor. 6:13.
Ana nan kawai, sai muka samu saƙo daga rashen ofishinmu cewa mu ƙaura zuwa wani gari mai suna Tracadie, da ke bakin kogi a gabashin New Brunswick. Ƙaura bai yi mana sauƙi ba, domin bai jima ba da muka biya kuɗin hayar wani gida. Kuma mun riga mun shirya da wata makaranta cewa zan riƙa musu koyarwa na ꞌyan awoyi kowane mako. Ban da haka ma, wasu ɗalibanmu ba su daɗe da zama masu shela ba, kuma lokacin muna kan gina Majamiꞌar Mulki.
Mun share ranakun Asabar da Lahadi muna adduꞌa game da batun. Sai muka je Tracadie don mu ga wurin. Tracadie kuwa dabam yake da Rimouski, amma sai muka ce tun da Jehobah yana so mu je Tracadie, za mu je. Mun gwada Jehobah kuma mun ga yadda ya taimaka mana muka shawo kan dukan matsaloli da suka so su hana mu zuwa wannan sabon wuri. (Mal. 3:10) Da yake matata Randi tana ƙaunar Jehobah sosai, ba ta da son kai, kuma tana da faraꞌa, don haka ƙaura bai yi mana wuya sosai ba.
A sabuwar ikilisiya da muka je, ɗanꞌuwa ɗaya ne kaɗai dattijo, kuma sunansa Robert Ross. A dā shi da matarsa Linda majagaba ne a wurin. Da suka haifi ɗansu na farko, sai suka zaɓi su ci gaba da zama a wurin. Duk da cewa suna renon yaro, sun karɓe mu hannu biyu-biyu kuma suna yin waꞌazi da ƙwazo. Halinsu ya ƙarfafa mu.
MUN YI FARIN CIKIN YIN HIDIMA A DUK INDA AKWAI BUKATA
Bayan mun yi shekaru biyu muna hidima a Tracadie, sai aka sake yi mana ba-zato. An ce mu soma yin hidimar mai kula da daꞌira. Mun yi shekaru bakwai muna hidima a daꞌirori da suke bangaren Turanci. Bayan haka, sai aka mai da mu daꞌirar da ake Faransanci a Quebec. Mai kula da gundumarmu a lokacin sunansa Léonce Crépeault. Yakan yaba min idan na yi jawabi. Bayan hakan, sai ya tambaye ni ko akwai abin da zan iya yi don jawabaina su ƙara zama da sauƙin fahimta. a Wannan taimako da ya dinga yi min, ya sa na ƙara mai da hankali ga yadda zan sauƙaƙa koyarwata don mutane su amfana.
A cikin ayyukan da na yi, wani da ba zan taɓa mantawa ba shi ne, aikin da na yi a sashen dafa abinci a wani taron ƙasashe mai jigo, “Victorious Faith,” da aka yi a birnin Montreal a 1978. Lokacin muna sa ran cewa mutane 80,000 za su zo taron. Kuma yadda aka ce mu ciyar da su ya yi dabam da yadda muka saba. Da kayan dafuwan, da irin abincin, da yadda za a girka su ma duk an canja. Muna da tireloli 20 ɗauke da manyan kwantena da suke a matsayin firiji. Amma wani lokaci wasunsu ba sa aiki. Ban da haka, har rana ɗaya kafin taron, an yi wasa a filin wasan da za a yi taron, don haka ba mu iya shiga mu soma shirya abubuwa ba sai da tsakar dare. Ga shi dole mu shirya kome don a samu a ci abincin safe. Mun gaji sosai, amma ꞌyanꞌuwa da muka yi aikin tare sun nuna kwarjini. ꞌYanꞌuwa ne da suka manyanta, kuma sun yi aikin da farin ciki. Na koyi abubuwa da yawa daga wurinsu. Mun ƙaunaci juna sosai kuma har yau mu abokai ne. Ba ƙaramin farin ciki muka yi ba da muka kasance a wannan taro na musamman da aka yi a yankin Quebec, domin an tsananta ma ꞌyanꞌuwa sosai a wannan yankin tsakanin shekara ta 1940 da 1960.
