Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Shawara a kan Yin Nazari

Shawara a kan Yin Nazari

Ka Soma da Abubuwan da Suka Fi Muhimmanci

Dukanmu ba mu da isashen lokaci don yin nazari. Don haka, ta yaya za mu yi amfani da lokacin da muke da shi da kyau? Da farko, kada ka yi hanzari. Za ka fi amfana idan kana nazarin abubuwa kaɗan da kyau, maimakon ka yi nazarin abubuwa da yawa cikin sauri.

Saꞌan nan ka soma da abubuwan da suka fi muhimmanci. (Afis. 5:​15, 16) Alal misali:

  • Ka karanta Littafi Mai Tsarki kowace rana. (Zab. 1:2) Za ka iya somawa da karatun Littafi Mai Tsarki na kowane mako da ke tsarin ayyuka na taron tsakiyar mako.

  • Ka shirya nazarin Hasumiyar Tsaro da kuma abubuwan da za a tattauna a taron tsakiyar mako don ka iya yin kalami.​—Zab. 22:22.

  • Bisa ga lokacin da kake da shi, ka bincika abubuwan da ƙungiyarmu ta wallafa kwana-kwanan nan. Misali, mujallu na waꞌazi da bidiyoyi da kuma abubuwan da ake sakawa a jw.org.

  • Ka bincika wani batun da kake so. Za ka iya yin bincike a kan wata matsala da kake fuskanta ko wata tambaya, ko wani batun da kake so ka ƙara fahimta. Ka duba sashen “Ayyuka don Nazarin Littafi Mai Tsarki” da ke jw.org/ha don ka ga misalin abubuwan da za ka iya bincikawa.