Na koyi abubuwa da dama daga wurin ꞌyanꞌuwa da su ma suka yi ja-goranci a manyan taro da muka yi a birnin Montreal. Akwai shekarar da Ɗanꞌuwa David Splane wanda a yanzu memban Hukumar
da Ke Kula da Ayyukanmu ne, ya ja-goranci shirye-shiryen taron. Da aka zo yin wani taron, sai aka ce in ja-goranci shirye-shiryen taron kamar yadda ya yi, kuma Ɗanꞌuwa Splane ya taimaka min sosai.Bayan mun yi shekaru 36 muna kula da daꞌira, sai a 2011, aka kira ni in zo in soma koyarwa a Makaranta don Dattawan Ikilisiya. Hakan ya sa mun yi ta ƙaura zuwa wurare 75 cikin shekaru biyu kawai. Amma kwalliya ta biya kuɗin sabulu, don kowane ƙarshen mako, dattawan da muka koyar sukan yi godiya sosai, saboda sun ga tabbacin cewa Hukumar da Ke Kula da Ayyukanmu suna so dattawa su ci gaba da kusantar Jehobah sosai.
Daga baya na yi koyarwa a Makarantar Masu Yaɗa Bisharar Mulki. Ɗaliban makarantar sukan gaji don sukan sha karatu. Kowace rana sukan yi awa bakwai a aji, bayan haka su yi awa uku suna aikin da aka ba su a gida (homework). Saꞌan nan kowane mako, akan ba su aiki kashi huɗu ko biyar da za su gudanar a aji (assignment). Ni da ɗanꞌuwa da muke koyar da su mun gaya musu cewa da taimakon Jehobah ne kaɗai za su iya yin duka abubuwan nan. Nakan tuna yadda ɗaliban sukan yi mamaki don sun ga yadda dogara ga Jehobah ya sa sun iya yin abubuwa fiye ma da yadda suka zata.
NUNA CEWA MUN DAMU DA MUTANE YANA KAWO ALBARKA
Yadda mahaifiyata ta nuna cewa ta damu da mutane ya taimaka wa ɗalibanta su samu ci gaba, kuma ya sa mahaifinmu ya soma son gaskiya. Kwana uku bayan rasuwarta, sai kawai muka ga mahaifinmu ya zo Majamiꞌar Mulki, kuma ya saurari jawabi da aka yi ga jamaꞌa. Bayan haka kuma, ya yi shekaru 26 yana zuwan taro babu fashi. Ko da yake mahaifinmu bai yi baftisma ba, dattawan ikilisiyar sun gaya min cewa yakan riga kowa zuwa taro kowane mako.
Ban da haka, halin mahaifiyarmu ya taimaka mana sosai. Duka ꞌyanꞌuwana suna bauta ma Jehobah da aminci tare da mazajensu. Mata uku ne, biyu suna hidima a rashen ofishinmu, ɗaya a Portugal, ɗaya a Haiti.
Yanzu ni da matata majagaba na musamman ne a birnin Hamilton, a Ontario da ke Kanada. Da muke kula da daꞌira, mukan ji daɗi idan muka bi ꞌyanꞌuwa saꞌad da suke yin koma ziyara da kuma nazari da ɗalibansu. Amma yanzu muna farin ciki don muna da namu ɗalibai kuma muna taimaka musu su ƙaunaci Jehobah. Kuma yayin da muke kusantar ꞌyanꞌuwa da ke ikilisiyarmu, muna ganin yadda Jehobah yake taimaka musu su shawo kan matsalolinsu, kuma hakan yana ƙarfafa mu.
Duk saꞌad da muka tuna baya, mukan yi godiya sosai don yadda mutane suka taimaka mana. Mu ma hakan ya sa mun yi iya ƙoƙarinmu mu nuna cewa mun damu da ꞌyanꞌuwanmu ta wurin ƙarfafa su su yi iya ƙoƙarinsu a bautar Jehobah. (2 Kor. 7:6, 7) Misali, akwai wata iyali da matar da yaransu biyu dukansu majagaba na kullum ne. Da na ga hakan, sai na tambayi mai gidan ko shi ma ya taɓa tunanin yin hidimar majagaba. Ya ce ba zai iya ba don yana taimaka wa mutane uku a iyalinsa su iya yin hidimar. Sai na tambaye shi: “Kana ganin idan ka zama majagaba, Jehobah ba zai iya kula da su fiye da yadda kake yi ba?” Na ƙarfafa shi ya bi su don shi ma ya samu albarkun da suke morewa. Bayan wata shida, sai ɗanꞌuwan ya zama majagaba.
Ni da matata Randi, za mu ci gaba da gaya wa “tsara masu zuwa” ayyuka “na ban mamaki” da Jehobah ya yi mana. Fatanmu shi ne su ma su ci moriyar yi wa Jehobah hidima kamar yadda muka yi.—Zab. 71:17, 18.
a Ka duba labarin Ɗanꞌuwa Léonce Crépeault da ke Hasumiyar Tsaro ta Fabrairu 2020, shafi na 26-30.